Sashe 36
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kut uban kuturu ma yayi kaɗan wallahi, kai ka isa? Ni zaka kalli idona kace in share maka ɗaki saboda tsaurin ido to wall... Bata ƙarasa ba taga Sadik yai ball da robar wanke wanken gaban ta, kwanukan sun watse.
Saroro tai tana binsa da kallo tare da mamakin jarabar Sadik.
Da yatsansa ya nuna ta yace "idan kika kuskura kika min rashin kunya, yadda nai da kwanukan nan haka zan miki"
Aikuwa ta miƙe zata fara zazzaga masa bala'i itama, taji gyaran muryar Hakimi, hakan ya tilasata mata haɗiye maganganun da suke cinta, take so tai amansu.
Hakimi yace"In kin gama wanke wanken, ki share masa É—akin ai yayanki ne gaba yake da ke, kuma ya isa dake"
Seda Nana ta buɗe baki dan mamaki, ita ce ma zata sharewa wannan fitinannan ɗaki, shiru tai ta fara tattara kayan wanke wanken, tana jin yadda ranta ke mata ƙuna, tare da ƙudurce ramuwar gayya.
Se da ta gama wanke wanken, Sannan ta tafi yin sharar, ta tarar da shi ya barbaje ƙafafuwansa a tsakar ɗakin, ya Ajiye pillow a ƙasa ya kashingiɗa.
Ba ta ko kula shi ba, ta hau shararta facar facar, facar tana watsa masa datti a jiki.
"Ke Mahaukaciya! Ba kya gani nee?"
Ba ta ko saurare shi ba, ta cigaba da abunda take, tana watsa masa shara a jiki Sam Sadik baya son ƙura, dan haka ba shiri ya fita ya bata Guri ta cigaba da sharar tana ƙunƙuni.
Ya zamana kusan kullum se sunyi faÉ—a, da abun nasa ya lafa amma yanzu kamar kaji, ko wasu abokan gaba haka suke yi.
Da ne Inna take shiga ta tsawatar musu, amma yanzu kam ta ƙyale su. In zasu kashe kansu ko a jikinta, suyi tayi, sedai in ta gaji ta ƙarewa Nana zagi.
Lilly ta rasa ta in da zata ɓullowa lamarin da ke tsakanin ta da Nazir, Sosai take sake jinsa a ranta, kuma ba iya Soyayyarsa ce ke damunta ba, har da muradin sake kasancewa da shi.
Abu kamar wasa ko Abinci da baccin kirki suka gagari Lilly, kamar yadda take karantawa a Novels, haka ta auri shan Lipton da lemon tsami, dan samawa kanta rangwame.
Abun ya fara damunta psychologically, gaba ɗaya ta koma wata irin shiru shiru, kusan kullum ta na ɗaki, se in waya take da Nazir, shine take rage damuwa, shima kasamcewar ita kaɗaice a ɗakinta, wasu lokutan wayar tasu ta kan zarce ƙa'idar Addini, su shiga wani fage daban.
Kusan kullum se ya tambayeta, ya ake ciki tai maganar Aurensu kuwa a gidan su, amma tace a'a ita tsoro take ji.
Yau da ita da Mamanta da Daddynta kasancewar yana gida hutu, suna Dinner da daddare, amma sam ya lura da yadda ba ta iya cin Abinci, se juya cokali da take, tai shiru tana zancen zuci.
"Hey what are you thinking of?"
Maganar mahaifinta ce ta dawo da ita daga tunanin da take, firgigit ta kalleshi tace "Nothing"
Yace "No, akwai wani abu, ba kiga yadda ta rame ba? Gaba É—aya kamar bata walwala" yai maganar yana kallon maman Lilly.
Tace "Na gani wallahi, i even ask her tace min bakomai, shiyasa na ƙyaleta kawai.
Yace "ko dai haryanzu jikin ne?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
Yace "to meke damunki, Gayamin kinji Babyn Daddy"
Ji tai kamar ta gaya masa, amma yai mata wani irin kwarjini da ta kasa ko É—aga ido ta kalleshi, tace "bakomai fa Daddy"
Yace "oya, maza É—auki Abinci ki ci, ko in baki da kaina ne?"
Ta girgiza kai tace "zan ci da kaina Daddy"
Yace "oya maza É—au spoon ki ci ina kallon ki"
Haka nam ta É—au cokali tana cin Abincin, ba dan tana jin daÉ—in sa ba.
Farhan tunda su kai wayar nan ta ƙarshe da Sadik, ba su sake waya ba, ta kira wayarsa in ta shiga ma baya ɗagawa, jikinta gaba ɗaya yayi sanyi da lamarin, ga lokacin da za a kawo kuɗin Auren ta da Sunusi se ƙaratowa yake yi.
Ta rame tayi duhu, amma hakan be sa Ummanta saurararta ba balle taji abunda yake damunta ba.
Duk da lokuta da dama ko Abinci aka bar mata a Kitchen haka za'aje a tarar da shi ba ta ci ba, in kuma ita ta girka haka zata raba ga bawa kowa, amma ita ba zata ci ba, dan ɗaci Abincin yake mata a baki, mussaman idan yaje maƙogwaronta.
Wata irin matsananciyar soyayyar sa ce take cigaba da nuƙurƙusa zuciyarta, mussaman lokuta masu hatsari da suka faru a rayuwar soyayyar su, her first kiss with Sadik, his romantic actions towards her, how supportive and protective he is, wata karaya ce ta sake baibaye Farhan, da tunanin idan ta rasa Sadik waye ze maye mata gurbinsa, Sadik ya koyar da ita abubuwa masu ruɗani, da tsayawa a zuciya, ba ta tunanin za ta so wani kamarsa.
Sadik ya cire layikan wayoyinsa gaba ɗaya, ya ƙulle su ya saka a ƙarƙashin kilisan ɗakin, dan sam baya son wani ma ya kirashi a waya, sam ji yake wayoyin ma sun fita daga ransa, yaita ƙoƙarin tuna wani abu, amma ya kasa se dai ya haƙura.
Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana, yana kwance yai rigingine, kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fito ya nufi turakar Hakimi, abun mamaki yana zuwa ya tarar da Abba da Faruk.
Turus yai yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Abba ya kalli Sadik ya ganshi so calm, yai ƙiba yai haske saboda babu yawo, sedai kana kallon fuskar sa kasan a cikin damuwa yake, dan samu babu walwala a tare da shi.
Tsayawa yana binsu da kallo, kamar be sansu ba, in lissafin sa daidai ne, yau watansa uku da kwana Ashirin da biyu kenan a garin nan, ba tare da ya ga wani daga gidan su ba, kuma ba tare da ya saka ƙafarsa a waje ba.
Abba yace "to ba zaka ƙaraso ciki mu gaisa ba kenan?"
Jiki a sanyaye Sadik ya shiga É—akin ya zauna a kusa da Abba, amma be ce Komai ba.
Faruk ya taɓa shi yace "meye hakan kake yi kamar wani ƙaramin Yaro?"
Ɗagowar da Sadik ze yi sega hawaye a fuskar sa, take Abba yaji yana neman ya karaya, wani tausayin Sadik ya shige shi, ya san zaman ƙauye baze zama abu me sauƙi ga Sadik ba, tunda tun haihuwar sa a cikin gata yake, amma an ajiye shi a nan tsawon kwanaki ba tare da ganin kowa daga gida ba.
Cikin dakiya Abba yace "meye kuma na kukan? Sekace wani ƙaramin Yaro?"
Faruk ne ya rungume Sadik a jikinsa, yana duddukan bayansa alamar rarrashi yace "we Miss You Brother"
Sadik yace "don't lie to me, you don't Miss me at all"
"Who told you so? Zo muje waje kaji"
Sadik ya yunƙura ze tashi, amma Hakimi yace "Uban naka ma ba zaka gaishe shi ba?"
Ya kalli Abba yana son yai Magana, amma ya kasa se kuka.
Abba yace "Ranka ya daɗe ƙyaleshi ma gaisa an jima"
Faruk ya ja hannunsa suka fita daga turakar, Inna ta taɓe baki, banda sangarta kamar Sadik ya zauna yana wannan uban kuka haka kamar wani ɗan yaye.
Hakimi ya maida hankalinsa kan Abba yace 'Amma Bawan Allah, nace ya batun tafiyar Yaron nan nemx
Abba yace "muna ta shiri ranka ya daÉ—e, nan da abunda be fi sati uku ba insha Allah ze tafi, ana ta shirye shirye"
Hakimi yace "yayi kyau, abunda nake so da kai shine, a sati ukun nan ina son a nemawa 'yar uwarsa Makaranta a inda ze karatu"
Abba yace "Nana?"
"Eh ita"
Abba yace "Amma ranka ya daɗe, ai shi jami'a ze shiga ita kuma tana aji biyu a ƙaramar Sakandire"
"Eh, ai ba a jami'ar nake nufi ba, Makaranta nake son a sakata daidai da karatunta"
Inna tace "Amma Allah ya baka yawan rai, Nanan za'a kai turai karatu a wannan shekarun nata?"
Hakimi yace "haka nace, umarni nake bayarwa ba shawara ba"
Abba yace "shikenan, ai hakan baze gagara ba, insh Allah za'a nema mata"
Gaba ɗaya kan Inna ya kulle, me Hakimi yake nufi da yin haka? Wannan wane irin hukunci ne? Yarinyar da ke kan ganiyar tashen balaga ita za'a kai ƙasar waje karatu? To waye ze kula da ita a can?'
Sadik kam Faruk ne ke ta rarrashin sa, Sadik yace "Yanzu meyasa baku taho min da Mother ba? Shikenan an tsaneni an kawoni nan an ajiye kamar wani ɓarawo?"
"Kayi haƙuri Sadik, yama za'ai ace ba'a sonka, Abba ne yace Mother ba zata biyo mu ba, amma ita ma tayi kewarka sosai, kai kasan kukan da tai saboda an bar mata kai a nan, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe Insha Allah"
"Amma tare zamu tafi ko?"
Faruk yace "wallahi ban sani ba, amma bari muga zuwa mu tafi me zece"
Shi kansa Faruk yai mamakin yadda Sadik ya zama wani shiru shiru.
A hankali ya dinga É—aukar Sadik da hira, har Sadik ya manta da damuwar da yake ciki suka cigaba da hira.
Sedai ga mamakin Sadik yaji Abba yace Faruk ya tashi su tafi, gaba É—aya zuwansu basu fi awa É—aya da rabi ba zasu tafi.
Sadik yace "Abba ni fa?"
"Ban da kai Sadik, a nan zamu barka se lokacin tafiyar ka tukuna"
"Abba saboda me?"
"Saboda haka nace" Abba ya bashi amsa.
"Abba yanzu ma tafiya za kai ka barni?"
"Eh, zama guri ɗaya yasa ka nutsu ka ƙara kyau"
Sadik bece komai ba ya juya ya tafi ɗakinsa ya rufo ƙofa.
Gaba É—aya jikin Faruk yai sanyi, shi kansa Abba ba haka ya so ba, amma ba yadda ya iya.
Hakimi yace "Bawan Allah, ko baka faɗa ba, nasan zuciyarka da ta matarka babu daɗi na riƙe muku ɗa, amma banyi hakan dan muzguna muku ba, duk abunda kaga inayi da dalili nake yi, wanda base na zauna ina faɗar dalilin ba idan na isa, dan haka in anje gida a bata haƙuri, muna ɗaukar matakin da ya dace ne, Allah ya kiyaye hanya"
Abba yace "babu wani dalili da ze sa ayi abunda za'a cutarmu, muna godiya duk matakin da aka É—auka akanmu daidai ne, kai da kaya ai mallakar wuya ne"
Hakimi yace "hakane, Allah yayi albarka"