← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 115

Sashe 67

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mother tace "Yasalam, ina fatan dai ka je Asibiti, dan na san halinka, ba ka son magani"

Yai ajiyar zuciya yace "ai ba wani abun damuwa bane zan ware Insha Allah"

Mother tace "A'a, babban ciwo da ƙarami yake faraws, kaje ka ga likita yafi"

Yace "to shikenan, insha Allah zan je ina Abba?"

'"Abbanku yana gurin aiki, ba ya gari"

"Ok, hakane na manta ne, ina Dr. Da Matarsa?"

"Duk suna nan lafiya ƙalau Alhamdilillah"

"Ba bu dai wata matsala ko?"
Mother tace "kai Sadik, ba wata matsala fa"

Yace "to shikenan, amma naji kimce Abba ya koma aiki, ya jikin Hakimin, za'a kai shi jamus É—in kuwa?"

Mother tace "eh to, ka san halinsa, ya ɗan samu sauƙi gaskiya, yace ba in da za shi, yaje a sake wahala da shi, a barshi ya mutu a ƙasarsa a binne shi cikin salama, ba se an kai shi ya mutu a can, a wahalar da gawarsa ba"

Sadik yace "Allah sarki, cuta ai ba mutuwa bace, Allah ya ƙara sauƙi"

Ta amsa masa da Ameen, da ga nan suka ɗan taɓa hira, sannan su kai sallama.

Still dai ya ji be samu nutsuwa ba, se da ya kira Abba a waya, nan ma ya dinga tambayar Abba Komai lafiya? Abba ya tabattar masa da komai lafiya, sedai su cigaba da yiwa Hakimi Addu'ar samun lafiya a gurin Allah.

Haka Sadik ya dinga bi yana kiran waya, yana jin lafiyar 'yan uwansa, da kowa da kowa, amma be ji ance masa ga wata matsala, haka ya haƙura ya ajiye Wayar, ya cigaba da zancen zuci shikaɗai.

Tun kan mutane su gama taruwa a wajen É—aurin Aure, Malam Zakari ya hallara, yana jiran zuwan Magabatan Sunusi, dan ya fuskanci alamu sun nuna kamar ba su da dattako ko kaÉ—an.
Da suka iso gari ma, ba su wuce ko ina ba, se gurin É—aurin Aure matan ne suka tafi gidan malam Labaran, aka sauke su a can, mazan kuma suka hallara a masallaci.
Sanin sanyin hali irin na Abban Farhan, ya sa Malam Zakari tsayawa bil haƙƙi, dan ganin ba a ƙwari Farhan ba.
Bayan an gama gaisawa, ana jira mutane su ƙarasa zuwa, lokaci ya cika afara ɗaurin Aure, a gaban Liman Malam Zakari ya kalli Sunusi da ahalinsa yace "Bayin Allah, ina alƙawarin da mu kai da ku?"

Wani kawun Sunusi yace "Wane alƙawarin kuma?"

"Eh, ai shi malamin da yaron sun sani, na farko ba ku gaya mana in da za'a ajiye mana Yarinya ba, sannan abu na gaba kamar yadda na gaya muku, mu a nan ba a É—aura Aure, se an kawo sakamakon gwaji Sannan ake É—aura Aure".

Ƙanin baban Sunusi yace "Ikon Allah, to ai batun in ds Yarinya zata zauna, anyi wannan maganar in da za ta zauna, ai can garin su yaron ne wato Sunusi, sannan ni ban san wani batun gwajin Asibiti ba, tun da mu a ƙauye ba a yi, amma kai Sunusi ya abun yake ne?"

Malam Zakari yace "eh ai shi ya san yadda mu kai da shi, be muku bayani ba dama?"

Sunusi yace "Nifa gaskiya ba ni da halin da zan wani kama mata gida a garin nan, dama a garin mu za ta zauna, nikuma ina nan ina ɗan buge buge na ina aikata mata, amma ai an san bani da ƙarfi, tunda ba kaina zan siyar in kama nata gida ba"

A nan 'yan uwan Farhan suka fara jinjina Wannan lamari, sam Sunusi ba shi da É—a'a, se wani Magana yake cikin gadara ba wani girmamawa.
Shi kansa Abban Farhan, be taɓa zaton haka Sunusi yake ba.

Liman ya kalli Sunusi da magabantasa yace "bayin Allah, ai ko a karkara ilimi ya wadata, ana gwaji kan Aure, dan haka mu a nan ba ma É—aura Aure se an kawo mana sakamakon gwaji, idan ba bu kuma zakuje se an kawo sannan zan É—aura Aure"

Malam Zakari yace "kuma, ba zamu bada 'yar mu a kai mana karkara ba, muna nan akan bakanmu, aka ma wa yarinya gida a birni, saboda karatun ta"

Liman yace "Malam Zakari, ai batun zama a ƙauye ko a birni, ba shi a cikin sharaɗin Aure".

Malam Zakari yace "duk da haka Allah gafarta malam, mu bamu gamsu da in da za'a kai mana Yarinya a ajiye ba, kuma shi angon ya san akan wannan sharaÉ—in muke"

Mutane sun gama taruwa, dan har sun fara ƙosawa, a ɗaura aure abu ya gagara, ga rana ta ɗaga Sosai.

Liman yace "to ku, kunji abunda iyayen wannan amarya suka ce me zaku ce, Sannan ya batun gwajin? A É—aga É—aurin Auren kuje ku yo gwajin ku dawo ne, ko zuwa in Allah ya kaimu la'asar se a É—aura?"

Malam Labaran yace "to, ni Allah gafarta malam, wai me ye amfanin gwajin nan ne? Me za'a gani a gwajin?"

Liman yace "Yawwa, abunda ya kamata dama ku tambaya a wayar muku da kai kenan, idan ba ku sani ba.
Shi wannan gwajin yana da mahimmanci ƙwarai da gaske, duba da yanayin cututtukan ƙarshen Zamanin nan da su kai yawa, akwai nau'in cututtukan da idan ɗaya daga cikin ma'aurata yana da shi ɗaya ba shi da shi, to ɗaya ze shafawa ɗaya.
Ko kuma, akwai kuma wanda idan suna É—auke da wani nau'in jini, ba ze yuwu suyi Aure ba, saboda za su iya samun yara marasa lafiya, masu É—auke da ciwon sickler wato Amosanin jini.
Idan aka kawo mana gwajin muna Duba, rukunin jinin ze yuwu ma'auratan suyi Aure, ba tare da sun haifi yaro me larurar sickler ba.
Muna duba ciwon hanta, tun da shima likitoci ance ciwo ne da ake ɗauka, amma shi ba a fiye damuwa da duba shi ba kamar yadda muke duba ciwon ƙanjamau, wannan shine mafi hatsari ma, tun da shi ciwon hanta ana warkewa, ƙanjamau kuwa ba a warkewa, ka ga kuwa gwaje gwajen duk suna da mahimmanci, dan tabattar da babu wanda aka cuta a lamarin".

Sunusi yace "ni lafiyata ƙalau, babu wani gwajin da zan yi, kawai an shigo da yahudanci cikin lamarin Aure, duk dan salon barin abunda addini ya ɗora mu a kai, ai idan ma cuta ce sedai a samu a jikinta ba ni ba, dama ai jihadi zan in Aureta, babu wanda be san yawo take ba.
Maza ne ka ɗaukarta suna yawo da ita a mota, saboda shegen son abun duniya. Ranar a gabana suka shiga gida ita da wani, sunfi mintuna arba'in sannan suka fito, kuma a gaban mutane suka fito, dan se da na kira shedu suka gani, ita ba a samu ciwon a jikinta ba se ni za a samu a jikina, na ga ai temaka mata zanyi, da an san ba za a bani yarinyar nan ba se an gama wulaƙanta ni, meyasa aka ce za a bani, ko da ma can ƙaƙaba min za ai an san ba ta da lafiya, ta gama yawon banzanta, shine za a zo ana min burga, kamar tainaka min za ai"
Da ƙarfi Sunusi yake magana ba a hankali ba a hankali ba, hakan ya janyo hankalin mutane da suke gurin,  kai tsit ana sauraren sa, Abba yai shiru ya rasa abunda yake masa daɗi.

Malam Zakari yace "sadaƙallahul azeem, dama in da muke jira a zo kenan, mu ga gwajin 'yar mu a hannun mu, ba ta da ciwon Komai, lafiyarta ƙalau, kai kuma kaje sharrin da kaiwa 'yar mu mun barka da Allah, duk unguwar nan ba wanda be san tarbiyyar da yaranmu ke da ita ba, wanda har ake son haɗa zuriya da mu"

Malam Labaran yace "A'a Malam Zakari, ai ba a shedar ɗan yau, ta idonka daban, ta bayan idonka daban, amma duk da haka, nasan Sunusi be kyauta ba, haka yake da zafin zuciya idan ransa ya ɓaci, amma mutumin kirki ne, ina nan ina masa rubutun samun sanyin zuciya.
Ayi haƙuri dan Allah, yanzu dai zamu je ayo gwajin a kawo, se a ɗaura Auren"

Sunusi yace "gaskiya ni Malam, ba in da za ni, ba wani gwaji da zan, in sunga za su bani a haka su bani"

"Wai Sunus ba ka da hankali ne? Ya ana ƙoƙarin saita lamura, kai kuma ka na sake ɓata lamarin"

Malam Zakari yace "ba zamu bawa mara mutunci, wanda be san darajar kansa 'ya ba, Allah ya ha É—a kowa da rabonsa"

Abba yace "A'a, É—an uwa babu yadda za'ai a gyara lamarin nan? Ka ga fa mun tara jama'a"

"Dan dai jama'a, bakoma sa watse Allah ya haÉ—a kowa da rabonsa, dama yarinyar ba wani girma ne da ita ba, a kunnen ka ya gama ci mana mutunci, da aibata mana 'ya yaiwa kansa, tun da be san abun arziki ba"

Sunusi ya sake tinzira, ya dinga bala'i yana cigaba da aibata Farhan, a gaban al'ummar da suka zo dan halartar É—aurin Auren.

Umma ta na cikin matuƙar zullumin halin da Farhan ke ciki, gashi tun sha ɗaya aka  ce za'a ɗaura Aure, amma har ɗaya saura shiru ba su dawo ba, ga mutane sun cika gida, babu Amarya babu dalilin ta ta na can ta na fama, ba ta san in da knata yake ba, gashi angwaye shiru suma babu su ba bu dalilin su.

Huzaifa ne yai sallama ya shigo, cikin faran shadda, Babbar rigarsa riƙe a hannunsa.

Umma na ganinsa tace "Huzaifa yaya, ina su baban naku an É—aur ne?"

Hauzaifa yai dariya yace "aka É—aura me? Ai an fasa Aure"

Tace "kamar yaya, kai bana son shashanci fa"

Yace "wallahi dagaske nake an fasa É—aura Auren"

Umma ta janyo Huzaifa gefe tace "ka gayamin tsakani da Allah, ka san ba na wasa da kai ko?"

Yace "wallahi Umma ba ƙarya na ke gaya miki ba, an fasa ɗaurin Auren nan"

"Huzaifa ko dai za'a É—aura an jima?"

"Wallahi Umma fasawa a kai"

"Amma saboda me?"

Huzaifa yace "Nima ban sani ba, se dai in su Abban sun dawo"

Please manage, bana jin daÉ—i ne.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Not Edited!
Chapter 67 · 0% Book details