Sashe 54
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Mother ta kalli Faruk tace "ni miƙomin wayar in ga meka nuna masa haka?"
Faruk ya miƙa mata wayar, hoton Sadik ne a beach, daga shi se gajeren wando, ya tara uwar suma kaya guda a kansa, ya yiwa gefenta ado da pink color, ga matan turawa da bikini, irin watsatsun kayan nan da suke sawa, halittu a waje, duk halittu da tsiraicin su a waje.
Ya ɗaura wani ƙaramin abu a wuyansa, fuskarsa ɗauke da baƙin glass, matan nan duk suna kusa da shi su kusan huɗu a kai hoton.
Mother tai scrolling, hotuna kala kala, na Sadik da wannan mata, wasu da abokansa, wasu a club babu guda É—aya da yayi ma a cikin ajin.
Mother tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Faruk meyasa ka nuna masa?"
Faruk yace "wallahi rikicewa nayi, kuma ko ban Gaya masa ba ze iya samun labarin hakan"
Mother tace "kaiii, Sadik sam baya gudun matsala, kullum cikin jawa kansa magana yake, Allah kaÉ—ai yasan hukuncin da ze yanke a kansa.
Ta tashi da sauri tabi Abba É—akinsa, ta tarar da shi a zaune a gefen gado ya dafe kansa, yai shiruuu yana tunani.
"Abba dan Allah kar wannan abun ya É—aga maka hankali, abi komai a sannu"
Abba ya kalleta yace "karya ɗagamin hankali kika ce? Meyasa ke kullum ƙoƙarin ki ki kare yaran nan in sunyi laifi, ba tunanin yadda za'a maganace matsalar da suka ɗakko ba?. Ba zan ɗauki wannan sakarcin ba sam.
Se yanzu na sake gane hikimar Hakimi, da yace kar a turashi ƙasar waje karatu, kin sa ina ganin kamar takurawa yaran nan ake, amma Sadik kam fitinar sa ta shallake tunani na, duk 'yan uwansa da sukaje su kai karatu ba wanda yai haka se shi, gaba ɗaya ya fita zakka a cikin yaran nan, babu wanda yai fitinar sa, dole ya dawo gida, yazo yai karatun a nan, nan da shekara goma ƙila ya gama degree, iya azabar strike da strees na karatun Nigeria ma ya ishe shi"
Mother tace "dan Allah Abba, kar kace ya dawo yayi karatu a nan, dan Allah kayi haƙuri"
Abba ya miƙe yace "se kuma kiyi" daga nan ya fice ya bar mata ɗakin.
Wayarta ta É—akko, ta kira wayar Sadik, ta kirashi ya kai sau huÉ—u sannan ya É—aga, yana É—agawa yace "what's up Mum, am sorry bana kusa da wayar ne"
"What's up É—in ubanka? Sadik meka aikata haka?"
A ɗan shagwaɓe yace "me nayi?"
"Kamar ya me kayi, dama abunda aka turaka ƙasar waje yi kenan? Hotuna da 'yan mata tsirara"
Yace 'Mother, ba fa wani abun nai ba, naje beach ni da friend's É—ina ne, suka ganni sukace suna son muyi hoto tare, so ni kuma naga ba wani abun bane dan dai hoto kawai shine mukayi"
"Zakaga ba wani abun bane, aikuwa gashi nan ya fusata ya fara iƙirarin seka dawo Nigeria"
"In dawo Nigeria kuma? Ya akai yaga hoton ne?"
"Muna zaune muna cin abinci, Faruk ya gano hotunan a social media, ni dai ba ruwana"
Sadik ya marairaice yace "haba Mother, ba fa wani abun bane, dan Allah ki ganar da shi, ya za'ai ace in dawo Nigeria, ai se ai min dariya ma, dan Allah ki bashi haƙuri"
Mother tace "Ni kai na ba zan so ka dawo Nigeria ba, amma dai zan an yadda zan da shi, amma ka kiyaye na gaya maka, idan ka kuma É—ebo wata rigimar zan sa muku ido"
"Ok, Mum thank you very much I miss you so much"
"I miss you too, ya school É—in?"
"Alhamdilillah, mun kusa fara exams ma"
"To masha Allah, Allah ya bada sa'a"
"Ameen, ashe Broz shima ya kusa tafiya ya barku ku kaÉ—ai?"
"Eh a wannan watan ze tafi matsers Insha Allah, Allah ya bada sa'a"
Ya amsa da Ameen sannan ya kashe wayar.
Ana ta hayaniya gidan su Farhan, Abba ya dawo ya tarar da su cireki cirko, yace "lafiya meke faruwa ne?"
Umma tace "yarinyar nan ce, muke tunanin ko iska ta tayar"
Cikin rashin fahimta Abba yace "Iska kamar yaya?"
Adda Maryam tace "yo tun da ta shigo, ta wuce É—aka ta faÉ—a kan katifa ba ta kula kowa ba, shiyasa nace wannan hadda lamarin iskokai"
Sunusi ne yai sallama a gidan ya risina ya gaida su Umma.
Abba ya kalli Sunusi yace "ya akayi ne?"
Umma tace "na aika a kirashi ne, ko karatu za'ai mata"
Abba yace A'a ba ta kai ga haka ba, bari inga Farhan É—in.
Abba ya shiga É—akinta, ya tarar da ita a kwance ta lumshe idanunta, kanta ko É—ankwali babu, gashin ta duk ya cukurkuÉ—e, da alama ko tazar Kirki baya gani, gata masha Allah tana da gashi Sosai.
Abba ya ɗakko bedsheet ɗin dake kan katifarta a ninke, ya lulluɓa mata, sannan ya sa mata hula a kanta.
Adda Maryam ta buɗe baki tana kallon ikon Allah, yadda yake taɓa 'yar sa ta fari ba kunya.
A hankali ya kira sunan Farhan.
Da ƙyar ta buɗe idanunta da su kai mata nauyin gaske, ta kalli cikin idon Abba.
Seda ya tsorata ganin yadda idanunta su kai jawur, tamkar an zuba mata barkono a idon.
Yace "meya sameki haka?"
Ji tai kamar tace masa Auren nan ne ba ta so.
Amma ta lumshe Idonta.
Ya kuma cewa "ki gayamin meke damunki?"
A hankali ta nuna masa kanta da ƙirjinta.
Abba yace "ciwo suke miki?"
Ta jinjina masa kai, "Sannu Allah ya baki lafiya, bari muzo mu tafi Asibiti"
Tai saurin girgizawa Abban kai.
Abba ya kalli Umma yace 'ko tana da sauran magungunan ta, a bata ta sha?"
Ita Umma ko kalar magungunan Farhan É—in ma ba ta sani ba, balle ta san ko akwai ko babu.
Tace "ni ban san in da ta Ajiye magungunan ba"
Abba yace "shikenan, bari inwa Ko Isa me chemist ne magana ya zo ya duba, yaga maganin da za'a bata, in kuma Asibiti zamu tafi shikenan"
Abba ya fito tsakar gida, ya tarar da Sunusi a tsaye, ya kalleshi yace "karka damu, ba wasu iskokai da suke damunta, Kamar wannan ciwon da tai ne, tace kanta da ƙirjinta ke ciwo, bari inje gun yaron nan me chemist ya zo ya ga abunda ya dace ayi"
Sunusi yace "Abba ai duk ba se anyi wannan ba, bari inje in mata rubutu yanzu zata warware, ba se an kira wani ya dubata ba"
Abba yace "ban ƙi ta taka ba, amma a dubatan ma yana da kyau, saboda a san daga ina matsalar take, karka damu"
Abba yaja Sunusi suka fita.
Farhan kuwa ita kaÉ—ai ta san abunda take ji a ranta, kwata kwata ko surutun mutane ba ta son ji, ji take ina ma zata samu wani guri in da zata kasance ita kaÉ—ai ba tare da wani ya takurawa Rayuwar ta ba.
Ba a jima ba se ga Abba da me chemist, tana nan kwance ya auna BP ɗinta ya ga ya hau, ga zazzaɓi da ya rufeta.
Ya kalli Abba yace "gaskiya jininta ne ya hau, kuma naji ga jikinta da zafi sosai, bari in bata taimakon da zan iya, da yamma abunda hali yai in ta warware shikenan, in bata warware ba se a tafi Asibiti".
Abba yace "ba damuwa, amma ina mamakin abunda yake sa Yarinyar nan hawan jini haka, 'yar mitsitsiyar yarinya kamarta"
Ya saka mata ruwa da allurai, nan da nan wani wahallalen bacci yai awon gab da Farhan, wanda rabon da tai baccin awa biyar cikakke har ta manta.
Sunusi Kuwa cika yai tayi yana batsewa, yana hura hanci.
Haladu yace "wai yau kuma kai da wa kake ta wannan buɗe ƙofar hanci haka?"
"Wannan mutanen mana, kawai idan yarinya ba ta da lafiya se kira wani, kwazgwamemen ƙato ya rufu a kanta,nace in mata rubutu ya isa amma babanta yaƙi"
"Kaga Sunusi, har yanzu fa baka Aureta ba, suna da cikakken iko akan 'yar su, kai ka fiye Matsala wallahi"
"Wace irin matsala? Ya ni da matata ba zan kishi a kanta ba, ni bama wannan ba, ina ga nayi nasara akan wannan yaron da take kulawa Sadik, naga bam sake ganinsa ba, yanzu É—an gidan waccan matar ne naga yana rawar kai da shishshsige mata, wallahi idan be wasa ba idan nai masa wani zazzafan aikin, se ya kusa haukacewa"
Haladu yace "Subhanallah, Sunusi wannan kuma ai kazo da son zuciya, ya zaka haukata mutum akan abunda be kai ya kawo ba"
"Agurinka ne be kai ya kawo ba, ni agurina lamari ne me girman gaske, kana ganinsa da kyau da Mota, ni ina yawo a ƙasa haka kurum inje ta koma son sa, ni nayi nayi ta soni Yarinyar nan taƙi, kwata kwata aiki baya tasiri a kanta sam, yi nake amma Kamar bana yi"
Haladu yace "to ai kaine baka mata yadda suke mata, shiyasa taƙi sonka, ka dena mata hargowa da nuna isa, kalli Ranar da suka fito da ɗan gidan Hajiyar nan, kamar ze shige cikin ta, babba da shi amma yayi ƙasa da muryar sa, se Magana yake mata cikin nutsuwa, kai kuma komai naka cikin hargowa kake yi mata, kalli yadda ka tara mu a ƙofar Gidan nan dan Allah, ka gayamata miyagun maganganu a gaban mu, ta yaya zata soka?"
"To nima ɗin ce maka a nai bana mata, wallahi ina lallaɓa Yarinyar nan shegen taurin kai ne da ita da kuma kwaɗayi, su suke ɗawainiya da ita kawai"
Haladu yace "to Allah ya kyauta, kamata yai dai ka gano in da matsalar take ka gayara, ni zanje aiken da malam da yai min"
Sunusi yace "seka dawo"
Farhan ba ta sake sanin in da kanta yake ba, se bayan sallar magariba, ba ƙaramin jin daɗin baccin nan tai ba, dan rabonta da bacci haka har ta manta.
Adda Maryam ta haɗa mata ruwa tai wanka, amma Abinci ya gagara ciwuwa, da ƙyar ta sha tea, tace ta ƙoshi.
Abba ya ƙi gayawa Mother matakin da ze ɗauka akan Sadik, tunda yace se Sadik ya dawo gida be kuma ce mata komai ba.