Sashe 77
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah ya shirye ka Sadik, na san wataƙila Mother ta kusa ɗaukan jika ko?"
Gaban Sadik ya faÉ—i, amma ya maze yace "Ni yaro ne gaskiya, akace Mother za ta É—au jika daga gurinmu ai kashin mu ya bushe"
"Ba wani kashinku ya bushe, Kamar ba nan ka ke zuwa ka sameni kake gayamin wai kai Aure kake so ba, kai akwai wadda ka ke so something like that"
Sadik yai shiru ya fara tunani, wace ce yake so to? Kamar wani abu ya taɓa faruwa, amma ya kasa tunawa.
"Friend, wai me kake a É—aki ne, ka zo ka taya ni kwalemar falon nan"
Sadik ya kalli Nana yace, zo ku gaisa da Faruk.
Murmushi Nana tai ta ƙaraso ta kwanta a jikin Sadik tace "Yaya Faruk ya kake?"
Faruk yace "Lafiya ƙalau Nana, ya karatu?"
"Alhamdilillah, Yaushe zaka zo ka ganmu"?
Faruk yace "Nana ina Makaranta nima, tunda na tafi bana samun lokaci isashe, amma na so zuwa nima in ganku"
Nana tace "Allah ya temaka, ai mun kusa zuwa Nigeria hutu, ko Friend?" Tai maganar tana kallon Sadik.
Sadik yace "yaushe mu kai haka dake?"
"Kai ne fa kace zamu je Nigeria in kunyi hutu"
"To mun fasa"
Hararar Sadik tai tare da tura baki, Faruk ba ƙaramin farin ciki yai ba, ganin Sadik da Nana suna cikin kwanciyar hankali, da alama babu wata damuwa a tare da su.
Faruk yace "mhmm, nikam se anjiman ku, naga abun naku bana ƙare bane"
Sadik yace "Allah sarki Gwauro, ka huta lafiya muma bari muje muyi feeding É—in juna"
"Kaci ubanka ne, nine gwauro ko? Zan kama ka ne"
Sadik ya ajiye system É—in tare da É—an lumshe ido.
Nana ta kalli Fuskar Sadik, zuwa ƙirjinsa, wani kwantaccen gashi ya fito a ƙirjinsa, gashi gemu ya fara fitowa a haɓarsa.
Murmushi tai, ta kai hannu gemunsa ta shafa Sannan tace "su friend an girma, mun fara gemu irin na Yaya Faruk"
BuÉ—e idonsa yai ya kalleta yace "Au ke haryanzu a gurinki ban girma ba?"
"To ai se mutum yai gemu, Sannan ya zama babba, Allah yasa kai ma naka yai yawa kamar irin na Yaya Faruk"
"Hmmm, kina son gemu ne?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To daga yau ba zaki sake gaisawa da Faruk ba, tun da gemunsa burge ki yake"
Ta ɗan ɓata fuska sannan tace "daga na ce Allah ya sa gemunka ya zama irin nasa shine kuma abun Magana?"
"Eh É—in, É—agani ma"
Ƙara narke masa tai a jiki tana kukan shagwaɓa tace "ni fa bance yana burgeni ba, kawai cewa nai Allah yasa gemunka yai irin nasa"
"To naji, amma daga yau kar wanda ya ƙara burgeki in bani ba, kin ji ko?"
Tace "to naji"
"Good girl" yai maganar yana murmushi.
Tsaye yake a bakin gate ɗin gidan, yana ƙarewa layin kallo, yana tuna Yaushe rabonsa da layin, komai yana nan yadda yake, a guje yaga an fafaro wata farar mota vibe, wata uwar ƙura ta tashi a layin, mamaki ne ya kama shi, yabi motar da kallo yana tunanin waye wannan yake gudu irin haka, a wannan ɗan ƙaramin layin?.
Mamkine ya kama shi ganin wadda ta fito daga motar, se dai yana tantama anya wadda yake tunanin ce?.
Sunusi ne ya sha gaban Farhan, ta fito daga cikin mota, sanye da riga da skirt mayafinta a hannu, da jakarta.
"Yanzu Farhan wai ba kya jin kunyar yawon da kike a gari haka? Haba Farhan kiyi haƙuri ki zo mu sasanta in rufa miki Asiri, muyi Aurenmu ni haryanzu ina sonki wallafa"
"Lallai, ya tabatta ka haukace Sosai da sosai, kalleni ka sake kallona, ko a lokacin da aka amsa za'a baka Aurena kai ka san ni ba sa'ar Aurnka ba ce, yau Da ace kai mutumin kirki ne zan iya haƙuri in Aureka, amma mutumin banza irinka, mutum na farko da ya fara haɗani da iyayena, da in Aureka gara in ƙare rayuwata a titi ba Aure"
"Ke har ni zaki gayawa Magana, kina karuwa wulaƙantacciya, dama niyyar caka min ke a kai, Allah ya rufan Asiri"
"To tun da Allah ya rufa maka Asiri ba a caka makan ba, wani munafuncin ne ya sa ka zo kake cewa in Aureka?" Ta daki jikin motar da ƙarfi sannan ta nuna Sunusi tace "wallahi idan ba ka fita daga sabgata ba, sena sa an casa min kai wallahi, sakarai ƙazami kawai" galala Sunusi ya bi Farhan da kallo tare da mamakin maganganun ta.
Cikin Azama Abbas ya shiga cikin gidan Hajiya, yana ƙwala mata kira.
Hajiya tace "Subhanallahi, wane irin kira ne haka Abbas? Daga dawowar ka ka zo mu gaisa, seka dinga min wannan kiran?"
Ajiyar zuciya Abbas yai yace "yi haƙuri Hajiya, wallahi wani abu ne ya ɗan rikita ni, barka da gida"
"Yawwa barka, shigo"
Abbas ya shiga falon Hajiya, ya tarar da manya manyan kuloli da ta shirya masa Abinci, kwanansa biyu da dawowa, yau ya shigo gurin Hajiya.
Suka zauna su ka gaisa, tana masa ya hanya ya karatu?.
Ya nisa yace "Hajiya, wata na gani kamar Farhan, amma ina tantama, a mota na ganta da shigar da ban taɓa ganinta ba ba hijjabi a jikinta"
Hajiya tace "kai dai bari Abbas, zancen ne ba daÉ—i"
"Hajiya, ba daÉ—i kamar yaya? Meke faruwa ne?"
Hajiya tace"zancen babu daÉ—i Abbas, abunda a kaita gufunyne dai, yanzu Farhan ta canza daga yadda ka santa, ba a samu É—aura Aurenta da wannan yaron ba, kamar dai yadda kai ta gargaÉ—i da gudun karta shiga wani hali, amma dai Allah be ba abun da ake gudun ya faru"
Abbas yace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Hajiya meyasa baki gayamin ba, amma tukuna wai ma meya faru da ita ne?"
"Yawon banza Abbas, ga kuma shaye shaye, dan tun a ranar É—aurin Aurenta tayi mankas, ba ta san me take ba"
Hannu bibbiyu Abbas ya saka ya dafe kansa, yana sauke numfashi.
Ya ɗago yace "Hajiya, iyayen Yarinyar nan ba su yiwa kansu adalci ba, Allah ya basu nutsatsiyya yarinya, amma sakaci ya sa sun bar rayuwarta ta gurɓace"
"To kowa da irinsa ne, aikin gama ya riga ya gama sedai a tayata da Addu'a, Allah ya shirya"
Abbas kasa cewa komai yai, ya shiga cikin damuwa sosai, gaba É—aya hirar ma sama sama su kai da Hajiya, Abincin ma kaÉ—an yaci, yaiwa Hajiya Sallama yace tafiya zeyi.
Haryai niyyar hawa motarsa ya tafi, amma ya hangi motar Da ya hangi Farhan ta zo da ita É—azu.
Ƙofar gidan su Farhan ɗin ya nufa, yana nan tsaye yana kallon Motar, sega wani Almajiri ze wuce, yace ya shiga gidan yace ana sallama da Farhan.
Tace Ba za ta zo ba, shine amsar da yaron ya bawa Abbas, yace inji Farhan.
Guri ya nema ya zauna akan wata baranda, yana ta juya tare da mamakin yadda Farhan wai ta koma yawon banza.
Yana nan zaune sega Farhan ta fito cikin wata haÉ—aÉ—iyar purple É—in abaya, ta sha duwatsu Fuskarta tai fresh, tare da bayyanar da tsantsar yarintar ta.
"Assalamu alaikum" shine abunda kunnuwan Farhan suka jiyo, fasa buÉ—e motar tai, ta waiwayo ga mamakinta se ta ga Abbas a tsaye.
FaÉ—aÉ—a murmushin ta tai tace "Saukar Yaushe ba labari?"
Murmushin ƙarfin hali yai yace "kinyi mamakin ganina ko? Tun shekaranjiya na sauka amma se yau na shigo unguwar ta ku"
"Masha Allah, ka kammala course É—in kenan?"
"Eh na kammala Alhamdilillah, dan se da na ƙara watanni ma na huta sosai"
"To Allah ya Sanya albarka a abunda ka karanta, yasa al'umma su amfana"
Abbas yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nace in ba damuwa ko in zo in rakaki in da zaki?"
Ta girgiza kai tace "a'a Nagode"
"Meyasa ba kya son rakiyar tawa?"
"Haka kawai" ta bashi amsa.
"Ban taɓa tunanin zan dawo in ganki a wannan yanayin ba Farhan, why? Garin yaya haka ta faru?"
Farhan ji tai kamar ya soso mata in da yake mata ƙaiƙayi se hawaye.
Ya ɗan matsa gabanta yace "Farhan why? Kalli yadda kika maida rayuwar ki, kina ɗaya daga cikin wanda ake kwatancen nagartattun yara ne masu tarbiyya a unguwar nan, meyasa kika zaɓi canza akalar waccan rayuwar zuwa wannan me munin?"
Ba ta ce masa uffan ba, tana kuka ta buɗe motar, ta shiga ta tafi. Abbas ya daɗe a tsaye yana jinjina lamarin, Farhan Just needs guidance and counseling to save her, and he promised to do so for her, saboda yana matuƙar jin tausayin ta.
"Sadik dan Allah kai min magana, a tsorace nake amma na gaya maka abunda ke damuna ka ƙi kulani"
Sadik yace "to me zance miki?"
"Kalleni fa, kalli yadda na koma, na zama wata ƙatuwa, wallahi wani abu ne yake min yawo a ciki na, kuma kalli cikin ƙara girma yake dan Allah ka mai da ni Asibiti" tai maganar cikin kuka.
'malama karki É—aga min hankali, Abincin da kike ci ne yai yawa, shiyasa cikin yake girma"
"Ni yaushe nake cin abinci balle cikina yai girma, shikenan wata Cutar ce ta kamani, dan Allah ka maida ni Asibiti"
"Ke, ciki ne ba wani abu ba" ya bata amsa kai tsaye.
Saroro tai tana kallon Sadik, se taji kamar ba ta ji daidai ba, tace "me kace?"
"You Are pregnant, abunda likitoci suka gayamin kenan wancan lokacin da muka je Asibiti, You Are four months pregnant"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Ciki ne dani? Na shiga uku na lalace"
"Ke meye haka? Wace irin magana ce haka kin shiga uku kin lalace"
"Ban sani ba, shikenan ka gama da rayuwa ta, ya zanyi da ciki Sadik? Kawai se in koma gida a ganni da ciki na shiga uku, wallahi se an zubar da shi lalacewar tai min yawa"
Wani Mugun kallo Sadik yaiwa Nana yace "mutuwa zaki a banza, ƙarafa za su sa miki a jiki, in aka zubar da cikin ki mutu a banza, wani Auren zanyi ni ba ruwana"
Nana ta sake ɓare baki tana hawaye, har da majina tace "shikenan ka gama da Rayuwata, 'yar yarinyata da ni ace ina da ciki, shikenan na dena zuwa Makaranta, Inna kasheni za tai ta koreni daga ƙauye, ina zan sa kaina? Wallahi seka sakeni, ba zan cigaba da zama ba kana cuta ta"