← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 115

Sashe 56

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana gajiya tai da zama, dan babu alamar Sadik ze dawo Gidan nan, ta tashi ta shiga lelleƙa ɗakunan, haka kurum gidan yake mata kama da wani gida, a wani film na horo da ta taɓa kalla a gidan Dr. A tsorace ta samu banɗaki tai alwala tai salla ta dawo falon ta zauna, se zazzare ido take kamar korarriya.

Wata irin yunwa se sakatar ta take, ta rasa in da zata sa kanta, wasa wasa har duhun magariba ya fara yi, babu Sadik babu alamarsa, hankalin Nana ya tashi, tsoro take ji sosai ta koma wajen ƙofa ta zauna, tana ɗaɗɗaga kai tana kallon gidan.

Ba zato ba tsammani taji an buɗe ƙofa, a gigice ta tashi zata zura da gud, amma taga Sadik ne, kallo ɗaya yai mata ya tsaki ya wuce ya nufi wani ɗaki, yasa mukulli ya buɗe ɗakin ya shiga.

Miƙewa Nana tayi ta koma kan kujera ta zauna, tana jiran Sadik ya nuna mata in da zata ajiye Akwatunan ta.

Sedai ko motsinsa ba ta kuma ji ba, tashi tai ta nufi in da ya shiga, ta tura ƙofar da sallama.

Yana zaune a gefen gado, hannunsa É—auke da sabuwar waya yana dudduba ta, ya É—aga kai ya kalleta yace "uban me kika biyo ni ki min?"

Ta cuna baki tace "ni yunwa nake ji, kuma baka nunan in da zan ajiye kayana ba"

"Meya hana ki tambayi wanda ya kawo ki abun da zaki ci?" Mamaki ya kama Nana, meyasa Sadik sam ba shi da ta ido ba shi kunya?

"In da zaki kwana kuma, in kin ga dama ki kwana a waje, matsalar ki ce, ki ɓace min daga gani na kan in zo in saɓa miki" mamaki ya hana Nana motsawa daga in da take, Sadik ya taso ya turata waje, ya rufe ƙofar ɗakinsa.

Jiki a sanyaye, ta koma kan kujera ta kwanta, zuciyarta na wani irin tafasa, nan da nan ta fara kuka, dama ba ai mata wannan transfer É—in ba, an barta a boarding É—in ta, dan babu alamar imani a tare da Sadik sam.

Garin akwai sanyi sosai, ta buɗe kayanta ta ɗakko bargo ta lulluɓa, ta dinga kuka a cikin bargon, ta san kashinta ya bushe a wannan zama da za suyi.

Da Abba ya koma gida ba yadda Mother ba tai ba, akan se taji matakin da Abba ya ɗauka akan Sadik, amma fafur yaƙi gaya mata, ta kira wayar Sadik amma wayar ba ta shiga.

"Dan Allah ka gayamin matakin da ka É—auka akan Yaron nan"

Abba yace "Ai na gaya miki ni ba gurinsa naje ba, gurin 'yata naje"

"Amma na kira layinsa baya shiga fa"

Abba yace "wannan kuma ban san dalili ba"

Cikin damuwa Mother tace "Yanzu kaje har ƙasar ka dawo, ba ka je ka ganshi ba?"

Abba yace "to menene a ciki, tunda ya nuna ban isa da shi ba"

Kan Mother ta kuma magana, yai tafiyarsa ya barta a gurin.

In da a kai sa'a, in da su Nana suke akwai wani ɗan ƙaramin masallaci, kasancewar akwai musulmi a unguwar.

Kan Sadik ya tashi Nana ta tashi, dan sanyi ya dameta sosai da sosai, tai alwala ta tada salla, Sadik ya wuce ta ya fice ya tafi masallaci.

Bacci ne ya kuma kwashe Nana, motsin Sadik ne ya tashe ta, ta buÉ—e ido taga ya shirya ya É—au jaka, alamar fita zeyi.
Nana ta kwaɓe fuska tace "wai yanzu ma fita za kai? Ni wallahi tsoro nake ji"

Wani Mugun kallo yai mata, yace "uwar tsoro kike ji ba tsoro ba"

"Dan Allah to ka bani abunda zan ci, kar yunwa tai min illa"

Ko saurarar Nana be ba, ya fice yace "zaki gane baki da wayo, izayar da kakanninki su kai min akan ki zan rama".

Haka Nana ta kuma wuni da yunwa, banda kuka ba abun da ta ke yi, se wajen ƙarfe tara na dare sannan Sadik ya koma gida, ya tarar da ita ta ci kuka, idanunta sunyi wuri wuri, ya wuce ɗaki abunsa, wajen mintuna goma da wucewar sa Nana ta tashi ta bi shi ɗakin.

Yana zaune yana cin Abinci, wanda Nana sam ba ta san me yake ci É—in ba, kawai se ganinta yai a gabansa, ta sa hannu ta fara cin Abunda yake cin.

Ba shiri ta furzar da abunda ta sa a bakin nata saboda azabar yaji, kawai ta kuma fashewa da kuka.

Sadik ya bita da ido, yace "ubanwa yace ki zo min É—aki?"

"Yunwa nake ji wallahi, gaba É—aya cikina ciwo yake"

"To ni na ajiye ki da zan nemo abun baki?"

"Dan Allah ka temaka min, kar in mutu"

Kawai Sadik ya tuna yadda ta dinga sintirin ba shi Abinci a ɓoye, idan aka bashi abunda ba ya so a ƙauye.

Tashi yai ya barta a É—akin, mintuna kaÉ—an se ga shi ya dawo, ya ajiye mata madara da fruit a gabanta.

Ta kalleshi tace "nifa Abinci nake son naci, yunwa nake ji, ta yaya wannan zam ci in ƙoshi?"

Tana faɗar haka ya durƙusa ya ɗau plate ɗin ya koma gefe, ya fara yankawa ya na ci.

Haushi ya kama Nana, hankalinsa kwance yake cin abunsa, wato ta mutu da yunwa.

Tashi tai ta ɗauke plate ɗin daga gaban Sadik, tai waje tana kuka, dan ba yadda za'ai ta ƙoshi yadda ta kwana biyu ba ta ci ba.

Farhan taji daɗin maganin nan da ta karɓa a chemist, tayi bacci Sosai da sosai, wanda rabon da Farhan tayi shi tun suna tare da Sadik, taji ta samu sassaucin baƙin cikin da take ciki.

Kamar yadda me Chemist ya gaya mata, kwana uku ta ajiye ta dena sha, amma fa damuwa ta kuma dawowa, mussaman yanzu da saura wata É—aya ya rage Aurenta da Sunusi!!!

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Haka Farhan ta cigaba da gudanar da rayuwarta, kamar mara cikakkiyar lafiya.

Babu wanda ta gayawa batun za tai Aure a cikin 'yan makarantar su, dama ba harkar mutane take shiga ba, dan ba ta da wasu ƙawaye, rayuwarta kawai take yi.

Tana zaune a ajinsu, tai zurfi a cikin tunani, taji an dafa ta, a hankali ta waiga taga waye ya dafata.
Tai tozali da Lilly, Lilly ta zauna a kusa da ita tace "Farhan, wai dan Allah meyake damunki haka?"

Fahan tace "me kika gani?"

"Kin ga yadda ki kai wata irin rama kuwa? Kullum cikin tunani kike, ga malamai suna ta complain akan kin dena karatu yanzu haba Farhan"

Shiru Farhan tai ta sunkuyar da kai ƙasa.

"Farhan" Lilly ta kira sunanta.

Ta É—ago ta kalli Lilly.

"Ko dai dan Sadik ba ya makarantar nan ne yasa duk kika zama wani iri?"

Jurewa Farhan take ƙoƙarin yi, ta girgizawa Lilly kai, amma cikin rashin sa'a ƙwalla ta taru a idon Farhan, dan tun bayan Doctor Abbas babu wanda ya kuma taɓo mata abun da yake damunta.

"Yasalam, yi haƙuri idan na faɗi wani abu da be miki daɗi ba, amma ki yi haƙuri, naji ance babu wanda ya san ze yi tafiyar nan, ciki kuwa har da ke, sam be kyauta ba, amma kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, wallahi duk kin rame Farhan"

Farhan a ranta tace 'da za a ƙyaleni da Auren Sunusi, a barni da tunanin Sadik kawai, da na samu sassauci a raina'

Amma a fili ta kasa Magana sam, se ƙoƙarin mai da hawaye kawai da take yi.

Lilly tace "Farhan, ke naki me sauƙi ne, Soyayya shu'umar a bace, mussaman idan ta kama ka a lokacin da baka shirya mata ba, Sadik be kyauta ba, dan babu wanda be san Soyayyar ku ba, amma ni dai roƙona a gareki kiyi haƙuri ki manta da shi"

Se da ƙirjin Farhan ya buga, kowa seyace ta manta da Sadik, how could this be possible, ya tabatta Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kenan?.

A zahiri ta jinjinawa Lilly kai, dan zuwa yanzu surutan Lillyn sun cika mata kunne, sam ba ta son hayaniya ko yaya take yanzu.

Sam Nana ba ta ji ta ƙoshi ba, saboda yunwa take ji sosai da sosai, amma Sadik ya haɗata da fruit, har gara madarar ta temaka mata, saboda maiƙon da ke jikin madarar.

Yau ma a falon ta kwana, kwanciyar ƙasa da ta kan kujera ta sa, haƙarƙarinta da wuyanta se ciwo suke mata.

Yau bayan tai sallar Asuba, taƙi komawa bacci ta nemi guri ta zauna, Har ƙarfe bakwai, Sadik ya shirya ze tafi makaranta, miƙewa tai tsaye ya zo ze wuce ta kalleshi tace "Nifa yunwa bake ji wallahi"

"Se ki cinye ni ai, bani hanya ni zan wuce"

"Dan Allah ka bani abun da zan sawa cikina, wallahi yunwa za ta kashe ni"

"In da zata kashe kin ai da na huta"

Hawaye ya taru a idon Nana, dan karma tai kuka yaji tausayinta, ya raɓata ya fice.

Nana ta zauna ta ci uban kuka, har wajen ƙarfe tara, sannan ta gaji ta tashi, ga wanka ta na son yi, ga yunwa ta addabeta.

Ta tashi ta dinga leƙe leƙe, har ta gano Kitchen, ta shiga tana duba Kitchen ɗin, kayan da ke Kitchen ɗin, sun sha banban da irin namu na Nigeria, wasu abun akwai a Nigeria wasu babu ba ta sansu ba, mussaman ita da take ƙauye.

Ta buÉ—e fridge É—in da ke Kitchen É—in, amma bakomai a ciki se wani sauran yoghurt.

A kitchen ɗin ta zauna ta shanye shi tsaf, ta ajiye kwalbar amma ba ta ji alamar ƙoshi ba.

Ga shi wanka take son yi, amma babu sabulu a banÉ—akin da take Alwala.

Daga baya ta yanke shawarar shiga É—akin da Sadik yake, aikuwa ta samu kayan wanka a ciki, ta samu tai wanka, ta canza kaya ta shafa creams É—in sa, ta haye gadonsa tai kwanciyarta.

Se bayan azahar Sannan ta tashi, tai salla ta É—akko Akwatinan ta ta ajiye su a cikin É—akinsa.
Chapter 56 · 0% Book details