Sashe 100
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Usman ya ƙaraso ya ɓanɓare Nana daga jikin Sadik yace "wuce muje, baze sa miki hawan jinin ba kema, kun zo kunawa mutane kuka, haryanzu ba ku san kun girma ba, kun haifi ɗa amma kunawa mutane koke koke".
Nana tana kuka haka Dr. Ya sata a gaba ya maida ita gida.
"Farhan, ranar Asabar insha Allah, nake sa ran in ji feedback É—in yayyan babana, zasu kawo kuÉ—in Auren mu, amma dan Allah zan miki wata tambaya, ki gayamin tsakanin ki da Allah"
Farhan tace "to doctor, Allah yasa na sani"
Abbas ya gyara zamansa yace "do you still love him?"
"Who?"
"Sadik".
Gaban Farhan ne yai wata mummunar faÉ—uwa, ta ja wata ajiyar zuciya tace "meyasa ka tambaye ni?"
"Saboda sonki nake tsakani da Allah, ba na son in cutar da ke, ko in miki dole idan haryanzu kina son Sadik ni me fahimtar ki ne, farincikin ki nake so Farhan".
Zuciyar Farhan ce ta tsananta bugawa, amma tai jarumta tace "yanzu doctor idan ka ga zan komawa Sadik seka barni? Guda nawa yake ta yaya ze iya riƙe mata biyu?"
"Farhan, yana daga cikin matsalolin mu a yanzu, haramtawa kanmu abunda Addini ya halarta mana, Dan haka ki dena duba wannan".
Farhan tace "Doctor, ba na buƙatar Sadik a rayuwata, lokaci yayi da zan fuskanci rayuwata, dan ka dena kawo zancensa, Soyayar mu Ruɗin ƙuriciya ce kawai, dan haka a manta da wannan maganar".
Abbas ya kalleta yana wani iri murmushi da shi kaÉ—ai ya san ma'anarsa.
Farhan tace "dariyar me kake yi kuma?"
Yace "bakomai".
Nana tun da doctor ya dawo da ita gida, ta kasa nutsuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa in da zata saka ranta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, ko Abinci ta kasa ci haka ta wuni gaba É—aya babu daÉ—i.
Se bayan ƙarfe goma na dare, sanann ta ji tsayuwar motar Abba, alamar sun dawo daga Asibiti.
Ta ɗan jira zuwa ƙarfe goma da rabi, sha ɗaya saura sannan ta shiga cikin gida.
Abba yace "Daughter ba ki bacci ba?"
Nana tace "eh, Abba ya jikin baban Sahal É—in?"
Mother tace "ni idan kika ce baban Sahal É—in nan, dariya kike bani da kunya".
Sukayi dariya banda Nana da fuskarta ke bayyanar da damuwa.
Abba yace "jikinsa yayi sauƙi sosai, dan ina ga gobe in Allah ya kaimu za'a sallame shi, ya tashi har yace a gaishe ku".
"Abba yayi Magana kenan?"
"Sosai makuwa, munyi hira da shi sosai".
Jiki a sanyaye Nana ta durƙusa akan gwiwowinta tace "Abba, Mother a madadin Sadik, dan Allah dan Annabi ina roƙa masa alfarma ba danmu ba, dan Allah ku ba shi dama yai Auren nan, in dai hakan ze sa ya samu farinciki".
Saroro suka bi Nana da kallo, Mother tace "ke anya kina da hankali kuwa? A biye muku kuyi ta shirme, ta yaya Sadik ze iya riƙe mata har biyu?"
Nana tace "tun da ya iya riƙeni mu biyun ma ze iya insha Allah, bana son Sahal ya zama Maraya, duk da rayuwa a hannun Allah take, Hakimi yai min Nasiha, na rungumi ƙaddara ta, zan cigaba da zama in kula da yarona, amma shi dai a ƙyaleshi ya Auri wadda yake so, tun da yace ita yake so, ita ya fara so dama".
Abba yace "Nana, tashi kije ki kwanta dare yayi".
"Abba, in kana son ka shiga cikin ceton Annabin rahama, dan Allah ku bari yayi, ka nema masa Auren nan, Mother dan Allah ki sa baki, ku bar shi yayi, in dai hakan ze sama masa kwanciyar hankali".
Abba yace "Naji, jeki za muyi shawara".
"Abba dan Allah ka yanke wannan shawarar yanzu, bana son Sahal ya rasa mahaifinsa akan abunda za'a iya magance shi, kaga yayi ƙarami ace yana da hawan jini, hawan jini se mutum ya fara tsufa, ko gane muta8fa ba yayi sosai, in dai ze iya faɗuwa jininsa ya hau saboda soyayya, to abun a duba lamarin ne, ni dan ta tawa me sauƙi ce, na yadda da ƙaddara, ƙaddarar Haihuwar Sahal ce ya sa na aure shi, amma dan Allah ku bari ya auri wadda yake so".
Wani irin tausayin Nana ne ya kama Mother, jiki a sanyaye Mother tace "Nana, shikenan kije ki samu ki kwanta".
Nana tace "to yaushe za'aje a tambayo masa Auren, bana son ya mutu" Nana tai maganar tana kuka sosai, kamar zata shiÉ—e.
Abba yace "Ai na riga na amince, kije Allah yai miki albarka, kin cika 'yar halak Nana, bari ya samu sauƙi zamu ga abunda zamuyi a kai".
Nana tace 'to kun yadda zaku yi masa Auren?"
Abba yace "za'ai masa, tashi kije ki dena kukan haka".
Nana tace "to Abba nagode sosai, Allah ya saka muku da Alkhairi ya sa ku gama da duniya da lafiya, Allah ya baku abunda kuke nema".
Abba yace "Ameen, Allah yai miki albarka". Nana ta tashi da goyon Sahal a bayansa, ta bar falon.
Mother tace "Allah sarki, so bala'i ne, banda haka me zesa yarinyar nan ta damu aiwa Sadik abunda yake so? Waye yake son ai masa kishiya, ji nake kamar in mata kuka, ga kishi a tare da ita kuma ga mafita take nema masa, Sadik bewa kansa adalci ba"
Abba yai shiru, dan shi kansa tausayin Nana ne ya cika zuciyar sa.
Duk da wannan jihadin da Nana tai, kwana tai tana kuka, saboda tausayin kanta da kuma tsananin kishin Sadik da ya addabi zuciyarta.
Farhan kwana biyu taji wani iri, saboda sam ta dena ganin gilmawar Sadik, gashi haka kurum idan ta tuna wai kuÉ—in Aurenta Abbas ze kawo, se gabanta ya tsananta bugawa.
Seda Sadik ya kwa huÉ—u a Asibiti sannan aka sallamo shi, bayan hawan jini har da ulcer da typhoid suka kama shi, likita ya kakkafa wa Sadik dokoki, sannan aka sallami Sadik.
Mutane suka dinga zuwa duba Sadik, tsawon kwanakin nan sau biyu aka bari Nna taje ta ga Sadik, saboda koke koke take idan ta ganshi, yau tun da ya dawo ta shigo tai masa sannu ta koma gefe, Sadik se binta yake da ido, yana son yai mata magana, amma baya son yin Magana saboda hakin da yake yi.
Nana ta tausayawa Sadik yadda ya kamu da wannan ciwon, da ƙanan shekaru haka, sedai ƙasan zuciyarta ta kan ji haushin sa idan ta tuna, Aure zeyi tai sharing ɗin sa da Wata, wani irin kishi ya dinga taso mata.
Da dare yai BQ tai tafiyarta ta bar shi a nan ɗakinsa na cikin gida, yana son ta zauna a kusa da shi, amma sam taƙi kula shi, ko Sahal ta hana shi, duk da yadda yaron yake ta koke koken yana son yaje gurin Sadik, amma ta hana shi ta wayance da ai Sadik ba shi da lafiya.
Abun mamaki har su Abba sun kwanta, se ga waya daga ƙauye, hankalin Abba ya tashi sosai da sosai, ya ɗaga wayar jikinsa na rawa Mother kuma tai masa ƙuri da ido, tana jiran jin dalilin kiran.
Muryar Hakimi yaji yai masa sallama, Abba yai ajiyar zuciya yace "Alhaji da kan ka?".
Hakimi yace "eh da kai na bawan Allah, nace ya batun maganar da mu ka ne? An tambayowa Yaron nan Auren?"
Abba yace "Alhaji ai Sadik É—in ma ba lafiya, yau muka dawo daga Asibiti".
Hakimi yace "Subhanallah, kuma ba ku faÉ—a ba? Ya jikin nasa?".
"Jiki yayi sauƙi, an sallamo shi ma".
"To Allah ya bashi lafiya, dan Allah Abdullahi ba na son in mutu ban cikawa Yaron nan alƙawarin sa ba, yai min halacci yana riƙe da abar ƙaunata, ba cin mutunci ba wulaƙanci, nima dan Allah ina roƙon ku bari ya auri wadda yake so, kar in zama tsohon banza, kar ku duba ƙanƙantarsa, Addini be hana masa ba, kuma kai Allah yai maka arzikin da zaka tallafa masa ya riƙe su".
Abba yace "to shikenan Alhaji, za'ai yadda kace insha Allah".
Alhaji yace "to madalla, ai masa sannu a gaidamin Nana da abokina, ace ina son su sosai, A cewa Sadik ga amanar abar ƙaunata nan, a kulamin da marainiyar Allah"
"To ranka ya daÉ—e insha Allah zan gaya musu".
Su kai sallama Abba yai shiru yana sake jinjina lamarin.
Sadik ya warke ras, sedai jikinsa babu wani ƙwarin kirki, hankalinsa yana kan Nana sosai, da yadda ze yaje ya ga Farhan.
Yau a bedroom É—insu ya tarar da Nana, ya zauna a kusa da ita, kallo É—aya tai masa ta cigaba da danna wayarta.
Karɓe wayar yai, ya ɗan tsura mata ido sannan yace "haryanzu fushi kike da ni ko Nana?"
"Akan me zan fushi da kai kuma?"
"Ba gashi ba, tun da na dawo bata sauya zani ba, sam bana gabanki"
Nana tace "A'a, meye nawa na cigaba da shishshigi kuma, ai na sadsƙar, ni yanzu zaman ɗana zan yi kawai".
"Nana me zan gaya miki wanda ze sa ki yarda da ni?".
"Ka ga Please, haryanzu ba ka da lafiya, kar kaje ka kuma sumewa, in dai nice kaje kai Aurenka ka dena faÉ—uwa kana suma saboda soyayya".
Shiru yai yana cigaba da binta da ido, se ƙoƙarin mai da hawaye take kar su zubo, kishinta ƙarara ya kasa ɓoyuwa.
"Ni me laifi ne a gareki, ba zan fasa baki haƙuri ba, amma ina sonki Nana ba zan taɓa wulaƙanta ki ba".
"Dan girman Allah ka dena gayamin kalmar nan, ƙona min zuciya kake, ka dena yaudarata da kana sona, bana son ji dan Allah" ta ƙarasa maganar hawayen da take riƙewa suna zubowa.
Jiki a sanyaye ya tashi ya bar mata É—akin, ya fita ya É—au mota ya bar gidan.
A ƙofar gidansu Farhan ya ja ya tsaya, yana ta waige waige, yana son ya samu wanda ze aika ya kira masa ita.
Kawai ya hango ta tana ƙoƙarin shiga gida, hannunta riƙe da leda "'yan mata daga ina"? Yai maganar cikin sanyin murya.
Se da gaban Farhan ya faÉ—i, yadda Sadik yai duhu ga rama, alamu suka Bayyana ba shi da lafiya.
Hararsa tai zata wuce, amma ƙasan zuciyarta ji taka tamkar cikin shagwaɓa ta tambayi meya same shi haka.