Sashe 51
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba É—aya zuciyar Farhan ta bushe, meyasa Sadik ze tafi ba tare da ya sanar da ita ba?.
Ta rasa tunanin meyakamata tayi, kuka ko farinciki? Sadik yana nan lafiya, amma har ya tafi karatu ƙasar waje be nemeta ba, what does that mean? The relationship is over, he don't want her anymore, he dumps her aside? So Abbas gaskiya yake gayamata kenan, Sadik ya barta kenan?! Ya ilahi.
Idanunta su kai jawur, does she deserves this from him? Tana zamanta lafiya, ya koyar da ita son shi, kuma ya tafi ya barta ba tare da tunanin wani hali zata shiga ba.
'No, he can't do this to me? Sadik yana sona, akwai dalilin da yasa ya tafi be neme ni ba, shikenan Aurena da Sunusi ze tabatta, Ashe doctor gaskiya yake gaya min? Gaba É—aya ta rasa tunanin meya kamata tayi.
Seda ta É—aga kai taga ba kowa a ajin, sanann ta gane an tashi kowa ya tafi.
Haka ta É—au jakarta ta bi hanya itama, ba tare da ta É—au ko babban hijjabin ta da ta saba sawa ba.
Ji take kamar ta samu wani gurin da babu kowa ta ƙwala ihu da ƙarfi ko ta samu sassauci Amma babu halin hakan. (This is how depression starts, and later on you will see what it leads to)
Yauma akan idon Sunusi Farhan ta dawo, da skirt iya ƙwaurinta, ya matse ta rigar Makaranta duk a ɗame, ga wani ɗan mitsitsin hijjabi, kasa Magana yai sema buɗe baki da yayi yana kallonta dan be taɓa sanin haka Uniform ɗinta na Makaranta suke ba, ga wani irin kyau da sukai mata, dirarriyar budurwa me kyakykyawar ƙira komai nata daidai da jikinta.
Se ya rasa kishi zeyi, ko kuma farincikin ganin abunda ze aura?.
Haka ta shiga gida babu ko sallama, Umma ta bita da kallo, tana zuwa tai jifa da jakar Makarantar ta, ta faÉ—a kan katifarta.
Adda Maryam tace "yarinyar nan kuwa Lafiya take?"
Umma tace "oho mata"
Adda Maryam ta shiga ɗakin Farhan tana mata Magana, amma Farhan ta ƙi kulata.
"Anya Innar Farhan ba aljanu ne suka kada ita ba, Sannan kalli kayan jikinta wannan ai dole Aljanu ma su shafeta dama wannan watsewar ake makarantar? Wannan ne kayan makarantar ta ta?"
Umma tace "to ni me zance, bani da yadda zanyi babanta ne ya dage se tayi, kuma ni bata taɓa aljanu ba, amma bari Amira ya shigo ya kira Malamin su Sunusi ko Sunusin su zo suyi mata addu'a"
Farhan na jinsu tai musu shiru, amma yadda take ji a ranta idan aka kusakura Sunusi ya zo in da take a halin yanzu, seta masa Illa!.
Abba da su Mother suna kan dining suna cin abincin rana, suna ta hira Faruk se dannan waya yake.
Mother tace "wai ba zaka ajiye Wayar nan kaci Abinci ba, ka ƙi maida hankali, idonka akan waya"
Yai murmushi yace "Am sorry maam, ina ganin wani abune a IG yanzu zan ajiye"
Abba yace "ai matasan mu se fatan Allah ya shirya, amma sun maida waya kamar wani nau'i na ibada, in basu Danna waya ba ba sa jin daÉ—i"
Faruk yai murmushi yace "Abba kenan, kasan yanzu Komai ya koma kan waya shiya........ Kai!"
Abba yace "ya dai?"
Faruk ya ƙurawa wayarsa ido.
Abba yace "wai menene?"
Faruk ya miƙawa Abba wayar, Abba ya karɓa yana dubawa.
ÆŠiffff Abba yai, yan nazarin abunda ya gani a wayar.
Ba tare da yace uffan ba, ya ajiye wayar ya tashi fuuuuuu!
(Me Abba ya gani 🥺🙄🙄)
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Take tsigar jikin Farhan ta tashi, taji kanta yai wata irin sarawa, wani irin sanyi ya shiga Ratsa ta, taji tamkar an ɗora mata dutse a ƙirjinta, zuciyarta ta bushe hawayen ma suka gagara zubowa balle ta ji sauƙi a ranta.
Umma da ke tsakar gida tace "dubu Ashirin da biyar kuma?"
"Eh, sun ta bada haƙuri kin san ba masu ƙarfi bane, sedai yaron akwai zuciyar nema"
"Hakane, Allah ya sa albarka ya kaimu lokacin ya sa ayi damu"
Ya amsa mata da "Ameen"
"Allahumma ajirni fi museebati, wa akhlifni khairan min ha" shi Farhan ta dinga maimaitawa, dan wata irin muguwar tsanar Sunusi take ji tana ƙara ratsata, ji take kamar ta kwashi kayanta ta gudu, da tai ido huɗu da wannan mummunar rana da za ace Sunusi shine mijin da zata aura.
"Why Sadik? Meyasa kai nisa da ni ka bari nake shan wahala haka, come back to me please" tai Maganar tana ƙanƙame pillow a ƙirjinta, tana tura hancinta jikin pillown, tamkar zata ji ƙamshin turaren Sadik a jikin pillown, gashi tai tai tayi kuka, amma kukan ya gagara zuwa sam, se wata irin Azabar raɗaɗi da zuciyar ta ta take mata.
Tana jiyo Ummanta tana ta kiran danginta tana gaya Musu, ai an kawo kuÉ—in Auren Farhan, suna ta murna suna yaren fullanci suna mata barka da arziki.
Huzaifa ne yai sallama ya shigo gidan, dan tun da Umma ta ritsa shi ta sa ya karanta mat saƙonnin cikin wayar Farhan, yake jin kunyar zuwa gidan su haɗu da Farhan, dan lokacin da Umman ta bashi wayar ya duba mata, be san wayar waye ba, dan a saninsa Farhan ba ta da waya, sedai yai nisa a karanta saƙonnin sannan ya fuskanci wayar Farhan ce.
Ɗakin Farhan ya leƙa, ya hangota tayi ruf da ciki akan katifar ta, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin ta ya hargitse, ta dunƙule guri ɗaya da Sauri ya saki labulen yana ambaton Allah, dan be san a haka ze ganta ba, amma kana ganin yadda take zaka gane tana cikin damuwa da tashin hankali, ko ba a faɗa ba yanayin ta ze nuna tana cikin damuwa sosai.
"Ahh Huzaifa har ka zo?"
Yaji Maganar Umma, ya waigo da sauri yace "eh Umma, wai ki bani kayan in tafi da su"
"To Huzaifa, kai ko Allah sanya Alkhairi ma baka mana ba, bayan a gidan ku aka karɓi kuɗin Auren ta"
Huzaifa kawai ya sunkuyar da kai yana murmushin yaƙe, dan kwata kwata ya rasa meya rufewa su Umma ido, suka ga dacewar haɗa Auren Farhan da wannan ƙazamin mutumin me masifar tsiya.
Yana karɓar saƙon da ze karɓa ya tafi, dan ji yake kamar yaiwa Farhan kuka, messages ɗin wayar nan ya tabattar masa akwai wanda take so, ba wannan Sunusin ba, zuciyarta na tare da wani daban, gashi an gaza ba ta damar zaɓen abokin rayuwa, ga katse mata karatu da akayi.
Sadik kuwa tuni yai sabbin abokai, dama shi ba ruwansa ba shi da wuyar sabo idan ya ga dama. Dan ba ko yaushe yake miskilancin ba. har wani group ne da su shi da abokansa, ba ya taɓa ɗaukar littafi yai karatu, abune me wahala yai wannan, sedai abubuwa sun fara caza masa kai daga lokacin da ya fara bin abokai zuwa club, wanda Addinin su da al'adar su ba ɗaya bane, hugging, shaking hands and Even hugging is not something big a gurinsu.
Mussaman da Sadik yake burge 'yan mata, he is young but looking sexy and hot (ba inji ni ba, kun san dai su ba ruwansu faɗa za suyi 🙄🙄🙄) yana da suffa me kyan gaske, mussaman idan ya cire rigarsa ya shiga ninƙaya a ruwa, yana samun masu zuwa su ɗauki hoto da shi.
Mata suje hostel É—in maza, ko maza suje hostel É—in mata wannan duk ba wani abu bane normal ne, suna iya haÉ—uwa su yi wa junansu bitar karatun da a kayi a aji.
Sadik yana iya ƙoƙarin sa, gurin kula da addinin sa, da kiyaye abunda ze kaucewa hanya, amma abubuwa na nema sufi ƙarfinsa.
Hajiya Nana kuwa, ta É—an fara sakin jiki da Linda, wato room mate É—inta, idan ta saurara da kyau, tana iya gane abunda Lindar take faÉ—a, tana yawan tambayar Nana kukan me take yi, idan ta ga ta zauna tana kuka, ko in taga Nana tana salla ta tambaye ta menene wannan take yi haka?
Linda akwai shegiyar tambayar tsiya, yayinda Nana wasu tambayoyin suke bata haushi, dan ba ta san ta ya zata fara gaya mata ba, lokuta da dama se tai mata mixing our Nigerian English da hausa ta bata amsa (lolz ðŸ¤ðŸ˜‚).
Linda ta kan gayyaci Nana ta zo suje gurin motsa jiki, ko wasannin Nana tace ba zata ba, saboda ba zata iya shiga ba hijjabi ba, kuma ta lura in dai zata fito da hijjabin nan se ta zama abun kallo a gurin su.
Ƙawayen Linda kan kawo mata ziyara ɗakin su, suyi ta kallon Nana, suna mata magana amma tai banza da su sema tace "in ku mayu ne Yakamata ku ƙyaleni haka, se wani kallona kuke kamar an kawo muku buranya, dama ance haka kuke ce mana bururruka, banzaye zabiyai kawai, kuma ai munanan ne daga me ƙaton leɓe se me zanzana da cin zuma a haƙori, masu kyan kawai ake nunawa a TV"
Da yake basu sa me Nana take cewa ba, sedai su bita da ido, ta ƙare musu zagi tsaf ba su san me take cewa ba.
A hankali kuma Nanan ta fara gane turancin, dan har tana iya mayarwa, yadda Lindar zata gane.
Har su kanyi hira koma Linda ta gayyace ta suje suyi karatu a Library.
Sam Linda ba ta nunawa Nana ƙyama, mussaman da taji ance 'yar Afrika ce Nigeria ta na son Sanin abubuwa da yawa a game da Afrika especially Nigeria, shiyasa take yawan yiwa Nana tambayoyi, duk da Nanan ba bata amsa take ba.
Abubuwa da dama na bawa mamaki game da rayuwar yaran turawa, ko laifi su kayi ba a fiye tsawatar musu ba.