Sashe 69
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malam Zakari yace "Umman Farhan, haƙuri za kiyi, duk abunda kika ga ya samu bawa to yana rubuce a cikin kundin ƙaddararsa ne, ki sa a ranki, da ma Allah be ƙaddara mijinta bane"
Cikin kuka Umma tace "Baban Huzaifa, kamar ni ka ɗai na taɓa haihuwar 'ya a rayuwa ta, daga wannan se wannan, yarinyar nan duk wani salo da za ta janyo min abun kunya, da abun faɗa ta sanshi, kuma za ta aikata. Kalli fa maye take Ranar ɗaurin Aurenta, kuma Sunusi ba ƙarya yai ba, na kamata da wayar da saurayi ya bata, zamanta a gidan miji ba shi yafi Alkhairi ba, yanzu ta samu lasisin aikata abun da ta ga dama, na rasa wannan wace irin kangararriyar yarinya ce!"
Kalmar kangararriyar yarinya ta daki zuciyar Farhan, fiye da kima, ta É—aga jajayen idanunta ta kalli Ummanta, yau ita Umman take dangantawa da kangararriyar yarinya, tabbas ko da ace mafarki take abubuwan nan da suke faruwa, har ta koma ga Allah ba zata manta wannan kalma ba.
"Ashsha, ya kike kamanta 'yar da kika haifa da kangarewa, duk biyayyar da Yarinyar nan take da shi, dan an samu wannan akasin se ki danganta ta da kangara? Kin san meye kangarewa kuwa? Kar ki sake wannan kuskuren, da kika ganta da wayar saurayi wane mataki kika É—auka? Dan Allah kar wannan abun ya sa ku yiwa Yarinyar nan baki, dan yarinya ce me biyayya a baya, kamata yayi aji meyasa tai shaye shaye, garin yaya a kai ta rasa lokacin da zata sha wani abu se ranar É—aurin Aurenta, ni anya ma kuwa tana son Yaron nan?"
Daga Abba har Umma ba wanda yave uffan, se ma Umma da tace "shikenan, tun da haka ta zaɓawa kanta, taje ta ƙarata, ga gidan nan ta zo tai ta zama muna jerawa, tana kallona ina kallonta, ai duniya makaranta ce"
Umma ta tashi fuuu ta bar É—akin, Abba ma bece komai ba ya tashi ya bar É—akin, haka kowa ya fice aka bar Farhan.
'yan biki duk aka watse, ana ta gulmar ashe ma Yarinyar lalatacciya ce, bin maza take ga shaye shaye tana yi.
Lamarin ba ƙaramin dukan Hajiyar Abbas yai ba, ta yi mamakin yadda aka ce wai Farhan tana shaye shaye, da yake ran ɗaurin Auren ba ta gari, se da yamma ta dawo, kan ta shirya ta shiga gidan su Farhan, har gida aka sameta aka bata labarin abunda ya faru, da yadda aka fasa Auren Farhan ɗin.
Ita kanta Hajiya, ta lura da yadda Farhan ke cikin damuwa, amma iyayenta ba su maida kai, dan gano meye damuwar ta ta ba, su dai kawai su mata Aure, dan haka dama dole ta nemawa kanta mafita, wannan abun dama Abbas yake ta ji, masu irin halin Farhan in damuwa tai musu yawa, a ƙarshe dole su nemawa kan su mafita.
Baƙinciki ya hana Hajiya ko zuwa gidan su Farhan, ta sha takaicin yadda sunan Farhan ya ɓaci, gaba ɗaya unguwa ta ɗauka, an innocent kid like this, gashi mutane ba sa wa kansu adalci, suna hukunci ne da iya abinda idonsu ya gane musu.
Tabbas, ba dan abun ya zo a ƙurarraen lokaci ba, kuma ba tattauna da dangin baban su Abbas ba, da ba abunda ze hana tace a ɗaura da Abbas, dan ba ta yanke hukunci akansu se da sanin dangin mahaifinsu, saboda a tsaye suke a kansu.
Nana ko haɗuwa taƙi yadda suyi da Sadik, suka koma wasan 'yar ɓuya, da ta ji motsinsa a falo, ba zata fito ba.
Jin shiru ya sa ta É—auka ya fita, yana kallonta ta window É—akinsa, tan sanÉ—a, ta shiga Kitchen.
Se da ya bari an É—au lokaci da shigarta, ta sakankance, sannan ya fito ya risketa a Kitchen É—in.
Tana ganinsa ta hau ƙwalala ido, ya shiga takowa a hankali, tana ja da baya har suka ƙure bango, ya kalleta yace "Yau ni zan gyara ɗakin nawa?"
Ta tura baki tace "zan gyara, amma se anjima"
"Wace anjima kuma? Azahar ce fa Yanzu, tun safe yakamata ki gyaramin ai.
Amm an gayyacemu cin Abinci da yamma"
Nana ta kalleshi tace "Ni gaskiya ba zani ba"
Yai ƙasa da murya yace "idan naje ni kaɗai gaskiya zan taɓa mata"
Tace "Allah yana kallonka"
Yai murmushi ya sunkuyo daidai da tsawonta, ya sa hancinsa a wuyanta, seda ta saki ludayin da ke hannunta, ta ƙanƙame jikinta, tana jin wani abu da ba ta san menene ba.
Sadik yana kallon reaction É—in ta, yace "Mijinki yaro da shi, amma se....." Se kuma yai shiru yana wani miskilin murmushi.
"Abincin ze ƙone fa" ta faɗa a daƙile.
Shiru yai bece komai ba, ji tai abun nasa yana zarce hankalinta, ta dage iya ƙarfinta ta kurma ihu, a gigice ya cikata yace "meye haka?"
"Wallahi ni ba 'yar iska ba ce, da zaka dinga min irin wannan abubuwan'
Tsaki yai a ransa yace "wannan kwantacciyar Yarinyar ba ta san abunda ya halatta a aure ba ne?"
A fili yace "karki wuce ƙarfe huɗu ba ki shirya ba, idan ba haka na tafi ba zan dawo ba se gobe in Allah ya kaimu"
Ita Nana dan ya tafi ya kwana ba damuwar ta bace, dan yanzu ta saba da zaman kaɗaici, jin yace idan yaje ze taɓa mata ne ya sa ta ƙuduri se ta bishi.
Ƙarfe huɗu ta shirya suka fita, wani katafaren gurin cin Abinci sukaje, gurin ya haɗu Sosai da sosai.
Wani ɗaki ya ja Nana suka nufa, a nan ta tarar da Abokansa da suka taɓa zuwa gidan su, nan suka shiga gaisawa, abun takaici har da Matam duk se da Sadik ya bi ya gaisa da su.
Nana se hararsa take, amma yaƙi ko kallonta.
Nan wasu suke tambayar sa, wannan me aikin ta sa ce, yace tsokanar ta yake Ranar, amma ƙanwarsa ce, suka miƙawa Nana hannu dan su yi musabuha, aikuwa ta miƙa wa wanda ya miƙo mata hannu suka gaisa, na biyun ma har ta kai hannu za su gaisa, Sadik ya sa nasa hannun ya kalleta cikin masifa yace "ba ki da hankali ne? Da auren naki kike gaisawa da maza?"
"Kai ma da Aurenka kake gaisawa da mata?" Tai maganar tana murguÉ—a baki.
"To ni da ke É—aya ne?"
"Eh mana, da biyu ne, kai kake cemin 'yar ƙauye ai, gara in abunda zan waye"
Sadik ba ya son su raba abun faɗa a cikin jama'a, dan haka ya ƙyaleta, ya ƙwafeta a ransa.
Suka dinga yaba kyan Nana, suna cewa tana da kyau, har wani abokin Sadik yana cewa, akwai yiwuwar in ya tashi Aure, ya zo Nigeria ya samu mata, dan ace suna da Black beauties kamar Nana.
Sadik kasa cin Abincin yai saboda takaici, Itama Nana ba ta saba da cin abinci a gaban mutane ba, dan haka ta kasa sakewa ta ci.
"Ke tashi mu tafi" y faÉ—a a kausashe.
"Ni gaskiya ba zan tafi yanzu ba, daga zuwanmu se tafiya"
"Wallahi se kin tashi, tun da baki da man kai, tsabar rashin mutunci kike gaisawa da mazs, a gabana shashasha kawai"
"Ikon Allah, na ga kai ka fara yi ai, kuma gaisawa ce fa kawai, ai kai na gani kina yi"
"Za ki min shiri, ko se na ɓarar da kanki a nan gurin?"
Wata yarinya ce a cikin su ta ke tambayar su lafiya kuwa?.
Sadik yace lafiya ƙalau, tafiya za suyu.
Nan suka shiga tambayar meyasa za su tafi yanzu.
Sadik yace wani uzuri ne da shi a gida, dan haka za su tafi.
Mussaman saboda nasarar da Sadik ya samu suka shirya wannan cin abinci, amma Sadik yace tafiya ze yi.
Suna tafe a hanya yana wa Nana masifa kamar ze maketa, ita kuma se ƙunƙuni take, ta na harare harare.
Abubuwa fa sun ƙara damalmalewa Farhan, dan ba cinya ba ƙafar baya, dan a maimakon fasa Aurenta da Sunusi ya sata a farinciki, sema sake shiga cikin wata damuwar da tai.
Dan bayan ƙwayar ta saketa, ta gane duk abubuwan da suka faru gaske ne, Abba ya dena shiga harkarta gaba ɗaya, yai watsi da ita, dama Umma ba a magana, ta tattara Farhan ta watsar ko kallon in da take Umma ba ta yi.
Ga mutane da suke ta shigowa, wai yiwa Umma jaje da yawa ba jajen ne ke kawo su ba, zunzurutun gulma ce ke kawo su.
Haka a waje ma, Abba tararsa ake da maganganu daban daban, wasu na masa jaje wasu kuma na gulma, nan fa abun duniya ya kuma tsayewa Farhan, kullum cikin wunin É—aki take, in ta fito banÉ—aki za taje.
Abun duniya ya sake sakota a gaba, ta rasa abunda yake mata daɗi, har ɗaki taje ta samu Abba ta durƙusa akan gwiwowinta tace "Abba, dan Allah dan Annabi kayi haƙuri, nasan nayi kuskure amma ku yafemin dan Allah"
"A'a Farhan, karki sake cewa kuskure, ganganci dai da son zuciya, Farhan 'ya'ya na maza ba suyi shaye shaye ba, ki barni inji da alhinin abunda ya sameki, na fasa Aurenki, amma dan ki kunya tani a idon duniya, Ranar É—aurin Auren ki ita ce zaki sha abun maye?"
"Abba, maganin ciwon kai na siyo, ban san abun maye bane wallahi, na zaci maganin ciwon ka ne kawai, dan Allah Abba ka yafe min"
Abba yace "Ai dama bance miki komai ba, tashi kije"
Jiki a sanyaye Farhan ta bar ɗakin Abba, tana zubda hawaye, tana kallon yadda Umma ke wurga mata wani irin mugun kallo, amma Farhan ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta wuce ɗakinta.
Sedai fa maganin nan da ta sha, ta ji sauƙin nauyin da kanta ke mata, ta ɗorawa kanta laifi ne saboda rabi aka ce ta sha, amma ta sha fiye da haka, sedai tunda maganin ya saketa, take jin kanta ya cigaba da nauyi, zuciyarta na mata wani irin zafi.
Washegari da safe, Umma ta ga Farhan ta shiryo cikin Uniform, ta kalli Farhan tace "ina zaki?"
"Umma makaranta zan koma"
"Wallahi baki isa ba, bayan abun kunyar da kika janyo mana, ki wanke ƙafa kice zaki wata makaranta, me karatun naki ya amfana mana, kik biyewa saurayi ya hure miki kunne, kinyi kutungwilar da aka fasa Aurenki"