Sashe 16
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amin yace "kaga Mubarak dan Allah ka bar wannan maganar, duk matan da kake bi a ciki da wajen makarantar nan be isheka ba, wannan dai ita Sadik ya ƙallafa rai a kai, dan Allah ka bar masa kayarsa, ka bar ganin baya makarantar, kasan halinsa ze iya nemoka wallahi"
Mubarak yace "wallahi tunda na ƙyasa sena ɗana, kaima kasan bana ɗora raina akan abu in janye, and I will show her" yai Maganar yana kallon Farhan da ke zazzare ido.
Amin yace "wannan amanar Sadik ce, ka nemi wata dai banda wannan, in ba haka ba kaima akwai sister É—inka a school É—in nan semu far mata"
"Kutmar, karka kusakura wallahi kar kayi wannan gangancin" yai maganar yana nuna Amin.
Amin yace "Ashe ba daɗi kake lalube na wasu, ai iya wuya Sadik namu ne, idan muka bari a kai masa ɓarna bamu kyauta ba, Farhan wuce kiyi tafiyarki"
Farhan har da haɗawa da gudu ta bar cikin makarantar, ƙirjinta na dukan uku uku. Da godewa Allah ta tsira daga sharrin Mubarak.
Farhan duk lokacin da suka so haÉ—uwa da Sadik, se su haÉ—a meeting point lokacim tafiyarta Makarantar dare, su shiga mota su yi hira sannan ya tafi.
Gefe guda kuma tana ta fama da Sunusi, kasancewar sa mutum me nacin tsiya, wanda ba ya zuciya, yayi burus yaƙi nunawa Farhan yana jin haushin rashin saurarsa da take.
Wasa wasa kusan kullum se Mubarak ya zo Makarantar nan, duk da ba uwar da take kawo shi, sedai zuwa yiwa Farhan barazana, gashi ta kasa gayawa Sadik saboda buyagin sa.
Yau fitsarar Babba tasa har ajinsu Farhan ya bita, tana zaune tana solving Maths, 'yan ajinsu ana can gurin raye raye da support, kasancewar juma'a ce, seji tai Mutum ya zauna a kusa da ita.
A zabure ta miƙe tsaye, amma ya tare mata hanyar fita.
"Dan Allah ka rabu dani" ta faÉ—a muryar ta na rawa.
"Yarinya kenan, haryanzu baki yadda da abunda na faÉ—a ba kenan, idan so nake zan iya sawa a kamo min ke, inyi yadda na ga dama da ke, sedai sonake a karan kanki zaki amince dani*
Yasa hannu ya matse mata kumatunta da ƙarfi.
Taɓa ta yake da hannun sa, tana buge hannunsa tana kuka, tana neman hanyar fita, sukaji an daki ƙofar ajin da ƙarfi.
He was very shocked da ya ga Sadik, dan tunda suka kammala jarrabawa, Sadik be sake shiga makaranta ba.
Be tsaya ba ya janyo Mubarak ya É—ura masa wata irin Ashariya.
Jijiyoyin Kan Sadik duk sun ɗaɗɗaga, idonsa yai ja ya kalli Mubarak yace "kai dan baka da mutunci ka rasa wadda zaka bi se abunda nace nawa ne? Tunda muka bar makarantar nan ka fara bibiyarta ake gayamin, dan na ƙyale banyi Magana ba shine kake son zarce gona da iri, an gayamaka a banza zan bar makarantar nan in ƙyaleta? I already put my CID on her, me tai maka kake bibiyar ta? Ko abunda ke tsakanin mu ne ya shafe ta?"
Sadik yai maganar yana hankaÉ—a Babba.
Mubarak yafi Sadik girma sedai Sadik ya fishi siffar ƙarfi.
Ya kalli Farhan a fusace yace "dan me kika ɓoyemin yana bibiyar ki? Yanzu ba dan an sanarmin ba nazo da shieknan komai ze iya faruwa? Farhan why?"
Kasa Magana tai se kuka da take.
Sadik ya kuma kallon Mubarak yace "wannan shine magana ta da kai ta ƙarshe, kar ka kuskura abunda ke tsakanin mu ya shafi Farhan na gaya maka"
Mubarak yace "Ai kowa yaci tuwo da ni miya ya sha, ka rubuta ka ajiye idan har ina raye, sena wulaƙanta yarinyar nan, tunda ita ce abunda ka ɗora ranka a kai"
Sadik be kuma cewa komai ba, ya fizgo Farhan da jakarta, sukai waje yana huci.
A mota suna tafe se kuka take, "malama ki rufen baki, yanzu ba dan an gayamin yana bibiyar ki ba da komai ze iya faruwa, kin san halin Yaron nan kuwa? Meya haÉ—aki da shi ma tukuna?"
Cikin kuka Farhan ta gayawa Sadik Komai, haka ya dinga mata faÉ—a yace duk lokacin da aka tashi ze zo ya dimga É—aukarta, kuma ya na da masu yi masa CID a kanta a cikin ajinsu ba a wani guri ba.
Haka ya kaita gida, sannan ya tafi.
Farhan ta tsorata da lamarin Babba, amma ta rasa meye a tsakanin Sadik da Babba, saboda wasu lokutan tana ganinsu tare, kuma shi Babba yana zuwa sha'anin Sadik sosai, amma meye a tsakanin su haka?.
Abba yana zaune a falo, yana kallon labarai, Mother na masa hira.
Faruk ya shigo falon da sauri.
Abba yace "Jarumin maza, saurin me kake haka? Ya akayi?"
Cikin damuwa Faruk yace "Abba, yanzun nan aka kirani a waya daga gidan Hakimi, wai ba shi da lafiya, an kira wayar ka ba ta shiga, kusan sati biyu kenan ba shi da lafiya"
Da sauri Abba yace "subhanallah, ai idan ina can layina baya shiga, amma ya akai ba'a kira gidan nan an faÉ—a ba?"
Faruk ya kalli Mother, ya É—auke kai Yace "Abba, ance min an kira wayar Mother an gayamata, amma ba wanda yaje duba shi a gidan nan, ni da na sani zanje"
Abba ya kalli Mother yace "Yanzu Hauwa har a kiraki mahaifina ba lafiya, ba kije kin duba shi ba, ba ki tura wani daga yaran nan ba, kuma in dawo ki kasa sanar min?"
Wani Mugun kallo Mother taiwa Faruk sannaan yace "Wallahi ban zaci abun ya kai haka ba, da mu ka waya cemin sukai kawai zazzaɓi ne ke damunsa, aka kwan biyu na kuma kira aka cemin jikin da sauƙi, shiyasa ban gaya maka ba"
A fusace Abba yace "ya isa haka, dattijo kamar wannan ba lafiya, ai yafi ƙarfin ace is not that serious, ko daya ke tunda ba mahaifinki bane ai dole kice haka nagode" ya tashi ya bar mata falon ransa a matuƙar ɓace.
Mother ta dawo da idonta kan Faruk tace "Sannu mara mutunci, ka tunzura shi yamin masifa hankalinka ya kwanta kaji ko, saboda tsabar rashin mutunci maimakon ka bar maganar a iya an kiraka ance ba shi Da lafiya, shine har da gaya masa ai sun gayamin ban gaya masa ba"
Faruk yace "Mother ba haka bane, yanzu shi Abba se suga lafinsa, da aka kira aka faÉ—a kinga da koni kin aika naje na duba shi ai kinga da abun baze zo a haka ba"
"Dallacan rufemin baki, sakarai kawai shiyasa nafi son Auta ai, da Shine da babu yadda za'ai yaimin wannan shirmen da kai min"
Faruk ya girgiza kai yace "ai ko baki faɗa ba dama nasan ni ba sona kike ba, kinfi son Sadik, amma yadda muke ƙaunar ku haka shima yake ƙaunar su, Mother ba zaki ji daɗi ba ace yai koke ko Abba wani ba lafiya, amma ba wanda ya zo kanku a cikin mu, hakan ai ba daɗi but am so sorry Insha Allah ba zan sake aikata hakan ba"
Ya juya ya bar falon.
Duk cikin su ukun nan babu me biyayyar Faruk, shi dr. Dama ba magana yake ba, ko laifi yai maka sedai baƙin ciki ya kashe ka, in zaka kwaɗa shi ka cinye da faɗa wai ya ɓata maka rai, baze ma nuna maka yasan da shi kake ba balle ya baka haƙuri.
Sadik kuwa ƙeƙe da ƙeƙe me ba'a tursasa shi, idan yai laifi kai masa faɗa ma se yai zuciya, koma ya bar maka gurin gaba ɗaya, baya son tashin hankali sam, shi ko laifi yai yafi som ai masa nasiha akan ai masa faɗa.
Faruk ne kawai ko yayi laifi ko beyi laifi ba, dan a zauna lafiya zece ayi haƙuri, sam baya son yaga ya ɓatawa wani rai ace yayi laifi, sedai idan aka fusata shi kamar wuta haka yake, baya sakkowa ta daɗin rai.
Duk da son da akewa Sadik a gidan, amma Abba yana wa Faruk so na musamman, saboda sanyin halinsa da rashin son hayaniya.
Yau kowa a ɓangaren sa ya kwana daga Abba har Mother, dan yayi fushi sosai ga fushinsa ba sauƙi sam, Mother ta rasa in da zata sa kanta.
Faruk ya koma sashinsu, ransa a ɓace ya tarar da Sadik da wayarsa a hannu, yana cin bredi.
Messages ɗin Farhan yake kallo tana ba shi haƙuri, amma yaƙi tankawa dan soyake ya nuna mata yaji haushin ɓoye masa abu da tayi.
Messages ɗin ta na ban haƙuri kala kala, amma yaƙi reply.
Faruk yace "Autan Mother, Hakimi ba lafiya fa, ashe tun kan Abba ya dawo Hakimi ba shi da lafiya"
Sadik ya ɗago ya kalli Faruk yace "Allah ya jiƙansa" ya maida hankalinsa kan wayarsa.
Faruk ya buɗe baki yace "dan ubanka ce maka nai ba shi da lafiya, amma kace Allah ya jiƙansa"
"Ohh sorry, na zi cewa nai Allah ya sawwaƙe"
Gaba ɗaya Faruk ya lura, hankalin Sadik na kan wayarsa, dan haka ya ƙyaleshi kawai.
Farhan ganin Sadik yaƙi kulata duk tarin messages ɗin da tura masa yasa ta haƙura, ta tabattar yayi fushi ne sosai haka, abunda be taɓa yi mata, yai fushi da ita haka.
Ƙarfe bakwai na safe Abba ya shirya tsaf, da nufin tafiya ƙauye gurin mahaifinsa, yana ƙoƙarin fitowa ne sega Mother ta shigo, ta kalleshi tace "Yallaɓai dan Allah ka tsaya ko breakfast kayi seka tafi"
"Bana buƙata" Abba ya bata amsa a taƙaice.
"Dan Allah kayi haƙuri, ka karya kan nan gama shiryawa semu tafi tare"
Be bata amsa ba ya raɓata ya wuce, ta biyo shi tana masa Magana, Amma yaƙi saurarar ta.
Bawan Allah, Yana fita harabar Ajiye motoci, yaga Faruk ya shirya harya fito da mota.
Abba yace "Faruk ya dai?"
Faruk yace "Abba ai nasan yau zakace zaka, shine kawai na shirya da wuri na fito da mota, yanzu dama nake sa ran shigowa cikin gidan, inji da Yaushe zaka tafi in bika"
Abba yai murmushi yace "to shikenan, mu tafi kawai na shirya"
Ya buÉ—ewa Abba mota ya shiga, ya zaga ya buÉ—e motar shima ya shiga sannan yace "Mother semun dawo"
Ya fara jan motar sannu a hankali suka bar gidan.