← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 115

Sashe 105

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To shi yanzu likitan idan ya kai nasa kuÉ—in ya zasu yi kenan? Bayan sun tambaya ance an basu?"

Umma tace "to kaji ance sun kai ɗin ne? Tun yaushe suke cewa zasu kai? Kayi haƙuri kaje ku tattauna"

"Kin san Allah, ba in da zani suje su ƙarata can, ai shima ubanta me ya isa da ita, dan haka ba hannuna".

Sadik yai sallma a ɗakin Nana, ya tarar tana ta shirin makaranta, ga ƙoƙarin shirya Sahal da ya hanat sakat, gaba ɗaya tausayi take ba shi,shi kansa rainon na ƙaramin ƙoƙari take yi ba.

"Makarantar zaki tafi ne?" Yai tambayar yana kallonta.

Tace "eh".

Yace "Ajiye Sahal ɗin, tashi kije Sabo ya kai ki, bari in ƙrasa shirya shi in kaiwa Mother, in an tashi zan zo in ɗakko ki"

Nana tace "to" ta ƙarasa shiryawa ta fita, shikuma Sadik ya ɗau Sahal zuwa gurin Mother.

Ya tarar da ita a falo, tana bawa Talatu umarnin, gyaran kitchen da take so ai mata yau.

Yace "Mother ina kwana" kallo ɗaya taiwa Sadik ta ɗauke kai, ba tare da ta amsa gaisuwar tasa ba ta karɓe Sahal daga hannunsa.

"Mother gaisheki fa nai".

Mother tace "Ai zuwa yanzu Sadik kafi ƙarfin ka gaisheni, ai na tashi daga matsayina na uwarka zuwa wani abu daban, tun da har zaka iya dagewa akan abunda ba na so, Yanzu Sadik ashe yarinyar da ka dage seka Aura ɗin makaranta ɗaya ku kai, bana wannan ba, an tabattar da yarinyar mutuniyar banza ce, har gida aka kawo wa ubanka takadda, kuma ya tura a kai masa bincike aka kuka tabattar masa da hakane, anya Sadik kanawa kanka adalci? Ita wadda kake tare da ita meye ta gaza da har hange hangenka ya hango maka waccan ɗin?" Sadik yai shiru ya kasa furta komai.

Mother tace "Ai shikenan kaje kayi, amma ni dai kama ba da yawuna ba".daga haka ta gyarawa Sahal kwanciyar sa a kafaÉ—arta da yake bacci yake, ta wuce sashinta da shi.

Sadik ya rasa abunda yake masa daɗi ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ko ina babu daɗi, amma yasan wannan Auren da ze yana kan ƙa'idar shari'a sedai ze cigaba da Addu'a Allah ya kawo masa mafita.

Ƙarfe biyar na Yamma Sadik yana ƙofar gidansu Farhan, tun da aka kai kuɗin nan be sake zuwa ba se yau, ya tura Amir yace yai masa sallama da Farhan.
Da Amir ya samu Farhan a tsakar gida ya sanar mata, se cewa tai yaje yace masa ba zata zo ba.
Abba da yake aswaki yace "baki isa ba, tashi ki fita, tashi kan in saɓa miki"
Haka nan ta shiga ta ɗakko hijjabinta, ta saka ta fita ranta a matuƙar ɓace.

Ko da taje zuwa tai ta tsaya ko kallon in da yake taƙi yi.

"Barka da yamma 'yan mata"
"Meye kawoka gurina? Sadik meyasa zakamin haka, da izinin wa kaje kai kuɗin Aurena gurin ƙanin mahaifina?"

"Au sena nemi iznin ki? Ai tun farko na gaya miki"

"Akan me zakamin haka? Ni nace maka na dena sonka ya za'ai mutumin da ya sha wuya gurin ganin dawowar farinciki na, a lokacin da ka gujeni lokaci É—aya ai masa haka? Na zama butulu irinka kenan?".

Sadik yace "Nine farincikin dama, da na tafi kuma gashi na dawo, dan haka kawai ki dena wannan goce gocen"

"Ba zan dena ba, ba zan dena ba ɗin, bana sonka Sadik bana son ganinka, kuma ba zan Aureka, idan kuma kai gangancin Aurena ka shirya karɓar abunda ba kai zato ba, ni ba butulu bace irinka, Abbas zan Aura, mayaudari kawai" har ta gama masifar kallonta kawai yake yi, tai masifarta ta.

Sadik yace "in kin gama masifar, ina son inji meye tsare-tsaren ki na bikin, kuÉ—i zan baki ko kayan lefe kike so?"

"Bana so, ka riƙe abunka dan ba zan taɓa Aurenka ba" tai wucewarta cikin gida ta barshi a tsaye yana binta da kallo.

Nana ta dawo a gajiye sosai, ta wuce ta É—akko Sahal sannan ta koma BQ, dan ta san maybe yana nan yanawa Mother kuka.
Ta tarar ana ta shirye-shirye, Nana tace "Mother, baƙi za'ayi ne?"

Mother tace "A'a Faruk ne ze dawo, ya kammala master's É—insa, se abunda ba'a rasa ba"

Nana ta É—anyi shiru Sannan tace "Mother, ki yiwa Baban Sahal Magana ya koma makaranta shima"

Mother tace "ni ƙyaleni da batun mijin nan naki, daɗi Aure ya zauna yai tayi, kar Allah ya sa ya koma makarantar, ni na zuba masa ido yaje yai abunda yaga dama"

"Dan Allah Mother karki ce haka, Yakamata ya cigaba da makarantar ss"

Mother tace "kunfi kusa, kema zaki iya gaya masa ai, Khairat kawo mata abinci ta ci"

Gaba É—aya Khairat haushin Nana take ji, yanzu haka ji tai kamar ta cewa Mother ba zata zubo mata Abincin ba.

"Mother, Sahal yau yai kukan kuwa?"

Mother tace "ɗan ƙaniya, yayi amma ba sosai ba, Dr. ne ya tafi da shi, be daɗe da dawo da shi yai bacci ba"

Nana tace "to shikenan, tun da bacci yake, nima naje in É—an kwanta".

"ÆŠan uwa, wai tunda aka kawo kuÉ—in yarinyar nan na zata zaka zo, a tattauana yadda al'amarin ze gudana amma na jika shiru"

Abba yace "dan me ba zaka jini shiru ba, ni ka nemeni ne? Ko da kuka tashi yanke hukuncin ku ni nemana kukayi, kawai inji labarin wai kuɗin wannan yaron ka karɓar mata"

Malam Zakari yace "A'a, shi Abbas É—in be zo ya sameka bane?"

"Ni ba wanda ya zo ya sameni"

Malam Zakari yace "to ai Abbas É—in har gidan nan ya zo, yace min ya janyewa shi wancan yaro, kuma yai min bayani na gamsu"

Abba yace "kamsr yaya, kaga yaron kuwa? Yaro ne fa ƙarami sosai"

"To Addini ya hana ne? Na ga yaron har gidan da nake yaje, na ganshi, Abbas ya tabattar min da tana son yaron nan, kuma shima yaron yana sonta.
Ɗan uwa a karon farko kasan laifinka ne da na matarka ya ingiza yarinyar nan shiga wannan halin, a dalilin Yaron nan ta faɗa mawuyacin hali kuma ya dawo yace yana sonta a haka, addini be haramta auren nan ba, meyasa kake son kai ka haramta, mahaifinsa sanannane ne mutumin kirki, kuma duk da mutum ne me kuɗi, cikin girmamawa da mutunci suka kawo kuɗin nan, ita kanta Farhan ban tsaya bi takanta ba na karɓi kuɗin, shi wannan likita yace idan aka tsaya biye ta tata za tsce ba ta so ne, amma kuma ƙasan ta shi take so.
Zamanin iyayenmu har a shekara sha bakwai anwa ɗa Aure kuma ya zauna, addinin mu be haramta ba, dan haka ai musu addu'a kawai, kayi haƙuri ta ta ƙaddarar kenan".

Abba yai ajiyar zuciya yace "shikenan É—an uwa, Allah ya basu zaman lafiya"

Malam Zakari ya amsa da Ameen.

Sadik yaji daɗin dawowar Faruk sosai da sosai, a wannan karon ma Khairat se ƙoƙarin yiwa Faruk ɗin bajinta take, amma shi sam be ɗau hakan a matsayin wani abu na musamman ba.
Dama da yazo jana'izar Hakimi, kwanan sa uku a ƙauye, ya koma in da yake karatu kasancewar exams zasu fara, dan haka Wannan karon da ya dawo, ɗakin Sadik Na cikin gida ya koma, kasancewar su Nana suna BQ.

Sadik yana tare da Faruk suna hira, Faruk yace "Man, gaskiya kayi ganganci Sadik, ka duba yadda ake ji da kai a gidan nan, amma kowa ya watsar da kai saboda abunda ka ɗakko, guda nawa kake da har zaka ɗorwa kanka wani ƙarin Aure, Auren ma na yarinya mara ɗa'a, dan Allah me Maman Sahal ta rage ka da shi?"

Sadik ya nisa sannan yace "Bro, kowa yaƙi fahimta ta amma ina sa ran, kai ka fahimceni" ya ɗakko wayarsa ya nunawa Faruk hoton Farhan yace "ka gane wannan yarinyar?"

Faruk ya É—anyi shiru sannan yace "nasan fuskar nan amma na manta in da na santa"

Sadik yace "2yrs back, ita ce yarinyar da na ɗorawa raina cewar Lallai sena Aureta, na dinga cewa Aure nake so kana cemin RUƊIN ƘURUCIYA ne, itace yarinya ta farko da na fara so a rayuwata, ka san meya ja hankali na ta burgeni na fara sonta? Tsananin kamun kai da tarbiyyar ta, da karatun addini.
Tun yarinyar nan tana guduna, se da ta fara yadda da ni, soyayya me ƙarfin gaske ta shiga tsakaninmu, zanniya cewa ƙaddarar haihuwar Sahal ce ta gifta Hakimi ya Auramin Nana, a lokacin da gaba ɗaya aka shafe tunanin Farhan a zuciyata na manta da ita, cikin ikon Allah Maman Sahal ta zo da gagarumin sauyi a rayuwata, kuma ta zame min wani kyakkyawan bago da na jingina a jiki.
Duk abunda Farhan tai na lalacewa, nine sila Faruk, Yarinya ce me tarbiyya duk a sanadina komai ya sameta, yanzu idan na gujeta na ƙi Aurenta naiwa kaina adalci? Nima fa yanzu na zama uba, na fara tara iyali, ba zan so aiwa ɗana abunda naiwa Farhan ba, duk da shi Allah ba'a masa wayo.
Amma su Mother sunƙi su saurareni balle su ji uzurina, a tunaninsu son zuciya ne kawai yasa nake son ƙara Auren nan, amma hatta jumping class da nai, duk cikin planing ɗina ne na in auri Farhan, ina matuƙar sonta she's my first Love, gashi Husna kanta yanzu haushina take ji, ta dena shiga sabgata wanda hakan shima ba ƙaramin damuna yake ba, duk da nasan kishi ke damunta, amma ba zan hanata kishi a kaina ba, saboda koma mene laifina ne na shammaceta ban taɓa nuna mata nai soyayya da wata ba, wanda nima ba laifina bane, yadda nake ɗin nan fa nake Magana ina kan maganin hawan jini ne fa haryanzu, na rasa in da zan saka kaina"
Faruk yai ajiyar zuciya yace "ni na fuskance ka Sadik, zan cigaba da tayaka da addu'a Allah ya kawo komai cikin sauƙi"

Sadik ya amsa da Ameen.
Chapter 105 · 0% Book details