← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 115

Sashe 66

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadik yayi bajinta sosai a wasan ƙwallon da akai a makarantar su, duk da kasancewar sa baƙar fata, amma yana da magoya baya sosai da sosai, club ɗin sa ne suka ci 4 abokan karawar su kuma suka ci 2, Sadik ne ya saka ƙwallaye uku a raga.
Bayan an tashi daga wasan, aka dinga hotuna da Sadik, Nana tana gefe tana kallonsa tana murmushi.
Tana nan zaune tana kallon yadda ake É—aga shi sama ana hotuna da shi, sedai abun takaicin bayan ya je ya canza kaya, sun shiga cikin makarantar, nan 'yan matan turawan nan ma suka dinga rungumarsa, suna É—aukar hotuna har da masu masa kiss a goshinsa.
Hakan ba ƙaramin ɓatawa Nana rai yai ba, dan haka Sadik ya nemata ya rasa a gurin ko sama ko ƙasa.
Hankalinsa ya tashi sosai ya shiga nemanta a gurin, sedai be ganta ba sam, ga guri ba ƙaramin guri ba balle yace bari ya zaga ko ze ganta, idan ma zagawar ze ta ina ze fara.
Nan da nan ransa ya fara ɓaci, wannan wace irin kudahumar Yarinya ce da ba aiwa abun arziki, daga zuwa da ita guri ta kama Gabanta.
  Tun Sadik yana ɗaukar abun wasa, ya ga Dagaske ba ta gurin,ba ita ba alamunta, nan hankalinsa ya ƙara tashi, gashi babu waya a hannunta a balle yai mata waya yaji ina ta shiga.
Ga duhun magariba ya fara yi, ga London ba Nigeria bace, kowa sabgar gabansa yake, balle ya bi mutane ya fara tambayar su, to wa ma ze tambaya, kuma ma me ze ce?.

Ya kuma komawa im da take zaune da farko, amma be ganta ba, nan ya fara tunanin ko report ze kai, Gurin jami'an tsaro? Yarinyar nan idan ɓata ta yi me zance wa Abba?" Ya tambayi kansa yana cigaba da rarraba ido.

Abu kamar wasa har isha'i, Sadik yana neman Nana amma be ganta ba, ya yanke shawarar bari yaje gida, daga nan ya ga me ya dace yayi.

Haka ya kama hanyar tafiya gida, ya manta da batun É—akko kayan da suka siya a shagon siyayya gaba É—aya hankalinsa na kan, ina ze ga Nana.

Se da yana zuwa gida, ya tarar da ita a gida tana kwance abunta tana kallon cartoon, tana ciye ciye.

"Ke, dama gida kika taho, ki barni ina ta bulayin nemanki tun É—azu?"

"Eh, gida na taho, na biyo wasu 'yan makarantar mu da na gani, suka kawo ni gida suka tafi,  na barka, kaji daɗin rungume mata son ranka, dan ni ba zan iya kallon zunubi ba, tun da kai in baka taɓa mata ba baka jin daɗin rayuwa" tai maganar cikin tsiwa da tsantsar kishi.

Wani irin marurun baƙin ciki ne ya turnuƙe Sadik, ji yake tamkar ya rufeta da duka, saboda ba ƙaramin tashi hankalinsa yai ba, yai zaton ɓata  yi.
Bece mata uffan ba ya wuce É—akinsa ya barta, tun da ya shiga É—akinsa be kuma fitowa ba, har gari ya waye.

Da sassafe Nana ta shiga É—akinsa, dan tai dutyn ta da ta saba, ta tarar Sadik yana toilet yana wanka, ta fara gyara masa gafoy, tana cikin gyarawa ya fito.

"Me kike min a É—aki?" Ya faÉ—a a kausashe.

"A'a, me kuwa nake yi, gyara maka mana kar in makara"

"Get out from my room" ya faÉ—a cikin tsawa.

Nana tace "to me nai maka?"

"I said get out" ya maimaita.

A razane ta juya ta fita, dan ya koma Sadik É—in sa na ainihi.

Se kuma ta tuna abunda tai masa jiya, tai shiru tace "haushi yaji kenan? To amma ai gaskiya na faɗa ba ƙarya nai ba.

Sedai kuma a wani ɓangare na zuciyarta, sam ba ta ji daɗin yadda Sadik yai watsi da ita ba, dan a 'yan kwanakin nan tafi sakewa, da suke shiri da shi.

Haka nan ta tafi Makarantar sukuku.

Farhan maye sosai take a É—akinta, dan bata san in da kanta yake ba, ba ta gane mafarki take ko zahiri ne abunda ke faruwa.
  An girke tukwanen biki, ana ƙoƙarin aza wutar tuwon 'yan ɗaurin Aure.

Malam Zakari ya tashi É—an aike, yace ace a gayawa malam Labaran da magabatan Sunusi cewar, muddin be nuna musu in da ze Ajiye musu 'ya ba baza'a É—aura Auren nan ba, kuma ya tabattar Ya zo da takaddar gwajin Asibiti, na lafiyarsa, idan ba haka ba ba za su ba su 'yar su ba.

Shi ko Sunusi na can garinsu, ana ta shiri daga can zasu ta ho gaba É—aya gurin É—aurin Aure.

Adda Hafsatu ta shiga ɗakin Farhan tana mita "wai wannan wace irin Amarya ce haka? Ana ta faman shiri amma kin ƙule a ɗaka ko wanka ba ki ba, balle a sa ran ki kintsa kafin dangin mijinki su zo, ba zaki ta shi ba ina miki Magana?"

Shiru Farhan ba ta amsa ba se ma sake juyi da tayi akan katifar ta.

Zuwa tai ta daki ƙafafuwan Farhan, "ke dan ƙaniyar ki magana nake miki fa, ba zaki ta shi ba"

Cikin maye Farhan ta fara magana "Wai..wai..... Meeee zan miki ne?kiiiiiii ƙyaleni ba na son in buɗe ido na...hmmmmmm... wai ba kya ganin gini ne ze faɗo a kaina?"

BuÉ—e baki Adda Hafsatu tai tace "Na shiga uku ni Hafsatu, Farhan me ya sameki haka? Me kike yi haka Farhan?"

"Ni,ni,niiii dalla ki rabu da ni, ba na son kowa ya zo gurina dan Allah"

Cikin azama Adda ta fita waje, ta janyo Umman Farhan gefe tace "kin san halin da 'yar ki kuwa take ciki?"

"Kamar yaya?"

"Wallahi gani nai kamar tana maye, amma zo muje ki gani"

A tare suka shiga É—akin Farhan, suka tarar da ita kamar Mahaukaciya, duk ta ware gyaran gashin nan, gashin na ta ya hargitse gaba É—aya.
Ta na zaune ya jingina jikinta a bango, ta lumshe idanunta.

Umma tace "Ke! Menene haka?"

Farhan tai shiru ba ta motsa ba.

Umma ta zo, ta kai hannu ta taɓa Farhan.

Farhan ta bige hannun Umma tace "Ni,niiiii..... Kar ki sake taɓa ni......tun da kin tsane ni.. ba na son ganinki, ki tafi ki bar nii"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ke me kika sha haka? Me zan gani, maue fa take Hafsatu"

"Nima abunda na gani kenan, da ma ta na shaye shaye ne?'"

Umma cikin tashin hankali tace "Ni ina na sani? Idan ma yin take saboda tsabar wulaƙanci ta rasa lokacin da za ta sha abun maye, se lokacin aurenta, mutsne sun cika gida, dan ta kunyata ni, tana mace za tai shaye shaye, wannan wace irin yarinya ce, da ma fa nema take ta lalace, Yaron nan ya sha kawo ƙarar ya ganta cikin mota ana kawota, mahaifinta ya ƙi yadda, ji wannan abun kunya ina zan sa kaina, mace da shaye shaye?" Umma tai maganar cikin rauni.

Adda Hafsatu tace "da ma abunda ake jiye muku kenan, shiyasa muka damu a aurar da ita, ka aura da 'yar tun tana ƙarama ba ta san komai ba, shine rufin Asiri da kwanciyar hankali, amma kuka ƙi, wai ku se tai boko, ga sakamakon bokon nan ai"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu meye abun yi?"

Farhan ta kalli Ummanta, idanunta jawur, cikin maye amma ta tsurawa Umma ido Sannan ta fara Magana "Meyasa......ki ka tsane ni? Meee nai miki...... Ni bana son Auren nan, ba na son ammma kika dage, ni ki tashi ki tafi, ko in kashe kaina, zuciyata zata buga......damuwa tai min yawa ku ƙyaleniii......" Farhan ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tare da ƙwala ihu, tana mimmiƙewa. Har se da hankalin mutane ya so ya kai gurin.

Cikin azama Umma ta miƙe jikinta na tsuma, cike da tsoro da fargaba. Ita dai a iya saninta Farhan ko ytsa ka sa mata a baki, ba lallai ta iya taunawa, amma ita ce ke wannan ƙarajin take mata tsawa.

Adda Hafsatu tace "Maryamu, wannan ba maye bane, Farhana Aljanu ne da ita wallahi, kinga muje waje maza, a samo mukulli a rufeta a É—aki, wallahi iskokai ne, zata iya mana duka a É—akin nan, rufe ta a É—akin a jira zuwa lokacin da iyayenta zasu dawo daga gurin É—aurin Aure, a ji me za su ce"

Cikin damuwa Umma tace "abun ya bani mamaki, ni na kasa gane kan wannan lamari, kuma aljanun ne se Ranar É—aurin Aure?"

"Kin ga ni ban hanya in wuce, ba ki ji suna cewa ba sa son Auren ba, shiyasa sam ba ya walwala tun da aka fara shirin bikin nan, ashe ba ita kaɗai ba ce, ni ban hanya kan ta haɗa min jikina a safiyar nan, dama ni ba ƙwari na cika ba"

Haka suka fito suka kulle Farhan a É—akin, ita kuwa Farhan sam ba ta san a zahiri tai wa Ummanta tsawa ba, zaton ta a mafarki komai ke faruwa!

Mutaina ta shigowa suna tambayar ina Amarya, se ace musu ai bata da lafiya, da yake a can Babban masallacin juma'a da ke unguwar su Farhan za a É—aura aure, duk danginsu maza, sun tafi can.

Sadik kam yau, ba da iya takaicin Abun da Nana tai masa ya tashi ba, har da wata irin damuwa, da tsananin fargaba da ya ta shi da ita, wadda be san dalilin hakan ba.
Wata irin faɗuwar gaba yake ta fama da ita, haɗi da Zullumi, yai iya ƙoƙarin sa dan ya gano, meke sa shi wannan fargabar da zullumin amma ya ka sa tuna Komai.

Yana jin Nana ta fita ta tafi makaranta, amma ya na ɗakinsa be fito ba, dan ko makaranta ma ƙin zuwa yai, yai kwanciyar sa a ɗaki, yana jin yadda zuciyar sa ke ta bugawa da ƙarfin gaske.
Tunani yai kowane abune yake faruwa a gida, ya miƙa hannu ya ɗakko wayarsa, ya kira layin Mother.

Se da ta kusa tsinkewa sannan ta É—aga tace "Sadik lafiya kake kirana a wannan safiyar haka?"

Yace "kune a nan safiya, amma mu a nan ai rana ta yi, barka da safiya"

"Yawwa, kana lafiya?"

"Eh, lafiya ƙalau Alhamdilillah"

Mother tace "be lectures ne, ka kirani yanzu?"

"Banje makaranta ba yau"

"Saboda me?" Ta tambaya cike da kulawa.

Yace "bana jin daÉ—in jikina ne gaba É—aya"
Chapter 66 · 0% Book details