← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 115

Sashe 7

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan ta tashi kuka ya dinga rarrashi kenan, tare da Alƙawarin ze Aureta, Wannan shine babban dalilin da ze sa ya kammala secondary a shekarar.

Batun irin kusanci da shaƙuwar da ke tsakanin Sadik da Farhan kuwa ba'a magana, Sunyi shaƙuwa me ƙarfin gaske, ji take idan ya bar makarantar ta rasa wani abu me matuƙar mahimmanci a kusa da ita.

Yau bayan sallar isha'i, Farhan ta dawo daga makarantar dare, ƙaninta Imam ya sanar da ita cewar Abban su yana kiranta.

Ta maida hijjabinta ta fito, ta nufi É—akin Abban, ta shiga da Sallama a bakinta.

Abba ya amsa mata, taga Umma a zaune a gefensa, ta durƙusa ƙasa tace "Abba gani"

Abba yai gyaran murya yace "Farhan, waye yake kawoki a mota daga Makaranta?"

Cikinta ne yai wata irin ƙara, gumi ya shiga tsatsafowa daga goshin ta, ya a kai Abba ya san haka, bayan a can baya ake ajiye ta?.

"Magana nake miki, ki bani amsa waye yake kawoki a Mota, É—azu Sunusi ya gayawa malam bara'u, shikuma ya zo ya sameni"

Farhan ta sunkuyar da kai ba tace komai ba.

Umma tace "kaga abunda nake gaya maka ko malam, ana miki magana ba kya ji ne?"

Farhan ta ɗanyi jimm, ta karanto duk Addu'oin da zata iya sannan tace "Abba bani kaɗai ake kawowa ba, 'yar ajinmu ce ake zuwa ɗauka, idan ta tashi duk na hanya se a ɗakko mu tare, kowa a sauke shi se a ƙarsa da ita gida"

"KuÉ—in motar da nake baki ne baya isarki?" Abba ya jefo mata tambayar.

"A'a Abba suna isata"

"To meyasa sedai ki biyo motar yaran masu kuÉ—i?"

"Babu komai Abba"

"Farhan lalacewar zamani nake jiye miki, yaran masu kuɗin nan wasu ba Kirki ne da su ba, wataƙila a banza wataran za'a goranta miki, wanda babu daɗi, dan Allah Farhan ki kula da kanki ki tsare mutuncinki"

"To Abba insha Allah"

Abba yace "se magana ta biyu, da tuntuni yakamata in miki amma ban miki ba, malam Uba ya zomin da batun Yana son in bawa Almajiransa Sunusi ke, to na yaba da hankalin Yaron da nutsuwarsa, ba shi da wata damuwa, kuma an gayamin garinsu da suwaye iyayen sa, duk ba su da wata matsala dan haka gobe in Allah ya kaimu ze fara zuwa wajenki, ku fuskanci juna, dan Mahaifiyar ki ta nuna da wur take son ai miki Aure, tunda kinga mu dangin mu duk ba karatun muke ba, kuma baffan Ummanki har waya yayo yana mitar ance kin girma amma ba'a fara zancen Aurenki ba se karatun boko"

Gaba É—aya Farhan ta dena gane komai, se tsananin bugubda zuciyarta keyi, ta rasa meke mata daÉ—i sam.

Abba yace "naji kinyi shiru"

Cikin rauni Farhan tace "Abba karatu na fa?"

"Ai ba yanzu za'ai Auren ba, a samu dai ku fuskanci juna, kinga Farhan gara ki auri talaka dai dai ke, ba zan so aurar da ke in da za'a wulaƙanta ki ba dan bamu da Komai, amma kinga wannan shima ba shi da koma, kin ga se kuyi arzikin tare"

Farhan tai shiru ta kasa ko ƙwaƙwaƙwaran motsi.

Abba yace "ko akwai abunda zaki ce?"

Farhan ta girgiza kai alamar a'a.

Yace "yawwa, tashi kije Allah yai mil albarka"

Ai ko amsawa ba ta iya yi ba, ta tashi jiki a matuƙar sanyaye, ta nufi ɗakinta, ta na zuwa ta zube akan katifarta, ta fashe da kuka.

Wata irin masifaffayar soyayyar Sadik ce ke bijiro mata, ga shi ba ta son yin duk wani abu da ze sa ta saɓawa iyayen ta, amma ya za'ai ta auri wanda ba ta so kwata kwata, bayan ga wanda zuciyarta ke so? Dole tajewa Sadik da wannan maganar dan samo bakin zaren.

Tunda ta shiga É—akin nan ba ta sake fitowa ba har gari ya waye.

A Library taje ta samu Sadik, ya duƙufa yana karatu, ta sa hannu ta rufe littafin.

Da sauri ya É—ago ya kalleta, se kuma yai murmushi yace "kefa kin fiye neman Magana, da na tashi a zuciye na make ki fa?"

Tai murmushi tace "sannu da hutawa"

"Hmm ina fa hutu, lokacin exams na ta ƙaratowa, gaba ɗaya kamar kaina ya fashe"

"To ka dinga hutawa mana, ba naji ance expo ce za'a baku ba"

Sadik ya harareta yace "me kika maida mijin nakinne? Daƙiƙi ko me? Dan abun kunya duk tsawon shekarun nan Abba na kashe kuɗin makaranta a ƙarshe ace se an bani expo wuce nan"

Tai mit tace "kaga gifted, ni ban taɓa tunanin gifted suna karatu ba ai"

"Waye yace miki ni gifted ne, ba wani gifted, yanzu dai meye labari?"

Tai ajiyar zuciya ta kalli Sadik tace "labari babu daÉ—i"

"Subhanallahi how comes? Meke faruwa kuma?"

"An gayawa Abba kana kawoni a mota, jiya yai min Magana"

Sadik yace "garin yaya, wanene ya gaya masa?"

"Ba ma ita ce babbar matsalar ba, kwanakin baya ƙanwar Umma ta zo gidanmu, tana ta mita akan lallai wai se an min Aure, Abba yace se na gama makaranta, tunda ta koma suke kiran Abba a waya, akan lallai a fitarmin da miji, wai tunda 'yarta sa'ata ce ita ma Aure za'ai mata"

Sadik yai mata ƙuri da ido yace "ina jinki"

"Sadik Abba yamin miji"

Dammm! Yaji ƙirjinsa ya buga yace "ina jinki"

Cikin matuƙar rauni ta cigaba da cewa "Sadik i don't know what to do, you are leaving me soon, zaka tafi karatu, zaka barni idan ka tafi mahaifina ze iya yanke Kowane irin hukunci, dan Yanzu haka ya ba da ni, harya ba shi damar ya fara zuwa gurina, da na kammala secondary School yace ze aura masa ni". Ta ƙarasa maganar ƙwalla ta taru a idonta.

Kasancewar suka ɗai ne a cikin Library, ya sa ya kamo hannunta cikin nasa, duk da wani irin azababben kishi da yaji yana taso masa, ga matuƙar tashin zuciya da ya shiga, amma ya dake cikin tattausar murya yace "Allah ne yake da nan da shekaru ukun, ke mallakina ce, duk wanna fafutukar da nake saboda mu kasance tare ne, kuma Insha Allah zamu kasance tare, dagaske nake sonki Farhan ba kamar yadda ake cewa RUƊIN ƘURUCIYA bane"

"I know, but bana son bijirewa iyaye na"

"Ba zamu bijire musu ba, zasu fahimce mu Insha Allah"

Haka Sadik ya cigaba da lallaɓata yana kwantar mata da hankali, amma ƙasan zuciyarsa wata irin fargaba ce da tashin hankali mara misaltuwa.

Da Sadik ya koma gida ɗakinsa na cikin falo ya tafi, sedai ji yake kamar yai kuka, yana son Farhan matuƙar so, idan aka aura masa ita ze iya riƙeta amma kowa ya kasa fahimtar su.

Jiki a Sanyaye yai wanka ya fito falon, a falon yai karo da Mother, ya ɗan ƙura mata, ta dube shi tace "Lafiya kake min wannan kallon haka?"

Yace "ƙamshin Abba naji"

"Iyayi, Abban naka har wani ƙamshi ne da shi na musamman?"

"Eh mana ya dawo ne?"

Tai murmushi tace "ya dawo, amma yana hutawa ne"

Yai murna yace "I know I guess it right, bari inje idan ya tashi na ganshi anjima"

Mother tace "Abinci fa?"

"Mother zan dawo ba yanzu ba" ya juya ya fita yana ta lissafin abun yi.

Lilly Kuwa da ta koma gida ta tarar mamanta wai ta tafi Sokoto anyi haihuwa, dama babanta ba mazauni bane, daga ita se masu aiki kenan a gidan.
Dama ba yau aka saba tafiya a barta a gidan ba, daga ita se masu aiki, Mum É—inta ta maida zuwa Sakwatto bakomai ba, nan da nan taje ta dawo, wataran idan ta tafi se tai kwanaki ba ta dawo ba.

Hakan ya ƙara bata damar sakewa sosai a gidan.

Sir Nazir mutum ne me matuƙar aji da kwarjini, ba student ba har a staffs mata akwai masu son shi, amma tsabar kwarjininsa yasa ba su samu fuska a gurinsa ba, amma gashi a karon banza yarinya ƙarama ta samo kansa tana juya shi yadda take so, da tenakon ƙawayenta da kuma kallace kallacen fina finai da uwa uba karance karancen dake ƙara ruɗa tunanin yaran da ke tashen ƙuruciya.

Sadik kuwa gidan su Khairat ya tafi, yana tunanin ko ze samu mafita Khairat ta bashi shawara, dan wasu lokutan duk shirirtar ta ta kan bada shawarar da ke ɓullewa.

"Kace min magana za muyi kuma kayi shiru"

Sadik yace "Khairat na rasa ta ina zan fara ne, abun ya cushemin da yawa"

"To daure dai ka gayamin" cewar Khairat dake kallonsa.

"Khairat, kin gane Farhan ai?"

Khairat tace "ji wata tambaya, ganewa kai"

"Khairat, ina matuƙar son yarinyar nan, a dalilinta na takura in gama makaranta a SS2, yanzu zancen da nake miki babanta ya bawa wani ita, nan da 3years za'a aurar da ita, ni Kuma lokacin ina level 3 kenan, bana son in rasata, na so yiwa Mother bayani, amma taƙi saurarata, na rasa yadda zanyi"

Khairat tace "bro, lokacin mace fa da na namiji na É—aya bane, idan kace se an jira ja gama karatu zaka aureta kasan shekarun da saura, kuma haryanzu yarintar ka ake gani"

"Naji na gane, ai dama ba cewa nai yanzu ba, sonake a neman aurenta, ni ta jira zuwa kan ta gama secondary ina level 3 se muyi auren, na rasa wanda zan tunkara, Faruk ma ya ƙi fuskanta ta na rasa abunyi gaba ɗaya"

Khairat tace "Nima kaina ya kulle wallahi, amma kayi magana ds Abba mana kaji me zece"

"Khairat, Mother ma ba ta saurareni ba balle shi"

"Kuma kaga ra'ayin su É—aya da ko Daddy, da se ince ko shi za'a gayawa yaiwa Abba Magana, amma nasan ba zasu amince ba, cewa za suyi kayi yarinta da yawa"

Sadik ya dafe kai yai shiru, kawai ya miƙe ya fice daga falon jikinsa ba ƙwari

Misalin ƙarfe takwas na dare, Alhaji Abdullahi yana falon dake shashensa shi da kafatanin iyalan sa, ciki hards dr. Da matarsa Jidda suna cin abincin dare.

Sedai Sadik se jujjuya spoon yake, ya kasa cin Abincin kirki.

"My boy, ya akayi ne naga baka cin Abincin ina fatan ba matsala?"

Sadik yai murmushi yace "bakomai Abba"

"Yayi kyau, ya shirye shiryen exams kuma?"

"Alhamdilillah Abba, mun kusa farawa soon Insha Allah"
Chapter 7 · 0% Book details