← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 115

Sashe 108

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yayanki me amma yana da iyaka, ni kaÉ—ai na cancanci kiyi kuka in rarrasheki ba hurimin Faruk bane"

Nana cikin mamaki tace "Abun harya kaimu ga haka? Yau na fara hira da Faruk? Kasan ma akan me muke magana? Kawai zaka fara yi min faÉ—a?"

"Bana buƙatar jin koma menene, amma ki sani akwai iyaka tsakanin ki da shi" mamaki ne ya kama Nana, bayan ficewar Sadik, tun kan yai Auren kenan, idan yai Auren kuma wataƙila dukanta ze farayi, amma ai ba yau ta fara hira da Faruk ba, gaba ɗaya se jikinta ya sake yin sanyi sosai.

Shikuwa Sadik kishi ne ya kama shi, dan Nanan ba ƙaramin kyau tai ba, gashi duk in da ta shiga ƙamshin turare take, hakan ne yasa yaji wani haushi ya tokare masa wuya da ya ganta da Faruk.

Sadik ya cigaba da hada hadarsa, groups na 'yan makarantarsu ya ɗauka akan cewa Prince ze angwance da Farhan, kowa da abunda yake faɗa akan Auren nasu, wasu na son barka wasu na tofa abunda ba'a so, wasu suna ba su taɓa ganin Soyayar gaskiya ba irin wadda Sadik yakewa Farhan.

Sadik reception kawai ya shirya zeyi da abokansa, idan aka dawo daga É—aurin Aure.

Sadik jinsa yake Tamkar ze sauke wani gagarumin nauyi da yake kansa, yakama gobe in Allah y kaimu ne ɗaurin Aure, se wani nishaɗi yake yi, har ze kwanta kawai ya tuna da wani hali Nana zata shiga, shifa ganinta yai kawai da Faruk suna hira yaji haushi, ita kuma ya zata ji, shi da ze tare da wata ya take ji a ranta, nan take nadamar abunda yai mata ya baibaiye shi, tashi yai ya zura rigarsa ya koma cikin gida, yana mitar da suna tare a BQ da ba wanda ya sani ze bata haƙuri, amma yanzu Mother ta hanata zuwa in da yake, wai se sun tare, haka ya tafi yana mita.

Dubawa É—akin da take kwana yai amma bata nan, ya nufi sashin Mother, da Mother ya fara haÉ—uwa yace "Mother dan Allah ina Besty?"

Mother tace "ban sani ba"

Sadik yace "Mother Magana kawai zan mata dan Allah"

"Nace maka ban sani ba, ka ɓacemin daga ganina" tunani ya shiga yi ko dai ta gayawa Mother abunda yai mata ne.

A lokacin ya sake jinjinawa ƙoƙarin ta, tabbas kishi babu daɗi sam, ya koma BQ ya kira layinta amma a kashe, daga ƙarshe se haƙura yai.

Yau haka Sunusi ya wayi gari sukuku, kamar wanda aka yashe, ga wani irin ciwon kai da ya tashi da shi, ko sallar juma'a be samu ya halarta ba, unguwar su Farhan shiru, Kamar ba sauran mutane a unguwar, can ya fara jin hayaniya, alamar an dawo.

Haladu ne ya shigo ɗakinsu yana faɗin kai Abu na Allah, Allah me ƙudira sassauya lamuransa yadda ya so.

Sunusi yace "wai meyafaru ne?"

Haladu yace "kan in gaya maka, duk da bani da murya bari in rera waƙar mawaƙin nan Wayeka oho dai da yake cewa "duk yawan rabo, in ba kai kar ka ɗau salon jahili, in rabo ya tsago da kai, kuma abun ya tabbata da kai, Rabbu ne yace se da kai, in seda kai kawai se da kai.
in abun ya zo babu kai, Rabbu ne yace babu kai, in babu kai kawai babu duk duniya ba me sa da kai, Rayuwa wucewa take kawai, Rayuwa mubi a hankali kawai"

"Wai dan Allah ka gayamin meyafaru ka tsaya a kaina, ka saki murya kamar fitar tusa kana waƙa, kamar wani maroƙi"

Haladu yace "koma kamar zubar zawo ce, in dai saƙona ya fita ai shikenan, Allah ne ya nuna ƙudurarsa, yaron da kaiwa Farraƙu da Farhan, ashe shi zata Aura, an ɗaura musu Aure da sadakinsa dubu ɗari Wallahi".

A zabure Sunusi ya tashi zaune yace "wannan É—an yaron?"

Haladu yace "shi fa, Allah ya nuna maka shike da komai, kai kaga tarin motoci na alfarma a unguwar nan, Allah ne yai yarinyar nan ba ta da rabon shan wahala dan dama sam baku dace ba, shiyasa tsabar taurin kanka da ƙauyanci yasa baka sameta ba.
Kai kaga yadda yaron ya É—au wanka tubarkallah, se haskawa yake kai turaren da yake tashi a jikinsa shi da 'yan uwansa yadda kasan a kamfani, kai abun arziki na masu arziki ne, na matsiyata se Innalillahi wa Innalillahi raji'un".

"Dalla rufemin baki, waye matsiyacin ka bar wannan cika bakin, ka bari ka gani idan zasuyi zaman Auren cikin daÉ—in rai, har yau har gobe matata ce"

"Matarka ta ina, ba dai jahilci ya ja maka ba? Meye aibu dan ance kai gwaji, kuma ba kama mata gida a birni, ka tsaya kana cin zarafinta, Allah ya ƙara yanzu sedai kaga wani ya mora ba dai kai, ba ɗan cicif daidai ita ga gayu kamar ita ba kai ba , da seka kwana uku baka wake baki ba"

Haladu yasa Sunusi a gaba da cin mutumci, ƙarshe seda su kai faɗa baran baran uwaki ubaki, ga ciwon kai da ya addabi Sunusi.

Gidansu Farhan ya kaure da hayaniya, tare da shewa ana ta rangaÉ—a kuÉ—in Sadakin Farhan, ita Farhan duk jin abun take kamar a mafarki, wai ita aka É—aurawa Aure da Sadik, ikon Allah.
Su Sadik suka shigo domin ɗaukar hotuna, Farhan ta saka farin lace me golden color, shikuma Sadii ya sanya fararen kaya, ya ɗora farar alkyabba me adon golden yayi kyau matuƙa.

Fuskar Farhan ba yabo ba fallasa, kallon Sadik kawai take ji take kamar almara, amma da ta tuna Abbas gaba É—aya se taji Auren Sadik ya fita a kanta.

"You look so much beautiful, Alhamdilillah yau kin yadda son da nake miki ba RUƊIN ƘURUCIYA bane?" Wata uwar harara ta galla masa, Murmushi kawai yai be kuma cewa komai ba.

Duk da Sadik yana da girman jiki, dan idan aka faɗi shekarunsa wasu har mamaki suke, amma a haka Wasu suka dinga surutun Angon Farhan ɗin yaro ne, kuma a haka yana da mata kuɗi iyayenta suka bi suka ba shi 'yar su, 'yan baƙin ciki kuma na kwanan nan ze sakota dan duk abunda a kai ba dan Allah ba baya lasting.

Mother ta shiga bedroom ɗinta tarar da Nana a kwance ta zubawa guri ɗaya ido, gaba daya Mother tausayin Nana take, ta ƙarasa gaban gadon tace "ya baki tashi kinyi wanka ba? Yanzu 'yan ɗaurin Auren nan zasu dawo, su cika gidan nan ki maza ki shirya, kar a zo a ganki a yanayi na ba daɗi, ki daure bari in sa a kawo miki Abinci.

Nana gaba ɗaya tun da ta fuskanci an ɗaura Auren jikinta yai sanyi ƙalau, dan tun abunda Sadik yai mata akan Faruk gaba ɗaya ta sare da lamarin.

Jiki a sanyaye tai wanka, ta fito tana shafa abubuwan gyaran jikinta, me kwalliya ta shigo tai mata light makeup, ta saka wani danƙareren leshi da Mother ta sai mata, ta fito ras da ita tai kyau.

Mother ta shigo tana faÉ—in "Masha Allah, kinyi kyau sosai, yanzu abunda nake so da ke, zamu fita falo wasu basu sanki ba, yau zasu ganki, dan Allah ki daure ranki karki bayyanar da damuwarki, ki nuna komai normal kinji ko?"

Nana ta jinjina kai, Sannan tai gaba Nana na binta a baya, da yawa wasu se ranar sukaga uwar gidan Sadik, musamman matan abokan Abba, nan suka dinga yabata suna gata yarinya ƙarama kyakykyawa, lallai Sadik ya more.

Nana kam a nutse take komai, bayan sun gama gaisawa ta samu guri ta kame ta cigaba da sabgoginta.

'yan ajiksu Sadik sunje reception Sosai, suna cewa sun zata gagarumin party ze shirya musu, Sadik yace "da kenan, yanzu an girma, har da É—a, ai dole a nutsu" har da wasu daga cikin malaman makarantar sunje bikin na Sadik.

Ƙarfe huɗu Mother tace azo wasu su raka Nana kan a kai amarya, Sadik ya shiga cikin hada hada sosai, ƙarfe biyar ya sauya wasu haɗaɗɗun kayan, ya shigo cikin gidan, ana ta tsokanar sa, ya wuce ɗakin Mother in da aka gama shirya Nana, yanzu wani material ne a jikinta, me wasu duwatsu kallo ɗaya Sadik yai mata yasan dauriya kawai take, tayi kyau matuƙa.
Ya shiga bedroom É—in ya kalli wasu cousins É—insa yace "A bamu guri zan ga matata"

"Ikon Allah, lallai Sadik yanzu mu kake kora, wai kai magidanci?"
"Eh ya ranku?" Suka fita suka basu guri.

Se uban ƙamshi yake, ita ma Nanan haka se zuba ƙamshi take yace "Ina ɗa na?"

Nana jiki a sanyaye tace "ina ga yana gurin dr. Ko Anty Jidda".

"Idan ya ɓata a taro kya samo mana wani, tunda zuwa yanzu kin manta labor room" Sunkuyar da kai tai tana wasa da dogayen yatsunta.

"Besty, shekaranjiya na miki laifi, Mother kuma ta hanani shigowa, kawai kishi ne ya kamani ranar a kanki, amma kiyi haƙuri dan Allah"

Nana tace "ya wuce".

Ya ɗago haɓarta tana kallonsa, ya haɗe bakinsa da nata, seda ya shanye jambakin bakinta tsaf, sannan ya cikata, ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda, ya cire mata yari da sarƙar kunnenta, ya ciro na zinare ya sakamata, saboda tunda ya fara hidimar bikin nan, ba abunda ya ɗauka ya bata.

Ya kamo hannunta ya ɗaura mata abun hannu, Sannan ya saka mata zobe yace "ba zan gaji da baki haƙuri ba, Nasan ni me laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki yi haƙuri Nana, Kamar yadda nai miki alƙawari, insha Allah zanyi iya yina gurin kamanta muku adalci, Sannan ki tayani da addu'a in cika alƙawarin da nai wa Hakimi, Besty kina da wata kima a idona da duk juyin zamani ba zan zama butulu a gareki ba, ina sonki Husna, ki sa a ranki ƙaddarar mu ce a haka"
Chapter 108 · 0% Book details