Sashe 24
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai daga zuwa duba mahaifinsa a ƙauye, ya ɗaukar min Sadik ya tafi da shi, wai se dawomin yai daga shi se Faruk kawai, wai ya baro shi a can"
"Kamar ya ya baro shi a can?"
"Wai kakanninsa ne sukace a barshi a can, saboda yana nuna wa garin ƙyama, tsakani da Allah an min adalci kenan, inyi magana ace bani da haƙuri, ta yaya Sadik ze iya zama a garin nan fisabilillahi? Tsabar abu kuma ina masa magana ya tafi part ɗinsa ya rufe ɗakinsa"
Mummy tace "Subhanallah, ai riƙon mahaukaci se sarki, waze iya riƙe wannan yaron naki ɗan hutu in ba ke ba, Sadii baya son wahala da takura, gaskiya ba'ai miki adalci ba, amma karki ce zaki matsa ki bi Komai a hankali, kiyi ta lallaɓa shi har ya ɗakko miki ɗanki, kar kice zaki fushi kin san zaki kuma janyowa kanki matsala ne, dan haka kiyi haƙuri na san ba'a kyauta miki ba"
Mother tace "shikenan Yanzu a can ze kwana? Wannan wane irin abu ne, ni na san halin kayana wahala ze sha a garin nan wallahi be saba ba"
"Na sani Hauwa'u, amma dai kiyi haƙuri dama kin san yadda Akuyarki tai kuka a dangin mijinki, dan haka karki ce zaki matsa ki ƙara baƙin jini"
"Wallahi ji nake kamar in É—au mota inje in É—akko shi, sedai ai duk wadda za'ai"
"Ke karki kuskura, garin son ɗa da neman gira ki rasa idanu, shi dai baban nasu zaki cigaba da lallaɓawa"
"Shikenan Mummy, ki gaida su Khairat"
"Bakomai za suji amma ki kwantar da hankalinki".
"Shikenan se an jima" ta katse kiran.
Mummy tace "Ikon Allah, wannan kakannin na su Faruk sun fiye Matsala wallahi"
Khairat dake kusa da Mummy a kwance ta ɗaga kai ta kalleta tace "Wai Mummy Sadik aka kai ƙauye?"
"Wallahi kuwa, baki ji muryar babarsa ba ina ga ma kuka take, kai Allah ya jarrabi Hauwa'u da son 'ya'ya mussaman Sadik"
Khairat tace "gaskiya ba'a kyauta ba, wallahi ze sha wahala ne kawai amma kin san Sadik da son hutu"
"Aikuwa yanzu se ta Allah, wannan ƙasurgumin ƙauye ina ze ga wani hutu".
Wasawasa har la'asar Sadik yana zaune a tsakar gida, ya ƙi cin abinci kuma ya ƙi tashi ya shiga ɗaki, da fari Nana dariya ta dinga yi masa, amma daga bisani kuma se ya fara bata tausayi, ganin har taje ta dawo daga Islamiyya amma yana zaune a tsakar gida, haka kurum rana tsaka a bar mutum a in da be saba zuwa ba, alhalin da uwarsa da ubansa a raye, se taga ba'a kyauta masa ba.
Idanunsa sunyi jawur, saboda tsabagen yunwa ga kuma baƙin taurin kai irin na Sadik.
Aka yi sallar magariba, yai salla a in da yake ya nemi guri ya zauna, aikuwa sauro ya fara ɗawafi a kansa, saura ya fara zagaye baƙar sumarsa, ga yunwa dake sakatar cikin sa kamar ze ci babu.
Nana ta fito daga ɗakin Inna, ta tarar da shi a zaune yana kore sauro da hannunsa, ga network ɗin wayarsa sam yaƙi harbawa.
"Ka taso daga nan ka koma É—akin da kuka kwana jiya, in ba haka ba sauro se ya kusa halaka ka a gurin nan"
Banza yai mata kamar be ji me tace ba, daga ɗaki Inna tace "ke ina ruwanki da shi? Waye yace ki masa Magana se kunzo kuna faɗa ko?, Ki ƙyale shi yai ta zama a gurin, idan saurayen suka gama tsotse masa jini, ya tashi ya bar gurin, ai bari ba shegiya bace da ubanta.
Sadik a ransa yace 'wannan tsohuwar yadda ta tsaneni ba ta ƙi in mutu a gurin nan ba' dan haka ya miƙe ya tafi in da suka kwana jiya ya kunna fitilar wayarsa yana sake haske ɗakin.
Ɗakin ƙasa ne na gaske, an masa sumunti da ƙasa aka kawo farar ƙasa aka shafe ɗakin da shi.
Se wata 'yar taga 'yar ƙut a sama kamar gurin kiwon tattabara, ɗakin ɗauke yake da ƙatuwar katifa da manyan matasai.
Ga shimfiÉ—ar buzu a gurin, wanda akeyi da fatar dabbobi, wanda warinsu kawai damun Sadik yake.
Ya ajiye wayoyinsa akan katifar ya nemi guri ya zauna, yai tagumi yana jin yadda cikinsa ke wata irin juyawa.
Ganin ba kowa a tsakar gida yasa Nana ta nufi É—akin Hakimi.
Ta tarar da shi yana kan sallaya yana jan carbi.
Wata tasa taje ta buÉ—e ta É—ebi gurasa, har zata fita Hakimi yai gyaran murya.
Ta waigo tace "Ci zanyi, yau ba zanci tuwo ba"
Tana gama maganar tai waje, É—akin da Sadik yake ta nufa, tana yi tana waige kar Inna ta kamata, ta É—ebo ruwa a kofin silba ta shiga É—akin.
Ta tarar da Sadik yai uban tagumi, kamar wanda yake jiran wani mummunan saƙo.
Ta dire masa tace "gashi nan in ka ga dama kaci, in baka ga dama ba kai ta zama da yunwa bame lallaɓa ka yace se ka ci, sedai ka mutu da yunwa"
Tana gama maganar ta juya ta fita, yayin da Sadik ko kallonta be ba, ya cigaba da taguminsa.
Wunin nan guda yau be wanka ba, ya nemi guri ya kwanta akan katifar nan, ga tunanin Mother ga na Farhan, ga Faruk É—insa shima yana missing.
Kawai yaji zuciyarsa na raya masa yaiwa tsofaffin nan Allah ya isa, saboda a ganinsa abunda su kai masa zunzurutun zalunci ne, saboda tsabar mugunta a dole se sun azabtar da shi.
Jin sa da yake kamar ze mutu saboda yunwa yasa ya tashi zaune, ya janyo kwanon gurasar nan ya dinga danna ta haka gaya ba miya bakomai.
Ya nayi yana shaƙewa yana korawa da ruwa, gashi ta fara bushewa, se yayi kokawa da ƙyar take haɗiyuwa, kamar yana cin takadda.
Be tsaya duba wane irin ruwa bane, haka ya sha ruwan nan dan samawa kansa mafita.
Da ya gama ci saboda tsabar takaici yai cilli da kwanukan a tsakar É—akin yana huci.
Ya hau kan katifar ya kwanta, zuciyarsa kamar ta tsaga ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki.
Ba wuta, ba fanka ba sanyin AC, É—akin se uban zafi, ga ba fitila se fitilar wayarsa da ya kunna.
'wannan É—aki ko kabari ne se haka' ya furta yana tsaki.
Ya dinga juyi amma ya kasa bacci, saboda ƙaiƙayi da jikinsa ya dinga yi, beyi wanka ba, ga sauro da uban zafi da ya addabe shi.
Tashi yai zaune zaman dirshan, ya rasa abunda ze yi dan yaji daÉ—i.
Farhan kam ta ɗan damu, dan yadda sukai da Sadik a Ranar zasu dawo, amma har yau Lahadi babu message ɗin sa tsawon wuni guda, tun saƙon da ya tura mata cewar a can za su kwana, tai ta kiran wayarsa amma ba ta shiga, haka ta haƙura ta kashe wayar ta maida ita in da take ɓoye ta.
Tsakar dare Sadik ya kasa bacci sam, be san lokacin da hawaye suka fara bin idanunsa ba, hawaye É—aya bayan É—aya.
Tsakar gidan ya fito yana ƙarewa gidan kallo, hasken farin wata ya haske ko ina, kawai se yaga gidan somehow look scary to him, toilet yake son shiga amma tsoro da fargaba suka hana shi hakan.
Inna da take salla taji motsi a tsakar gida, ta É—aga labule, taga yadda Sadik yake tsaye yana rarraba ido.
"Me kake a nan gurin?" Maganar da Inna tai seda Sadik ya kusa zurawa da gudu, saboda jin maganar yai from no where.
Se da ga baya ya fuskanci Inna ce, ya tsuke fuska yace "wanka zan na kasa bacci"
"Wanka a tsohon daren nan, maza cigaba da tsaiwa a gurin kar kaje ka kwanta, akwai mayu idan suka fito suka lashe ka shikenan"
Zare ido Sadik yai, be san takamaimai meye maita ba, amma dai yasan tabbas maita wani abune nau'i na tsoro, aikuwa cikin hanzari ya kwasa da sauri ya koma É—akin da yake.
Inna ta saki labule tace "ba dai kace kai baka ji ba, zaka ga tsiya ai ja'iri"
Sadik sosai ya dinga kuka, kamar ƙaramin yaro me shan nono.
Se wajen Asuba sannan bacci ya saci Sadik, Asubar fari aka zo aka tashe shi, yai Alwala zuwa masallacin cikin gidan Hakimi.
Yana shirin ya miƙe yaje ya samu ya kwanta ya koma bacci, saboda rashin baccin da be samu ba jiya.
Aka ce ba in da za shi za'a zauna karatun Alqur'ani.
Aka rarraba Alqur'ani, amma Sadik ya ajiye nasa yace ko yayi ba lada dan be niyya ba, saboda haka baze ba.
Ana ta karatun Alkur'ani, ya jingina da bango yana baccinsa, baccinsa ya fara nisa yaji an tsula masa carbi a ƙafa, ya buɗe ido a gigice.
Wani dogari yace "ka buÉ—e idonka ka dena mana bacci"
Tsaki Sadik yai, dan yaji zafin dukan carbin nan, dan se yace Allah ya isa.
Haka Sadik ya zauna yai zuru yana rarraba ido.
Mother kam baccin dare gagarar ta yayi, saboda tunanin halin da É—anta yake ciki, ta san babu Lallai Sadik ya iya bacci a wannan garin, yadda ta ga dare haka taga rana, zuciyarta cike da tunani da tausayin É—anta.
Se kusan ƙarfe bakwai na safe aka tashi daga wannan karatun, Sadik ya tashi idonsa har mannewa yake saboda tsabar baccin da yake ji.
A tsakar gida ya tarar da Inna da Nana, ba wanda ya gaisar ko ya kula a cikinsu ya wuce É—akin da ya kwana.
Ya haye kan katifa ya fara bacci, ƙafarsa na ta zugin dukan da aka masa da carbi.
Ji yai an watsa masa ruwa, ya tashi firgigit.
"Ka taso ana kiran ka" a hankali ya ƙarewa Nana kallo da take tsaye a kansa da kofin ruwa.
A fusace yace "ke wace irin dabba ce zaki watsamin ruwa haka?"
"Cewa a kai in tashe ka, kuma ahir É—in ka da sake zagina"
Juyawa yai akan katifar ze cigaba da bacci, yaji muryar Inna a kansa "zaka fito ne ko se an sa an fito da kai mara Kunya"
Tashi yai yana kumbura baki ya fita tsakar gida yana tunanin wannan wane irin abu ne haka?"
A tsakar gida ya ga An shimfiɗawa Hakimi dadduma, yana kashingiɗe, gefensa ga wasu dogarai guda biyu riƙe da bulalai, Sadik ya nemi guri ya zauna yana tura baki.
Hakimi ya kalleshi yace 'ina kwana?"