Sashe 58
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da alama a gajiye yake, ya É—an jima a É—akinsa sannan ya dawo falo ya zauna, ya kalli Nana yace "kawon ruwa a fridge"
Kamar ba zata tashi ba, se kuma ta tashi tana tafiya a hankali, kamar mara lafiya, ta kawo masa ruwa da kofi.
Sedai tana kawowa ta tarar ya É—auke remote, ya canzs channel.
Ta dire masa a gabansa, ta koma gefe tana kumbure kumbure, be ko kulata ba ya É—au ruwansa yana sha.
Kallonsa take, saboda Ruwan da sanyi sosai, ga yanayin garin da sanyi Sosai,
Amma yake shan ruwa me sanyi.
"In kin ga dama, kije É—aki na kan gafo, ki É—au Abinci"
Ba musu ta miƙe, taje ta ɗakko wata jaka, wadda ita kaɗai ta gani a ksn gadon ta dawo falo.
Ta zauna ta buÉ—e, amma gugguru ne a ciki.
Ta kalleshi tace "wannan ne Abinci?"
Be ko kulata ba ya maida hankalinsa kan TV.
"Wannan ai ba Abinci bane, ni wallahi na gaji da cin wannan abubuwan, wannan ai ba Abinci bane, ya mutum ze ƙoshi da wannan, ni Wallahi Abinci nake so na fi ƙoshi, ko wannan bredin da kake siyo min, amma wannan ai dan nishaɗi ake ci ba yunwa ba"
Kamar be existing a É—akin ba, haka ta fara ci tana mita.
Can ta maida hankali kan abunda Sadik yake kallo, wani horror Film ne me matuƙar razanarwa yake kallo (the conjuring), nan da nan mood ɗin ta ya canza, ta shiga tsoro Sosai, ba ta taɓa ganin bala'i a film kamar wannan ba.
Wani razanannen ihu da Nana tai, seda shi kansa Sadik É—in ya razana.
"Meye haka, baki da hankali zaki wa mutane irin wannan ihun?"
Kamar za tai kuka tace "tsoro naji fa"
"Kuma se kiwa mutane wannan ihun, saboda hauka da ƙauyanci? Tashi ki bar falon nan kije ki kwanta, dama ai dare yayi"
Ta noƙe kafaɗa tace "bana jin bacci ai"
"Zaki tashi ko sena make ki?"
Ba shiri ta tashi tana tura baki, duk ta ɓata gurin da gugguru, tai tafiyarta ɗakinta tana ƙunƙuni.
Tai wanka, ta sa kayanta na bacci ta É—ora da kayan sanyi, Sannan ta saka hijjabi ta kwanta, se dai tana kashe fitila ta kwanta, se ta ga kamar teddies É—in É—akinta na motsi.
A razane ta tashi zaune, ta kunna fitila tana waige waige.
Sedai ta ga komai normal, har wani gumin wahala ta fara, ta kasa bacci se zazzare ido, sedai da yake bacci ɓarawo ne, ya kwashi Nana tana daga zaune ba tare da ta shirya ba.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un!" shine abunda ta furta lokacin da ta diro da kan gadonta, tai waje da gudu ta nufi É—akin Sadik, saboda mummunan mafarkin da tai akan film É—in.
Ya cire kaya, daga shi se gajeren wando ya saka rigar wanka, ze wanka dan ya kwanta se gata kamar an jefota tana haki.
"Ke meye haka?"
Kamar za tai kuka tace "tsoro nake ji"
"Tsoron me?"
"Wani abu ne a É—akina yake tsorata ni"
"Kuma ni seki zo min nan, fitar min daga É—aki"
Hawaye ya cika idonta tace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi tsoro nake ji"
Tsaki yai ya gyara rigar wankansa ya nufi hanyar banÉ—aki ai kuwa ta bishi.
Ya tura ƙofar banɗakin ze shiga, nan ma ta biyo shi.
"Au banÉ—akin zaki biyo ni? Dama so kike ki ganni tsirara kenan, to bismillah shigo"
A dirirce tace "yi haƙuri, ni ba biyoka zan ba, akan me zan ganka tsirara? Ni tsoro nake ji ne"
Ta nemi guri ta tsaya a waje, se haki take. tsaki Sadik yai, ya shige banÉ—akin.
A ƙofar banɗakin ta tsuguna, tana ta haki jikinta yana rawa.
Ya gama wankansa ya fito sanye da rigar wanka, ya ga yadda take jujjuya idanu.
Shi dariya ma ta so ta bashi, horror film ne ya sa ta zama haka, ga iya rashin kunya ga uban tsoro.
Ya sa kayan baccin sa, ya nufi kan gado ze kwanta, nan ma ta bishi.
"Ke wai uban me zan miki ne? Ki fita ki koma É—akinki ba zan kwana É—aki É—aya da ke ba"
Har da hawaye tace "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ina ga wannan yarinyar ce a ɗakina, ta film ɗin ɗazu"
Sadik yace "Wai wa ya gaya miki film gaske ne?"
"Wallahi motsi naji a É—akin"
Sadik ya ɗan taɓe baki yace "seki kwanta a ƙasa, dan ba zan baki pillow ba, da pillow biyu nake amfani"
"To ka bani bargonka, se in shimfiɗa a ƙasan"
"Baki da hankali" shine amsar da ya bata ya kwanta.
Haka ta duƙunƙune a cikin hijjabinta, tana karanto duk Addu'ar da ta zo bakinta.
Cikin dare Sadik ya farka ya ganshi ba a cikin bargo ba, yana kunna fitila ya ga ta É—auke bargon da filillukan ta barshi a haka, yana can yana bacci.
Seda ya kusa zagi, ya sa hannu ze fincike bargonsa daga jikinta, amma hakan ya sa ta farka a matuƙar razane, kamar numfashinta ze ɗauke.
Tunda Sadik yake be taɓa ganin mutum me tsoron tsiya irin Nana ba.
"Dan kin raina min hankali, shine kika janye min bargo da fililluka?"
Se ya lura kamar a gigice take gaba ɗaya, se maida numfashi take, sam ba ta jin me yake cewa, yaga idan ya matsa kar ta zo ta haukace masa, ƙarshe se ƙyaleta yai.
Faruk ana idar da sallar Asuba, yaje ya samu Mother yai mata sallama, sedai a wannan karon ma se da tai kuka, Faruk akwai biyayya tai masa Addu'a ta fatan Alkhairi, Abba ds Usman ne zasu kai Faruk airport, suna shirin tafiya Khairat ta fito, idonta jawur alamar tayi kuka.
Faruk ya sakar mata murmushi yace "Khairat, ko zaki bini ne?"
Ta girgiza masa kai tace "Allah ya tsare"
Yace "Ameen Bloody na, am gonna Miss you my chef, zan missing girkin ki wataran me daÉ—i wataran jagwalgwalo"
Su Abba su kai dariya, daga nan suka shuka shiga mota suka tafi.
Ta daÉ—e a gurin a tsaye, tana tunani kan ta koma cikin gida.
Zuciyar Farhan ta kasa gazagata cewar Sadik ya barta, tana ji a jikinta a kowane lokaci ze iya dawowa gareta, ko ta yi niyyar cire shi daga zuriyar ta, ko ta ji haushinsa se ta ji ta ka sa, se taji yakamata tai masa uzuri kan ta yanke masa hukunci, kullum Addu'ar ta Allah ya dawo da Sadik cikin Rayuwar ta.
Iyayen Sunusi sun aiko wai Ranar juma'a zasu kawo kayan lefe, duk unguwa ta É—auka Sunusi ze auri Farhan.
Wasu suna ganin an ƙwareta, wasu kuma suna ganin ze temaka mata ne, tunda ba wanda a unguwar ba shi da labarin an kamata ita da Abbas a gidan Hajiyar sa, Kamar yadda akai ta yaya tawa a unguwar.
"Ke! Ke! Wai ba zaki tashi bane?"
A hankali Nana ta motsa tai miƙa, tare da buɗe idonta tana ɗan tura baki.
"Dalla ta shi" Sadik yai maganar yana kallon ta.
Ta tashi zaune sannan tace "dan Allah ka dena ce min ke, ni bana so"
"Zaki tashi ki barmin ɗaki, ko sena ɓaɓɓala ki na bawa karnuka".
Ta tura baki tace "wallahi na fi ƙarfin karnuka su cinye ni. Yawwa nace me zanci da safen nan ne, wallahi jiya da yunwa na kwana"
"Se ki ci kan ki ai, ba uwar da ki ka iya dafawa, sedai nike nan cikin yawon nemo miki abunda zaki ci, har ki na gayan magana"
Nana tace "To akan me zan kuma garajen shiga wannan Kitchen É—in in ci wani abu, bayan ranar ka ce min nonon karya na sha, har yanzu istigfari nake Allah ya yafe min. kuma ni ban iya amfani da wannan kayan da suke a Kitchen É—in ba"
Sadik yace "tashi muje Kitchen É—in"
Nana ta miƙe ta bi shi, suka shiga nan ya dinga nuna mata komai da amfanin sa, ya nuna mata in da kayan Abinci suke.
Nana tace "ikon Allah shinkafa a kwali, ni na saba ganinta a buhu, ban taɓa zaton zan ganta a kwali ba, har su wake duk a kwali Lallai cigaba"
Sadik dai be kulata ba ya nuna mata yadda za tai amfani da gas cooker.
Nana tace ita Allah karta tsoron wannan abun take ji, kar yai bindiga da ita, sedai a san yadda za'ai a samo mata murhu, ko risho.
Sadik Kamar ya ɗora hannu a ka yai ihu, idan yai gabas se tai yamma, duk da ta ɗan waye amma haryanzu da ƙauyanci a kanta, wanda Sadik ya fi dangant hakan da hauka.
Ƙarshe Sadik ne ya kunna gas ɗin, Suka dafa tea, suka fere dankali su ka soya, kai kaca kaca da Kitchen ɗin, suna yi suna faɗa, Nana rashin kunya shi kuma masifa.
Suka gama, suka dawo falo su karya, Sadik ya É—akko ketchop ze ci dankali da shi, Nana tace ita ma ya samata ta ci da shi, yace mata jinin alade ne, in zata iya ci kuma shikenan.
Lilly ta ɗan ƙurawa Farhan ido, kullum jiya i yau, kullum rama take da tunani.
Lilly ta kalli Haseena tace "Hassyy, dan Allah ki bani lambar Khairat É—in nan mana, sister É—in Sadik"
"Me zaki da ita?"
"Se kin tambayeni, abu ne me mahimmancin gaske"
Haseena tace "gaskiya ba zan bayar ba, se kin gayamin me zaki da ita"
"Ke riƙe ki cinye in Abinci ce" Lilly ta faɗa a fusace.
Haseena tace "sorry masoyiya, ai bama haka bari in baki lambar"
Ta bawa Lilly lambar Khairat.
Dama Lilly so take ta kira Khairat, a gaban Farhan in da hali ta taimaka ta basu lambar Sadik ta ƙasar waje, sedai Farhan ba ta gurin zamanta.
Library ta tafi, dan mafi akasari yanzu nan ne gurin zaman Farhan.
Aikuwa tai sa'a ta tarar da Farhan a Library, sedai idanunta sunyi wani irin ja, kamar wuta ta ƙurawa guri ɗaya ido.
Lilly tace "Farhan, ga lambar ƙanwar Sadik Khairat, na karɓo se mu kirata"
"No need" Farhan ta faÉ—a a hankali.
"Meyasa zaki ce haka? Ai yakamata kiji a wani babin ya ajiyeki, dakon soyayya wahala ce Farhan"
"No need! Soyayya ta da Sadik RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai, an sha gayamin ban yadda ba, duk Makaranta ta ɗauka he got married to his cousin"