← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 115

Sashe 17

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani marurun takaici ya tokarewa Mother rai, saboda tsabar abu da rashin hankali irin na Faruk, wannan ƙungurmin ƙauyen yabi mahaifinsa, abun takaicin ma wai shi ze ja motar har can, ta ja ƙaramin tsaki ta juya ta koma.

Sadik ƙarfe goma ya tashi kamar yadda ya saba tunda ya gama makaranta, wayarsa ya fara ɗakkowa ya duba messages ɗin Farhan, murmushi yai, tare da kissing ɗin message ɗin yace "ina sonki Babyna, amma dole ina nuna miki rashin jin daɗi na akan laifin da ki kai min" ya ajiye Wayar ya shiga yai wanka ya fito ya tafi sashen Mother.

Yaje ya tarar da ita a zaune tayi shiru, an kawo mata breakfast amma ba ta ci ba.

"What's up Mom, Good morning"

Ajiyar zuciya tai tace "ka tashi kenan?"

"Eh Mother, wai na ganki somehow worried, meke faruwa ne?"

Nan ta gaya masa abunda ya faru, da yadda Abba da Faruk suka tafi ƙauye.

Sadik yace "to Mother meye abun damuwa a nan? Zaki zauna ki ƙi cin Abinci?"

"Bari Sadik, nasan da kaine ba zaka min wautar da Faruk yai min ba, saboda tsabar shirme ya san halin babanku da ɗaukar zafi amma yaimin wannan kwaɓar haka, yadda kasan in mangare shi wallahi, yaita abu kamar ƙaramin yaro, wai a nan ya kammala degree ze koma masters, amma yai ta abu kamar wani mara wayau"

"Easy Mother, ni wallahi idan kina masa faÉ—a haushi nake ji, bana son inji kina masa faÉ—an nan wallahi"

Mother tace "Au goyon bayansa kake?"

"A'a ba goyon bayansa nake ba, kawai dai bana som in ga ana ɓata masa rai ne, duk da nima wasu lokutan yana ɓatamin rai, amma haƙurinsa ne yasa yake ban tausayi, dan nafi sonsa akan wannan dukun dunkun ɗin"

"Waye dunkun dunkun É—in?"

Sadik yai murmushi yace "ba kowa, amma dai na ari bakins na bada haƙuri, dan Allah ayi haƙuri a dena mai faɗa, ji nake kamar ni akewa"

Mother tace "to me É—an uwa, nima ina son abina ai, dan duk ya fiku hankali"

Sadik kawai ya girgiza kai yace "Mother kina da abun mamaki, bari in zo in karya"

Ya fara haÉ—a kayan tea da suke gaban Mother ya fara karyawa, ya barta da tunani.

Farhan Alla Alla take a tashi, Sadik ya zo ɗaukarta ta kuma bashi haƙuri, sedai direba ya turo ya ɗauke ta shi be zo ba, ji tai kamar tace ba zata bishi ba, amma gudun karta kuma wani Laifin yasa ta bishi ya kaita gida.

Abba wajen ƙarfe goma na safe suka isa.

Sedai jikin Hakimin da sauƙi, amma dai yayi rama sosai da alama ya sha jiki.

Inna tace "Allah yayi ka zo kenan Hakima ta barka ka zo duba shi?"

"Inna ba haka bane, bana gari ne, shiyasa kuma itama ba ta da lafiya wallahi ban sani ba"

"Eh ai dama ba za saka sani ba, tunda da ka dawo baka damu da kazo in da muke ba, ni ban damu lallai seka zo ba ma, ai ko ta waya ka kira kaji yadda muke, Abdullahi ka kiyaye ni fa"

Abba ya kwantar da kai ya dinga ba da haƙuri.

Faruk yace "Inna na Nana ne?"

Inna tace "ta tafi Makaranta, se anjima zata shigo"

Inna tai ta yiwa Abba faÉ—a, Faruk ya koma kusa da Hakimi ya É—auki man zafi ya dinga shashafa masa a bayansa zuwa hannayensa, yana mammatsa masa yatsunsa cike da kulawa da tausaya wa.

Hakimi yace "Anya ba za'a bar min wannan mutumin a nan ba, ya iya jinya fa" yai maganar cike da zolaya.

Abba yace "ko Asibitin cikin gari za'a tafi da shi a duba shi sosai?"

Hakimi yace "A'a, ga ƙaton Asibiti nan da ka gina mana, akwai kayan aiki sun min duk abunda ya dace, dama hawan jini ne, kuma sunce ya sauka Yanzu Alhamdilillah"

Faruk yace "Ai can akwai ƙwararru fiye da nan, ka bari mu tafi da kai kawai, kaga daga nan semu riƙe ka, ka barwa Hajiya Inna karagar"

Sosai Hakimi yai dariya, har seda wushiryarsa ta fito yace "waini ina Ango ne, da kuma shi wancan É—aya abokin nawa?"

Abba yace "Usman baya gari, shi kuma Sadik basu daÉ—e da kammala jarrabawa ba, muna masa shirye shiryen tafiya karatu ne"

Tunda Abba ya fara wannan bayanin Inna ta ƙura masa ido, ya kai aya sannan tace "Ina ze tafi karatun?"

Abba yace "ƙasar waje ne, kamar yadda 'yan uwansa suma su kaje, Faruk ma ya kusa komawa Master's"

"Shi Wannan fitsararraen yaron zaka kai ƙasar waje karatun?"

Abba yace "Inna ai ba wata damuwa, karatu kawai zeje yayi"

Inna tace "gaskiya ne"

Faruk ya samu fura da kilishi ya dinga ci, Abba yace "kaga kaci a hankali, in ba haka ba ze ɓata maka ciki, kuma ba banɗaki a hanya sedai ka yanki jeki kaje kayi"

Faruk yace "Abba ai a can ba Fura me daÉ—in wannan" hira suke sosai, yayin da Inna ke ta maimaita batun tafiyar Sadik cikin turawa yayi karatu.

Suna nan zaune se ga Nana ta dawo daga Makaranta, kasancewar tsananin soyayya dake tsakanin Hakimi da Nana, tunda ya fara rashin lafiya, duk in da taje ta dawo gueinsa take fara zuwa ta ga jikinsa, ko cikin dare se ta É—au fitila taje ta haska taga ko yana numfashi.
Ranar da jikinsa ya hana shi cin Abinci kuwa, ita ma ba zata ci ba.

Shiyasa tana shigowa ta nufi turakar sa, tana faÉ—in "Inna ya jikin Kakana?"

Inna tana daga ɗakin tace "ban sani ba, tunda ba zaki iya ƙarasowa ki gani ba"

"To ai Inna takalmi na nake cirewa, yau ba abunda na gane a makarantar nan, duk hankalina yana gida ji nake kamar in gudo gida in ganshi".

Ta ƙarasa maganar tana shigowa ɗakin, sedai tai turus ganin su Abba da Faruk.

Murmushi tai da ta ga Faruk, ya miƙa mata hannu da nufin su gaisa, wani irin kallo Inna tai mata, wanda ya sa Nana tsugunawa tana gaishe su.

Abba yace "Hajiya ta, ya makarantar?"

"Lafiya ƙalau, ya aiki?"

Abba yace "Alhamdilillah, ya me jiki?"

"Da sauƙi Alhamdilillah" ta miƙe ta nufi gurin Hakimi, ta ɗora hannunta a goshinsa tace "Sannu ya jikin naka?"

Hakimi yace "naji sauƙi tunda naga ɗana"

Nana tace "Inna kin bashi Abinci ne?"

"A'a babata ke nake jira ki zo ki dafa ki bashi, ke da ba'a iya miki daga ke har kakan naki"

Ba ƙaramin dariya Inna da Nana ke bashi ba.

Lokacin sallar Azahar yayi, Sukai alwala suka tafi salla, har da Hakimi.

Bayan sun idar Abba da Hakimi suka tsaya a É—akinsa na waje, in da mutane ke cigaba da zuwa dubiya.

Faruk ya shigo gidan, ya tarar Nana tana cin Abinci, ya tsaya yana kallonta, ya shafi sumar kansa tare da yi mata murmushi yace "Shine kina kallona kika ƙi kulani ko?"

Murmushi tai tana ɓoye fuskarta a tsakanin cinyoyin ta.

Ya zauna a gabanta yace "Abincin ma baki iya yiwa mutane bismillah ba, bani cokalin muci tare"

Ɗagowa tai ta zaro ido, taci Abinci da namiji, taɓ ashe yau zata sha terere a gurin Inna, kan ta yunƙura ta tashi Inna ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta.

07063065680

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Zazzare ido Nana tai, Inna ta zabga mata uwar harara, sannan tace "me nake gani haka?"

Faruk ya kalli Inna sannan yace "taƙi kulani, ta gaida babana amma ni tai min banza, kamar ba ta Sanni ba shine na zauna inji ba'asi, inji dalilin hakan"

Inna tace "eh Lallai kam, gara kaji ba'asi" tai maganar tare da ajiue butar hannunta ta shiga É—aki.

Inna na tafiya Nana ta miƙe tsaye, Faruk yace "ina zaki kuma?"

"Wanka zanyi in tafi makarantar Islamiyya"

Yace "To shikenan, ki É—auke sauran Abincin kije ki rufe" Nana ta É—auka ta tafi ta ajiye sauran Abincin.

Faruk ya shiga É—akin Inna da sallama, ta amsa masa ya samu guri ya zauna.

Yace "Inna dan Allah ki bar mana Nana, mu tafi da ita a canza mata Makaranta"

Inna tace "Tofa wani sabon fi'ili, Nan É—in ce maka aka yi bata karatu?"

"A'a ba haka nake nufi ba, gidanmu ba 'ya mace ƙarama haka kamar ita, nifa wallahi ina son 'yar uwa mace, inji tana Yaya, ince na'am Sisto what do you want"

Inna ta bishi da kallo tace "kai kam akwai ka da iyayi na gaske, ba naga wannan Yarinyar a gidanku ba ai itama ƙanwarku ce"

Faruk yace 'Khairat ai ba ta zama a gidan mu, sannan dai ni Nana nake son ki bamu, in ga ina koya mata Assignment, in dinga kaita outing, in sai mata abubuwan da take so, i want pampered her"

"Kai ka san me kake faÉ—a ni ban san me kake cewa ba"

Yace "haba Inna, Ki bar mana ita dan Allah"

Inna tace "wai ni ko san Nanan nan kake ne a Aura maka mu huta? Wannan magiya haka"

Zare ido yai yace "Aure kuma? yanzu se aiwa wannan yarinyar Aure? Ai this is child abuse, ni ba Aurenta nake son yi ba, kawai so nake in ganta a gidanmu, ace ƙanwarmu ce"

"To bazan bayar ba" Inna tai maganar tana hararsa

"Inna dan Allah ki bamu ita"

"Kai nace Ba zan bayar ba, babanka ma yayi nacin ya gaji,  zan iya bada komai da na mallaka dan a barmin Nana, idan ina ganin ta Kamar mahaifinta nake gani, kuma idan na baku ita shikenan ba wanda zan kalla a gabana, ku ba zuwa in da muke kuke ba, wannan ɗin guda ɗaya ai kwa barmin" Inna tai Maganar ƙwalla na taruwa a idon ta.

Faruk yace "eyya, am sorry i understand you, na gane Inna, bakomai kiyi haƙuri, Allah ya jiƙan 'ya'yanki da kika rasa, ita kuma Allah ya rayata da Imani, dan Allah kar ki kuka, sannan in dai mune insha Allah kan in koma Master's zan dinga zuwa inyi kwanaki tare da ku" yai maganar cike da damuwa.
Chapter 17 · 0% Book details