← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 115

Sashe 50

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Naji Muryar ki a shaƙe, ko baki da lafiya ne?"

"A'a" ta bata amsa a taƙaice.

Bayan fitar Adda Maryam, Farhan ta zura hijjabin ta da niyyar tana zuwa, ta huce abunda ke damunta akan Sunusi, sedai tun daga soro ta fara jin ƙamshin turare, tana zuwa ta ga Abbas maimakon Sunusi.

Ya kalleta yai murmushi yace "muje Hajiya ke neman ki dama"

Tace "to bari in faÉ—a a gida"

Ta koma gida ta sanar da Umma, sannan ta fito suka jera da Abbas zuwa gidan Hajiya, ba tare da wani ya furta komai ba.

A kai sa'a akan idon Sunusi suka nufi Gidan Hajiyar sa.

Farhan ta zauna a falon Hajiya, Abbas ma ya nemi guri ya zauna ya kalli Farhan yace "ba Hajiya ce ke kiranki ba, dama ni nake neman ki"

Ta É—ago ta kalleshi ta sunkuyar da kanta.

"Bana son mu tsaya a ƙofar Gidan ku ne, wannan shashashan, sorry in dena zaginsa shi zaki aura, bana son yazo ya samu gaba da masifa shiyasa na janyo ki nan"

"Amma ina Hajiyar?"

Yai murmushi yace "Hajiya tana nan, tana É—akinta tana salla, na gaya mata zanje in taho da ke muyi Sallama, je ki duba É—akinta in baki yadda tana nan ba"

Ta girgiza kai tace "na yadda"

Ya gyara zama yace "gobe in Allah ya kaimu zan tafi, tafiyar tawa ce nayi ba nayi ba, se yau Allah ya nufa gobe in Allah ya kaimu zan tafi, na zo in sake ganinki ne, sedai haryanzu ba wani cigaba se ramewa kike kuma yi"

Farhan tai shiru ba tace komai ba.

"Farhan, kowane bawa da kika gani a rayuwarsa, da irin ta sa ƙaddarar kiyi haƙuri ki karɓi taki, tun ranar da na fara ganinki zuwa haɗuwar mu ta ƙarshe, da naga wanda zaki aura, naji ina matuƙar tausayinki, kina cikin hatsari Sosai da sosai sedai dan Allah duk abunda ze faru, You have to maintain your diginity, kar kije garin nemawa kanki mafita ki faɗa wata hanyar daban kiyi haƙuri"

Farhan bata gama gane inda maganganun Abbas suka nufa ba, ita dai tana jinsa ne kawai.

Tana cikin nazarin maganganun sa taji ya riƙo hannunta cikin hanzari ta kalleshi, a hankali tai ƙoƙarin zame hannunta amma taji ya riƙe gam.

Wata irin fargaba ta shige ta, ya kai hannunsa ze cire zoben hannunta, wanda Sadik ne ya bata a lokacin birthday É—in ta.

Da hanzari ta miƙe tace "ka sakarmin hannu tafiya zanyi"

"Nima ba wani abun zan miki ba, ba mutumin banza bane ni, mahaifiyata tana nan, ya za'ai in yi wani mummunan kuskure, nima ina da 'ya'ya, na san irreplaceable Sadik ne ya baki wannan zoben, so I want substitute him from your life".

"Dan Allah ka bari" ta faÉ—a a raunane.

"Ba kya son ki manta da shi ko? Bayan shi ya manta da ke?"

"Be manta dani ba"

"Meyasa zuciyar ki ba ta son Gaskiya ne? Farhan?"

Shiru tai tana goge hawaye da hannu É—aya.

"Shikenan muje in rakaki gida, nasan kan in dawo daga karatu kinyi Aure, ina fatan Allah ya baku zaman lafiya, ina kuma yi miki nasiha akan kiyi haƙuri na bawa Hajiya gift ɗina na Aurenki ta baki, kiyi haƙuri kinji?"

Ta jinjina kai alamar to.

Seda suka fito tsakar gida, sega Hajiya ta fito daga ɗakin ta tace "Farhan, seda yaje ya tattago ki ko? Wa shi me 'ya, salla nake ne, nace in so yake sedai ya haƙura kin zama rabon wani, amma na kasa gane inda ya dosa, wai ai ke 'yarsa ce"

Abbas yace "Hajiya kenan, bari in rakata gida"

"To shikenan, ki gaida Ummanki"

Farhan tace "to zan gayamata insha Allah seda safe"

Suna fitowa daga gate ɗin gidan su Abbas, suka ga Sunusi da wasu abokansa a ƙofar Gidan yace "kun gani ko? Yanzu kun yadda da abunda na gaya maku? Sun kusa awa guda cikin gidan nan, daga ita se shi ba kowa a gidan, yanzu da nai magana ace sharri nake mata.

Haladu ne yace "haba Sunusi, ya za ka dinga zargin matar da zaka aura? Baka da tabbas fa akan maganar da kake"

"Kamar ya bani da tabbas? A gaban idona fa ta fito daga gida, suka shiga gidan nan tare, saboda sheda shiyasa na kiraku"

Abbas ya kalli Farhan yace "muje"

Hawaye wani na bin wani ta cewa Abbas "kalli irin mutumin da zan aura? Kullum ƙoƙari yake yabi diddigi na ya wulaƙanta ni, Hajiya fa tana cikin gidan nan amma kalli abunda ya tara mutane yake faɗa"

Abbas ne kaÉ—ai yake iya jin me take faÉ—a.

Yace "bakomai, ki barwa Allah, muje kawai"

Har ƙofar gida ya raka Farhan, yayin da Sunusi ke ta zazzaga bala'i.

Farhan na shiga gida, gurin Abba ta shiga tana kuka, hankali a tashe yace "Lafiya kukan me kike haka?"

"Abba Sunusi ne"

"Me Sunusin yai miki?"

Nan ta kwashe Abinda ya faru ta gaya masa, Abune mawuyaci Farhan ta kai ƙara tace gashi an mata laifi, ko lokacin yarinta sosai, ba ta zuwa ta kawo ƙara duk girman laifin da akai mata ko cutarwa kuwa.
Shi kansa Abba yaji babu daÉ—i abun da Sunusin yai, dan haka yace "ki dena kuka, tashi ki tafi É—akinki zan masa Magana"

Farhan ta tashi ta fita tana kuka.

Aikuwa tana shiga ɗaki aka turo ana sallama da Abba, Abba ya miƙe ya fita yana zuwa ya tarar da Malam Labaran da kuma Sunusi.

Abba suka gaisa da su, Sannan Malam Labaran yace "to ina zaune Sunusi ya zo min da wata Magana akan matarsa, to nace ban sani ba ko kana da masaniya a kai"

Abba yace "Malam Labaran, girma da mutuncinka na gani ya sa zan bawa Sunusi yarinyar nan, da kuma nustuwar sa da addininsa da yadda yake girmama mutane, daga fara neman Auren nan zuwa yanzu ba zan iya faɗar adadin sau nawa ya kawo min ƙarar ta ba, shi fa lamarin Aure ɗan haƙuri ne, yarinyar nan baka Aureta ba tukuna dole wataran samari zasu biyo ta tun da yanzu take kan ganiyar ƙuruciya yanzu take girma, idan ka kawo min ƙararta ina ɗaukar mataki bata taɓa nuna damuwarta akan haka ba, ba fa dan bana sonta nake mata haka ba, yau da bakinta ta kawomin ƙarar ka akan abinda kai mata, ka tara mutane a waje kace wai ta keɓe da namiji a cikin gida, ƙaddara ma hakane ai kai me rufa mata Asiri ne,balle seda ta shigo ta faɗa a cikin gida, Hajiya ta turo ɗanta wane tace taje tana nemanta, ba'a Aure da zargi fa in ka san kana zarginta to a haƙura da lamarin nan kawai"

Da sauri Malam Labaran yace "A'a ba za ai haka ba, dan Allah ayi haƙuri insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, kai kuma Sunusi kar ka sake haka, zaka ɓata mata suna a unguwa, ba a haka baka kyauta ba"

Cikin ikon Allah suna cikin maganar sega Hajiya da Abbas, ta ƙara so suka gaisa da su Abba Sannan ta kalli Abba tace "Malam Ali banji daɗin abunda ya faru yanzu ba, Ina cikin gidan da izini na Abbas ya kira Farhan, ba zan taɓa bari ayi ɓarna a gaban idona ba, saboda nima ina da baya, Abbas shine likitan da ya duba Farhan, ze tafiya ƙaro karatu, yace min yana son suyi sallama, ya kuma bata abunda ze bata ance za tai Aure, amma an tara min jama'a a ƙofar gida wai ɗana ya keɓe da 'yar wajenka a cikin gida ne, wanda maganar ba haka take ba"

Abba yace "dan Allah kiyi haƙuri, kinga yanzu haka zancen da muke kenan"

Nan suka taru suka ƙarewa Sunusi ta tas, suka nuna masa ba a haka.

Abbas yace "wallahi ba dan Hajiya ta sa baki ba, se nayi karar Yaron nan hukuma tabi min haƙƙina na yunƙurin ɓatamin suna da yai"

Sukai ta bawa Abbas haƙuri sanann suka bar gurin.

Sunusi be taɓa zaton Abba ze iya iƙrarin hana shi Farhan ba, yaji Abba ya fara cewa ai yanzu take girma dole samari su biyota, dan haka ya fara tunanin abunda ze yi wanda ze hana faruwar hakan.

Maganar Kamar wutar daji, a daren Magana ta fara bazuwa wai an kama Farhan da Abbas a gidan su, alhalin da kuÉ—in Auren wani a kanta.

Baiwar Allah sam Farhan ba ta san meke faruwa ba, ita abunda ya dameta kadai take tunanin mafita a kai.

Amin yana kwance yana duba waya, ya shiga IG yai posting hotunan sa na friday, daga nan ya cigaba da kallon hotuna.
Yana shirin ya rufe datar yai karatu, kasancewar jarrabawar WAEC na ƙaratowa, kawai yaci karo da hoton Sadik a gym tare da turawa wata baturiya ta ɗora tare da caption of "ma hottest mate dude"

Da sauri ya tashi zaune, ya cigaba da duba hotunan tabbas Sadik ne, kuma wannan hotunan na kwanan nan ne, kenan Sadik ya tafi karatu ba tare da yayi wa kowa sallama ba, kuma ya kashe wayoyin sa gaba É—aya, to meyasa yai haka sekace wanda ba shi da gaskiya.

Da sauri yai screenshots É—in hotunan, ya tura group É—in su na whats app na 'yan ajin su, nan da nan suka fara Sharhi wasu suka ce suka sun gani.

Sunyi mamakin yadda Sadik yai tafiya haka ba labari.

Washegari a school, su Nas da sauran 'yan ajinsu ma, haka suka ci-gaba da tattauna batun tafiyar Sadik ba labari.

Har ajinsu Farhan Amin yaje, ya tarar da ita tai shiru ta zubawa 'yan ajinsu ido, suna ta hirarsu, suna sha'aninsu banda ita da se kallonsu kawai da take.

"Sannu dai" Amin ya faÉ—a yana zama.

Farhan ta kalleshi tace "yawa sannu"

Amin yace "na zo da labari ne, wanda ban san ya zaki ɗauki abun ba, amma koma dai ya ne ki ɗauki lamarin da sauƙi. Jiya na ci karo da hotunan Sadik a Instagram, da alama ya tafi karatu ne, dan a cikin turawa naga hotunan nasa, hakan na nufin ya tafi karatu ne"

Farhan tai murmushi tace "shikenan, tunda yana lafiya Alhamdilillah, Nagode sosai"

Amin ya dinga binta da ido, dan ganin reaction É—in ta amma ya kasa gano halin da take ciki.
Chapter 50 · 0% Book details