← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 115

Sashe 49

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yarinyar nan ba ta son mutumin nan, sun san negative impact ɗin abunda suke shirin yi ka iya haifarwa? Yarinyar da ta farfaɗo da kyar kamar zata mutu saboda damuwa, ni da ita ta gayamin ba ta son sa, akwai wanda take so fa, tayi ƙanƙanta da irin wannan stress ɗin, what If she commit suicide? Ko ta faɗa wani hali da ba'a so?"

Hajiya tace "to rufeni da duka Abbas, tunda nice zan mata Auren, ko dai kishi ka ke ne, wannan zaƙalƙalewa haka?"

Abbas ya sassauta muryarsa yace "Hajiya, am a doctor, ina hangewa iyayenta abunda ze iya faruwa akan Yarinyar nan, mutane masu irin ɗabi'arta na zurfin ciki damuwa na iya kashe su lokaci ɗaya, ko kuma su sami taɓin hankali, da alama ba ta da wani wanda zata raɓa taji daɗi, sedai ba abunda take yawan nanata wa kamar Sadik, that means he means a lot to her, se su bincika waye Sadik? Kuma su ƙyaleta da Auren nan tunda ba ta so, tana nunawa iyayen duk hukuncin da su kai akanta dai-dai ne, su kuma zasu kashe ta indirectly, nace zan Magana da babanta amma taƙi yadda, wace irin rayuwa ce haka za'a kashe ƙaramar yarinya, waya san baiwar da Allah ya ajiye a tare da ita?"

"To, ni dai bani da ta cewa, tun da ba 'ya ta bace, abunda yafi kawai mu tayata da Addu'a, tunda 'yar su ce bamu da iko da ita"

Abbas yace "Allah dai kawai ya kyauta, Allah ya basu 'ya ta gari, amma za suyi dalilin shigarta wani yanayi a banza"

Ƙarshe Hajiya se bin Abbas tai da ido, saboda yadda ya zage yana ta surfa bala'i akan Farhan.

Farhan kuwa da Sauri ta wuce gida, tai sa'a ba kowa a tsakar gida, tana zuwa tai cilli da jakarta, ta faɗa kan katifa ta rintse idanunta, tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa, da tsananin ƙiyayyar Sunusi, so take ko bacci ta samu tayi, amma abu ya gagare ta gaba ɗaya, 'yan kwanakin nan sam ba ta bacci, se dai tai ta juyi  in ta gaji ta tashi tayi Alwala tai salla, tai ta gayawa Allah damuwarta.

"Yanzu dan Allah kaima Yaya Faruk tafiya za kai?" Khairat da ke zaune a kusa da Faruk yana shan tea tai maganar a shagwaɓe.

"Eh mana, me zan zauna in muku?"

Khairat tace "wallahi i will Miss you, the house will be so boring, ba kai ba Auta"

Dariya Faruk yai yace "ai sekin fi missing Sadik, shine abokin shirirtarki"

"Ai na saba da rashinsa a gidan nan yanzu, amma gaskiya sena fi missing É—in ka"

Faruk yace "ba wani, faÉ—i gaskiya ni a wa zaki missing É—i na?"

"Kai a big Lovely brother na"

Murmushi ya kuma yi me ƙayatarwa yace "wannan yabo haka? Ko dai wani abun kike buƙata ne?"

"Shikenan ba zan yabe ka se ina buƙatar wani abu?"

"Hmm, to ai shikenan godiya nake Lil Sisy"

"Kai ba za kai missing É—ina ba?"

"Mmm to, gani nan dai ban sani ba ko zanyi ko ba zan ba"

ÆŠan shiru tai ta zuba masa ido tana kallonsa.

Miƙewa yai ya na murmushi yace "don't mind dear, i will so much Miss you"

Yai Maganar tare da ficewa daga falon yana murmushi, tabi bayansa da kallo.

Ji take tamkar ta sanar da Faruk cewa son shi take, amma ba ta san ta in da Yakamata ta fara ba, gashi yana ta shirin tafiya, ta rasa yadda zata ɓullowa lamarin.

Kusan duk bayan sati biyu Steve yake zuwar wa Nana visiting, ya kawo mata provision saboda Ba Komai na Abinci ake bata ba, ba a bata abunda ya wuce tea, fruit ko chips se bredi, saboda suna amfani da Naman alade, ita Nana ba ta san dalili ba, ba ta damuwa da yadda ake bambanta su gurin Abinci, da safe ta sha tea da ƙwai ko dankali, ga kayan siyayyar tarkacen madara da kayan ciye ciye da Steve yake kawo mata yace inji Abba.
Nana tana karatu sosai, duk da idan rigimar ta ta motsa zata zauna tai ta kuka, babu wanda yake takura mata komai gashi nan a wadace ba takura, amma ita hankalinta ya na kan gida Nigeria, dan tafi sakewa a nan.
Tayi ƙalau da ita kamar ba ita ba, fatarta tayi fresh saboda zama guri ɗaya, shi kansa Steve yai mamakin ganin yadda Nana ta ƙara kyau a cikin ƙanƙanin lokaci, gashi har harshen ta ya fara sauyawa, babban abunda yai masa daɗi yadda malaman suka yabeta academically and morally.

Ya kira Abba ya gaya masa cigaban da aka samu game da karatun Nana, Sannan ya bata Wayar.

"Abba ina wuni"

Abba yace "A'a turancin dai za'ai min, ya Makaranta Nana"

"Lafiya ƙalau Abba, ya su Faruk da Mother da su Anty Jidda"

"Duk suna nan lafiya, ai last week naje gidan, Inna na ta gaishe ki"

Nan da nan ƙwalla ta taru a idon Nana tace "ya jikin Alhaji?"

"Ahh jikinsa yai kyau sosai Alhamdilillah, kun kusa hutun session ko?"

"Eh mun kusa, ai zan dawo ko?"

"No, kuyi zamanku ku cigaba da karatu, zamu zo ai, zamu shigo muku visting insha Allah, ga kilishinki kayan guda Hakimi ya bani, zan zo miki da shi"

Nana tace "to Abba nagode, in kunyi waya kace ina gaishe su, nayi missing É—in su sosai"

"Bakomai kiyi haƙuri, ki kwantar da hankalinki kinji, kiyi karatunki da kyau, Steve ai yana kawo miki kayan buƙatunki ko?"

"Eh yana kawo min, duk sati biyu se ya zo"

"To Alhamdilillah, ya ɓangaren addinin ki, ba wata matsala da kike fuskanta ko?"

"Ba wata matsala, ina addini na ba ruwansu da ni"

"To Alhamdilillah, ki kwantar da hankalinki kiyi karatunki, wataran se labari"

"To Abba, Nagode sosai a gaida su Mother"

"Zata ji insha Allah, Faruk ma ya kusa tafiya matsers É—in sa, gidan ze zama se mu kaÉ—ai"

"Allah sarki Yaya Faruk, ace ina gaishe shi Allah ya bada sa'a"

"Ameen ya hayyu ya ƙayyum, se anjima"

Sukayi Sallama, Mother da ta shigo tun É—azu ta kalleshi tace "wao da wa kake waya haka ne? Se murmushi ka ke?"

"Ni da Nana ne, naji daɗin yadda ake yabonta tana ƙoƙari Sosai a makarantar, na jinjinawa ƙoƙarin ta sosai da sosai, a 'yan watannin nan ace tana capturing abunda suke gaskiya tayi ƙoƙari"

Taɓa baki Mother tai, tai masa shiru ta cigaba da abunds take, dan ko sunan Nana ba ta son ji.

Sadik ya zama famous a Makarantar su, yana da abokai da ƙawaye kala kala, gashi yai suna a team ɗin su na ƙwallon ƙafa na makaranta, ga competition da suke na gyming, gaba ɗaya ya canza kamar baƙin bature, ya tara uban gashi kullum cikin kashewa gashin nan kuɗi yake.

Amin har baya son ya haɗu da Farhan, dan da sun haɗu take expecting samun wani information daga gare shi akan Sadik, yaje gidan su Sadik sau biyu amma tun a gate ake sanar da shi baya nan, kuma baam wanda ya taɓa gaya masa ga in da ya tafi.
Duk da Farhan ɗin ba tambayar sa take in da Sadik yake ba, amma ya san yai mata alƙawarin ze bincika mata in da Sadik ɗin yake.
Yau ma a Library suka haɗu, duk da ba karatu ne ya kaita Library ɗin ba, taje ne dan ta keɓe kanta daga mutane, ta zauna a in da suka saba zama ita da Sadik tayi tunaninsa sosai ba tare da wani ya takura mata ba.

Amin ya zauna a kujerar gaban Farhan yace "sannu ina fatan ban takura miki ba"

Tace "A'a bakomai"

Yace "Na san na miki alƙawari, akan bincika miki in da Sadik yake, wallahi zuwa na biyu gidan su, amma tun a gate ake cemin baya nan, naga an canza musu megadi da wancan ne mun saba sosai ze bari in shiga ciki ko lambarsa in samo, amma wannan bama ya bari a shiga gidan nasu, amma dai ba zan gaji ba zan cigaba da bincikawar"

Farhan tace "bakomai kar ka damu, hakan ma Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"

Yace "bakomai karki damu, ki kwantar da hankalinki nasan duk in da yake shima kina nan a ransa, kuma ze dawo gare ki"

"To shikenan, Allah ya sa"

Yace "insha Allah"

Tana Library, har aka tashi daga Makaranta ta tashi ta tafi gida, taje ta tarar Umma ta dawo daga kasuwa, ta yo siyayyar kayan Kitchen, ga Adda Maryam ta zo suna ta dudduba kayan da Umma ta siyo.

Adda Maryam na ganin Farhan ta fara rangaÉ—a guÉ—a, wai ga Amaryar su.

Murmushin yaƙen ma kasa ƙaƙalo shi tai balle taiwa Adda Maryam, kawai ta shige ɗakinta ba tare da ko gaishe ta tayi ba.

Shirye shiryen su kawai suke na biki, yayin da hakan ke baƙantawa Farhan ɗin rai, babu wani karsashi ko ɗoki na amare a tare da ita.

Duk da adda Maryam ta san Farhan ba ta da magana, amma tayi mamakin yadda Farhan taƙi kulata sam, duk rashin son maganar Farhan tana hira da Adda Maryam, ko ita ko Adda Hafsatu, amma wannan karon Farhan taƙi kulata.

Farhan haushin Adda Maryam take ji, dan tana É—aya daga cikin wanda suka taka muhimmiyar rawa, akan lallai se an aurar da ita, suka dinga bugo waya suna cewa lallai ai mata Aure, sekace ance musu lalacewa tayi.

Bayan magariba Farhan na kwance a É—akinta, yau ba Islamiyya, sedai wata irin kewar Sadik tana damunta, ga wani irin feelings from no where da ya dameta, wanda hakan kan faru a duk lokacin da ta kusa yin period.
  Juyi kawai take akan katifar ta, wasu hawaye masu ɗumi suna bin gefen idonta, Babu abunda take buri banda ta ji ta a jikin Sadik, haka kurum take jin kamar ƙamshin turarensa take ji.

"Yasalam kar in haukace" ta furta lokacin da wasu hawayen ke zuba daga idonta Kamar an kunna famfo, ko ba komai zubar hawayen ma samun sassauci ne a gareta.

Adda Maryam ta ɗaga labulen ɗakin Farhan tace "ke 'yar Fulani ban san me nai miki ba kin ƙi kulani, ko duk kunyar ce? Kije ana Magana da ke a waje, ina ga ko angon namu ne?"

Farhan tace "to zanje"
Chapter 49 · 0% Book details