Sashe 57
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau a kai sa'a da la'asar ya dawo, amma ya tarar da ita a falo, duk tai wuri wuri saboda yunwa.
Ta na kallonsa ta shareshi ba ta kula shi ba, shima kuma be kulata ba, ya shiga ɗakinsa yai wanka ya canza kaya, Sannan ya dawo falon ya sameta ya ajiye mata wani ƙaramin pack a gabanta.
Cikin sauri ta buɗe park ɗin, farfesun wata ƙatuwar kaza ce a ciki, se ƙamshi take.
Ba ta san lokacin da tai murmushi ba, taje ta wanke hannunta, ta sa kazar na a gaba ta dinga ci saboda ba ƙaramar yunwa take ji.
"Ke! Ke! Kina ina?!"ta jiyo Sadik yana ƙwala mata kira.
"Kut, nice ma ke É—in, wallahi ba zan amsa ba" ta cigaba da cin kazarta.
A fusace Sadik ya fito yace "kina ji ina miki Magana kika shareni, uban waye yace ki ajiyemin Akwatin ki a É—akina?"
"To ni a ina zan ajiye?"
"A kaina zaki ajiye" ya bata amsa yana huci.
Ko kallonsa ba tai ba ta cigaba da cin abunda ke gabanta.
Sadik ya kai matuƙar ƙulewa da haushi, se jinsa tai yana janyo Akwatinan yana shiga wani lungu a falon.
Tashi tai da sauri ta bi shi, dan ganin ina ze kai mata kaya.
ÆŠakina babba, da gado da mudubi kamar na Sadik, har da kayan wasa su teddy da komai da komai, ga zane zane masu kyau, da a kai framing É—in su, aka saka a jikin bango.
Ya waigo ya kalleta, jin takunta a bayansa yace "Nan shine É—akinki, karki kuskura ki kuma shigarmin É—aki, na gaya miki"
Nama tace "Amma ka san da nan É—in, dan mugunta ka barni nake kwana a cikin sanyi, wuyana se ciwo yake"
Tsaki yai ya juya ze fita tace "Amma, naga ɗakin a ƙarshen gida, in abu tsoro ya zo fa, ko kuma gobara ta kama ai har abun ya cinye ni kan in fito"
Sadik ya kalleta da mamaki, wannan yarinyar wasu lokutan Mahaukaciya ce, wai batun gobara take da abun tsoro.
Tsaki ya ja, ya fice daga É—akin ya barta ta na cigaba da kallon É—akin.
Ta gama mamakinta ta fito, ta kasa cinye kazar da Sadik ya kawo, ta tashi zata kai sauran Kitchen, ta tarar da Sadik a Kitchen É—in yana ta shirya kaya a cikin fridge, wanda ba ta san da su ba ma.
Ya ɗakko kwalbar da ta shanye madarar ciki yace "ke kika taɓa wannan kwalbar ko?"
Ta tura baki tace "to ai yunwa nake ji, shiyasa na É—auka na sha"
Sadik yace "Yawwa, kin kyautawa kanki, a garin tsinannen kwaÉ—ayi kin sha wa kanki"
"Me na sha?" Ta tambaye shi tana zare ido.
"Madarar karnuka ce, Nonon karya ne a ciki"
Take ta dafe ƙirji tace "la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalumin, dan Allah meya kawo Nonon karya cikin fridge?"
"Ban sani ba, daga yanzu kya dinga kiyaye abunda zaki ci, in ba haka ba wataran naman karen zaki ci"
Ya fice ya barta dafe da ƙirji tan zare ido, take taji cikin ta na juyawa, naman da taci ma yana taso mata.
Sadik ya koma falo kan kujera yai zamansa, ya kunna tv, wanda tun da suka tare a gidan ba'a kunna ba.
Yana kallonta ta fito daga Kitchen ɗin jikinta a sanyaye, da alama ma kuka tayi, Ba wani Nonon karya da ta sha, Sadik yana sane ya gaya nata haka duk cikin salon yadda ze ƙuntatawa Nana.
Ta koma É—akin da yace shine nata, ta shirya kayanta a wardrobe, ta shiga banÉ—aki tai ta kakarin amai ko zata amayar da madarar nan, amma abu ya gagara abu da ta ri ga ta sha tun safe.
Ko da ta dawo Falo, Sadik ya fice ba kowa a gidan se ita kaÉ—ai.
Ta koma tana ta É—aÉ—É—aga teddies É—in dake É—akin, tana jujjuya su sedai abu guda, wata zundumemeiyar 'yar tsana ce take ba ta tsoro.
'yar tsanar tamkar É—an shekaru shida, se taga Kamar 'yar tsanar zata fara motsi.
Ƙarshe ta kuma komawa falo ta zauna, shima ta na yi tana waige waige, wai kar 'yar tsanar ta biyo ta falon.
Haka tai ta wannan zaman ɗarɗar ɗin, har ƙarfe goma na dare sannan Sadik ya shigo, sallama yai ta amsa ya zo da kaya niƙi niƙi ya wuce Kitchen, se dai tai ta hamdala da ya dawo ɗin, dan a tsorace take sosai.
Ya fito daga Kitchen har ze gota ta, ya jefo mata abu jikinta, wata roba ce a cikin 'yar ƙaramar jaka, ta zaro robar dabino ne a ciki da yawa, irin lubiyar nan.
Ta bi bayansa da kallo dan wulaƙanci maimakon ya bata, shine ya jefata da shi.
Ta girgiza kai ta É—an É—aga murya tace "Nagode"
Yana jinta yai banza da ita ya wuce É—aki.
Nana ba ta yadda za'ai ta iya kwana da wannan 'yar tsanar a É—aki É—aya, dan haka a falon yau ma ta kwana.
Washegari da safe ba Makaranta, Sadik da wuri ya shirya cikin wando 3quater, da 'yar shimi ya wuce Nana a falo tana bacci, ya fita jogging.
Se da gari yai haske sannan ya dawo, tuni Nana tai wanka ta canza kaya.
Sadik na shigowa kallo É—aya tai masa ta É—auke kanta, duk da ba wani datti a gidan, amma ta gyara ko ina fes, ta É—au ragowar kazarta ta ci.
Haka su kai sati a gidan nan, in ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba Sadik ba ya kula Nana, duk da Nana akwai rawar kai, ita dan be kulata ba, ba ya hanata yi masa Magana in tana buƙatar wani abu.
Kullum ze zo da Abinci, ya Ajiye Mata.
ÆŠakinta kuwa ta samu bargo ta rufe wannan 'yar tsana da ke bata tsoro, amma duk da haka a tsorace take kwana a É—akin.
Zaune yake a bakin wani ƙaton ruwa, akan fararen kujeru yai shiruuu yana tunani, teburin gabansa ɗauke da tarin littattafai, amma hankalinsa yana gurin.
Ji yai an taɓa shi, hakan ya dawo da shi da ga dogon tunanin da ya tafi.
"Abbas, ka kammala nazarin litattafan ne ka zauna tunani?"
Abbas ya ja wata irin ajiyar zuciya, tare da lumshe idonsa.
"Wai meyake damunka ne? Tunda mu ka zo garin nan naga kamar ba ka sukuni, ko akwai matsala ne?"
Abbas ya ɗanyi miƙa sannan ya gyara zamansa, ya kalli me masa maganar yace "Ahmad, wallahi hankalina yana Nigeria"
"Me kake tunani a Nigeria? In Madam kake tunani, ta biyoka nan É—in mana"
Abbas yace "Mmm, ita ma ina tunanin nata, se dai gaskiya abunda ya dameni daban ne, wallahi wata yarinya ce ta tsaye min a rai, ina tunanin halin da Yarinyar take ciki yanzu haka"
Ahmad yace "budurwa kai kenan?"
"A'a, ba budurwa ta bace, she's my client amma ina tunanin halin da take ciki".
Nan Abbas ya kwashe labarin Farhan ya gayawa Ahmad.
Ahmad yai murmushi yace "Lallai Yarinyar ta cancanci a tausaya mata, amma sonta kake"
"Kai, rufamin Asiri kar kasa Matata ta sakeni mana, yarinya ce Sosai not more than 14years, but she's deeply in love with someone, ga kuma a halin da iyayenta ke shirin sa ta".
Ahmad yace "Ni ban da lalacewar zamani, ina 'yar shekara huÉ—u ina wata Soyayya?"
Abbas yace "Ahmad kenan, Soyaya ai gaskiya ce ba ƙarya ba, kuma ka duba yanayin lokacin da muke ciki, akwai banbancin zamani, yanzu yaran yanzu idansu a buɗe yake, ga kallace kallacen fina finai, dan haka tunaninsu ba iri ɗaya ba ne da yaran da.
Ni babban abunda yake damuna, bagidajen da iyayenta zasu aura mata, wani wawa mara hankali, ga ta she's very calm, ko Magana ba tayi sosai, wallahi tausayinta duk ya cikan zuciya, idan lissafin da nake daidai ne, saura wata guda ya rage a É—aura mata Aure, ina tsoron kar deprssion ya kama Yarinyar nan, ko ta faÉ—a mummunan hali"
Ahmad yace "ka gama kewaye kewayenka ka dawo in da Magana take, You love her"
Abbas yai murmushi yace "ka ga, mu fara abunda ya kawo mu, a bar wannan zancen"
Haka kuwa akayi, nan su ka shiga nazarin litattafan da suke gaban Abbas.
Faruk ya samu delay a tafiyarsa, se yanzu Allah yai tafiyar, ya shirya komai tsaf, washegari da sassafe ze tafi.
Khairat ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk ta shiga cikin damuwa.
Ƙarfe tara da na dare, har Faruk ya fara shirin kwanciya se ga Khairat.
Da mamaki ya kalleta yace "Khairat, ya dai? Meyafaru na ganki yanzu, bayan yanzu na baro cikin gidan?"
"Magana nake so muyi"
Yace "ok, ina jinki"
Nan ta shiga in da in da, ta rasa ta ina zata fara masa bayani.
"Calm down, nag duk kin ruÉ—e Kamar wadda taje screening da fake result, Faruk ne fa feel free to tell me"
"Wata Magana nake so in gaya maka, amma ban san yadda zaka É—auke ta ba"
"Ina jinki Khairat"
Ta É—an kalleshi sannan tace "Yaya Faruk"
"Na'am sister Khairat"
"I...mm...dama"
"Dama me?"
"Ina son in gaya maka, Yaya ina sonka ne"
Murmushi Faruk yai yace "Nima ina sonki ai Khairat"
"I serious mean it, please keep joke aside, I want you to marry me"
Ɗan Jimm Faruk yai yana kallon Khairat, yai murmushi yace "Khairat, Nifa yayanki ne, ki bar wannan maganar kinji ko, kar ma ki bari wani yaji ta, babu wannan a tsakanin mu, zumunci da 'yan uwanta ka ne a tsakanin mu, you are still young Khairat, kar ki biyewa RUƊIN ƘURUCIYA kin ji, maza je ki ki kwanta kimga dare ya fara yi"
Jiki a sanyaye Khairat ta baro BQ, tana matuƙar son Faruk, ba ta taɓa zaton haka daga gareshi ba, gashi dai be mata wulaƙanci ba, amma dai be karɓi Soyayyar ta bs, wanda hakan ya tssye mata a rai.
Yanzu Nana idan Sadik baya nan, zama take ta kunna Tv dake falo tai kallo, hakan yana É—ebe mata kewa Sosai, duk da akwai tv a É—akinta amma ba ta san yadda za tai operating É—in ta ba, dan babu remote ta falon ce dai akwai remote, dan haka kullum cikin kallon cartoon take.
Yau ma ya dawo ya tarar da ita tana kallon cartoon É—in ta, kamar kullum ba wanda ya kula wani a cikin su.