← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 115

Sashe 32

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Galala Farhan tabi Sunusi da kallo, ya akai ya san Sadik, kuma ya san shi ke kawota gida a mota.

Guntun tsaki ta ja ta shige cikin gidan su, tana cigaba da tunani.

Yauma Sadik cike da zullumin yadda ze bacci a wannan ƙungurmin ƙauyen ya kwanta, yana duba hotunan wayarsa, sosai ya dinga kuka lokacin da yaci karo da hoton Mother, yana missing ɗin babarsa sosai da sosai, ya rungume wayar yana kuka.

Vibrating wayar tayi alamar saƙo ya shigo, ya ɗaga saƙon ya fara dubawa.

"Am missing You hubby, i pray you come back soon, kar wani abu ya faru"
Saƙon Farhan ne bana wani ba.

Ya kira layinta, amma wayar taƙi tafiya, ya watsa wayoyin gefen katifa, ya fashe da kuka.

Sir Nazir yana office ɗin sa, ya turawa Lilly saƙon yana son ganinta ta wayar salula.

Kusan mintuna ashirin da tura mata saƙon se gata ta shigo Office ɗin.

Yai sa'a lokacin corper George ya fita daga Office É—in nasa.

Ta samu guri ta zauna Sannan ta kalleshi cikin rauni tace "wace mafita ka samo mana?"

Ya gyara zamansa sannan yai ƙasa da muryar sa yace "Mafita ɗaya ce Fatima, shine a zubar da cikin nan"

Ta kalleshi tace "Amma ta yaya?"

"Ga magani na taho miki da shi, ki fara jarraba magani mu gani ko ze fita"

Lilly ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ancemin fa ana mutuwa garin zubar da ciki, ni tsoro nake ji kar Maman mu ta gane na shiga uku"

"Ba zata gane ba ai, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki bi instructions É—in da zan baki kiyi amfani da maganin"

Lilly tace "wallahi tsoro nake ji"

"Lilly idan ba ki yadda an zubar ba yaya zamuyi kenan? Ko so kike Asirin mu ya tonu?"

Ta girgiza masa kai, yace "Yawwa dan Allah kiyi haƙuri, ki amfani da maganin ba abunda ze faru insha Allah, idan ba kya so a gane ki bari se da daddare kowa ya kwanta seki sha"

Tace "to"

Ya ɗakko wata ƙaramar kwalba wadda babu sticker bakomai a jikinta ya bata yace "ga shi nan, idan kin ci Abinci kin ƙoshi, seki shanye maganin duka, in Allah ya yadda cikin ze fita"

Ta karɓa tare da zura kwalbar a aljihun rigarta.

Ya share mata hawaye, yaita rarrashin ta harta É—an kwantar da hankalinta Sannan ta koma aji.

Kwanakin Sadik uku a ƙauye, ba komai yake iya ci ba, ta dole ya iya amfani da banɗakin su, saboda yadda wani Abincin ke ɓata masa ciki, har wata rama yayi saboda azabar damuwa, Nana kuwa yanzu yake bata sosai da sosai, ita kanta ta san an takura shi fiye da kima.

Dama kusan kullum ana kawo kilishi ko tsire gidan Hakimi saboda Nana, ga tatattaciyar madarar shanu, ko fura da Nono da fulani ke kawowa duk dan saboda ita Hakimi yasa ake kawowa, saboda suna cikin abunda take matuƙar so.

Sadik na zaune da safe, an dawo daga wannan tilawar da ake in an idar da sallar Asuba, ya duba wayarsa yaga saura kara ɗaya a ƙaramar wayarsa, babbar kam tuni ta ɗauke.

Ba tsammani yaga kiran Mother ya shigo, cikin rawar jiki ya É—aga kiran ya kara a kunnensa.

"Auta na" shine abunda Mother ta faÉ—a cikin sanyin jiki.

Ai take Sadik ya fashe da kuka yace "Mother, kin manta dani kun dena sona ko? Kin san ba zan iya zama ba amma ki ka bari Abba ya kawoni ya barni a nan, life is so hard for me here"

"Sadik ba yadda zanyi da mahaifinka, fafur yace kar in kuskura in shiga maganar nan, nayi nayi da shi ya ɗakko min kai amma yaƙi, yanzu ya kake?"

"Mother wallahi zan mutu in ba'a zo an É—auke ni ba, na gaji wallahi, komai ba daÉ—i am missing You so much"

"Am missing you too my love, dan Allah Sadik ka dena kuka zan cigaba da lallaɓa mahaifinka wallahi ko bacci bana iyawa"

"Mother, am living for 3days without hearing from you, am missing home dan Allah Mother ki zo ki tafi da ni, wallahi bana son irin Abincin da suke bani, bana jin daÉ—in komai"

Kawai Mother ta fashe da kuka, ji tai an zare Wayar daga hannunta, ta juya da sauri taga Abba ne a tsaye ya kara wayar a kunnensa yace "Sadik meyasa zaka É—agawa mamanka hankali meye haka? Kukan me kake?"

"Abba ka dena sona, ka barni a garin nan ni ba zan iya zama ba, am missing home dan Allah kazo ka tafi dani"

Abba ya danne zuciyarsa a kausashe yace "Kai nutsu, da girmanka zaka dinga min kuka haka kamar wani É—an yaye, me ka rasa ci ko sha? Ka nutsu ka kwantar da hankalinka ka zauna, idan lokacin da suka ga ya dace zasu dawo da kai, ka gaishe su" Abba ya katse kiran.

Sadik ya ajiye wayar yana kuka yace "Abba Why"

Nana na tsaye a bakin ƙofar ɗakin, an aiketa ta kirashi taji duk wauar da yayi, jikinta yai matuƙar yin sanyi da jin yadda Sadik ke kuka, a saɓule ta koma tsakar gida ta zauna tai shiru.

Inna tace "yana ina?"

Nana tace "bacci yake"

"Wane irin bacci ba yanzu ya wuce É—akin ba"

Nana tace "to Inna yayi bacci fa"

Inna ta ƙyaleta ta cigaba da aikin ta.

Se can daf da la'asar sannan Sadik ya fito, idanunsa sunyi jajir sun kumbura, kana kallo ka san kuka yayi.

Ya shiga banÉ—aki ya fito, ya kalli in da Nana ke kwance akan cinyar Inna, Innan na tsefe mata dogon gashin ta.

Sadik yace "ke a ina ake cajin waya a garin nan"?

Banza Nana tai masa ta cigaba da lumshe ido.

"Ba kya ji na ne?" Yai maganar yana kallonta.

Inna a ranta tace 'wannan É—a ba dai tsarin ido ba'

"Ni karka sake cemin ke, kuma in dai garin nan ne se sati sati ake kunna inji a gurin masu caji"

Tsaki Sadik yai ya jiya ya nufi É—akin da yake, Inna tace "ga alala can a É—akina ka shiga ka É—auka, na aika a taso ka tace min bacci kake"

"Ni bana cin wannan abar"

"Ka huta" Inna ta bashi amsa, sannan ta É—ora da "babu me sake takuraka kaci wani abu, in ka mutu da yunwa kai ka so"

Be kuma bi ta kan Inna ba ya shige É—akin.

"Inna" Nana ta kira sunanta.

"Na'am"

"Inna dan girman Allah ku ƙyaleshi ya koma gida, wallahi har ya rame gashi baya cin abinci sosai, dan Allah ku bari ya koma gida"

"Sannu me É—an uwa, ai seki maida shi dan ubanki"

"A'a ni ba É—an uwana bane, amma Inna kuka fa ya ke yi É—azu, wallahi ni tausayi yake bani, dan Allah ku barshi ya koma gidansu"

Inna tai mata shiru, ta cigaba dai mata tsifa.

Nana ba ta gaji ba ta kuma cewa "Inna nan fa Yayansa yace 'dan Allah ki ba dani su tafi dani kika hana, amma shi meyasa zaku riƙe shi?"

Wani uban duka da Inna taiwa Nana a ka seda ta tashi ta zauna tana kallon Inna.

"Sekije ki samu kakanki ki masa wannan tistiyen bani ba, mara kunya"

Nana tai shiru tana sosa kai, ita dai ba taga aibun maganar ta ba.

Ta faki idon Inna lokacin ta shiga banÉ—aki, ta É—ebo kilishi da Alkaki, cikin sanÉ—a ta shiga É—akin da yake.

Ta tarar da shi a kwance yayi rigingine, yana kallon rufin É—akin.

Ta jefa masa ledar kan katifarsa, ta juya ta bar gurin da sauri.

Kamar yadda Sir Nazir yai mata bayani, da daddare bayan taci Abinci tai shirin kwanciya, ta É—akko jakar makarantar ta, ta É—akko kwalbar nan tai bismillah ta shanye É—an ruwan dake cikin kwalbar, da ta shanye ta buÉ—e tagar É—akin ta ta baya, ta jefa kwalbar waje.

Ta dawo tais shiru tana jiran taji wani sauyi amma shiru.

Tana nan tana saurare Nazir ya kirata hankali a tashe, tana É—agawa yace "Fatima yaya, ya fita kuwa?"

"Ni ba abunda naji" ta bashi amsa.

"Kuma kin shanye duka?"

"Eh na sha kamar yadda kace"

"To shikenan, ze fita insha Allah, Allah ya tashe mu Lafiya yasa kar a samu wata matsala"

Tace "Ameen"

Wasa wasa har bacci ya kwashe Lilly ba taji komai ba.

Cikin bacci taji wani irin azababben ciwo, tun daga kanta har yatsun ƙafarta, ga wani irin ciwo da mararta keyi kamar ana fizgo wani abu.

A razane ta buɗe idonta, taja jikinta ta kunna fitilar ɗakin, gadon da take kai yayi kaca kaca da jini, wanda hakan ya tsorata matuƙa ta fasa ihu da ƙarfi!

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Zabura Nana tai ta miƙe daga kan kwanon gabanta, ta kalli Sadik a fusace tace "meye haka zaka shigo mana ɗaki ba sallama" tai maganar tana waiwayen in da zata ga hijjabi ta sa ta suturta jikin ta.

Kan ta kai ga miƙa hannu ta ɗakko hijjabin, ya kai hannu ya danƙota, zazzare ido ta shiga yi ƙirjinta na dukan uku uku.

"Ka sakarmin hannu meye haka? Idan Inna ta zo ta ganka fa, kalen ka jamin masifa?" Tai maganar ƙirjinta na bugawa da sauri, saboda rashin sabo kasamcewar sun samu kusanci Sosai a tsakanin su.

Ba tare da yace mata uffan ba ya bata wasu irin lafiyayyun maruka guda biyu a kowane kunci.

Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki, Zani na neman kwancewa saboda Azabar zafi, da wayonta dai wani be taɓa marinta ba.

Wani irin kuka ne ya ƙwace mata, tana wata irin sheshsheƙa tana neman ta shiɗe.

"Kin ɗauka ƙarya nake da nake miki warning akan ki kiyayeni? Ni zaki kalla ki dinga zagi sa'anki ne ni? Ko dan kinga ina zaune a gidan ku shine zaki dinga gayamin abunda kika ga dama?"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, me zan gani haka? Kai Sadik wane irin abu ne haka? Wannan wace irin fitsara ce a cikin É—akina?"
Chapter 32 · 0% Book details