← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 115

Sashe 23

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana taje ta leƙa fuskar Hakimi ta tarar bacci yake, dan haka ta juya zata fita, ta kalli Sadik tai masa tsaki ba tare da yai mata komai ba.

Kawai ya ɗau murfin kofin dake gefensa, ya jefeta da shi a ƙafarta.

Ta waigo ta kalleshi tace "Allah ya isa na"

Hakimi kam idonsa biyu, ya lumshe idonsa ne kawai yana jinsu, amma bece musu komai ba.

Kunun tsamiya aka dama da wainar gero, Abba yana ta murna, dan yana missing ɗin Abincin gargajiya, yayin da Sadik ya sake cewa shi baze ci wannan abincin ba, shi kunun tsamiya gudawa yake sa shi, wannan baƙar abar kuwa baze iya ci ba.

Tunda Sadik yake iya shegensa, Hakimi be tofa komai ba, se a wannan karon da ya bi Sadik É—in da kallo shima.

Nana ta fito tsakar gida, tana bawa magunan Inna Abinci, kasancewar Innan kamar kiwon su take.

Sun kai su kusan bakwai magunan se tsalle tsalle sukeyi.

Faruk ya zo ya sameta a gurin, yace "wannan magunan fa kyawawa Masha Allah?"

Nana tace "Na Inna ne, nake basu Abinci, ni kaga nawa nan wannan farar da wannan É—an beutyn"

Faruk yace "Wow, gasky ne they are cute"

Sadik na gefe, ya shirya Fitowar Abba kawai yake jira su tafi, yana zaune yana harar Nana da zarar sun haÉ—a ido.

Nana tacewa Faruk "kaga wancan muzurun, me tsigaggen gashin nan, ya fiye fitinar tsiya, ga rawar kai gashi bashi da kunya, shiyasa gashi nan mummuna, ko fara'a ba ya yi, sunan sa Autan Mother"

Faruk ya É—aga kai ya kalli Sadik, wanda ya zubowa Nana ido, dan yasa wannan cin fuskar da shi take, wato muzuru ma ta sawa Autan Mother, hadda ce masa mummuna.

Tunanin abunda zewa Nana yake dan ya huce, sega Abba ya fito a shirye, da alama tafiya za suyi, abun mamaki sega Hakimi ma da ƙafafunsa ze rakasu mota tare da Inna.

Sadik yai saurin miƙewa, dan jinsa yake kamar akan ƙaya.

Hakimi ya kalli Sadik sannan ya kalli Abba yace "Wannan abokin nawa a nan zaka barmin shi"

Abba yai murmushi dan zatonsa Hakimi da wasa yake yi.

Sadik kam ya fara zoma kai gaba, yana jiran su Abba su wuce ya biyo bayansu.

Suna zuwa zaure na biyu, Hakimi ya kalli wani dogari yace "kar a bar wannan abokin nan nawa ya ɗaga ƙafarsa daga inda yake, a nan za'a barmin shi" yai maganar yana nuna Sadik.

Abba ya kalli Hakimin yace "Alhaji kana nufin a nan ze zauna?"

"Eh, ko ban isa bane?"

Abba yace "wane ni ja da maganar ka"

"A nan za'a barmin shi, kuma daga yau bana buƙatar ka sake zuwa, tunda naji sauƙi Alhamdilillah.

Aikuwa Sadik ya gigice, ze taka yabi Abba, a kai sama da shi aka mayar da shi cikin gida, yana kurma ihu yana kiran Abba!

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

Ko ku tuntuɓe ni ta wannan lambar
Ayshercool
07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Jiki a sanyaye Abba yai gaba, yana jiyo yadda Sadik ke ƙwala masa kira yana ihu.

Duk da shi kansa Abba beji daÉ—in abubuwan da Sadik É—in ya dinga yi ba a gidan, amma se yaji beji daÉ—i ba amma ba yadda ya iya.

Shi kansa Faruk, se yaji tausayin Sadik ya kama shi, yasan yadda Sadik yake a sangar ce ba ƙaranar wahala ze sha zama a garin nan ba.

Gashi Hakimi yace kar Abba ya sake zuwa garin. Se da wani ƙwaƙwalwa Dalili.

Har mota suka raka Abba da Faruk, sukai musu Sallama.

Nana kuwa da taga an saɓo Sadik a kafaɗa an dawo da shi, se abun ya bata mamaki.

Inna na shigowa Nana tace "Inna wai ya naga an dawo da shi? Ba tafiya za suyi ba"

"Kakansa yace a nan za'a barshi" Inna na faÉ—in haka ta shige É—akinta.

Sadik se kiran Abba yake kama wanibɗan yaye, ya kuma nufar ƙofar da gudu ze fita amma aka kuma hankaɗo shi aka hanashi fita.

Hakimi ne ya shigo yana takunsa cikin nutsuwa, yaga yadda ake dambarwa da Sadik akan lallai seya fita.

Ya kalli dogarin yace "ka ladabtar da shi idan ya kuma yunƙurin fita"

Zare ido Nana tai jin abunda Hakimi ya faÉ—a, aikuwa aka É—akko zumgureriyar bulalar dukan doki, Sadik na ganin wannan uwar bulalar ya shiga taitayinsa.

Nana kuwa ta tuntsure da dariya tace "yau naga ƙarshen taurin kai da raina mutane" ta dinga dariya yayin da Sadik bata ta yake ba, yadda ze ya gudu kawai yake tunani.

Daga Abba har Faruk su kai jugum jugum a mota, ba wanda yake magana, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, can Abba yace "Faruk kaga abunda ƙaninka ya jawa kansa ko? Da ya daure beyi wannan ƙaƙale ƙaƙalen nasa ba, da babu lallai Hakimi yace a barshi amma kaga abunda ya jawa kansa"

Faruk yace "wallahi kuwa Abba, Sadik yana da matsala halinsa se shi, ni kaina na nusar da shi amma yaƙi ganewa"

"Ai shike nan, kaga gobe ba ya kuma ba, kuma idan yace ze rashin ji jikinsa ne ze gaya masa, ni rigimar mahaifiyarku nake tunani, yanzu idan muka koma babu shi haka za tai ta sababi"

"Hakane kam, za tai mita sosai amma ai shine ya jawa kansa"

Haka suka cigaba da tafiya suna maida zancen.

Wasa wasa Sega Sadik yana hawaye, saboda shi ganinsa an zalunce shi idan aka ce ya cigaba da zama a nan, garin da babu wani abun more rayuwa a cikin sa.

Ya nemi guri yai zaman direshen a tsakar gida, se lokacin salla, ze tashi yai alwalwa yai salla a nan tsakar gidan.

Ba wanda ya kuma bi ta kansa, kowa sabgar gabansa kawai yake yi.

Ganin ba kowa a tsakar gidan yasa ya miƙe cikin sanɗa ya nufi hanyar fita, amma yana zuwa ya tarar da dogarai a soro na biyu riƙe da manyan bulalai.

Dawowa yayi kamar ya ɗora hannu a ka yai ihu, akai Abincin rana aka kawo masa, amma ya barshi a gurin be taɓa ba, har ƙarfe uku na rana yana tsakar gida a zaune kamar maye.

Wajen la'asar sannan su Abba suka isa gida, Mother najin tsayuwar motarsu ta fito, cike da burin ganin yaranta da aka kwasa a ka kai mata ƙauye suka kwana, mussaman Annurin zuciyarta wato Sadik.

Tana nan tsaye suka firfito daga mota, ta ƙarasa in da suke tana faɗin sannunku da zuwa, ina ɗan Autana?"

Abba bece komai ba yai gaba abunsa, Faruk ma ƙoƙarin barin gurin yake, ta kalli motar ta tabattar ba kowa a cikin ta, ta kalli Faruk tace "ina Sadik ɗin?"

Faruk yace "Ki tambayi Abba"

'ban gane in tambayu Abba ba, kai ka gayamin mana"

"Mother am pressed, i want ease myself" yai maganar tare da nufar BQ.

Mamakk ya kanainaye Mother tabi bayan Abba, tana zuwa yana shiga toilet É—auro Alwala.

Ta samu guri ta zauna tana jiransa, ko da ya fito kuma ya nuna mata salla zeyi ta ƙyale shi.

Ba ta gaji ba ta nemi Guri ta zauna dan jiransa ya idar da sallar, taji ba'asin in da aka baro mata É—a.

Abba ji yai kamar kar ya idar da sallar nan, saboda be san ta yadda ze fara mata bayani ba, dan ya san ba ƙaramin haurawa za suyi ba.

Aikuwa yana shafa addu'a tace "Abba nifa baku cemin komai ba, ina Sadik ne?"

Abba ya kalleta yace "zan siyar da Sadik É—in ne? Idan ma siyar da shi nai ai dai É—ana ne ko?"

"Eh naji na kuma yadda É—anka ne, amma Yakamata in san in da yake, kun tafi kun dawon ba shi dole in tambaya"

Abba ya É—an haÉ—e rai, cikin basarwa yace "mun baro shi a can"

"Can ina?" Tai maganar tana zaro idanuwa.

"Can ƙauye mahaifata, gidan Hakimi"

"Amma meyasa zaka baromin yaro a can, kasan fa ba iya zama ze ba"

"Saboda nima da na rayu a can ɗin kan ki haɗu dani a birni, ban mutu ba, dan haka shima baze mutu saboda zaman ƙauye ba se lokacinsa yayi"

"Haba dan Allah, ai ba ka haɗa rayuwar da kai da wadda ze ba, haba Abba, Sadik be taɓa nisa dani na kwana biyu ba, duk in da yake muna tare, ni da Faruk ka bari ba zan damu ba, amma Sadik be saba ba baze iya zama ba, dan Allah in laifi yayi ka baro shi kayi haƙuri ka ɗakkon ɗana"

Abba ya numfasa yace "bani yaiwa laifii ba, bana ce kai tsaye ga abunda yai ba, amma zan iya cewa koma mene shi ya jawowa kansa, tunda mukaje yake wasu irin abubuwa na nuna ƙyama ga garin, kuma bani na yanke wannan hukuncin ba, Hakimi ne yace a barshi a garin"

"Amma maimakon ka basu haƙuri, ka san Sadik baze iya zama ba wallahi, ai seka basu haƙuri amm ba ka baro min shi a can ba"

"Kinga Hauwa'u ki kiyayeni, ba zan bijirewa iyayena dan in faranta miki rai ba, yadda kike son É—anki haka nima suke sona, kuma ba za suyi abunda zasu cutar da abunda na haifa ba"

"Amma duk da haka se a duba yaron nan, tsakani da Allah baze samu yadda ya saba a nan a can garin ba"

Ganin Mother na neman sake ɓata masa rai yasa ya miƙe, ya koma sashinsa ya rufe ɗaki.

Wasu irin hawayen takaici ne suka taru a idon Mother, sam ba ai mata adalci ba, koma me Sadik zeyi ai bekamata ai masa wannan hukuncin ba, wannan uban ƙauye ina Sadik ze iya zama a cikin sa.

Wayarta ta É—akko ta kira Mummy, wato Maman Khairat, seda ta kusa katsewa sannan Mummy ta É—aga Tare da faÉ—in "Afuwa Please, salla nake ne ya gida ya yaran?"

"Gida lafiya ƙalau"

Mummy tace "ya naji Muryar ki haka ne?"

Cikin ƙufula Mother tace "kin san kuwa abunda Baban yaran nan yai min?"

Mummy tace "to yau kuma ke da sweetheart É—in ne? Meyafaru?"
Chapter 23 · 0% Book details