Sashe 89
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Matsalata shine ka koma, ba zaka shiga É—akin nan ba"
"A saboda me?" Mutumin ya tambayi Sadik cikin mamaki.
"A saboda mata ta ce a ciki"
"Ikon Allah, wato Farhan ta fara mu'amala da mahaukata kenan"
Cikin ɗaga murya Sadik yace "kaine mahaukaci, tsohon banza da na wofi, ka zo kana haikewa ƙanƙanuwar yarinya 'yar cikinka dan Allah dube ka mutumin banza da na wofi"
Galala ya buɗe baki yana kallon Sadik, ba'a taɓa baƙanta masa rai aka ci mutuncin sa kamar yadda Sadik yai masa yau ba.
Ya nuna kansa da yatsansa yace "ka san ko ni waye kuwa?"
"Mutumin Banza mana, wanda be san ciwon kansa ba"
"Yayi kyau, dole in sa akawomin ƙarshen rashin kunyarka a yau ba se gobe ba"
Sadik yace "ba irina akewa barazana ba kaji ko"
Jin hayaniya yasa Farhan Fitowa daga É—akin, sedai ga mamakin ta taga Sadik a tsaye a gurin.
Ta kalli Alhajin tace "ashe ka zo amma ba ka min magana ba"
"Eh na zo, wannan sakaran yaron ne yai min rashin kunya ya hanani shigowa, waya zan azo a tafarmin da shi a koya masa hankali"
Sadik ya tunkaro Farhan yana cewa "dan Allah Farhan ki saurareni, yanzu ki bari ina kai ki a duba hannunki, se muyi Magana"
"Wallahi ka kuma doso in da nake, sena baka mamaki" ta maida Idonta ga mutumin nan tace "Ya ci arzikina, ka ƙyaleshi ba ruwanka da shi, muje kawai"
Cikin hanzari Farhan tai gaba, Sadik ya bita yana cigaba da kiran sunanta.
Ba ta tsaya ko ina ba se jikin motar mutumin nan, cikin takaici mutumin yace "wai ke ina kika samo wannan mayen yaron ne mara hankali"?
Abun takaici se taji Maganar da Alhajin yai ta ɓata mata rai, amma ta basar tace "buɗe min ni in shiga mu tafi"
A zafafe Sadik ya ƙaraso gurin, dai dai lokacin ya buɗe mata motar za ta shiga, amma Sadik ya ture shi ya sa ƙafa ya daki murfin motar, ya juya kan Farhan yana huci, amma ya gaza furta komai.
Tuni hankalin mutane ya fara dawowa kansu, Sadik ya kalli mutumin nan yace "wallahi idan ba ka fasa bibiyarta ba, se na tona maka Asiri a garin nan, se nayi maganinka kan ka kayi maganina tsohon banza da na wofi"
Kan Sadik ya waiga tuni Farhan ta kak gate ɗin Hotel ɗin, ya zura da gudu ya bita sedai kan ya cin mata ta haye Napep tai gaba, ya juya kamar mahaukaci ya hau motarsa ya bisu, sedai ɓat suka ɓace masa.
Duk da haka be karaya ba haka ya cigaba da bulayi a tsakanin unguwar nan, amma be ga Farhan ba balle alamarta.
Be koma gida ba se bayan ƙarfe tara na dare, haka ya koma wujiga wujiga kamar wanda ya dawo daga filin yaƙi.
Already yayi Sallah isha'i a waje, bq ya wuce dan kar ma Mother ta ganshi ta sa shi a gaba da tambayoyi.
Ya É—au wayarsa ya fara kiran wayar Farhan, sedai ya jita a kashe.
Inna ce ta shigo ɗakin da Nana, take tana ta jijjiga Sahal da hannu ɗaya, yana ta uban kuka, hannu ɗaya kuma tana riƙe da wayarta tana dannawa, hasken wayar ya haska fuskar Nana tana zubar da hawaye.
"Ke lafiyar ki kuwa?" Firgigit Nana ta shiga goge hawayenta, tace "bakomai"
"Kamar ya bakomai kina kuka?"
Aikuwa ta sake fashewa da kuka tace "Inna yau fa kwana takwas Besty be kirani ba, kuma ni na kira tasa wayar ba ta shiga"
"Ikon Allah, saboda mijin naki kika zauna kina kuka haka? Ke da kika ce ba kya son sa da"
Nana ta tura baki tana ci-gaba da share hawaye.
"To ki kula da yaron hannunki, ki rarrashe shi, seki kira uwarsa kiji ko yana lafiya"
"Inna Kunya nake ji, ba zan iya kiranta ba"
"To ni ki kira, se ki bani in mata Magana"
Cikin Sauri Nana ta nemo lambar Mother, ta kira ta miƙawa Inna.
Mother taga baƙuwar lamba, dan ba ta da lambar Nana, amma jin muryar Inna ta ɗan sake suka gaisa.
Inna tace "dama matar Sadik ce tace ko lafiya, yau kusa kwana takwas be kira su ba, duk tabi ta É—aga hankalinta, kuma shi tasa wayar ba ta shiga"
Mother tace "ai Sadik É—in ne gaba É—aya na kasa gane kansa kwanan nan, ban san meke damunsa ba amma bari in bashi wayar"
Mother ta katse kiran, ta wuce BQ ta tarar da shi a kwance akan kujera, yai shiru ya dulmiya cikin tunani.
Mother tace "Allah yai maka maganin ko ma mene yake damunka, na rasa gane kanka gaba ɗaya kwanan nan, kuma kaƙi gayamin meke damunka"
Sadik yai shiru bece komai ba, se gyara kwanciyarsa da yai.
Mother ta kira layin Nana, Nana ta gaisheta, ta amsa mata tace ya suke ya Sahal, Nana tace suna lafiya, daga haka ta miƙawa Sadik wayar.
"Assalamu alaikum" Sadik ya faÉ—a a Sanyaye.
"Besty, laifin me mu kai maka haka, ka manta damu gaba É—aya, na kiraka wayarka a kashe me mu kai maka ne?"
Jikin Sadik yau sanyi ƙalau, cikin rashin ƙwarin jiki yace "Am sorry Nana, bana jin daɗi ne"
"Shine kake faɗan sunana ko? Me nai maka dan Allah" ta ƙarasa maganar tana kuka sosai.
"Subhanallah, ya da kuka kuma ke baki san kin zama Mum ba ne, ke ki kuka Daddyna ma yayi"
"To ba kai ne ba, ka manta da mu gaba É—aya, hankalina duk ya tashi na rasa meke faruwa"
"Tabbas nayi muku laifi, amma kiyi haƙuri bana jin daɗi ne"
Cikin kulawa Nana tace "eyya, meke damunka?"
"Ciwon kai nake fama ne"
"Sannu, ko dai in dawo ne? Nasan ba ka wani kula da kanka, kai in baka da lafiya gaba É—aya wani iri kake komawa"
Yai murmushi na ƙarfin hali yace "No, kar ki damu ina kula da kaina Sosai, ki zamanki idan kin huta se in zo in ɗakko ku"
"To kaje Asibiti ne?"
"Eh naje, har an bani magani ma"
"Nifa duk hankalina ya tashi, muryarka fa duk tayi wani iri Allah" tai maganar cikin shagwaɓa.
Ya lumshe ido yace "Besty"
"Na'am Besty na" ta amsa masa.
"Dan Allah ki rarrasan min É—a, ina jin kukan sa fa"
"Bayan ma ka dena kiransa a waya kaji ya yake"
"Kiyi haƙuri, insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, ki tai min Addu'a"
Tace "to shikenan, Allah ya baka lafiya nan ma ana tai mana saukar Alqur'ani Allah ya ƙara mana zaman lafiya ya baka lafiya, kuma kullum a idan nai salla ina maka Addu'a Allah ya yaye maka damuwar ka ya biya maka dukkan buƙatunka na Alkhairi"
Tabbas yasan Nana tana yawan yi masa addu'a, ko ya sani ko be sani ba, wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Sadik, tabbas yana son Nana, amma baze iya haƙura da Farhan ba, ko me ze faru ze yi duk me yuwuwa ya mallaki Farhan.
"Besty ya kai shiru?"
"Bakomai, anything special for me? Am missing you fa" yai maganar yana son basar da abunda ke ransa.
"We are missing you too, in gaya maka Sahal ya fara dariya"
"Dagaske, Allah ya sa be riga yi miki dariya kafin ni ba"
"Ai se yana bacci yake yi, amma Inna tace ya fara ƙyuya, kallon mutane yake Sosai"
"Ahh gaskiya gara in zo in taho da ku, tun kan ya fara yi min ƙyuya"
Tai murmushi tace "Naji daÉ—i da naji muryarka, ka kula da kanka sosai kaji Besty na"
Sadik yace "to my Asma, Ummu Sahal, Yarinya ta zama Mummy"
"Hmm ai zama Mummyn nan ma ba sauƙi, daga Sahal na gama"
"Baki isa ba, next year by now insha Allah kin kuma haihuwa"
Nana tace "ba ka san ya ake ji in za'a haihu ba ko?"
"Na sani mana, tunda tare mu kai naƙuda"
Dariya tai tace "besty me, se da na zo ƙauye naji muna missing ɗin ka wallahi"
Ya shafi sumar kansa yace "karki damu, insha Allah zuwa next week zan shigo in É—akko ku, nima na fi son in jiku a kusa dani"
"To shikenan, have a nice day, Allah ya baka lafiya ingantacciya abu Sahal"
Sadik yace "thank you wifey, ki kulamin da kanki da babyna, a gaida Hakimi da Inna"
"Zasuji insha Allah"
"Kiss me before you quit the call"
Nana tai murmushi tace "i will kiss you when we meet"
"Da kiss da me?" Yai maganar yana murmushi.
"Da kiss da ba ruwana, Inna tana jinka"
Da sauri Sadik ya kashe wayar, ya lumshe ido tare da ajiyar zuciya, yana jin tausayin Nana sosai da sosai, saboda sosai alamu sun nuna ta na son Sa sosai da sosai.
Inna ta shigo É—akin tace 'ikon Allah, har kin watstsake kin dena kukan?"
Tai murmushi tana sunkuyar da kai cike da jin kunya.
"Hankalinki ya kwanta dai ko? Maman soyayya"
Nana ta rufe fuska tana dariya.
Sadik ya miƙe ya shiga gida, kaiwa Mother wayarta, ya shiga sashinta da Sallama ta amsa masa, ya ƙarasa ya miƙa mata wayar yace "Mother ga shi"
Mother 5a kalleshi tace "zauna za muyi magana ne"
Sadik ya nemi guri ya zauna, Mother ta ɗan ƙare masa kallo sannan tace "Sadik, ka gayamin gaskiya tsakanin ka da Allah, menene yake damunka"
Sadik yace "Mother me kika gani?"
"Kamar ya me na gani, kai baka ga yadda gaba É—aya ka koma bane? Ba ka walwala kamar mara lafiya duk ka canza, wanda da ba haka kake ba, ka gayamin ko dai har yanzu Auren ne ba ka so?"
Yace "A'a Ina so"
"Ko dai akwai wata matsala ne?"
Yace "Mother wallahia bakomai fa"
Mother tai shiru sannan tace "kaga kuwa yadda ka koma? Da Abba na gari da shi zan haɗaka ban sani ba ko shi ka gaya masa".
"Allah Mother bakomai dagaske nake"
Mother tai ajiyar zuciya tace "shikenan tashi ka je, Allah ya kyauta koma mene yake damunka Allah ya yaye maka"
Jiki a sanyaye ya amsa da Ameen, ya tashi ya fita Mother ta bi bayansa da kallo.