Sashe 97
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farhan ta kalleshi da mamaki tace "saboda me?"
"Saboda shine jigon matsalar ki, dawowarsa tamkar yaye fiye da rabin damuwarki ne"
"Doctor dan Allah ka dena wannan maganar, me zanyi da Sadik for God sake? Kalli irin rayuwar da na faÉ—a saboda soyayyarsa, me dawowarsa ze amfana min? Ni dai ba kuma gangancin komawa soyayyarsa zan ba, dan haka dawowarsa rayuwat ba amfani"
"Idan ke kin dena son shi ai shi haryanzu yana sonki, kuma yana kishinki"
"Dan Allah doctor ka bar Wannan maganar ka ji, kayi haƙuri Please"
"Ai ba ki min laifi ba"
"No, na maka laifi mana, gashi har ka faÉ—a min. ina neman afuwarka Please"
"Farhan kenan, to naji shikenan ya wuce, yanzu me kike so ayi?"
"Ina son kaje ka karya, ka zauna a office ka duba marasa lafiya"
Abbas yai murmushi yace "ya akai kika san ban karya ba?"
"Doctor saboda na san damuwa farin sani, na san wahalarta da ƙalubalenta"
Murmushi kawai yai ya sakko daga kan gadon, ya biyo Farhan suka fito.
A ƙasan zuciyar Inna tana jin tausayin Nana, amma ta danne dan da Nana ta gano hakan za ta cigaba da taɓara, da iya shege kala kala, dan haka ta danne ta ƙi nunawa Nana tana tausayinta.
Tana zaune tana ta uban kuka, Sahal ma kukan yake ta tsalawa, Inna tai faÉ—an tai faÉ—an amma Nana tai burus tana ta kukanta.
Sallamar Sadik da ta ji se da ta tsagaita, dan tabbatar da in Sadik É—in ne da gaske.
Sallama ya sake yi, Inna ta amsa masa, Sadik ya shiga cikin É—akin, yana shiga su kai ido huÉ—u da Nana, da idanunta su ka kumbure saboda azabar kuka da kishi.
Ya gaida Inna ta amsa masa cike da kulawa, ta tashi ta ba shi guri, ya nufi in da Sahal yake tsala kuka, ya É—auke shi jikinsa duk a sanyaye, ya rungume Sahal a jikinsa yana rarrashinsa, Nana ko kallon in da yake ba tai ba, ta É—auke kanta.
Sadik ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya zauna amma ta ɗauke kanta.
"Besty" ya kira sunanta.
Wata uwar harara ta wurga masa, cike da tsiwa tace "Nana dai kamar yadda kowa ke kirana, ba wata Besty ba sunan yaudara"
"Nana nine nake yaudarar ta ki?"
"Au to da me kake? Tun da nake da kai ka taɓa gayamin kai ka na da wadda kake so? Ka dinga cewa kana sona ashe kai da wadda kake so rainamin hankali kawai kake"
Sadik yai ajiyar zuciya yace "Husna, meyasa kika taho ba izini na?"
"Saboda ba zan koma in cigaba da zama da kai ba, daga nan sakina za kai ka ɗau ɗanka ka kaiwa wadda kake so ta riƙe maka"
"Nine zan sake kin?"
"Eh ka sakeni"
"Haba Nana, ina ilimin naki na addini, Wallahi baki ƙarasa jin abunda zan faɗa bane ranar, ina sonki Nana, ƙara Auren da nake son yi, ba dan in cuzguna miki bane dalili ya kawo hakan, kar ki manta gidan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam mata goma sha ɗaya ne".
"Eh mana, tunda nake da kai ba ka taɓa cemin Annabi yace ba, se yanzu da yake Aure zaka ƙara, zaka wani fara cemin meye meye, waima ta yaya zaka iya riƙe mu mu biyu? Gaba ɗaya shekarunmu nawa ne, ni Wallahi ka gama dani ka gama raina min hankali, kawai kaje ka bawa Hakimi takarda ta"
Sadik yace "haka kike so?"
Tace "eh, haka nake so"
"Shikenan, tashi muje gurin Hakimin ki gaya masa, abunda yace shikenan"
"Ni ba zan wani je gurin Hakimi in gaya masa ba, kai ne zakaje ka gaya masa"
"Malama, ba sakin kike so ba tashi mu tafi gida"
"Wallahi ba zan tafi ba, ai ba asararriya ce ni ba, da zaka ce ba ka sona ba, kuma in koma in cigaba da zama da kai ba"
"Nana, da ba na sonki ba zan biyo ki nan ba, dan Allah kizo mu koma gidanmu, Please".
Se kuma kayi, tai maganar tana juya masa ƙeya.
"Ke Nana ku hanzarta, ku zo kuyi sallama da kakanku kuzo ku wuce ku tafi" cewar Inna da ke tsakar gida.
Ai take Nana ta sake fashewa da kuka, Inna taga abun Nana nayi ne, dan haka ta dinga zaginta ta sa ta a gaba, ta shirya suka shiga gurin Hakimi, ya daÉ—e yana musu nasiha, Sannan suka nufi tafiya.
Ta ajiyewa Sadik Sahal a gaban mota, ta koma bayan mota, tai zamanta.
Sadik ya fara jinjina yadda ze fara zama da Nana da Farhan, kowacce be san halinta ba se yanzu da wannan Magana ta taso.
Har suka je gida Nana ba ta kula Sadik ba, yai surutun harya gaji tai masa banza, ta ma yi kwanciyarta a bayan mota ta bar shi da É—ansa.
Mother tayi mamakin yadda Nana ta dawo, amma ba abun mamaki bane dama ta san Inna ba zata barta ba, tun da Nana ta dawo, ta bawa banza ajiyar Sadik, dama ba girki take ba, daga cikin gida ake kawo musu, sedai idan tana son ta girka masa wani abu, ko kuma yace yana son ta dafa masa wani abu, idan tai wankanta ta gyara É—anta se tai tafiyarta É—akin da ke sashin Mother tai zamanta.
Sadik be taɓa zaton son da yake wa Nana ya kai haka ba, se da ta dena shiga sabgarsa gaba ɗaya, lokacin da suke normal in dai yana nan tana jikinsa, tana zuba masa shirirta suyi ta ƙuruciyarsu tare, ga uwa uba ba shi girmasa da take yi, duk da Nana akwai lafiyar tsiwa amma ba ta raina Sadik ba, ba shi girma da take yasa take ƙara burge shi, sam ta manta da miyagun maganganu da yake mata a baya, saboda ba sa jituwa in sun tuna ma sedai kawai tayi dariya.
Amma yanzu gaba É—aya ta buntsure ya kasa gane kanta, yai missing É—inta over, ko gurin kwana ba ta haÉ—awa da shi.
Yanzu ma ya dawo daga gidansu Farhan, amma be samu ganin Farhan É—in ba, ga wata irin yunwa da take addabar cikinsa, ya tarar ta tsuke a cikin wando da vest, sabgar gabanta kawai take kamar ba ta ganshi ba, ga gashin kanta da tai parking ya sha gyara, da da ne idan be yaba ba da ya sha mita da haÉ—e rai, ta dinga binsa kenan tana wai ba ka ganni bane? Amma yau ko kallo be ishe ta ba.
Kamar me jin tsoronta yace "Husna dan Allah zan sha tea"
Ba ta amsa masa ba, ta shiga kitchen ta dafa ta kawo masa, daga nan ta wuce É—aki tai kwanciyar ta.
Har bacci ya fara ɗaukarta, taji yana shafa gashin kanta, da yake ta ƙamshin man gashi.
"Meye haka wai?" Tai maganar tana ture hannun Sadik.
"Nana, nine fa"
"Kai É—in fa lafiya?"
"Tambayata kike lafiya dan na zo in da kike? Kina ganin abunda ki kai na watsar da ni kin kyauta dan kawai nace zan ƙara Aure, gaba ɗaya kin ƙaurace min?"
"Kai da za kai sabon Aure a kawo maka amaraya, me kuma za kai da ni? Dama amfanina gurinka kenan, ka biya buƙatar ka in samu ciki in haihu, matar so tana nan tafe za'a kawo maka"
"Yasalam, Wallahi Nana ba dan wani abu nake son yin Auren nan ba, kuma ni ba don abunda nake sonki kenan ba, ina sonki ne saboda Allah, amma kiyi haƙuri".
Daga haka ya juya mata baya, yai shiru yana tunanin meye mafita a gare shi, dan ya rasa mema Yakamata yayi akan wannan al'amarin.
Can dare Nana tai juyi, ta zata bacci yake, gari yayi sanyi sosai sedai Sadik be rufa ba, saboda a yanzu ko sanyin ba ya ji, ta janyo bargo ta lulluɓe shi, ta dafa goshinsa taji ya ɗau zafi, ba ta sauke hannunta ba ta shiga karanto masa adduoin bacci, da sauran adduoin da suka sawwaƙa a bakinta, dan ita ce take sa shi a gaba yayi dama kan su kwanta, se suyi tare dan haka yanzu ta san ba lallai yayi Adduoin bacci ya ɗauke shi.
Ta idar ta tofa masa, ta sake rufeshi sanann ta kuma juya masa baya.
Sadik ya sauke ajiyar zuciya a ransa yace "You love me too Husna, kishi ke damunki, amma ta ya zan wulaƙantaki, zan yi haƙuri da duk abunda zakiyi, Allah ya kawomin mafita"
Saukar numfashinta ya fara ji, alamar bacci ya kwasheta, ya matsa kusa da ita, ya rungumota jikinsa yana shaƙar sassanyan ƙamshin da take, yana jin yadda yai kewarta, amma Yanzu da yai yunƙurin wani abu, ko za ta yadda se sunyi faɗa, shi kuma baya son ya takurata sam.
Usman takanas ya zo gidan, da Mother ta ba shi labarin abunda Sadik ya É—akko, kuma kakansa ya bashi goyon baya, har gida ya zo, ya samu Sadik ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, yai masa tatas ya zage shi.
"Guda nawa kake dudu, shekarunka nawa saboda hauka da rashin hankali, kace wai zaka ƙara Aure, dan ubanka dukiyar da kake taƙama da ita, ai ubanmu ne ya tara sanannan muka samu, kuma kasuwanci yi maka ake, ba kai kake yi ba, ba ka san wahalar komai ba, makaranta ma kaƙi komawa, sedai ka ci ka tara mata, kai ga wanda ya kawo jarabar bin mata duniya, to Wallahi ka shiga hankalinka idan ka sake ɗaga wannan maganar se nai maganinka Wallahi"
Sadik ya fusata ainun, su ba su san ɓarnar da ya tafka a bayan ƙasa ba, su ƙyleshi tun da yana da halin riƙewa yayi, amma anyi caa a kansa, iya haihuwar da Nana tai, ya isa su ɗau darasi amma an kasa fahimtar sa, shi ba dan Nana ta gaza ze Auri Farhan ba, sedai Auren Farhan shine mafita ɗaya da ze cetota kuma ya wanke lafimsa na baya, ya nawa Farhan son da baya tunanin ko Aure tai ze iya rabuwa da ita, a irin son da yake mata, kowane hali take ze iya haƙuri ya aureta, amma kowa yaƙi fahimtar sa, yaji haushin maganganun da dr. Yai masa, amma be ce uffan ba ya bar masa falon shi da Mother, kuma be ji alamar ze janye abunda yai ƙuuduri ba.