Sashe 110
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Be ce mata komai ba yaje kitchen, ya tarar da Manyan warmers, kunun gyaɗa a teaflask, se soyayyan dankali da ƙwai a flask ɗaya.
Ya zubo dai-dai cikin Nana, ya koma ɗakinta, ya sata a gaba ya takura mata, ya dinga bata a baki da kansa, cikin kulawa Kamar ba wanda yake da sabuwar Amarya ba, se da ya tabattar ta ƙoshi sannan yace "Yawwa yanzu Sahal ze samu Abinci sosai shima, ki dena min wasa da cikinku in ba baka ba za muyi faɗa, wai ina Sahal ɗin ma yake?"
"Da aka kawo Abinci, Mother ta saka aka tafi da shi"
"Kai Mother dai na fuskanci so take mu bar mata É—an nan, kuma ba wanda zan iya bawa, bari ajima inje in É—akko shi"
Nana tace "to in dai kaje ni dai ba ruwana, bance a É—akko shi ba"
Bece komai ba ya miƙe ya fita, sashin Farhan ya koma, ya tarar ta tashi har tai wanka ta canza bedsheet, ta zauna tana shafa mai a jikinta, sam ba ta san yana nan be fita ba, da Abincin da aka kawo ya shigo, yace "Princess, barka da safiya"
Kamar ba ta ji ba tai masa shiru, ya ƙara so gaban mirror yace "kina jina fa, amma ki kai min shiru, kawo in tayaki shafa man"
"A'a Nagode, tai maganar tana karɓe robar man, ta gama shafa manta ta ɗau kayan sawarta ta shige toilet, shi dariya ma ta ba shi.
Ta fito cikin riga da skirt na atamfa, se kare jikinta take saboda yadda kayan suka matsteta, aikuwa ya zuba mata kyawawan idanunsa, se wani haÉ—e rai take wai ita a dole dole a kai mata ta Aureshi ta dena son sa.
"In kin gama ɓoye ɓoyen, seki zo mu karya"
"Ka ci naka, in ka fita naci nawa" ta bashi amsa.
Sadik yace "Ina zan fita in je, ina da zankaÉ—eÉ—iyar Amarya a É—aki, ba in da zani muna tare tip da tire, soyayya zamu sha".
"Se dai ka sha da matarka ba ni ba, ita ke sonka se kuyi ba dani ba"
"To ke yanzu ina ruwanki da mata ta? Kuma kema ai mata ta ce" neman guri tai ta kwanta, ta share Sadik.
Tana kwanciya Sadik be jira komai ba, shima ya bi bayanta kan gadon yace "Ai ta kwana gidan Sauƙi Beb, na gane abunda kike nufi"
Wani uban tsalle tai ta sakko tana haki, yai dariya yace "kin raina ni Farhan, hmm to ko ki zauna ko kuma ni in zo in sameki"
Haka Farhan ta zauna, Sadik ya dinga bata Abincin nan da kansa, tana karɓa idonta har da guntun hawaye.
Sha biyun rana ƙannnen babar su Farhan da wasu 'yan uwansu suka zo gidan, bayan sun gaisa da Sadik ya fita ya bar gidan.
Suka kawowa Farhan miya da akai mata, ta sha nama, ga Nono kaya guda da suka kawo mata, da su kayan daddawa da kaÉ—in miya, Adda Hafsa tace "Ina abokiyar zaman naki ne mu gaisa, mu yau zamu koma"
Farhan tace "nima ban san in da take ba"
"Kamar yaya baki san in da take ba?"
Farhan tace "to ai ni tunda na zo ban ganta ba"
"To shi mijin naki be haÉ—aku ya muku nasiha ba"
Farhan ta jinjina kai, Adda Hafsa tace "dama abunka ds harkar yara, gayyar shirirta wataƙila ma be san anayi ba"
Bayan azahar sukace zasu tafi, sukaiwa Farhan sallama tare da yi mata nasiha sosai, sukai mata sallama suka tafi.
Daga Nana har Farhan ba wadda ta kuma fitowa, balle wata taga wata.
Se magariba Sadik ya dawo, a zatonsa suna ta yin baƙi ne, part ɗin Nana ya fara zuwa, hannunsa ɗauke da Sahal, ya ajiye Sahal sannan yace "Besty, zamuyi dinner a falo tare gaba ɗayanmu, zan gabatar muku da juna".
Idan Sadik ya gani daidai wani mugun kallo Nana ta watsa masa, ji tai kamar tace ba zata fito ba, amma tai shiru bata faÉ—a ba.
Itama Farhan da ya je gurinta, haka su kaita artabu da ita, tsiwa kala kala, wadda be taɓa saninta da ita ba.
Bayan sallar isha'i yace mata "muje falo, zaki gaida uwargida na"
Yamutse fuska tai, ba tare da tace komai ba, ji yai kamar yai dariya, amma ya haɗiye, suka fito ƙaton falon tare, Sadik ya nufi sashin Nana, yana Addu'a, dan mutuniyar ba sauƙi hukuma ce se da rarrashi.
"Sarautar mata, ke muke jira fa"
Tace "Me za'ayi?"
"Kin manta maganar da mukai ne?"
"Dan Allah ni ka ƙyaleni, ba se naje ba"
Sadik yace "karki ɓatamin rai Please, tashi muje" ya ƙarasa maganar yana saɓa Sahal a kafaɗarsa yai waje.
Nana ta wani sake karkace É—aurin kallabinta, sannan ta biyo bayan Sadik.
Farhan na ganin Sahal ta fara murmushi, yaro tubarkallah lafiyayye, kai da ganinsa ka san akwai kulawa, ƙato da shi, fari tas me yawan suma a ka baƙi ƙirin, ko ya ya yamutsa fuskarsa se dimples ɗinsa sun lotsa, Sahal kyakykyawa ne yaron sosai.
Sadik na ƙarasowa Farhan ta miƙe tana murmushi, tana son ta karɓi Sahal, Sadik yace "mara kunya, kince ba kya so na, amma kina wa ɗana dariya zaki ɗauke shi, to ba zan bayar ba nima"
Saroro tai tana kallon Sadik, tace "dan Allah ka bani shi"
"Ba zan bayar ba, ba kya sona kike son É—ana?"
Nana ce ta fito ta same su, sedai tana fitowa suka haÉ—a ido da Farhan, sunawa juna kallon sani, a take gabansu ya faÉ—i, kowacce tana ganin anya 'yar uwatta ba ta fita komai ba.
Nana ta fara janye idonta, ta samu guri ta zauna, ta maida idonta kallon wani gurin, tana kaɗa ƙafafunta.
Sadik yace "bari mu fara da Addu'a, Besty yi mana addu'a"
Nana tace "ai kai yakamata kayi"
Be kuma tanka mata ba kar suyi faÉ—a, yai addu'a sannan ya fara bayani.
"To Dukkan yabo da godiya sun tabatta ga ubangijin talikai, buwayi gagara misali, wanda ya haɗa dukkanin mu ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure. Dukkanin ku ina alfahari da kasancewar ku a ƙarƙashina matsayin matana, wadda kowacce dan ina sonta ne nake tare da ita, babban fatana da roƙona a gareku be wuce dan Allah ku haɗa kanku ba, kar a samu wata ɓaraka da wani daga waje ze shigo ciki ba. Ku haɗa kanku ku bani damar in muku adalci, Nana ke ce Uwargida amma Farhan gaba take da ke, amma matsayinki na uwargida yana nan baze canza ba, Farhan kece ƙarama amma gaba kike da Nana, a bata girmanta a matsayin ta na uwargida na Please, Besty ga amanar Princess ɗina, Princess ga amanar Besty na nan, dan Allah ku haɗa kai ku zauna lafiya" har ya gama ɓaɓatunsa ba wadda ta tanka masa, dan Nana ma kashingiɗa tai akan kujerar tana shilla ƙafarta a hankali, rabin hankalinta akansa rabi akan tunani.
"Bestyna, ko kina da abinda zaki tofa?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Magana fa nake, nace ko kina da Magana?" "Babu"ta faɗa a taƙaice.
Ya kalli Farhan yace "Princess ke fa, do you have anything to say?"
"Babu" itama ta bashi amsa.
Sadik yace "Madalla, ga Abinci nan ku sakko muci Abinci".
Nana tace "Nikam na ƙoshi, a ci lafiya"
Sadik yace "meyasa?"
"Ka san bana cin abincin dare, saboda ban son in ƙiba".
Farhan wani dumm taji, tana tunanin ko dai magana Nana ta faÉ—a mata, dan ita 'yar duma duma ce.
Sadik be sam wani Nana ba ta cin abincin dare ba, tsabar kishi ne da iskanci kawai.
Be kulata ba, yace Farhan ta zo taci, ba ta wani ci ba, ta koma gefe tana kallon Sahal da Sadik ya kwantar da shi yana bacci.
Seda suka gama, Sadik yace "bari in kai mata Sahal, ina dawowa.
Yaje ya iske Nana har tai shirin bacci, ya ƙare mata kallo, Sannan yace "Haba Nana, Yakamata fa ki kula, kar kishi ya sa ki abunda zaki zubar da kimarki a gurin ta da wuri, she's very kind and simple, meye abun cewa wai ba zaki ci Abincin dare ba dan kar ki ƙiba?" Saboda cusa haushi, setai kamar ma ba ta san da ita yake ba
Fizgota yai tana fuskantar sa yace 'ba da ke nake magana bane? Wai yaushe kika zama haka ne? Shikenan ban isa in magana ba se ki rainamin hankali, kina ji ina miki Magana, se lalaɓaki nake amma kina buntsurewa ya kike so in yi da raina Nana? Da me zanji? Fushin su Mother ko kuma abunda kike min?"
Kuka ta fara yi masa, abunda Sadik ya tsana, kuma sanin baya son kukan yasa daga taji ya matsata se ta fara kuka.
"Me nai miki kuma kike min kuka?" Yai maganar a sanyaye.
"Ba kaine kake min faÉ—a ba"
"Haba Besty idan banyi faÉ—a ba ya zan miki? Duk kin bi kin É—agan hankali na kasa samun nutsuwa saboda halinki"
"To ni me nayi?" Tai maganar cikin sigar shagwaɓa, jikin Sadik yai sanyi ya fara bin bakinta da kallo, se tura shi take tana kuka.
"Allah ya shiryeki, da rikicin gangan"
"Ni ka cikani bacci nake ji"
"To Allah ya bamu alkhairi, kwanta in lulluɓeku"
Ta kwanta ya ja musu bargo, sannan ya kashe musu fitila ya tafi sashin Farhan.
Farhan har ta ƙule, daga zuwa kai Sahal, yaje yai zamansa aikuwa taji haushi, ta nemi guri ta kwanta.
Yana zuwa ɗakinta ya ga ranta a haɗe har ta kwanta, bece mata komai ba kuma be ƙudurci yai mata wani abu ba ya ƙyaleta, saboda ya ga yadda ta haɗe rai.
Khairat ta fito daga ita se rigar bacci, kanta ko ɗan kwali babu, zata fita babban falo neman aunda zata ci, tai kiciɓis da Faruk yana shigowa, wata kunyarsa cea kamata, dan tun lokacin da Nana tai wanan Maganar take jin kunyarsa.
"Ina zuwa?" Ya tambayeta yana kallonta.
"Kitchen zani, ina jin yunwa ne"
Yai gaba yace "follow me" ba musu tabi bayansa, be tsaya da ita a ko ina ba, se a gaban mudubi, yace "look at you, kalli rigar jikink kaki babu É—an kwali, kuma kin san haryanzu da sauran mutane a gidan nan, amma zaki fita a haka, am very jealous, idan har kina sona dagaske kina son mu shirya, to gaskiya ki dena yawo a haka"