Sashe 84
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya tashi da kansa ya je har ƙofar ɗakin Farhan ya ƙwanƙwasa, amma tai shiru.
Ya ɗaga labulen, amma kasancewar da wuta ya ga fuskarta a kumbure, ta dunƙule guri ɗaya.
"Meya sameki ne haka? Kukan me kike? Har kika ce acewa yaron nan ba zaki zo ba?"
Aikuwa ta kuma fashewa da kuka tace "Abba, da yawa maza ba sa tsoron Allah, Ba zan Auri Doctor ba dan Allah ni a ƙyaleni, wallahi Abba na gaji da Komai gani nake kamar a duniya ni ka ɗai aka tsana"
Abba ya ƙarasa cikin ɗakin ya zauna a kusa da ita yace 'ki dena irin wannan maganar, Allah ya jarrabi dubunki da abunda ya ninninka naki, ki godewa Allah ya baki rai ya baki lafiya, ki dena wannan maganar"
Gaba É—aya ta manta tare da Abba take magana, neman in da zata amayar da abunda ke ranta kawai take, cikin kuka tace "Yayi Aure fa Abba, har an masa haihuwa"
"Shi wa?" Abba ya tambaya cike da rashin fahimta.
"Abba Sadik mana, Sadik Abdullahi Rano, na so shi na so shi, ya kyautata min ya sa na fara son shi, amma ya yaudare ni Abba, kuma na kasa mantawa da shi" tai maganar tana wata irin whalalliyar ajiyar zuciya.
Abba ya jinjina sunan nasa, wato matashin nan da ya taɓa kawo mata invitation na bikin yayansa, tabbas ba ze manta yaron ba.
Wato shine silar duk wannan wahalar da Yarinyar tasa take sha, shine Yaron da take faÉ—a dama? Wanda ya dinga hure mata kunne?
Abba ya haɗiye wani abu me ɗaci a maƙogwaronsa sannan yace "banda abunki dama Farhan, ina ke ina wannan yaron, ai kyan ƙwarya tabi ƙwarya dama, idan ta bi Akushi fashewa za tai, wannan yaron ba sa'an Aurenki bane, yaro ne ƙarami kuma ɗan masu kuɗi ina ke ina shi?"
"Abba, da Umma ta ja ni a jiki kamar sauran 'ya'ya da Sadik beyi galaba a kaina na fara son shi ba, Astagfirullah, Astagfirullah Abba da Sadik da Sunusi, zan iya yafewa Sadik amma ba zan iya yafewa Sunusi ba, shine mutum na farko da ya fara ɓatani a gurin iyayena, da kuma mutanen unguwa, Abba ta yaya zan kuma yadda da wata Soyayya a gurin maza, Sunusi ba da'awar yana sona yake ba? Amma hakan be hana shi yi min wannan sakayya ba".
Shi kansa Abba daga baya yake godewa Allah, da yasa aka fasa Auren nan, dan yanzu idan Sunusi ya ganshi É—auke kai ya ke, koma ya fara yada masa maganganu da habaici.
"Na sani Farhan, Amma cikar kimarki, da abunda ze goge miki wannan tabon shine Aure, ba duka maza ne suke haka ba, Kamar yadda kuma wasu matan ba ku da kirki, kar laifin wasu ya shafi Abbas.
Na so ki koma Makaranta, amma a yanayin da kike ɗin nan ba zan so ki cigaba da zuwa Makaranta ba, kiyi haƙuri kinji Farhan"
A sanyaye tace "to Abba" ya dinga rarrashin ta yana mata Nasiha, har hankalinta ya É—an kwanta.
Abba da kansa yaje ya samu Abbas yace masa yayi haƙuri yau bata jin daɗi, sedai ya dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kai rai.
Abbas yace ai mata sannu daga nan ya tafi.
Tun da Faruk ya zo Nigeria, Khairat take ta ƙoƙarin yin shishshsigi a wajensa, amma ya basar da ita, sedai ya ɗan tsokane ta, ya ƙyaleta sam yaƙi yarda ta shiga jikinsa, tun da ya tafi ko ta waya ba shiga sabgarta yake ba, dan shi sam Faruk be damu da harkar mata ba balle wata Soyayya.
Tun ana i gobe suna aka kawo manyan raguna guda biyu na suna se saniya wadda za'ai hada hadar Abincin suna, Nana ta sha gyaran kai da lallae kamar Amarya.
Ranar suna yaron yaci sunan Abba, wato Abdallah, akai masa inkiya da Sahal.
Anci an sha a gurin taron sunan nan kamar ba gobe, Sadik ya sha shadda Nana kuma wani danƙareren leshi ta saka, sun samu kyaututtuka Sosai, mutane da yawa ba su san anwa Sadik Aure ba, se da a kai wannan haihuwar.
Wuni guda a kai ana cin Abinci daban daban a gurin nan, aka sha hotuna da raye raye, se bayan magariba sannan aka watse daga gurin sunan.
Tunda Abbas yaje gidansu Farhan akace ba ta jin daÉ—i, ya buga wayarta ya kai sau goma amma ko É—aya ba ta É—aga ba, a wannan karon ma ne gaji ba, ya kuma kiran wayar ta ta yai sa'a ta É—aga tai Sallama cikin sassanyar muryarta.
Yai ajiyar zuciya a sanyaye yace "ranki ya daÉ—e, yau Allah yayi an É—aga wayata?"
Tausayin Abbas ne yakamata, babban mutum kamar wannan yai ta wahala akanta, a hankali tace "Doctor kana lafiya?"
"Eh Alhamdilillah, sedai gaba É—aya bana jin daÉ—i kwana biyu da banji muryar ki ba kuma bamu haÉ—u ba"
Farhan tace "Ina cikin damuwa ne, amma yanzu Alhamdilillah"
Abbas yace "damuwa damuwa, Allah ya kawo mana ƙarshen wannan damuwowin naki"
Tace "Ameen, ka san meya sani a damuwa da kuma kokwanto"
Yace "A'a se kin faÉ—a"
Tace "Hoton Sadik na gani, matarsa ta haihu, se nai tunanin irin soyayyar da mu kai ya juyan baya, Sunusi yai iƙirarin yana sona, amma shima ya tozarta ni, shiyasa nake jin tsoron in saki jiki da kai Doctor, amma nasan kana haƙuri da ni"
"Farhan, duk abunda ya samu bawa a rubuce yake a cikin littafinsa na ƙaddara, haƙiƙa ya cancanci ki guji maza da halayenmu, saboda an ɗanɗan miki maɗaciya a silar Soyayya, amma hakak ba ya nufin duka maza haka muke, ki bani dama Farhan kar ki hukunta ni da laifin da ba nawa ba"
Ta gyara kwanciyarta tace "to Doctor, ya kake ya aikin?"
Yace "Aiki Alhamdilillah, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki makaranta fa, fatan baki manta ba?"
"Bance maka ni bana son makarantar nan ba?"
"Dan Allah Farhan, kar Muyi haka da ke, kinga na biya komai dan Allah ki amince ki koma Makaranta, alfarmar da nake nema a gurinki kenan, dan gara kice ba kya sona da ki ƙi cigaba da karatu"
Ta É—an ja numfashi Sannan tace "shikenan, se ka Zo"
"Kin amince im zo in kai ki?"
Tai murmushi tace "Na amince doctor"
Sukai Sallama sannan ya kashe wayar.
Inna ce zaune akan kujera Abba na ƙasa tana sanar masa da cewar za ta tafi da Nana can ƙauye, dan kula da ita zuwa Arba'in, da Nana taiwa Sadik zancen cewa yai wallahi ba in da zata, Inna dama ba ta bi ta kan wani Sadik ba, Abba takewa bayani.
Abba yace "to Inna, ban ƙi ta taki ba, amma abubuwa za suyi miki yawa sosai, ga jinyar Hakimi, ga mejego da jariri gashi ke ka ɗai ce, ga babu wanda ze dinga taya ki, kinga abun ze miki wahala sosai, amma kinga nan ga Hauwa'u, ga sauran mutane zasu tsaya su kula da ita sosai, ga kai yaro riga-kafi da cigaba da kula da ita Nanan, tunda kinga doguwar naƙuda tai ga ƙanƙantar shekarunta se ana zuwa ana cigaba da kula da lafiyar ta".
"Na san da haka, amma ni nafi ganewa inje in kula da ita a can, a nan ba ta da mataimaki se Allah, matarka ba wani ƙaunar Yarinyar nan take ba, wannan abubuwan da take ma, saboda jikanta takeyi, gara ka bani 'yata inje in kula da ita sosai"
Abba yace "dan Allah Inna, kiyi haƙuri ki barta a nan, na miki alƙawarin za'a kula miki da ita, ko ki zauna a nan se ki kula da ita"
"Shi kuma baban naku waze kulamin da shi?"
Abba yace "ga hadimansa nan da suke hidima da shi, shi kansa Sadik rigima ze sa akan a raba shi da yaron nan, kina ganin fitsarar da yake akan yaron, ba ya kara ko jin kunya sam, in yaso idan tai Arba'in se kuje ƙauye ko sati ɗaya tayi, kuma Hakimi ya ga ɗan jikansa".
Inna tace "ni ba zan zauna a garin nan har kwana Arba'in ba, tana yin sati uku zan tafi"
Da ƙyar Abba ya lallaɓa Inna ta Amince da shi.
"Baban Lilly kana ganin matakin da kale shirin ɗauka akan Yarinyar nan shine daidai? Kayi haƙuri a sasanta ai musu Aure da yaron nan kawai kowa ya huta"
Ya ɗan ɓata fuska yace "hmmm, Amina kenan, haryanzu maza sunan mu kike ji ba ki san suwaye mu ba, kina tunanin za tai daraja ko wani mutunci a idon yaron nan ne? Bayan abunda duk za'aiwa ɗokin ta gama ba shi, har da ciki ana zubarwa kashi kashi, wahala kawai za ta sha, matakin da na yanke akanta shine daidai"
"To shikuma malamin na su ya za kai da shi?"
"Se yai prison wallahi, Allah ma ya rufa masa Asiri, da wallahi duka na so in sa kurata suyi masa, dukan da se sun karya kowace gaɓa ta jikinsa, sannan aje a watsar da shi, zan saki kuɗi se an ɗaure min shi, ɗaurin wulaƙanci aita jan shari'ar se an manta da shi a prison".
"Amma yakamata shima ai masa adalci, yanzu ka gama cewa haryanzu ban san maza ba, duk da yawon da kai a duniya banjin haryanzu ka san menene kaidin mace, Lilly itace musababbin faÉ—awar yaron nan halaka, dan da bakinta tace da ba ruwansa, yanzu ka sassauta masa, Sannan ka sa a ranka kaima laifukan da ka aikata ne a baya suke bibiyar ka, ko ka manta irin gwagwarmayar da akai a baya?".
Yai ajiyar zuciya Tare da girgiza kai yace "Allah ya yafe mana kawai, amna jibi insha Allah zan wuce da ita can"
"Banji daÉ—in rabani da Lilly da za kai ba, amma ina fatan hakan ya zama silar shiriyarta".
Baban Lilly ya yanke shawarar kai Lilly gidan wani babban amininsa da ke aiki a Benue shima babban soja ne, ze kaita can ta cigaba da makaranta a can, ƙarƙashin kulawa da tsaro me ƙarfin gaske. Abokin baban Lilly ya santa farin sani, kuma shi ya bawa Baban Lilly shawarar ya kai masa ita can, ta ƙarasa makarantar a can, in ya so ko a cikin sojojin da ke Barrack ɗin ne a samu a aura mata wani, wanda be san Meta aikata ba.