Sashe 47
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe ɗaya suka isa Airport, kasancewar jirgin ƙarfe biyu zasu hau, ya sa suka tsaya su kai salla, suka ci Abinci banda Nana da tabi ta takura kanta.
Ƙarfe biyu jirgin su ya ɗaga, sedai Sadik yana ji a jikinsa ya bar wani abu me matuƙar kusanci da shi a Nigeria, amma ya kasa tuna ko menene.
Nana na kusa da kujerar Abba, Sadik kuma na ta bayansu, sam Abba yaƙi kula Sadik a Abunda Abban be taɓa yi ba, ya share Sadik tsawon kwanaki ba tare da ya kulashi ba, komai girman laifin da yai kuwa.
Abun duniya ya addabi Farhan, Rana zafi inuwa ƙuna, Umma ta ƙara watsi da lamuran Farhan fiye da da.
Hajiya ta shigo sake duba Farhan a gida, tana ta tsokanar ta wai babanta yace ta duba masa idan ta fara ƙiba.
Hajiya tace "Umman Farhan, wai ni ko dai haryanzu jikin ne na Farhan, naga duk ta ƙara zubewa bayan fitowar ta daga Asibiti, ta rame sosai tayi duhu"
Umma tace "A'a ai taji sauƙi sosai"
"Ai ni na ga ramar tayi yawa ne, yarinya me garin jiki tubarakallah amma duk tabi ta rame, ni gani nai kusan har gara tana Asibiti, amma yanzu ta rame sosai"
Umma tace "kuma kimga ta na shan magungunan ta"
"Hakane, to Allah ya ƙara Afuwa"
Nan Umma ta ku ma yiwa Hajiya godiya sosai, sannan Hajiya ta tafi.
Farhan kam ta yanke shawarar komawa Makaranta ko ba ta gama jin sauƙi ba, dan da ta cigaba da zama tana ganin ɓacin rai a fuskar Umman nata, gara ta koma Makaranta ta dinga tafiyar da mafi yawan lokacimta a can, ta samu ta dinga rage zafi.
Su Nana an sauka lafiya, sedai tun daga airport ta ga akwai banbanci tsakanin gida Nigeria da ƙasashen ƙetare, ba karonta na farko kenan ba da hawa jirgi, an taɓa zuwa da ita umara tana yarinya sosai, tana da burin sake hawan jirgi, amma da yake ba daɗi ne ya hau da ita jirgin ba, ko murna ba tayi da hakam.
Ko ina fitule ne a birnin kamar rana, saɓanin gida Nigeria, wani gurin da haske wani kuma babu.
Wani baƙin Bature ne ya zo da mota, ya ɗauke su daga airport ɗin.
Da alama sun san juna da Abba, dan suna haÉ—uwa suka gaisa, suka fara hira, Sadik ya gaishe shi, Nana kuwa tai shiru tana kallonsu, dan yadda Abban ya jiya harshe yana turanci shima Kamar Bature.
Wani gida mutumin ya kaisu, sedai gidan girmansa yayi yawa, ga mutane burjik a gidan suna shiga suna fita, wannan motar ta shiga wannan ta fita, a taƙaice dai Hotel ne, da yake Nana ba ta san ya abun yake ba ta ɗauka gida ne.
Wani É—aki suka shiga, falo da bedroom biyu, Abba yaiwa Nana umarni da ta shiga É—aya daga É—akunan, shi da Sadik kuma suka shiga É—aya, Mutumin nan yai musu Sallama ya tafi, har Abinci duk an samar a É—akin.
Suka fara rama salloli ta hanyar yin ƙasaru, Abba ya sa Nana a gaba taci Abinci sosai, ko ta kan Sadik ba ya bi da Nana yafi damuwa.
Bayan ta gama ci ya kalleta yace "to Nana, gobe in Allah ya kaimu da safe, zanje in kai ki Makarantar ku, a in da zaki zauna, ina me miki Nasiha da kiji tsoron Allah, na san ke me Addini ce ki kula da kanki, kiyi karatun ki, karki wasa da Addini ko kuma al'adar ki, sannan kiyi taka tsantsan kibi dokokin su, kin san nan ba Nigeria ba ce.
Ki nutus kiyi karatu da kyau kinji 'yar gidan Inna, duk abunda kike buƙata akwai in da zakije ki faɗa a makarantar za'a kirani a waya muyi magana, in munje duk za'a nuna miki Insha Allah, ni dai fatana kiyi karatu da kyau kinji?"
Nana tace "to zanyi in Allah ya yadda"
"Yawwa Allah yai miki Albarka, maza tashi kije ki kwanta"
Nana ta tashi jiki ba ƙwari ta shiga ɗakin, sedai ita gaba ɗaya ɗakin tsoro yake bata, ba ta tunanin zata iya kwana a ɗakin ita kaɗai.
Sadik yai shiru yana kallon Abba, yana tunanin wane irin zafi Abban ya É—auka haka?
"Lafiya kake kallona?" Abba ya tambayi Sadik.
"Abba, dan Allah ka dena fushin nan da ni, ba na jin daɗi wallahi, baka taɓa yi min haka ba"
Abba yai murmushi yace "kai harka damu da fushi na Sadik? Ni da ko gaisheni ka dena saboda uwarka ta na ziga ka, Ni Sadik ku ka sa yi min alfarma in bi nawa iyayen sannan kuce kuna son cigaba da Ganin walwala ta, duk abunda kuke shiryawa da ita na sani ƙyale ku kawai nake.
Idan ka wulaƙanta Yarinyar nan ni ka wulaƙanta ka nunawa Duniya ban isa da kai ba, amma ka sani yadda wannan Auren igiyarsa take a hannunka yin wasa da shi, tamkar wasa da igiyar Auren mahaifiyar ka ne da ke hannuna, dan da iyaye na kuka sameni ba zan zaɓe ku a kansu ba!"
Gaban Sadik yai mummuna faɗuwa, be taɓa zaton haka daga Abbansa ba, Lallai Abba da gaske yake, amma ya san Abba faɗa yake ba ze taɓa iya sakin Mother ba, Komai ze biyo baya za suyi settling daga baya, Amma ba ze taɓa zama da Nana a matsayin matarsa ba dole kowa ya kama gabansa.
Nana ido biyu ta kwana, saboda tsananin tsoro da fargaba, gaba ɗaya ɗakin tsoro yake bata, ƙarshe ta fito falon kan kujera ta kwanta, shima bacci se ɓarawo ne ya ɗauke ta.
Da safe suka shirya suka bar Hotel ɗin, mutumin jiya ya kaisu gidansa, matarsa baturiya ce fara sol, se yaransu uku, biyu farare ɗaya baƙi.
A nan su kai breakfast, sam Nana ba ta gane turancin da suke, da ƙyar take picking wasu kalmomin, a nan suka karya, Abincin na su duk gashi nan ta kasa gane kansa, tea ta iya sha se chips, shima ba sabawa tai da cin irin sa ba.
Suna gama karyawa, Abba yace su tashi su tafi, a zaton Nana Hotel za su koma.
Ashe Makaranta za'a kaita, an gama mata Komai, hatta kayan da zata buƙata an tanadar mada su, aji da ɗaki kawai za'a bata, se 'yan kayan da Abba ya sa ta ɗakko a akwati.
Nan Nana ta tubure ta sa kuka, Mutanen da ko yarensu ba ta ji, ta ina zata iya rayuwa da su, Abba yai ta rarrashin ta yana nata Nasiha, aka bata Uniform da ɗan ƙaramin veil ta saka, saɓanin sauran ɗaliban ma da basa saka hijjabi gaba ɗaya jikinsu a buɗe yake, Nana ta gansu duk farare kamar zabiyai saboda fari.
Kuka sosai Nana ta dinga yi, aka wuce aka kaita aji, ajin akwai farare da baƙaƙe dan akwai wanda suka fi Nanan ma baƙi a ajin, dan tana da hasken fata.
Se da Abba ya tabbatar komai yayi normal, sannan ya tafi shi da Steve, wannan Black É—in. Dama Sadik be bisu ba.
Farhan ta gama shirin Makaranta, ta fito yiwa Abba Sallama, yai mata addu'a ya bata kuÉ—in Makaranta, tana fitowa tsakar gida Umma ta kaalleta tace "Ina zaki haka?"
"Makaranta zani Umma"
"Ai wannan makarantar ma haƙura zaki da ita, tunda Aure zaki ai ba ta da wani Amfani ma a gareki"
Abba yana daga ɗaki yace "A'a, karatu akwai amfani, duk da Aure za tai, ai na gaya masa zata cigaba da Makaranta, ki ƙyaleta ta tafi"
Umma ji tai kamar ta gaya masa abunda ta kama Farhan da shi, Amma tai shiru ta fasa.
Farhan ta na tafe a hanya ta na kuka, kamar wata mara galihu, rana zafi inuwa ƙuna, zuciyarta a cunkushe haka taje makaranta.
Lilly na ganinta tace "Farhan lafiya kuwa kika dena zuwa makaranta?, Da fa yau zanje har gidan ku in ga ko lafiya?"
Farhan tai murmushin yaƙe tace "bani da lafiya ne"
"Eyya, shiyasa duk kin rame sosai wallahi, Allah ya sawwaƙe sannu"
Ta amsa da Ameen.
Kusan duk Malamin da ya shiga ajin in yaga Farhan se ya tambayi ya akai kwana biyu ba ta zuwa, Lilly tace ba ta da lafiya, sukaita mata sannu, dan kallo É—aya za kai mata ka tabattar hakan.
Bayan an fita break ne, taji su Lilly suna hira, wai an kama Mubarak Babba, saboda ta'amalli da kayan maye, anje kame aka kama da shi.
Duk da hakan yayiwa Farhan daÉ—i, ko banza yanzu ba ta da fargaba, amma ita babban abunda ya dameta be wuce son sanin halin da Sadik ke ciki ba.
Ba ta gana yanke shawara ba, ta tashi ta nufi ajin su Sadik, tana jin kamar zata ganshi idan taje.
Sedai ta na zuwa ajin, ta tsaya ta window tana leƙawa, zubawa gurin zamansa ido, in da suke zama yaita damunta yana tsokanar ta, ko ya kwanta ya ɗora ƙafafunsa akan benci yana danna waya.
Wasu irin hawaye ne suka shiga zubowa daga idon ta, tana jin wata wutar ƙaunarsa na sake Ratsa ta.
"Zan wuce" taji an mata Magana.
Da sauri ta waiwayawa, taga Amin ne abokin Sadik.
Ya kalli Farhan yace "Lafiya? Kukan me kike haka?"
Tai saurin share hawayen ta tace "ba kuka nake ba"
"Ba kuka kike ba, wannan hawayen fa?"
Farhan tace "ba kuka nake bax
Yace "shikenan, amma tsayuwar me kike a nan?"
Cikin in da in da tace "da..daa..dama zuwa nayi" se kuma tai shiru.
"Ko akan Sadik kika zo?".
Ko Sannu ba ta haÉ—ata da abikan Sadik, mussaman da ba jituwa suke ba, suna jin haushin ta, amma Da sauri ta É—aga masa kai alamar eh.
Yace "kaddai kice kema ba ya nemanki?"
Ta É—aga masa kai alamar eh.
Yace "Subhanallah, ni dai na san munyi waya, one month back, yace min yana ƙauye kuma in da yake ba service, tun daga nan ban sake jinsa a waya ba"
Farhan tace "Ni yafi wata É—aya ma ban same shi a waya ba"
Amin yace "ki kwantar da hankalinki, insha Allah zan bincika miki, zanje har gidan su inji in da yake, zan zo in gayamiki insha Allah"
Farhan tai murmushi tace "to nagode"
Yace "bakomai jeki aji, ki dena kuka"
Jiki a sanyaye, ta bar ƙofar ajin nasu.