Sashe 75
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar Abba da ta ji a ƙofar ɗakinta, ya sa ta dawo hayyacinta, ta amsa masa tare da gyara zamanta.
Abba ya shiga É—akin, ba tare da ya kalleta ba yace "nace a cikin manemanki wa kika turo gurina?"
Farhan ta kalli Abba tace "Abba ni ban turo maka kowa ba"
Yace "wani mutum yazo gurina, neman Aurenki, kuma da alamu mutumin kirki ne da gaske yake"
Farhan tace "Abba ban turo kowa ba gaskiya, kuma ni gaskiya Abba bana buƙatar yin Aure a yanzu"
Abba ya dubi Farhan yace "se zuwa Yaushe? Haka zaki cigaba da zama kina zubar min da mutunci a unguwa? Wannan yazo gurinki anjima wancan yazo, in ta raya miki ki bar gida ki kwanaki a waje, kina min adalci kenan?"
Farhan ta miƙe, ta dawo gaban Abba tace "Abbana, da zan tona maka zuciyata na san zaka tausaya min, kai kaɗai kake jin tausayi na, tunda Allah ya saukar min da ƙaddarar nan, ba ka taɓa buɗe baki ka aibata ni ba, saɓanin uwar da ta kawo ni duniya.
Abba ka sani, babu mutumin kirkin da ze bari É—ansa ya Aure ni, na sauka daga turbar da ka É—orani, na kama wani layi na daban, amma Abba kasani Addu'ar ka tana tasiri a kaina.
Bayan suna na da ya ɓaci a unguwar nan, duk wani mutumin kirki da ya zo neman Aurena, se an hana shi, kuma ba kowa ke min haka ba se Sunusi, ya hana kowa zuwa gurina. Duk wanda suke zuwa gurina ba Mutanen kirki bane ba".
Ta kamo hannnun Abba cikin na ta tace "dan girman Allah Abba kar kai min baki, kar kai min mummunar Addu'a, na sani zuciyarka na cike da takaicin lalacewa ta, Amma dan Allah Abba kar kai min baki, ka cigaba da yi min Addu'a, dan Allah kar ka tsaneni Abba, na rasa soyayyar uwa tun da ƙuruciya, dan Allah kaima kar in rasa taka.
Nasan ina ɓata maka rai, amma kar in mutu kana fushi da ni, Abba dan Allah kayi Magana".
Ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka me ban tausayi.
Abba kasa Magana yai, se hawaye da ke bin fuskarsa, ya ɗora hannunsa akan Farahan yace "Allah yai miki Albarka, Allah ya shirye min ke, da dukkan 'ya'yan musulmi, na ɗau wannan abu a matsayin ƙaddara, dan haka zan cigaba da yi miki Addu'a insha Allah"
Yana gama Maganar, ya fice daga É—akin nata, yana share hawayen dake bin fuskarsa.
Nana ce kwance a ƙasa, se juyu kawai take yi, ta rasa abunda yake mata daɗi, ita ba zafi take ji ba ita ba sanyi ba, ita dai gata nan gaba ɗaya zaman ƙasar nan ya isheta, shekara ɗaya da wani abu kenan, tana zaune a London, ba tare da taje gida ba, dan haka komai ma ya isheta.
A haka Sadik ya dawo daga Makaranta ya tarar da ita, se cika take tana batsewa.
Ya kalleta yace "Ikon Allah, yau kuma lafiya kike fushi ke kaÉ—ai?"
Ai yana rufe bakinsa se hawaye "Ni wallahi na gaji da zaman garin nan, haba dan Allah ai ko sau É—aya Yakamata in je in ga gida, amma in ayi hutu ma sedai in zauna a nan gaskiya ni na gaji"
"To yanzu ya kike so ayi?"
Tace "Ni ka gayawa in Abba in anyi hutu dan Allah ya bani dama in koma Nigeria in huta, wallahi na gaji"
Ya kalleta yace "in kunyi hutu, ni kuma ai lokacin ba muyi ba"
Ta kalleshi tace "to kai ba se ka zauna ba, ni wallahi na gaji, idan hutun ya ƙare na dawo, kai ba se ka zauna a nan ɗin ba"
Sadik yai murmushi, ya zauna a kusa da ita, ya rungumeta a jikinsa, yana kwantar da kansa a wuyanta, yai ƙasa da muryar sa yace "an kawoki ƙasar nan ki karatu ne, saboda kar in lalace kuma seki tafi ki barni, ba kya tsoron in lalace ko?"
Nana ta tura baki tace "Lalacewa ta nawa kuma? Tun da nima ban sha ba, ni kawai gida zan koma"
Sadik yace "to ba zaki koma ba, wa ze dinga kula da ni da min sauran ayyukan gida?"
"Kayi da kanka mana"
Sadik yace "Shikenan, tun da hakane, ki koma in ya so se a kawomin Khairat ta dinga kula da ni"
"Abunda yafi Khairat za'a kawo maka, É—agani"
"To meye kuma na fushi, bayan ke kika ce zaki tafi"
"To na fasa" ta faÉ—a tana murguÉ—a baki.
Yace "Aikuwa se kin tafi, dama duk kin isheni, rigimammiya Kawai"
"Ba zan tafi É—in ba" tai maganar tana share hawayen fuskarta.
Yai murmushi Sannan Yace "Stop crying, zamu je hutu insha Allah, ni kaina ina son zuwa Nigeria, ji nake akwai wani mahimmin abu da Yakamata in yi, amma na manta menene, amma zamuje tun da haka kike so"
Nana tai murmushi, tare da kwantar da kanta a na, Sadik da ke kafaÉ—arta.
Shiru ya É—an gudana a tsakanin su, sannan Sadik yace "ke ya naji Kamar jikin ki na É—aukar zafi ne?"
Nana tace "Wallahi nima ban sani ba, haka nan se in dinga jin sanyi sosai, se kuma zazzaɓi, se kuma anjima ya sauka"
"Kuma ba ki gayamin ba, se ya kwantar da ke tukuna?"
Nana tace "ai ba wani sosai yake kamani ba, shiyasa"
Yace "duk da haka yakamata muje Asibiti a duba ki"
Tace "to Besty, yadda kace, amma wallahi ba za'aimin allura ba"
"Koma dai meya ya kama yi miki za'ai, insha Allah kuma Allura ce".
"To É—agani, tun da Mugun fata kake min"
Sadik ya ƙi ɗaga ta se murmushi da yake faman yi.
"Na shiga uku Mummy, cikina ciwo yake zan mutu, dan Allah ki taimaka min!"
Mummy tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, na rasa wannan ciwon ciki da kike fama haka Lilly, bari in wa Peter magana, ya zo ya kaimu Asibiti.
Sosai Lilly take kuka, tare da riƙe cikin ta tana wani irin murƙususu, idanunta duk suka yo warwaje!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi a can.
Sosai Farhan ta zage, ta zazzage abunda ya daɗe yana ci mata tuwo a ƙwarya tsawon tasowarta, wanda ita kanta Umman ba ta san hakan cutarwa ne ga Farhan ɗin ba, ciki har da yadda ta ke nuna banbanci tsakanin ta da ƙannenta.
Fuskar Farhan duk hawaye tace "Umma na azabtu da wannan al'ada da bata da tushe a addini, Rayuwata ta shiga cikin garari, da kina jana a jiki ƙila da kin nusar dani illar soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, amma baki haka ba se da bakin alƙalami ya riga ya bushe, kuma still kina sake ɗoramin laifi, ina roƙonki idan wani laifin nai miki, da ya sa kike min haka, Allah ya baki haƙuri, ki yafemin"
Tana gama maganar ta tashi Fuuuuu za tai waje. Baban Huzaifa yace "dawo ki zauna ba mu gama maganar ba ai"
Farhan ta dawo ta zauna tana sheshsheƙar kuka
Baban Huzaifa ya ja ajiyar zuciya yace "gaskiya É—an uwa kunyi kuskure, yanzu dama irin wannan rayuwar Yarinyar nan take haka? Na san muna karantawa yaranmu na fari, kamar yadda muma a kai a kanmu a zamanin mu, amma wannan zamanin idan kai haka akan yara dole su lalace"
Cikin damuwa Abba yace "wallahi ɗan uwa, ba yadda ban ba akan ta dinga sassautawa yarinyar nan, amma ta ƙi gane hakan, bayan haka muna da matuƙar tsanani akan tarbiyyar yaranmu, mussaman ita da ita kaɗaice mace a cikin yaran, Allah ya nuna mana dabarar ka ba ita ke shirya maka ɗa ba, amma Alhamdilillah daidai gwargwado mun lura da tarbiyyar Farhan, se dai kam ta rasa soyayyar uwa da ja a jiki"
Umma ta share hawaye tace "duk da haka wannan ba hujja ba ce, yaran da iyayen su suka mutu suka bar su fa?"
Malam Zakari yace "wannan daban, wannan mutuwa su kai, amma ke kina raye tana kallonki kina kallonta, amma ba zata iya zuwa ta sameki ta gaya miki damuwar ta taji daÉ—i ba, gaskiya akwai matsala, kuma yanzu fisabilillahi kun san ba ta son wannan yaron amma kuka dage se kun aura mata shi?"
Abba yace "wallahi ni ban san ba ta son shi ba, kuma ni ban niyyar yi mata aure yanzu ba ma, mahaifiyarta ce ta damu, ga surutu da aka fara wai ana gani ana kawota gida a Mota, amma ban taɓa sanin ba ta ƙaunar Yaron ba, kuma ni ban san tana son wani ba"
Malam Zakari yace "Farhana kin ɓata rawar ki da tsalle, kin tashi yarinya me ilimi da addini, amma kalli yadda ki ka maida kan ki 'yar shaye shaye me zaman kanta, kinwa kan ki adalci kenan?"
Farhan ta girgiza kai tace "Baba ƙaddara ce"
Yace "ba ƙaddara ba ce Farhan, ganganci ne ke ki ka kai kanki, kar ki sake ɗorawa ƙaddara"
"Baba, ni kaina ban san shaye shaye na fara ba, na fara ne da rashin iya bacci, ga damuwa na cin raina ji nake kamar kaina ze tarwatse, na fara neman maganin rage damuwa da saka bacci, har yunƙurin kashe kaina nai, Huzaifa ya hana ni, a hankali ya zamana idan ban sha abun maye ba, bana bacci, saitin zuciyata yai ta min zafi, nai haka ne duk dan in manta damuwa ta"
"To yanzu ina shi Yaron da kike so É—in?" Malam Zakari ya tambayi Farhan yana tsareta da ido.
Tai murmushi me ciwo tace "ba Soyayya ba ce, RUƊIN ƘURUCIYA ne, hadda Soyayyar sa a cikin abunda ya jefani a damuwa, mutane sun sha gayamin Soyayyar mu RUƊIN ƘURUCIYA ce, amma na kasa yadda, ya jani a jiki, yana son farinciki na yana gudun damuwata, yana bani kulawa, na saki jiki da shi na sakankance, se ji nai yayi Aure ya tafi karatu ƙasar waje, ga shi ni kuma za'a Auran wanda ban taɓa ƙaunarsa ba a raina ba"
Abba yace "a ina shi Yaron yake É—an waye?"
Farhan tace "Abba dan Allah a bar maganar nan, wallahi ba na son tunowa da shi, ni dai ku cigaba da yi min Addu'a Allah ya shirya ni ya sa in dena abunda nake"