Sashe 81
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba yace "da ta fara se a kaita Asibiti, su sun san abunda ya dace suyi, yanzu seki tuntuɓe su, kiji cikin watanni nawa ne, sannan aje ai siyayyar da ya dace na haihuwa"
"Abba ni ta yaya zan fara wannan tambayar, ni na rasa kunya zanji ko me zanyi," tai maganar tana dafe kanta.
Murmushi kawai Abba yai ya cigaba da abunda yake.
Daga bisani yace "kinga yanzu kince wataƙila ta kusa haihuwa, ki tambayesu kiji, kuma ta dawo ɗakinsa su dinga kwana tare, dan na sh ganinsa yana sanɗa daga ɗakinta, ki ɗauke kanki akan su, da da hali gida zan ba su su koma su zauna, amma ban san yadda cigaba da karatunsu ze yuwu ba, kuma ba abun ince su koma BQ ba, ban san yadda haihuwar zata zo mata ba, kinga daga shi har ita ba me wani hankalin kirki.
Ajiyar zuciya kawai Mother Tai, amma bakinta ya gaza furta komai.
A waya ta kira Sadik tace ya sameta a É—akinta, be daÉ—e ba se gashi yaje, sedai shi kansa Kunyar Mother yake ji.
Tun da ya shigo take binsa da kallo tana ƙare masa kallo Daga sama har ƙasa, ya nemi guri ya zauna.
"Sannu ko" Mother ta faÉ—a tana kallonsa, yai shiru tare da sunkuyar da kai.
"Ka bani mamaki Sadik, ina ta ɓaɓatu akan an maka auren wuri, Auren dole se gashi ka kunyata ni, so as you are you can impregnent a lady?"
Tsuke Fuskar sa yai a ransa yana faÉ—in 'wannnan wace irin magana ce Mother'
"Wai ni garin yaya ma a kai haka ta faru Sadik? Gaba É—aya ka shammaceni"
"Mother dan Allah, ni Wallahi gaba ɗaya kin sani a kwana in ba so kike in gaya miki komai ba, dan Allah ni dai kiyi haƙuri ki manta da zancen nan"
"A'a nina isa in tambayeka yadda abu ya faru, Allah ya kyauta amma ka kunyatani, haryanzu ƙanƙantar ka nake gani Sadik"
Sadik ya sunkuyar da kai ya ƙi Magana.
"Hmm, cikin nata wata nawa ne?"
"Tara" ya bata amsa.
"Kuma shine da kuka dawo baku faÉ—a ba, balle a sa ran kaita Asibiti"
Yace "munje ɗazu da ba kya nan, an mata scanning da booking na komai da komai na masu ciki, sunce da ta fara naƙuda aje Asibiti"
"Ikon Allah, ashe har Asibiti kuka je, hmm aishi kenan, se batun siyayyar haihuwa, ko baka san anayi ba, cikin kawai ka iya"
Sadik yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un"
"Ni kake jawa wannan innalillahi dan ubanka"
Cikin shagwaɓa yace "Mother ni wallahi na rasa me ma zance, dan Allah ki dena wannan maganar, munyi siyayyar mu tun a can"
"Ina abunda kuka siyo É—in?"
Sadik yace "Suna É—akinta"
Mother ta sa shi a gaba zuwa É—akin Nana, Nana duk tai wuri wuri da ido.
Sadik ya kalli Nana yace "Ina Akwatunan nan, da mu ka sai kayan babies?"
Nana ta nuna masa in da Akwatunan suke, Sadik ya É—akko ya ajiyewa Mother a gabanta, ta bubbuÉ—e sun sai komai, hatta net É—in jariri sun siya, abun shanya da kayan robobi ne kawai babu.
Mother tace "kai waya nuna muku duk wannan kayan ake siya?"
Nana ta kalli Sadik, dan ko da sukaje siyayyar ku san shi ya sai komai.
Yace "a waya nai browsing"
Mother ta sasu a gaba tana ƙare musu kallo, ta rasa murnar samun jika za tai a'a ko kuwa, idan ta kalli Fuskar Nana gaba ɗaya tausayi take bata, tana tausaya mata idan labor ya zo, kuma se Yanzu ta lura Ashe tun da suka dawo a hankali take tafiya, bata abubuwa da kuzari sam hankalin Mother be kai kansu ba.
Mother tace "to seka tattara mata kayanta, ku koma É—akinka saboda ko da wani abu ze taso cikin dare, kar a barta ita kaÉ—ai, sannan ka bani result É—in teses É—in da a kai mata, zan haÉ—a Akwati a shirya mata kayan haihuwa, dan zata iya haihuwa a Kowane lokaci.
Sadik yaji daÉ—in yadda Mother ta nuna kulawarta akan Nana.
Haka kuwa akayi, Sadik cikin É—oki da murna ya kwashe kayan Nana zuwa É—akinsa da ke cikin falon.
Abbas yai ƙuri da ido yana kallon Farhan da ke cikin motarsa, tana ta dannan wayarta.
"Waya ta fini mahimmanci ko Farhan"
Ta ajiye wayar tace "Ni na isa ince haka, Tuba nake ranka ya daÉ—e"
Yai murmushi tare da shafar ƙasumbarsa yace "Farhan, ashe an rufe Makarantar ku?"
Tace "Eh, na gani a news, dama ai ta cancanci a rufeta, da za'a bi shawarata ma ƙoneta yakamata ayi"
"Meyasa?"
"Saboda makarantar nan tayi silar rusa rayuwar matasan yara da yawa irina, koma me ya faru da ni makarantar nan ce sila, malamin da abun ya faru akansa, yayi iya yin sa ya rabani da Sadik, yana akrar dani RUƊIN ƘURUCIYA ne yasa muke soyayya amma na ƙi yadda, laifinsa ɗaya ya dinga aibata mu da miyagun maganganu ni da Sadik, se shi kuma Allah ya sa ya faɗa tarkon RUƊIN ƘURUCIYA"
Abbas yace "Yasalam, abu be daÉ—i ba, Allah ya tsare ya kiyaye, yanzu in Allah ya kaimu ranar Monday, zan zo in É—auke ki muje makarantar da zan sa ki, ina son su kai ki ss2 ne, da kin fara se azo ai maganar Aurenmu ko beuty na?"
HaÉ—e rai tai ta tura baki, yace "laifin me kuma nayi?"
Tace "ni gaskiya na gama boko a rayuwata, ba zan sake ba"
"Yanzu wannan dalilin ze sa ki zaɓi dena makaranta, ki hana al'umma amfanuwa da baiwar da Allah yai miki?"
"Ni gaskiya ba zani ba" tai maganar a hankali tare da jingina da seat É—in Motar.
"Dan Allah ayi haƙuri a temakawa marayan Allah a koma makaranta, ko dan saboda feature kids ɗin da zamu haifa"
Shiru tai masa taƙi magana, ya kira sunanta amma tai shiru, kamo hannunta yai cikin nasa yana murzawa a hankali, yana cigaba da kiran sunanta.
"Sadik dan Allah ka bar.... Se kuma tai shiru.
"Sadik kuma? Believe me haryanzu kina son Sadik, ina kishin ki fa ki dena kiran sunansa a gabana"
"Dan Allah kayi haƙuri, wallahi bana son Sadik yanzu, haka kurum se jikina ya dinga bani yana daf dani, ko kuna kamar muna tare, amma na san sharrin ƙwayoyin da nake sha ne, amma ba zan kuna ba insha Allah kar kai fushi kaji Doctor, ba ka fushi fa"
Tai maganar tana leƙa fuskar sa.
"Ina fushi mana, in dai za'a taɓaki Dole in yi fushi, kuma ni na mayi fushin am jealous"
Ta marairaice murya tace "Ohh God am sorry please, na dena ba zan kuma ba ka dena fushi kaji Doctor"
"To shikenan na dena, dan Allah ki kwana a gida yau kinji"
"Insha Allah a gida zan kwana, na maka alƙawarin yau ba in da zani"
"Shikenan, good night za muyi waya kan in shiga gida"
Dariya Farhan tai tace "Mijin tace, in ba tsoro ba mutum ya bari se ya shiga gida muyi wayar mana"
Dariya yai yana sosa kai, Farhan ta fice daga motar.
Yai reverse ya koma ƙofar gidan Hajiyarsa yai parking ɗin motarsa, ya sakko ya shiga gidan.
Ya tarar da Hajiya na kallon Sunna TV, yai sallama ta É—ago ta amsa masa, ya nemi guri ya zauna yace "Barka da Yamma Hajiya"
"Yawwa barka, daga ina kake haka?"
Ya É—an sosa kai yace "daga Asibiti"
"Ni na kasa gane wannan sintirin da kake min a gida, tun da ka dawo kusan kullum kana layin nan, ka gayamin gaskiya me kake zuwa yi ne?"
"Hajiya bakomai fa, ba abunda nake zuwa yi"
"To ya akai se yanzu ka shigo, bayan tun ɗazu naji ƙarar motarka ka wuce"
Ƙuuu cikinsa yai ƙara, yai wuri wuri da ido.
Hajiya tace "daa gurin Farhan kake ko?"
Yai Shiru ya sunkuyar da kai.
"Abbas, tun kan ka tafi na gane son Yarinyar nan kake, ni kaina na maka sha'awar Aurenta a da, amma yanzu ba ka ga yadda ta koma ba?"
Ya ɗan marairaice yace "Hajiya, a ganina Farhan za'a iya taimaka mata ta gyara Rayuwar ta, saboda na san bakin zaren matsalar ta, kuma Insha Allah ina tunanin zan iya taimaka mata, idan aka ƙyaleta Rayuwar ta zata cigaba da lalacewa, dan Allah ki bari in Aureta"
Hajiya ta numfasa tace "tun kan ka fara tausayinta nake jin tausayin ta, se dai ni ba irin iyayen nan ce masu kafiya ba, dan ban san yadda Allah ze da tawa zuriyar ba, ba ka da matsala daga gareni, amma ka san dangin mahaifinka ba za su amince ba, dan dole se sunyi bincike akanta kan su yadda su nema maka Aurenta"
Abbas ya sharce gumi, dan ya san dangin mahaifinsu ba ƙanan masifaffu bane ga su da kafiyar tsiya, ko da mahaifinsu ba ya raye, a tsaye suke a kansu, ya san ba zasu amince ba, dan za'a kai ruwa rana sosai, mussaman da matar da yake Aure, daga ɓangaren su aka haɗa su.
Hajiya tace "kaje kai ta Addu'a, Allah ya zaɓa abunda yafi Alkhairi"
Ya amsa da Ameen Sannan yai shiru ya cigaba tunani.
Haladu ne ya shigo ya tarar da Sunusi yana ta zazzage wata 'yar ƙaramar jaka, Haladu yace "ya dai me kake nema ne?"
Sunusi yace "wani aiki zazzafan aiki zanyi ne"
"Allah mutumina, wane irin aiki kenan kuma wa za kaiwa aikin? Nasan an shaƙa maka kuɗi"
Sunusi yace "ba wani zanwa ba se Yarinyar nan Farhan da wannan shegen me motar"
Haladu yace "wannan karon me kuma tai maka?"
Sunusi yace "ni zata kalla tana gayawa baƙaƙen maganganu, kuma naga wannan ɗan Gidan matar can ya dage, dan haka dole inyi wani abu a kai"
"Haba Sunusi, wallahi yakamata ka bar Yarinyar nan ta huta haka, wallahi ka cutar da ita da yawa, ka rabata da masoyinta duk ta zama wata iri"
"Kaga ba ruwanka, yadda suka min wulaƙanci suka hanani ita Ranar ɗaurin Aure, se baƙincikinta ya kashe su, babu me Aurenta, dani suke zancen"
"Amma Sunusi yakamata....." "Kaga Haladu ka samun ido kawai, ka ƙyaleni"
Haladu yace "shikenan, daÉ—inta dai shi Allah ba Azzalumin sarki bane"
Sunusi yai masa Shiru, ya tattara jakarsa ya fice.
Haladu yai shiru yana nazari, gaba É—aya tausayin Farhan yake, Sunusi ya cutar da ita sosai da sosai.