← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 115

Sashe 96

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe ma Nana ba ta saurari Sadik ba, sedai yadda rana ɗaya duk tai wani iri ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya sake tabbatar da kishi bala'i ne, sedai hanyar da ze bi ya wanke kansa a gurin Nana yake.
A falo ya fito ya sami Nana ta na shayar da Sahal, ya samu guri ya zauna a kusa da ita ya kira sunanta "Husna" banza tai masa Kamar ba da ita yake ba.

"Magana fa nake miki, dan Allah ki tsaya in miki bayani"

"Ba ka da wani bayani da za kai min, ai bayani na gama jinsa kawai ka ƙyaleni, ka rubutan takarda sakina, ka Auri matar so wadda kake so, idan na yaye Sahal ma zan kawo maka ka bata, in ya so se in koma makaranta wataƙila a gaba, in samu wanda ze so ni saboda Allah"

"Dan Allah Besty ki saurareni"

Cikin kuka tace "ba wata Besty, dama ka sha gayamin ni ba komai bace face me aikin ka, ka cutar da ni baka sona ka bari na haihu da kai, ka kashemin rayuwa, Allah ya bani ladan biyayya amma na gama zama da kai, ƙauye zan koma na gama Auren"

Be taɓa zaton Nana mafaɗaciya ce haka ba, ya dai santa da tsiwar tsiya amma tana da matuƙar sauƙin kai sosai da sosai, amma a wannan karon kam ba ya tunanin za ta fahimce shi.

Ta shirya tai tafiyarta cikin gida, É—akin da tai jego taje tai kwanciyar ta.

Haka Sadik ya wanzu cikin tsananin damuwa, Besty ta caza masa kai, ga ɓangaren guda na zuciyar sa na son ganin Princess.

Da azahar ya shirya ya tafi gidansu Farhan, sedai zuciyarsa ba daɗi, abun ya zame masa biyu, da idan Farhan ta caza masa kai, rarrashinsa da Nana ke yi, ba ƙaramin nutsuwa yake samu ba, to gashi Yanzu ma Nana ta juya masa baya.

Tun da Motar Sadik ta shigo layin Farhan ta sha jinin jikinta, dan tana tare da Abbas, ya dawo da ita daga makaranta.

Abbas ya kalli Farhan yace "ya dai na ga kin canza?"

Sadik yai parking ya fito babu walwala, kai tsaye ya tunkaro in da su Farhan ke tsaye, ko kallon in da Abbas yake be ba, ya kalli Farhan yace "Farhan me nace miki ne wai? Bance ki sallami mutumin nan ba?"

Abbas ya kalleshi yace "bawan Allah ya dai?"

Sadik yace "ba da kai nake ba, da matata nake"

"Ya akai ta zama matarka? Nine nake shirin Aurenta ai"

"Ni kuma nine mijinta, ka tambayeta kaji" Sadik yai maganar yana maida idonsa kan Farhan.

"Sadik meye haka kake min ne? Meyasa kake min haka? Na gaya maka wannan shine wanda zan Aura, meyasa kake son ta ƙarfin tsiya se ka dawo rayuwata, nace maka bana buƙatar ka, bana sonka Sadik ka fita daga rayuwata, ka jefa rayuwata cikin bala'i kuma kana cigaba da bibiyata meya haka Sadik?"

Sadik ya kalleta ya jinjina kai yace "Nagode Farhan, amma ba gudu ba ja da baya, nine mijinki ki rubuta ki ajiye, idan ba ni ba Wallahi ko wa kika aura tare muka aureki" yana gama maganar ya nufi motarsa cikin hanzari.

Abbas yace "wannan ne Sadik É—in naki dama?"

Farhan kamar za tai kuka tace "Shine amma.....

Abbas yace "Shhhhh, no need to hear anything from you, se anjima" shima ya nufi tasa motar.

Farhan ba ta gane wani hali Abbas ya shiga ba, fushi ko akasin haka?.

Sadik kuwa ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, dan ba a hayyacinsa yake tuƙin nam ba saboda damuwa.

Yana zuwa gida BQ ya wuce sedai ya tarar Nana ba ta nan, ga wardrobe ɗin Sahal duk an watso kayansa ƙasa.

Cikin hanzari ya fito har da haɗawa da gudu, ya shiga cikin gida yana ƙwalawa Mother kira.

"Kiran me kake min haka?"

Sadik yace "Mother ina Besty? Naga bata BQ"

Mother tace "ta je gidan dr."

Sadik yace "Ya salam, Mother meyasa kika barta, Wallahi ƙauye zata tafi"

Mother tace "yo ni na sani ne? Na zaci ta da saninka, kuma koma mene banga laifinta ba, tunda kai ne baka da hankali, ba zaka kashe 'yar mutane da ƙuruciyarta ba"

"Mother yanzu kin goyi bayan ta tafi ta barni, Wallahi ina sonta Mother"

"Na goyi bayanta É—in, ko ni kaiwa abunda kai mata na gama zama da kai, mara hankali kawai!!!
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680

Sadik ya zauna akan kujera jiki babu ƙwari, yana murza goshinsa saboda wani irin zafi da kansa yake masa, gaba ɗaya ya rasa ina ma ze dafa yaji daɗi, Mother kuwa tai tafiyarta ta bar shi a gurin a zaune.

Ya tashi ya shiga ɗakinsa na nan falon ya nemi guri ya kwanta, yanzu azahar ta wuce, idan yaje ƙauye yanzu ba ze samu damar dawowa akan lokaci ba.

Nana kuwa tana É—akin Inna, se uban kuka take kamar wadda aka tsinewa, idanunta duk sun kumbure, fuskarta tai jawur.

Inna ta kalleta tace "to yanzu Nana ke yaji kika yo ko me?"

Nana tace '"Ni ba zan cigaba da zama da shi ba, kawai ya sakeni ya zauna da wadda yake so"

Inna tace "ba shakka sarauniyar marasa hankali, shi kuma É—an naki ya zaki da shi?".

"Ba shi abunsa zanyi, ba ze ƙara shan Nono a jikina ba, yaje ya san yadda ze yi da shi"

Inna tai murmushi irin nasu na manya tace "Yarinya ƙuruciya na ɗawainiya da ke, kin ban kunya Nana, kin ganni ban taɓa yaji ba duk zamana a gidan kakanki tsawon wannan shekaru ba dan kuma ba ma samun saɓani bax

Ba kunya Nana tace "kema dan bece ze miki kishiya bane, kuma ai ke sonki yake ya Aureki ni kuwa fa, aka cusa masa ni ya Aureni, dama ya sha yi min gorin sadakata aka ba shi bana damuwa, ashe da gaske yake, dan kunnena naji yana faɗar ba sona yake ba" ta ƙarasa maganar tana kuka.

Inna tace "sannu mara kunya, ni kike cewa dan ba ai min kishiya bane ba ko?"

"Inna kiyi haƙuri raina ne a ɓace wallahi"

Inna tace "kin kyauta, ki dena wannan kukan ki ɗau ɗanki ki shayar da shi yanzun nan kan in ɓata miki rai"

Haka nan Nana tana kuka, ta É—au Sahal tana rarrashinsa, ta fara shayar da shi.

Inna tace "ki kwana da shirin gobe in Allah ya kaimu da safe zaki wanke ƙafarki ki koma ɗakinki" Nana ta sake fashewa da kuka, gaba ɗaya Inna kamar ma ta tsanete ne duk wannan abun ko guri ɗaya ba ta ga alamar za su bawa Sadik laifi ba.

Taƙi cin abinci se aikin kuka, daga salla se kuka, har ta fara ji a ranta da iyayenta na da rai ba za'a nuna ba ta da amfani ba s gurin Sadik, sunfi son Sadik Yanzu a kanta.

"Ki ta so kakanki na kiranki" taji muryar Inna, kamar ba zata motasa ba se kuma ta tashi, ta nufi turakar Hakimi, ta tarar yana kashingiÉ—e gefensa ga Sahal a kwance yana shan hannunsa.

Nana ta shiga ta zauna ba tace komai ba, tana ta goge hawaye.

Hakimi yace "matso kusa dani abar sona"

Nana ta girgiza kai tace "Allah Alhaji ka dena sona, Sadik kuke so tun da kuka fifita farincikinsa kun dena sona"

Hakimi yai murmushi yace "haba Nana, ya kike tunani irin haka? Tun daga tasowarki muke riƙe da ke, ba mu taɓa zaɓa miki abunda ze cutar da ke ba, dan haka yanzu ma ba zamu zaɓa miki abunda ze cutar da ke ɗin ba, ki kwantar da hankalinki ki zauna a gudanki, ki rungumi mijinki da yaronki, dama shi namiji mijin mace huɗu ne, kiyi haƙuri na san an miki laifi amma kiyi haƙuri"

"Cewa fa yai ba ya sona, da kunne na naji, zaman me zanyi kenan?"

"A'a ba kiji dai dai bane, Ya tabbatar min da yana sonki sosai, kar ki bari sheɗan yai tasiri a rayuwar Aurenki, kiyi haƙuri, na san kinyi biyayya amma kiyi haƙuri ki ƙara kinji yarinyar kirki"

Nana a ranta tace dama idan akace kayi haƙuri an so cutarka ne, ba ta sake cewa uffan ba ta koma ɗakin Inna, ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take mata.

Washegari tun da wuri Inna ta saka Nana ta fara kintsawa wai ta koma, abun kunya ta fito be sani ba kuma a ga ta koma da ƙafafuwan ta, ta rasa abunda yake mata daɗi gaba ɗaya.

Tunds Abbasa ya tafi Farhan take kiran wayarsa, amma a kashe har wayewar gari, wayarsa ba ta shiga sam, kasa daurewa tai, ta tabbatar da tabbas Abbas yayi fushi ne, abunda tun haɗuwarsu be taɓa yi ba, duk irin girman laifin da zatai masa ba ya taɓs kai ya duba balle ya nuna yayi fushi, shiryawa tai ta bishi Asibiti.

Sedai da taje baya cikin office É—insa, wata Staff ta tambaya, ta sanar mata baya jin daÉ—i yana office É—in sa na saman bene ya kwanta.

Da hanzari Farhan ta bi matattakalar bene zuwa office ɗin saman, ta tura ƙofar tare da yin sallama.

Yana kwance akan aboservation bed ɗin da ke office ɗin, yana ganinta ya tashi zaune tare da ƙaƙalo fara'a yace "Madam yau da kanki?"
Da sauri ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin "doctor, na ganka a kwance ba ka da lafiya ne?"

Abbas yace "A'a hutawa nake yi kawai"

Farhan tace "Amma na ganka duk wani iri?"

Yace "bakomai fa, kar ki damu"

Farhan tace "dole in damu doctor, tun abunda ya faru jiya wayarka a kashe, doctor dan Allah ka fahimceni, Wallahi bakomai a tsakanina da Sadik a yanzu"

Ya ɗanyi murmushi sannan yace "meyasa kika ɓoyemin dawowarsa gareki?"

Tace "saboda ba abune me muhimmanci da zan sa a gaba har ya zama topic ɗin tattanawa ba, babu amfani dawowarsa ratuwar tawa, dan haka babu dalilin da ze sa in gayamaka, hakan ka iya ɓata maka rai"

"To ai ni rashin gayamin ɗin yafi ɓatamin rai Farhan, amma bakomai dai ya kike?"

Kamar za tai kuka tace "doctor bana son zama, butulu dan girman Allah kayi hsƙuri, nayi laifi amma kayi haƙuri Please"

"No,ba kya laifi Farhan naji daÉ—in dawowarsa rayuwar ki"
Chapter 96 · 0% Book details