← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 115

Sashe 13

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da labari ya samu Lilly, Nazir ba lafiya ta damu matuƙa, ta shiga tashin hankali.

Ta kirashi a waya tai masa sannu, amma jin yadda yake amsawar yasa ta san yana jin jiki.

Kasancewar Gidan ba kowa se ita kaɗai, yasa ta cewa masu gadi zata gidansu ƙawarta, ta kira Mummynta a waya ta gaya mata, ba musu suka bata hanya ta fice.

Taje ta yo siyayyar kayan marmari, da abubuwan sha'awa ga mara lafiya, ta tafi gidan Sir Nazir, dan in suna hira yana kwatan ta mata gidan da yake zaune.

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. 

Da Lilly tabi kwatancen sa ba ta wani sha wahala ba ta gano gidan, ɗan ƙaramin gida ne, kusan shikaɗai ne a tsukin gurin, dan sabuwar unguwa ce duk ba mutane, ba wasu gidajen kirki se tsilla tsilla.

Ƙaramar Ƙofar taje ta fara knocking, ta daɗe a tsaye dan har ta fara fidda ran za'a buɗe ƙofar, kawai taji an buɗe.

Turus yai ya tsaya yana kallonta, kallo ɗaya tai masa taga yayi rama sosai, idanun sa sunyi zuru zuru, sanye yake cikin dogon wando baƙi, da vest fara ƙal.

Duk da halin rashin lafiya da yake ciki, amma a haka ya daure yace "Lilly, me kike a nan?"

Tace "Duba ka na zo yi, na kasa samun nutsuwa tun da aka ce ba ka da lafiya"

"Shikenan, Nagode ki maza ki koma gida kar wani ya ganki a nan kinji"

Kallonsa tai da mamaki tace "meyasa?"

Yace "idan wani ya ganki za'a iya yi mana sharri fa"

Aikuwa ta haÉ—e rai tace "dama na sani nina damu da kai, har in zo in da kake in duba ka amma ka min haka shikenan nagode" ta juya zata tafi yace "am sorry ba haka bane, ina jin tsoron abunda zeje ya zo ne, amma shikenan shigo kawai"

Ya bata hanya ta wuce, kasancewar jikin sa ba ƙwari a hankali yabi bayan ta, suka shiga ƙaramin falon ya samu guri ya kwanta akan doguwar kujera. Ya lumshe idonsa.

Ƙura masa ido tayi sosai ta na binsa da kallo, duk da yayi rama amma hakan be hana kyawunsa fitowa Sosai ba, wata irin soyayyarsa na sake fizgarta.

"Sannu my love" ta faÉ—a cike da kulawa.
ya jinjina mata kai ba tare da ya buÉ—e idonsa ba.

Duk da ba shi da lafiya, amma ko ina tsaf da shi,a gidan a share, hadda ƙamshim roomfreshner.

Ta miƙe ta ɗakko ledar da ta zo da ita zuwa gaban sa, ta zauna tace "ka tashi ka duba abunda zaka iya ci ka samu ka ci kaji babyna"

Ya girgiza mata kai yace "bana buƙatar komai, bana son cin komai"

Cikin shagwaɓa tace "haba dan Allah, ka daure ko yaya ne ka ci"

A hankali ya buÉ—e ido ya kalleta, yaja numfashi yace "tashi daga kusa dani Lilly, ki tafi gida ma kar a nemeki"

"Ni kake kora ko?" Ta faÉ—a tana nuna kanta.

"Ba korar ki nake ba, kar a nemeki a gida, na san ba'a san nan kika zo ba"

"Mummy ta na Sakwatto, an musu haihuwa fa, daga nan za taje ganin Daddy a Abuja"

"Duk da haka dai" ya faÉ—a a hankali.

"Idan ba ka ci ba ba zan tafi ba"

Ya tashi zaune yace "bani abunda kike so inci, Nagode sosai da ziyarar nan, amma ki tafi gida"

"Wai se korata kake shikenan, ni idan ka zo gidan mu ba haka zan ma ba"

Nazir yace "Lilly is different ace ni na zo gidan ku, akan ace ke kika zo gidana, kin kasa gane me nake nufi"

Ba tace komai ba ta ɗakko masa madara ta miƙa masa.

Ya girgiza mata kai yace "zata iya sani amai, bani Ayabar in ci"

Ta ɗakko ta miƙa masa, da ganin yadda yake ci ka san yana jin jiki.

A hankali yace mata "miƙo min ruwa a bayan tv stand ɗin can"

Ta tashi kamar yadda yai mata umarni ta kawo masa ruwan roba, sedai yanzu kusancin da ke tsakanin su yafi na É—azu.

Ya karɓa ya sha, se bin sa take da ido.

Yana ƙoƙarin kwanciya, Amma  ta hana shi tace "guda ɗaya fa kaci, baka ci da yawa ba"

Yace "na ƙoshi, zan iya amai"

Ba tsammani taji ya kwanta a jikinta ga jikin sa da zafi sosai saboda zazzaɓi.

Da ƙyar tace "jikin ne?"

Maimakon ya bata amsa se sake ƙanƙameta da yayi a jikinsa, yana ta numfashi da kyar.

A hankali ta dinga shafa bayansa zuwa sumar kansa, tana masa Sannu.

Gefe kuma tana raya abubuwa daban daban a cikin ranta.

Tabbas mace duk ƙanƙantar mace mace ce, Ruɗin ƙuruciya da kururwar sheɗan, silar lalacewar ƙarshen zamani, abunda ake rubutawa a litattafai ya taka rawa a ƙwaƙwalwar Lilly gurin hilatar malamin nata zuwa ga afkawa tarkon sheɗan, shikuma bisa ga jagorancin sheɗan ya biyewa son zuciyarsa, suka afka tarko me matuƙar muni. Ya aikata zina da ɗalibar sa, abunda ko a mafarki be taɓa kawo faruwar hakan ba.

Ya kalli in da Lilly ke kwance, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta iya yi.

Dafe kansa yayi tare da É—orawa kansa dukkanin laifin, kan sa cigaba da sarawa yai, ya zubawa Lilly ido da hawaye ke bin gefen idonta.

A hankali ya É—agota yana mata Sannu, amma ta kasa magana se kuka da take.

A hakan ya temaka mata ta kintsa jikinta, sedai ko haÉ—a ido ya kasa yi da ita, saboda matsananciyar kunya da kuma nadama da suka shige shi.

Duk da yadda take jinta a galabaice, haka ta fice ta bar gidan, zuciyarta a cunkushe da dana sani da kuma zubar da hawaye, shikenan ta rasa abu mafi kima da daraja a tare da ita, duk da yadda ta ɗokanta da son gazgata abunda suke karantawa a littatafai, da yadda zuciyarta ke ƙawata mata malamin na ta, amma ta gane Barno gabas take.

Ta kuma ji nadamar abunda yafaru a tsakanin su da malamin nata.

Ta na zuwa gida tun a falo ta zube, ta dinga rusa kuka kamar ranta ze fita, tayi asarar da ba zata taɓa mayar da ita ba.

Ranar yau Sadik ya kasa bacci, shi kansa ya san jure rashin Farhan a kusa da shi ba abu ne me sauƙi ba, ya riga yayi matuƙar sabo da Masoyiyyarsa Farhan, yana jinta sosai a cikin ransa, sedai fargaba ta kan shige shi a duk lokacin da ya tuna wai mahaifinta ya mata miji, yana jin wani abu a ransa wanda ya kasa tantance ko menene.

Da safe ba zuwa Makaranta, se ƙarfe goma na safe sannan ya tashi daga bacci, ya tashi ya shiga cikin gida dan gaida Mother.

Tana ganinsa tace "Ahh, Sadik wai me ke damunka kwanan nan ne?"

Sadik yace "me kika gani?"

"Duk ka rame kayi wani iri, ance kun kammala exams amma ba wani alamar farinciki a tare da kai, balle a É—an shirya maka wani abu na musamman, whats wrong ne my Auta?"

Sadik baya son maimaita magana, ya san koya gayawa Mother damuwarsa ba abunda za tayi a kai, sema wataƙila ƙarshe suyi faɗa dan haka yace "bakomai kawai am not in mood ne"

"Ban gane you are not in mood ba, gaba É—aya fa ka dena walwala Sadik nifa bana son ganinka a haka"

Cike da shagwaɓa da kuma ƙosawa yace "haba Mother, nace miki fa bakomai am ok, just a little stress, kuma shima saboda exams ne, but i will be ok insha Allah"

"To shikenan, kaje Abbanku ya tashi ka gaishe shi"

Sadik bece komai ba ya nufi sashin Abba, ya tura ƙofar ya shiga da Sallama.

Abba dake shan tea ya É—ago ya kalli Sadik tare da sakar masa murmushi sannan ya amsa sallamar.

"Abba good morning"

"Morning dear, ka tashi lafiya"

"Alhamdilillah"

Abba yace "Masha Allah, director na makarantar ku ya kirani jiya, he tolds me that you wrote your last paper yesterday"

Sadik yace "eh Abba mun gama"

"Masha Allah My Son, Allah yayi albarka ya bada sa'ar jarrabawar, Insha Allah sakamako na fitowa zaka tafi karatun ka, kaje kai zamanka hankalinka kwance, idan ka kammala seka dawo"

"Abba dan Allah, ni dai dama a bar zuwa ƙasar wajen nan a nema min kawai a Nigeria ko a nan Kano ne"

Abba ya kalleshi yace "You Are not serious, Sadik da a zamaninmu shine a kai karatu na gaske a ƙasar nan, amma banda yanzu karatun da zaka kammala a shekara huɗu, se kai shekaru bakwai kana fama abu ya gagara, kullum cikin yajin aiki, yanzu idan kaje can kuwa ba ruwanka da wannan nan da nan ka kammala degree ɗinka, kayi Master's ɗinka a can, sannan ka dawo gaba ɗaya"

Sadik kamar ze kuka yace "Abba wai sena gama masters zan dawo?"

"To idan ka dawo ka zauna me zakayi, ka dinga zuwa mana hutu shiki, ka maida hankali ka gina rayuwar ka, duk da nasan ba zaka bani Kunya ba"

"Abba, ba zanyi Aure ba sena gama Master's É—in?"

Saroro Aba yai, dan har damuwa ta bayyana a fuskar Sadik É—in.

"Wace irin maganace kuma wannan Sadik? Guda nawa kake da kake wannan batun, kai ka san nauyin dake hawa kan mutum kuwa idan ya ajiye iyali, guda nawa kake gaba É—ayanka, yayanka ba abun koyi bane a gareka, ya kammala Master's É—in sa sannan yai aure, ai shi Aure lokacine ÆŠan gidan Abba, idan lokaci yayi zaka yi"

Ba fargabar Komai Sadik yace "Abba yarinyar da nake so ba zata jirani tsayin shekaru bakwai ba, kan in Aureta ba, Daddy wallahi ina sonta Sosai" Sadik yai maganar ƙwalla kwance a idonsa.

Abba ya jinjina kai yace "Sadik, kasan dai ba zan maka Aure yanzu ba ko? Kai kanka kasan ba ka isa Aure ba, ina son ka cire wannan tunanin a ranka ka maida hankali akan karatun ka"

"Abba ina sonta Sosai, idan na tafi zata iya Aure ta barni".

Tausayin Sadik ne ya kama Abba, amma ya bar hakan a zunzurutun shirmen ƙuruciya.
Chapter 13 · 0% Book details