← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 115

Sashe 59

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye ya gaya miki wannan maganar, ta yaya Sadik ze yi Aure a wannan ƙananan shekarun?"

"Is possible, har nan Abokinsa ya zo ya gayamin, ya haɗu da yayansa yau a airport, yaje raka babansa, Yayan Sadik ne ya tabbatar da hakan, am fool da na tsaya na yadda da maganganun Sadik da ya dinga furta su, ni kuma RUƊIN ƘURUCIYA ya ɗebe ni na amince da shi, am Stupid, am more than fool, am idiot!"
Cikin É—aga murya take Maganar, dan ma Library É—in ba kowa, jikinta na tsuma ta fice daga Library É—in.

Ba a tashi ba, amma Farhan ta tafi gida, idonta ya bushe babu hawaye, ƙoƙari take ta ga ko zata iya samawa Sunusi matsuguni a zuciyar ta, dan ta cire Sadik amma ina, Sadik ya mamaye ko ina, ya mu'amalance ta da kyakykyawar mu'amala a lokacin da ta rasa wanda zata raɓa.

Gidansu babu kowa, Umma ba ta nan suna ta shirye-shirye, ta tafi kasuwa, kuma a yau ne za'a saka ranar Aurenta, wanda baze fi sati biyu ba.

Wata irin wuta ce ta ke cin zuciyarta, ta rasa me za tai taji daÉ—i, ta buÉ—e jakarta ta É—akko sauran maganin baccin nan da aka bata, uku kawai ta sha a jiki Kamar yadda me chemist ya gaya Mata.

A take ta ɓalle uku ta watsa ta kora da ruwa, ta runtse idonta ta na jiran ta ji bacci ya ɗauketa amma abu ya gagara.

Ta dinga watsi da kayan da ke ɗakinta Kamar Mahaukaciya, ta watsar da komai tana zazzare ido, amma ba taji sauƙin abunda ke ranta ba, ta toshe kunnenta ta ƙwala ƙara, gaba ɗaya ta firgice ta fita hayyacinta, tamkar Mahaukaciya.

Cikin azama ta fito daga ɗakin ta, ta shiga Kitchen ta hau sauke kwanuka ta na dube dube, ta zaro wata sharɓeɓiyar wuƙa jikinta na ta karkarwa!!! (This is deprssion!)

(ME KUKE TUNANIN FARHAN ZA TAI? YA KUKE TUNANIN ZAMAN NANA DA SADIK? WACE IRIN RAYUWA FARHAN KE SHIRIN FAƊAWA? KUNA TUNANIN AUREN FARHAN DA SUNUSI ZE YUWU? WANE IRIN ZAMA ZA SUYI? 💃💃💃💃💃💃💃💃HAR KULLUM COOL TAKU CE, INA FATAN ANA ƊAUKAR DARUSSAN DA KE CIKIN LITTAFIN).
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

"Farhan!" Huzaifa ya kira sunanta da ƙarfi, ya saki kayan hannunsa ya ƙaraso in da take da gudu, ya fizge wuƙar da ke hannunta, idanunta gaba ɗaya sun juye, sunyi jawur gashin kanta a hargitse kamar Mahaukaciya.

"Farhan, meyafaru haka? Meyasa zaki yunƙurin kashe kanki?"

Hannayenta ta saka ta rufe fuskar ta, ta fashe da kuka, jikinta har rawa yake, cikin hanzari Huzaifa ya tattare kayan da ta sauke ƙasa ya kalleta yace "zo muje ɗaki ki sa ka hijjabi ki kintsa jikinki, an jima mutane zasu kawo lefenki da ga gidanmu"

Ko motsi ba tai ba se kuka da take, jijiyoyin kanta duk sun ɗaga sun kumbura, se sheshsheƙa take.

Huzaifa ba shi da zaɓi illa ya kamo hannunta, ya kaita ɗakinta ya tarar nan ma ta watsar da komai, ya shiga kwashe kayan yana mayar mata drower ɗin ta.

Ya ɗakko hijjabi ya miƙa mata ta ƙi karɓa, nan ma se shi ya samata, ya kalleta yace "Yaya, meke damunki haka? Koma meke damunki ina tauhidin ki? Wane irin hali zaki shiga ki manta da Ubangiji ki zaɓi nema ki kashe kanki? Kin san wuta ce makomar duk wanda ya kashe kansa, amma ki kai yunƙurin halaka kanki, haba Yaya meyasa?"

Maimakon tai Magana, sema ta nemi guri ta kwanta, saboda ji da tai kanta yana wata irin juyawa, tana ganin duhu a idonta.

Huzaifa ya ƙura mata ido,yana jin wani irin matsanancin tausayinta ya na ratsa shi.

Ya fuskanci kamar bacci ne ya ɗauketa, harya yunƙura ze tashi ya fita, yaji ta fara surutai.

"Meyasa! Meyasa zaka min haka? I still love you, but why? Why me?!"

Huzaifa ya san Farhan ba ta son Auren nan, akwai wanda take so, amma ba bu wanda ya taɓa tunanin zama da ita ya ji damuwarta.

Ya girgiza kai ya koma tsakar gida, dan kar ta farka ta kuma yunƙurin aikata wani abu.

Yau a falo Nana ta tarar da Sadik, ta ga kamar fuskaarsa a ɗan kumbure take, yana kwance akan kujera ya ɗage ƙafafunsa tare da lumshe idanunsa.

"Nace ba, yau me zamu ci?" Tai maganar tana hamma.

A ransa yace 'ji jarababbiya, ba ta da zance se na Abinci'

Banza yai mata yaƙi buɗe idonsa.

"Magana fa nake" ta maimaita cikin tsiwa.

Sadik be kulata ba se ma tari da ya fara yi, da alama mura ta kama shi sosai, se tari yake.

Nana tace "lokacin da kake shan ruwan sanyi, da nayi magana se kace bani da kunya, amma da nai maka shiru gashi nan jikinka ya na gaya maka"

BuÉ—e idonsa yai yana bin Nana da kallo, yadda take masa faÉ—a Kamar wata uwarsa.

Ya maida idanunsa ya lumshe, yana jin yadda kansa ke masa ciwo.

Ta wuce shi ta barshi a falo, can mintuna goma se gata ta dawo da tea a cup, ta ajiye masa tace "ga shayi ka sha, se ka je Asibiti a duba ka"

Be kulata ba yai banza da ita, hakan ba ƙaramin bawa Nana haushi yai ba, tace "wai ba zaka sha ba ne?"

"Ke! Dalla ki ƙyaleni, ina ruwanki da ni ne, dole ne se kin shiga sabgata?"

Seda ta razana saboda tsawar da yai mata, tace "Allah ya baka haƙuri"

Ta koma gefe ta tsura masa ido, se atishawa yake yana tari, da alama ba ƙaramin kamu murar nan tai masaba.
Ya bi ya dunƙule guri ɗaya, da alama har da sanyi yake ji.

"Ko in É—akko maka bargo, na ga kamar ka na jin sanyi?"

Se da ya harareta ta tuna yace karta kuma shiga harkarsa.

Suna nan zaune kamar kurame, taji ana kaɗa bell ɗin ƙofar gida.

Tun da suka zo gidan nan, da wasa ba ta taɓa leƙawa ko ƙofar gida ba, ta tashi da nufin ta je ta buɗe ƙofar amma ta kasa, tana ta kokawa da ƙofar, se ji tai an tureta gefe, ta ɗaga kai ta ga Sadik ne.

Ya buɗe ƙofar, wasu yaran turawa ne sa'anin Sadik uku maza, biyu mata.

Sadik yana ganinsu ya fara murmushi,yai musu iso zuwa cikin falo, ya bar Nana a bakin ƙofa.

Ta biyo bayansu, É—aya daga cikin matan, ta zauna a kusa da Sadik ta dafa goshin sa, cikin kulawa take masa sannu da harshen turanci.

Nana kam se bin su take da ido, É—aya daga cikin su ya kalli Nana, ya tambayi Sadik wannan fa.

Sadik ya kalli Nana yace "she's my made"

"Wow she's beautiful" cewar É—aya daga cikin 'yan matan.

ÆŠayar tacewa Nana "ya kike?"

Wata uwar harara Nana tai watsawa Yarinyar, Sadik yace "karki damu, ba ta jin turanci ai"

Wani abu ya tokarewa Nana a zuciya, ita Sadik ya kira da 'yar aiki, lallai wannan ƙarshen cin mutumci ne a gareta, seda ta ji wata ƙwallar baƙin ciki ta taru a idonta, ta wuce ɗakinta.
Nan suka baje kayan ciye ciye, suna ci su da Sadik, Kamar gidansu haka suka dinga shagalinsu a gidan.

Nana ba ta sake fitowa ba, har Azahar suna gidan, se bayan azahar Sannan ta dena jiyo motsinsu, ko da ta fito falon ta tarar ba sa nan har Sadik É—in.

Sunyi kaca kaca da Gidan, kuma sunyi tafiyar su sun bar gidan a haka, haka Nana ta zage ta na gyarawa, tare da tunanin in da Sadik ya tafi alhalin ba shi da lafiya.

Yau abun na Sadik ya zarce tunani, dan har fiye da ƙarfe goma na dare ba ta ji dawowarsa ba.

Tsoro ya gama cika zuciyar Nana, ta dawo jikin ƙofar gida ta zauna ta takure jikinta Sosai, a haka wani wahallalen bacci ya kwashe ta.

Se sha biyun dare sannan Sadik ya dawo, dan yawo suka tafi da abokansa, suka sai ticket suka tafi kallon ball, be sake tunawa da Nana ba seda ya dawo ya tarar da ita a takure a bayan ƙofa tana bacci.

Har yai gaba abunsa ze barta a gurin, se yag rashin dacewar hakan, ya dawo da baya yasa ƙafarsa yana taɓata.

A razane ta buɗe ido, ga miƙe tsaye tana waige waige, ta kalli Sadik ta kalli agogon da ke falon, ba tace masa uffan ba ta wuce ta kama hanyar ɗakinta ta na tangaɗi saboda baccin da take ji.

Jin hayaniyar da tai ne ya sa ta buÉ—e idonta a hankali, ta farka da wani irin matsanancin ciwon kai, se hayaniya take jiyowa sama sama.

"Ke Farhana, wai wannan wane irin bacci ne haka, ki tashi ki alwala ki sallar isha'i, tun da muka dawo Gidan nan kike bacci, ba yadda ba muyi ba ki tashi amma kin ƙi, wane irin bacci ne haka?"

Seda tai shiru na wasu lokuta, sa'annan ta gane muryar Maman Huzaifa ce.

A hankali ta gyara kwanciyarta, ta tashi zaune, sedai kanta juyawa kawai yake, ta yunƙura ta miƙe tsaye amma ta tafi luuuu za ta faɗi.

Maman Huzaifa ta riƙeta tace "ko baki da lafiya ne?"

Farhan ba tace mata komai ba, ta fara takawa, amma se ta dinga ganin Kamar ginin Gidan ze ruso a kanta, da kyar ta kai kanta banɗaki, tai alwala ta na jan ƙafa ta koma ɗaki.

Gidan Mutane se shiga suke suna fita, ana ganin kayan lefenta, sedai har ta fito tai alwala ba wanda ya kula da ita.

Ta jero sallolin da ba tai ba, ta idar ta dinga yiwa Allah godiya da be sa ta aikata abunda tai niyya ba, na kashe kanta.

Sedai jikinta sam ba ƙwari, tana kwance aka kawo mata Abincin dare, amma sam, ba ta jin za ta iya cin Abincin.

Sama sama take jin ana cewa "Masha Allah, kaya sunyi kyau, an saka sati huɗu biki, Akwatinan ta guda biyu, ƙatuwa da 'yar ƙarama se jakar bagco"

Ana haka kunnuwanta suka jiyo ana cewa, wai ana Sallama da ita inji Sunusi, Adda tace ba ta da lafiya yayi haƙuri ba zata iya fita ba.

Da haka wani baccin ya kuma awon gaba da ita.
Chapter 59 · 0% Book details