← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 115

Sashe 91

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban sani ba, ya kake so in yi da raina Sadik? Damuwaka fa ba kai kaɗai ta dama ba, farincikina da ɗanmu yana da alaƙa da farincikin ka na rasa laifin da nai maka, kace ban maka laifi ba amma kuma duk ka canza min, ba ka walwala ba ka isashen bacci, ni ya kake so inyi ne?" Tai maganar tana fashewa da kuka.

Sosai tausayinta ya mamaye zuciyar Sadik, idan da alƙawari be kamata ace ya bar hawayen Nana na zuba ba.

Ya janyo ta jikinsa, ya shiga shafa bayanta yace "Besty na, bana son ganin hawayen ki, dan Allah ki yafe min, ki cigaba da yi min Addu'a, Allah ya yaye min dmuwata"

"To Meye damuwar taka to?"

Kwanciya yai tare da kwantar da ita a jikinsa yace "Nana, kina sona ne?"

Jin tambayar tai banbarakwai, amma tai shiru.

"Ni ina sonki Nana" yarrr ta ji a jikinta.

"Ina sonki Nana, so da gaske ba wasa ba, amma....., Amma.... Asma"

"Na'am Besty"

"Dan Allah duk abunda ze taso, ki zama me min adalci, kema idan kika barni zan shiga damuwa, dan Allah Husna"

"Nifa ban gane duk wannan maganar taka ba"

Yai ajiyar zuciya yace "don't mind me, just believe that I love you"

Kwantar da kanta ta sake yi a jikinsa, yace "to ni ba kya sona?"

"Mmmm, ina sonka sosai da sosai baban Sahal, Allah yaye maka damuwar ka ya baka abinda kake so duniya da lahira"

"Ameen my Love"

Daga nan kuma suka shiga fagen soyayya.

Wayewar gari Sadik Nana na bacci, Sadik ya fita, unguwar su Farhan kai tsaye ya wuce, yai parking a bakin hanya, ya shiga cikin layinsu, ya samu guri ya zauna ya zubawa ƙofar gidansu ido, yana nan zaune se ga Motar Abbas tai parking, Sadik yana zaune yana kallon ƙofar gidan sega Farhan ta fito cikin uniform, Sadik ya miƙw cikin azama amma tuni ta shige Motar Abbas tace su tafi.

Kamar taɓaɓe haka ya koma tasa motar, ya dinga bin su a baya, Farhan ta ga Sadik, amma Abbas be lura da su yake bi ba.

Har ƙofar makarantar Sadik ya bisu, Abbas ya sauke Farhan, ta shiga makarantar, haka Sadik ya samu guri ya zauna, yana jiran har a tashi su Farhan daga makarantar.

Sadik ya daɗe a gurin, har ƙarfe biyu tun safe yana can, ɗalibai na ta fitowa Farhan ta fito itama, ta samu guri ta tsaya tana dannan wayar hannunta da alama kiran waya za tai.

Ƙamshin nan dai da ya saba kashe mata jiki, tare da narka mata zuciya shi taji.
Ta ɗag idanunta ta saka a na Sadik, ja da baya tai zata raɓa shi ta wuce, amma ya sha gabanta ya tsaya yana ƙare mata kallo.

"Bani hanya zan wuce ko"

"Farhan, yanzu ni kike gudu haka? Na san ni mai laifi ne, amma ki bani dama ko sau É—aya kiji ta bakina"

Tsaki tai ta juya zata bar gurin, amma ya riƙo dantsenta na dama, aikuwa ta sa na hagun ta bashi lafiyayyaen mari.

A fusace tace "kana da abunda zaka gayamin ne? Meyw baka gayamin a baya ba, tarin ƙarairayi da daɗin baki, idan ka kuma nuna ka sanni, se na maka tijarar da baka taɓa tunani ba, ba Farhan ɗin da ka sani bace a baya, wannan tantiriyar 'yar maye ce, da ta goge a hannun 'yan iskan abokanka"

Ya dafe kuncinsa yai murmushi yace "ni haryanzu Farhan ɗina nake gani, sam masifar taƙi hawa dake, soyayyata da kewata kawai nake gani a idonki!
AM SORRY NOT EDITED!

Tuni idon mutane ya dawo kansu Sadik, amma ko a jikinsa ya cigaba da yiwa Farhan magana, "Farhan ba haka kike ba, kuma wannan yanayin da kike ciki ma yaƙi karɓar zubin halayyar da Allah yai miki, dan Allah ki bani dama Farhan, kiji ta bakina"
Ko kallonsa ba ta kuma yi ba, kawai ta sa kai ta cigaba da tafiyarta, Yayin da wani irin tausayin sa ya fara mamaye ilahirin zuciyar ta.
Sadik ba ya son cigaba da takura mata, saboda haka ya hau motarsa ya koma gidansu Amin.

Ko da Amin ya ga Sadik, a nesa da shi ya tsaya yana kallonsa.

Sadik yace "magana na zo muyi Amin"

Amina yace "mu yi ta daga nan ba zan zo ka sake shaƙe ni a banza ba"

Sadik yace "am sorry, Wallahi ba abunda zan maka, Magana kawai nake son muyi"

Da ƙyar Amin ya amince, Sadik ya ƙarasa in da yake, ya miƙa masa hannu suka gaisa, Sannan Sadik yace "Amin, dan Allah ina son ka gayamin tsakani da Allah, abunda ka sani tsakanin Farhan da Mubarak"

Amin yai ajiyar zuciya sannan yace "tun bayan barinka makarantar, Farhan ta cigaba da zaryar neman ka, har ajinmu take zuwa, nine nake kwantar mata da hankali, ta ƙara nesanta kanta da mutane sosai fiye da da, se ta fara zuwa ajinmu tana neman a bata maganin hana damuwa, dan ta taɓa jin su Tasleem na maganar suka shan maganin rage damuwa.
A nan Mubarak da Nas suka fara ƙoƙarin bata kayan maye, Wallahi Sadik nayi iya yina akan kar Farhan ta fara shan kayan maye, amma ta sanar da ni ba zan gane irin halin da take ciki ba, dan haka in ƙyaleta, da haka suka fara bata kayan maye.
Am sorry da abunda zan gaya maka, wataran sun gayyaceta Hotel, da zuwan idan taje za su bata magani, ban sam meyafru ba, sedai a yadda suke hira kamar, kamar they rape her their"
Daram ƙirjin Sadik ya buga da ƙarfin gaske, ya dafe kansa yana sauke wani irin wahalallen numfashi, ya ɗago idanunsa da su kai ja yace "idan Mubarak yai min haka ba abun mamaki bane, amma Nas ban taɓa zaton ze min haka ba, kaimin alfarma ɗaya Amin"

Amin yace "wace Alfarma kenan?"

"Ka kaini in da zan samu su Mubarak"

Amin yace "nasan halinka Sadik, ina jin tsoron abunda ze biyo baya"

"Ba abunda ze biyo baya insha Allah, ka min wannan alfarmar dan Allah"

Amin yace "shikenan, amma kaima Sadik kome yarinyar nan tayi, da sa hannunka a ciki, kawai se nemarka mu kai muka rasa, mu kanmu abokanka ba bu wanda ya san in da kake, a airport fa naje raka babanmu na haÉ—u da Faruk ya gayamin kayi Aure, mu kanmu Banu sani ba, how comes Sadik?"

Sadik ya girgiza kai yace "ba zan iya yi maka bayani ba yanzu Amin, ni dai muje ka rakani"

Gaba É—aya Sadik tausayi ya bawa Faruk, dan haka bece komai ba ya shiga gayawa Sadik in da za su su samu su babba.

Farhan kuwa gida ta tafi, tana tuhumar kanta akan marin da taiwa Sadik a cikin mutane haka, gaba É—aya se taji ba taji daÉ—i ba sam.
Gefe guda Alhajin nan ya takura mata akan lallai se ta gaya masa waye Sadik, dan ba ya jin ze iya ƙyale shi akan abunda yai masa.

Wata mashaya Amin ya kai Sadik, ƙeyar mubarak kawai ya hango ya ganeshi, ya bawa in da suka shio baya yana ta sakin hayaƙi.
Sadik ji yake tamkar ya ƙarasa yaje ya shaƙe shi ya kashe shi kowama ya huta, saboda ba ƙaramin hatsari bane ga al'umma.
Sam Mubarak be lura da Sadik ba, harya ja kujerar gabansa ya zauna, ya busa hayaƙin wiwi, ze kuma zuƙa kawai ya saka idanunsa a na Sadik, seda yai wata irin zabura ya saki wiwin hannunsa, Sadik manakin yadda babba ya sake lalacewa yai, idanunsa duk sun fito waje, sunyi jawur saboda azabar shaye shaye.

Mubarak ya wani basar yace "Man yane, saukar yaushe?"

"Saukar uwarka da ubanka" Sadik ya bashi amsa a harzuƙe.

"Mubarak, me kaiwa Farhan meye alƙarka da ita?"

Wani irin murmushin rainin hankali Mubarak yai yace "kamar yaya, ai sanin wannan amsar ba shi da amfani a gareka, tunda ka tafi ka barta ba ka so, anyi mata abunda ya dace ne kawai"

Wata irin shaƙa Sadik yaiwa Mubarak, ya ɗagoshi tsaye yace "me kai mata? Why do you rape her? Me tai maka?"

Mubarak yace "haba Sadik, a tunaninka abunda kai min ka ci bulus ne? Se da na tabbatar da idan na taɓa ta zan maka illa, sannan nai mata abunda ba zaka manta ba, we rape her, four of us, a Hotel and we shoot a video mu saka a yanar Gizo ya kawo mana kuɗi, mun sata a layi yanzu haka kasuwancin da take kenan".

Sadik ji yai kamar zuciyar sa na ci da wuta, ya wujujjiga babba ya jefa shi ƙasa, ya dinga dukansa.

Cikin azama Amin ya riƙe Sadik yana faɗin "Sadik za kai kisa fa"

Nan mutanen da ke gurin su kayo kansu, ana bin ba'asin abunda ke faruwa.

Sadik ya ɗau wata kwalba a gefe ya fasata ya tunkari Babba jikinsa na rawa, aka rirriƙe Sadik, yayin da Mubarak ya dinga ƙyaƙyata masa dariya har da tuntsurawa.
Gashi ya kasa tashi saboda yadda ƙwaya tai masa laga laga.

Da Sadik yai wata girgiza, gaba ɗaya ya watsar da su, yai kan Mubarak cikin hanzari, kai tsaye cikin Mubarak ya nufa da kwalbar, amma Mubarak yai saurin juyawa Sadik ya caka masa ita a cinyarsa, take jini ya ɓalle, ya kuma soka masa a hannunsa, aikuwa ya kurma uban ihu cike ɗimuwa da azabar zafi, beyi zaton Sadik ze niyyar kashe shi ba.
Wasu suka riƙe Sadik, sukace a kira 'yan sanda, duk da Mubarak na cikin azabar raɗaɗi amma yace "kar su kuskura su kira jami'an tsaro, idan suka kira su kashinsa ya bushe ba na Sadik ba, saboda Sadik yana da legal backing akwai abunda ze kare shi.

Da ƙyar Amin ya janyo Sadik da ke ta zuba huci waje, yace "ka gani ko, saboda haka fa nace ba zan rako ka ba"

Sadik kamar ze kuka yace "could you imagine Amin, saboda ni ya lalata rayuwar yarinya, me tai masa meye laifinta dan kawai ina soyayya da ita?"

Amin yace "nikam dan Allah wai meke tsakanin ka da Mubarak ne haka, da har ze iya yi maka wannan abun?"
Chapter 91 · 0% Book details