Sashe 76
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ze kuma magana Malam Zakari ya girgiza masa kai alamar yai Shiru ya kalli Farhan yace "munji duk bayanan ki, an miki ba daidai ba ta wani fannin amma ta wani fannin ke ma me laifi ce, yanzu kiyi ƙoƙari ki tuba ga Allah, ki dena wannan yawace yawacen da kike, bin maza baze haifar miki da ɗa me ido ba"
Yaita yiwa Farhan Nasiha, ta sunkuyar da kai tana sauraren sa, yai ya ƙare Sannan ta miƙe, ta fita waje, kayan Abinci yara suka dinga shigowa da su, suka tsaya suka bi kayan da ido, Farhan ta dawo cikin gidan, Abba yace "wannan na menene?"
Farhan tace "kayan Abinci ne Abba na kawo muku"
Umma tace "ba zamu ci kayan haram ba, ki kwashe kayanki"
Farhan tace "Umma ta ya kika san kayan haram ne? Kyautar su aka bani nima, amma bana haram bane dama kayan al'umma ne nima aka bani, Allah ya nunan lokacin da Umma zaki bani kariya ko inga soyayya ta a cikin idanun ki, ko naji abunda 'ya'ya suke ji" tana gama faɗin haka tai waje,se ƙarar kunna mota suka ji, ko a ina ta samo mota har ta iya tuƙawa da wannan ƙananun shekarun naat oho mata.
Malam Zakari yai taiwa Umma Nasiha akan tai haƙuri da halin da Farhan ta shiga, ta janyota a jiki, ko Allah ze sa a samu ta dawo hanya.
Ita Umma har ga Allah lokacin da ta haifi Farhan, tana ƙaunar 'yar ta sosai da sosai, sedai a garinsu ta haifeta, kuma seda Farhan tai wata uku Sannan ta dawo, tun a can garin dama sun saba, ɗan fari ba a jansa a jiki sam.
Kuma ga ƙarancin shekaru lokacin, da tai wani yunƙuri na bawa Farhan kulawa se ayo caaa a kanta ana cewa ba ta da Kunya, ko Shayar da Farhan ba ta iya sakin jiki tayi, a garin gudun kar tai wani abu da zesa ace tai rashin kunya, ta fara watsi da lamarin Farhan, se ta ke ganin ai Kamar ba'a san ɗan fari ne, dan haka har suka dawo gida sam ba ta wani kula da Farhan.
Watan Farhan biyar ta samu wani cikin, dan haka tai ta fama da laulayi, daga can garinsu aka zo aka tafi da Farhan, aka yayeta tana da wata takwas, wataran Abba yaje duba Farhan a garin, ya tarar ba ta da lafiya kuma anƙi kai ta Asibiti se jiƙe jiƙe ake mata a gida, aiko yace da ita ze tafi, an kai ruwa rana sosai da Abba, tare da ƙananun maganganu akan rashin ta ido da ya nuna, dan seda Auren ya so ya samu matsala.
Umma taji haushin Abunda Abba yai Sosai, a cewarta ya zubar mata da mutunci a rigarsu.
Hakan ya sa ba ta wani bi ta kan Farhan, tana fama da laulayinta kusan Abba ne yakewa Farhan Komai, a haka har Umma ta haihu, ta haifi Amir aka sa masa sunan mahaifinta, nan ta ɗau ƙaunar duniya ta ɗora akan Amir, amma ba ta damu da Farhan ba, a haka Farhan ta tashi.
Wani uban gumi ne yake ketowa Sadik, tun bayan da sakamakon gwajin da akai wa Nana ya tabattar da tana da juna biyu har na watanni uku da sati biyu, idan lissafin sa daidai ne, to a karon farko da ya kasance da ita ta samu cikin turƙashi!.
Ya san akwai daru na gaske, idan har Nana ta san tana É—auke da juna biyu, shi kansa wata irin kunya ce ta kama shi, da wani ido ze kalli iyayensa musamman Mother, da ta ke ta kumfar bakin ita É—anta be isa Aure ba, ga kashedin ta a gareshi na babu ruwansa da Nana.
Da wani idon ze kalli Inna, da ya gama ce musu baya son jikarsu, katsam se su koma a ganta da ciki, ya fito da niyyar tafiya pharmacy ya karɓo magunan da likita ya tura musu, yaje ya karɓa, ya hangi Nana tana ta ciye ciyenta hankalinta a kwance tana kalle kalle, gaba ɗaya ƙuruciyarta ta sake fitowa Yarinya ce sharaf, chocolate ɗin da take sha, duk ta ɓata gefen bakinta da ita, kuma hankali kwance take sha, tan kaɗa ƙafafuwan ta.
Sadik ya kalli kamsa a madubi, shi kamsa kunyar kansa ce ta kama shi, as he is, he impregnent this little girl Subhanallah, abun kunya ya afku.
Yaje ya karɓo mata maganin, ya zo in da take zaune ya kalleta yace "taso mu tafi gida"
Ta ɗan ɓata fuska tace "ɗan yi haƙuri in ƙara hutawa, ƙamshin Asibitin ne yai min daɗi"
"Meye abun so a nan, ban da warin magani ba abunda Asibitin yake fa"
Nana tace "Wallahi ni dai ya min daÉ—i"
"Kimga ta so mu tafi, ko in barki a nan ina son zan shiga school ne, muna da training yau"
Nana ta tashi ta bi bayan Sadik, suna tafe a hanya tana ta sashi kashe kuÉ—i, tace zata ci wannan tace za ta ci wancan, shikam abun duniya ya ishe shi.
Tunani yake ta yaya ciki ze rayu a jikin Nana, da wani idon za su kalli iyayensu idan sun koma gida?"
Suna zuwa gida, Nana tun a falo ta cire kayan jikinta, ta bi lafiyar kujera ta kwanta, dan abu kaɗan yanzu se ta ji ta gaji, Sadik ya ɗan ƙurawa cikin ta ido, tabbas cikin ta ya ɗan ɗaga.
"Wai ya na ga kana ta kallona ne, Lafiya kuwa?"
Yace "Lafiya ƙalau"
Tace "yawwa, ni ba ka gayamin me ma sukace ba fa"
Ya É—an yi ajiyar zuciya yace "ba su ce komai ba, magunguna ne ga su nan in kin tashi shiga É—aki seki tafi da su"
Nana tace "to, amma meye yake damun?"
"Malarai ce kawai"
"Malarai kuma? A ina sauro ya ganni ya ciza, ai nan ƙasar babu sauro, ta yaya na samu malarai?"
Nana kenan, akwai shegiyar tambaya da kaifin basira.
Sadik yace "ke bana son yawan surutu, da wannan tambayoyin naki, typhoid ne kawai, da Ulcer kuma sunce idan ba kya cin Abinci mutuwa zaki, hanjinki ya tsitsinke"
Zare ido Nana tai tace "Na shiga uku, wani irin hanjina ya tsitsinke kamar taliya, wannan ai ba maganar da ya dace a gayawa mara lafiya bane"
"Ai in dai ba zaki kula da kan ki ba, ki maida kai ki dinga cin abinci ba, abunda ze faru da ke kenan"
"To ni ba amai nake ba idan naci, ba abunda ze sameni Insha Allah, ji min mutane da kalen tsiya" tai ta mitarta, Yayin da Sadik gaba É—aya jikinsa a sanyaye yake.
"Lilly ki gayamin Wanda yai miki cikin nan tun kan mahaifinki ya dawo, wallahi idan kika bari ya dawo daga ni har ke mun shiga uku, ki gayamin waye?"
Sosai Lilly take kuka tare da girgiza kai, amma ta kasa furta komai, se hawaye da ke zuba daga idanunta, ga wani uban gumi da ta haɗa, kamar me naƙuda.
Cikin zafin zuciya Mummy tace "zaki gayamin ne ko sena danne ki na shaƙeki, kan shi ya dawo ya kashe ki?"
"Mummy ban sani ba wallahi" Lilly tai Maganar da ƙyar kamar numfashinta ze ɗauke.
"Ƙarya kike munafuka, shegiya maƙaryaciya, ni zaki rainawa hankali, likita ya tabbatar min da ba wannan ne karonki na farko ba, wai Lilly har kin san ki ɗau ciki ki zubar, a wannan ƙananan shekarun naki Lilly, zaki gayamin waye ko sena yanka ki"
"Wallahi Mummy ban sani ba" tai maganar tana ja da baya.
"Kika kuma cemin ba ki sani ba, sena gwara kanki na fasa miki kai, ni zaki wa ƙarya? A ruwa kika sha dan ubanki? Ko a iska kika shaƙa, wane tsinanan ne yai miki ciki, zan farke wannan ɗinkin da ke jikinki idan baki gayamin gaskiya ba" Mummy tai maganar tana shaƙo wuyan Lilly.
Jikin Lilly na wata irin rawa, laɓɓanta se kakkarwa suke, ga gumi da yake ɗiga daga jikinta tamkar ana narka mai, ta janyo numfashinta da ke barazanar barin huhunta tace "zan faɗa miki Mummy, zan faɗa amma dan Allah kar ki kashe ni, ki cikani ba na iya shaƙar numfashi"
Tai jifa da Lilly a gurin, take Lilly ta fasa wata uwar ƙara, ta dafe cikin ta in daa a kai mata aiki, abunka da uwa, nan da nan kuma hankalin Mummy ya tashi, ta yo kan Lilly da gudu tana taɓata.
Tana duba gurin da a kai mata ɗinkin, taga yana tsatsafar da jini, alamar fama gurin tai, da fari ji tai kamar tai banza da ita ta ƙyaleta, amma taji ba zata iya ba, haka ta ɗau mayafi suka koma Asibiti.
Se da aka sake dressing É—in gurin, likita yai ta mita yace "Hajiya, ki kwantar da hankalinki wannan abun ba akan ku aka fara ba, sakaci ne dai an riga anyi shi, aikin gama ya gama, duk wata tuhuma da za kuyi mata, ku bari ta warke ta samu Lafiya tukuna, idan ba haka ba, zaku mayar mana da aiki baya ne, idan tana famawa gurin baze warke da wuri ba" haka yaita faÉ—a sannan ya sallame su suka koma gida.
Lilly ta rasa in da za ta saka ranta, dan gaba É—aya Mummy tai watsi da ita ba ta shiga harkarta, gashi ta kashe wayarta, duk wanda yaji labarina ba ta da lafiya ya zo dubiya, se ace ai appendicities ne yake damunta a kai mata aiki.
Faruk ne ke kwance yana video Call da Sadik, "Autan Mother, wai dan Allah me kake ci ne haka, ka wani zama ƙato Kamar ba kai ba"
Sadik yace "hutu da kwanciyar hankali mana"
"Lallai kam, kai karatu yana sa mutane su rame, amma kai ka zama ƙato, ni ba ka ga yadda duk na rame ba?"
Sadik yai murmushi yace "ni da kai É—aya ne? Ko ka manta ina da Aure ai akwai banbanci"
Faruk ya kwashe da dariya yace "kaga É—an banza, ni zaka gayawa Magana, wai kana da Aure, kamar ba kuka ka dinga yi kana cewa kai ba ka so ba"
Sadik yai dariya yace "to yanzu ina so, ya ranka?"
Faruk yace "rai na fes, ina Nanan?"
"Wai ina ruwanka da mata ta ne?"