← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 115

Sashe 83

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmm ai ba zan ƙara ba, daga wannan ɗan ba zan kuma haihuwa ba"

Murmushi yai ya miƙe, ya nufi in da aka kwantar da jaririn ya ɗakko shi yana cewa "Alhamdilillah, yanzu wannan namu ne Husna"

Nana tace "gashi nan da ƙaton kai kamar na babansa ba, ya ban wahala"

Sadik yace "wallahi bani da ƙaton kai, se kuma bakinsa irin na babarsa na tsiwa ba"

Nurse ta shigo tace "Ikon Allah, waye yace ka shigo ne?"

"Se ance in shigo ni da É—a na da matata"

Tace "lallai kam"

Su Abba suka shigo tare da Mother, Sadik ya miƙe yana murmushi, ya danƙawa Abba jaririn, yana faɗin "Abba kalleshi, kamar mu ɗaya da shi ko?"

Abba yace "sosai makuwa"

Usman yace "Wai kai ba ka da kunya ne?"

Sadik yace "wace kunya, tunda Allah yayi ya zo duniya"

Nan da nan aka shiga buge bugen waya, Inna ta rasa in da zata sa kanta dan murna, a ranar tace a aika mota a É—akkota.
Asibiti ya cika da jama'a, se zolayar su Sadik ake, wai yaran Iyaye.

Awan Nana shida a Asibiti bayan ta haihu aka sallame ta, sedai mursisi ta ƙi shayar da yaron, wai me ze sha.

Da labari ya samu Faruk ma, a ranar ya fara shirye-shiryen yadda ze dawo Nigeria, sun samu jariri a familyn, bayan shafe tsawon lokaci ba ai haihuwa ba, kasamcewar danginsu ba masu yawan haihuwa ba.

Mother ta riƙe jariri gam, Kamar ta haɗiye shi, saboda tana matuƙar ƙaunar yara.

Inna ta taho da kayayyakin ta da akewa mai jego, se da Inna ta zo ta sa Nana a gaba, sannan tai ƙoƙarin shayar da shi, shime da ya fara sha se ta sa kuka tace ita zafi.
Shi kuma Sadik da ya ɗan fita aka jima se ya dawo, ya shiga cikin 'yan barka ya karɓe ɗansa ya zauna yana kallonsa.
Inna tace "Yau naga abunda ya isheni, za'aga shiririta agun wannan sakarkarun iyayen".

Idan Sunusi baya nan, Haladu se yai ta bincike masa kaya, ko Allah ze sa ya gano wane irin Asiri yaiwa Farhan, Sunusi ya na ɗan taɓa harkar tsubbu, ya sa a ransa cewa duk yadda ze zeyi dan ya taimaki rayuwar Farhan da Sunusi ya tarwatsa.

Tana zaune a gurin cin Abinci ita da Alhajinta, da yake kashe mata kuɗi, yana ɗan duba wayarsa yace "Farhan, kalli wasu young couples, kina cewa wai ke baki isa Aure ba, kin ƙi yadda muyi Aure, ko ki bani haɗin kai mu huta, kalli wannan young couples ɗin, sun haihu"

Ta sa hannu ta karɓi wayar tana kallon screen ɗin wayar, a Instagram ne, hoton Nana da Sadik sun haɗa kai suna murmushi, gefe an saka hoton jaririn.
Take Jikin Farhan ya kama rawa, yawun da take ƙoƙarin haɗiya ya kasa wucewa, take ta saki wayar ta fara tari!.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. 

Tari ne ya sarƙe Farhan, ya shiga jera mata sannu, sedai a sannun nasa ko ɗaya ba ta amsa ba, ta miƙe ta ɗau jakarta tai hanyar fita, ko gabanta ba ta gani sosai tafiya kawai take.
Bayanta ya biyo yana kiran sunanta, amma ba ta saurare shi ba, ta tari abun hawa ta shige, suna tafe tana kuka, kuka me tsuma zuciya, me Napep ɗin yana ta cewa Baiwar Allah kiyi haƙuri, ki sassauta kukan nan dan Allah.
Ko saurarensa ba tai ba ta cigaba da rera kukanta.

Suna zuwa gida ƙofar gidansu, ta cillawa me Napep ɗin dubu ɗaya ta shige gida, a ɗakinta ta tsaya ta rufe ƙofa ta sa sakata, ta zube a gurin ta dinga kuka, kamar zuciyarta zata tsaga ƙirjinta ta fito.

Allah ya temake ta gidan ba kowa balle a rarrashe ta, ta rasa wace irin Soyayya da shaƙuwsce haka tsakanin ta da Sadik, ta kasa mantawa da shi, ta kasa rufe babinsa daga rayuwar ta, yayi Aurensa har an haifa masa ɗa, ita kuwa tana nan tana gararamba a titi, ba Auren ba karatu sema lalacewa.

Ta sake fashewa da kuka, ga Wani irin kishinsa da ya dinga taso mata, ya haÉ—a jikinsa da wata, bayan ta riga ta yadda da shi, shine namiji na farko da ta amince ta haÉ—a jikinta na sa.

Ji tai wani irin abu yana taso mata daga zuciyarta, ga wani irin ciwon kai da ya addabe ta, ta watso kayan drower É—inta, ta É—au wata kwalba, ta shanye abunda ke ciki tas, ta jefar da kwalbar ta kife kan katifarta tana cigaba da zubda hawaye.

"Sadik ka Cutar dani, cutarwa mafi muni, ka rusa rayuwata da ban sanka ba da ba lallai wannan abubuwan su faru da ni ba, nayi dana sanin saninka, ba zan maka Allah ya isa ba, ba zan iya ba, Allah ya dawwamar da kai a cikin farinciki ni kuma ya bani mafita" ta ƙarasa maganar cike da rauni.

Tana jin yadda zuciyar ta keta tafasa, ga wayarta se ringing take, amma ta kasa ko da motsa yatsanta ne, saboda maganin da ta sha ya fara aiki a jikinta, wani irin bacci ya fara fizgarta.

Da yawa mutane ba su san Sadik yai Aure ba, se labarin haihuwa suka ji, ga yaron Kamar Sadik yai kaki ya ajiye, kamarsa É—aya da Sadik sosai da sosai.
Kwanansu uku da haihuwa, Faruk ya iso Nigeria, cike da ɗokin ganin ɗan Sadik, Sadik kamar su cinye juna shi da Faruk, gidan aka rasa wanda yafi wani ƙaunar jaririn nan, hatta Khairat rawar kai take akan jairin nan.

Se jaririn nan yaita kuka, Nana tai mursisi kamar bata san yanayi ba.

Sadik ya shigo ya tarar da Mummyn Khairat taiwa jaririn wanka, se rarrashin sa take amma se tsala kuka yake.

Sadik yace "Mummy ba yunwa yake ji ba kuwa?"

Mummy tace "to ai uwar ta sa ce se a hankali, ina ga Madara yakamata a nemowa yaron nan a dinga haÉ—a masa da ita"

Sadik yace "kawo shi" ya karɓe ɗansa ya saɓa shi a kafaɗa, yana shafa bayansa ya nufi ɗakin sa Nana take.

Ta harɗe ƙafa tana shan shayi da farfesun kaza.

Sadik yace "Friend meyasa kike haka ne? Yaro se kuka yake amma ke kina nan kina cin Abincin ki, shi kuma ko oho?"

"To ni ya zan masa, shikenan ni ba zanci Abinci ba?"

"A'a waye yace karki ci Abinci? Amma shima seki ba shi nasa"

"Dan ba ka san zafin da nake ji ba ko? To ka ba shi naka ya sha, shikenan da na motsa ko a cikin mutane ne sai ya ta kuka"

Sadik yace "to yanzu ai ba a cikin mutane bane, dan Allah ki karɓe shi  ki bashi"
Ta ƙara tura baki tana tauna bredinta.

"So kike ya mutu da yunwa?"

Ta zazzare ido tace "ya mutu kuma?"

"Eh mana, kalli yadda yake kuka fa, anya kina son sa?"

Nana tace "wallahi ina son shi sosai, zafi nake ji sosai in zan Shayar da shi, tun daga ciki har raino duk ba sauƙi friend"

Sadik ya gyara zamansa yace "ai duk aikin lada babu sauƙi, a cikin sa yanzu dai daure ki karɓe shi,"

Ta sa hannu ta karɓe shi, ta fara ƙoƙarin Shayar da shi, sedai yadda take rintse idonta, zaka gane tabbas da gaske take zafi take ji.

Sadik ya zuba mata ido cike da tausaywa, gaba ɗaya lamarin babu me sauƙi, yace "Sannu" tace "yawwa"

Yana tsaka da sha, Nana ta tsige shi ta miƙawa Sadik shi tace "karɓe shi na gaji wallahi"

"Haba Nana, be ƙoshi ba fa"

"Kar ka kuma cemin Nana" tai maganar tana zumɓura baki.

"To naji, amma kinga fa kuka yake, Allah Sarki babyna, yi haƙuri ita ma maman naka ba'a daɗe da yayeta ba, shiyasa take baka wahala"

Inna ce ta shigo tana ƙwalawa Nana kira "ke ki taso ga ruwa can an kai banɗaki"

Nana ta É—ora hannu a ka tace "Na shiga uku, daga wannan se wancan, wallahi wankan nan da zafi dan Allah ku min rai"

Inna tace "yau naga shashasha, in ba'ai wankan ba so kike ki lalaltaccen jego? Kaikuma kasa ta a gaba, da É—a hannu yana faman kuka, ka bata shi mana"

Sadik yace "Ai yanzu ta bani shi, bari in kaiwa Mother shi ta goya shi ko ze bacci"

Inna tace "A'a wataƙila yunwa yake ji, ki karɓe shi"

Sadik yace "A'a Inna, ƙyaleshi Kawai, amma dan Allah wankan a bari ruwan ya huce, naji tana cewa yai mata zafi da yawa"

Inna tace "jimin ɗa da feleƙe, ni tafi ka bani guri, ke kuma zaki ta so ko sena zo na janyo ki?"

Haka Nana ta taso, tana ta zubar da hawaye, ta wuce akai wankan nan.

Sosai Mother ke shiri akan taron Suna da za'ai abun har mamaki yake bawa Inna, ba Inna ba hatta Nana abun mamaki yake bata.

Katin gayyata na Online da na bugawa, anyi Nana ba ta san adadin su ba.
Daga haihuwar zuwa yanzu kuwa, 'yan barka kawai sun tarawa Nana sha tara ta arziki, dan ma wani abun Mother ake bawa, kowa yai sallama da abunda ze kawo.

Kayan fitar Suna kuwa, lefe da ba'aiwa Nana ba, shi Abba ya saka ai mata, kaya na gani na faÉ—a.

Gefe guda Jairi na ta shan wuya a gurin yarinyar uwarsa, tana son yaron amma idan ya isheta da kuka, zama take ta taya shi kukan, idan yaa isheta da tsotso ma haka take dire shi, ta cigaba da sabgogin ta, ai tai mata faÉ—a amma ko a jikinta, ba abunda yake bata haushi irin cikin dare yaita tsala kuka, Kamar ana cire masa ido, ta juya ta shige bargo ta bar mutan gidan da rarrashin sa.

Har magariba sannan Farhan ta farka daga mayen da take, tai alwala ta rama sallolin da ba tai ba, tana kwance a É—akinta Amir yai sallama yace "Yaya, Doctor yana sallama da ke"

"Kaje ka ce masa ba zan zo ba"

Mamaki ya kama Amir, ze yi Magana amma tai masa tsawa tace "kace ba zan zo ba"

Yaron yaji maganar tai nauyi yaje ya gayawa Doctor, dan haka ya wuce yaje ya gayawa Abba abunda Farhan tace.
Chapter 83 · 0% Book details