← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 115

Sashe 82

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khairat ta shigo falo ta tarar da Mother zaune, da uban kaya a gabanta, Khairat tace "Mother me zaki da kayan jego?"

"Hmm jika zan É—auka"

"Jika kamar yaya?"

"Matar Sadik ce ta kusa haihuwa"

Zaro ido Khairat tai tace "wai wannan Yarinyar?"

"Ita fa tsohon ciki ne da ita"

Khairat tace "turƙashi, ke kina nan kina fafutukar raba Aure ashe kallonki kawai suke?"

"Kema dai kya faÉ—a, ni duk kaina ya kwance" haka suka gaba da jajanta lamarin.

Mother tayo siyayya abunda ya rage ba su siya ba, tana yi tana sake cika da Mamaki, wai Sadik za'aiwa haihuwa.

Duk da halin da Nana ke ciki na wannan tsohon ciki, Sadik yaji daɗin dawowar ta ɗakinsa, ɓangaren Nana kuwa ba ta so wannan haɗen ba, dan Sadik akwai takura, seda ta samu yai bacci, ita kuma ta kasa baccin gaba ɗaya ta tashi ta koma falo.
Cikin dare Mother ta fito É—aukar ruwa, ta tarar da Nana a zaune a babban falo se juyi take akan kujera.
"Ke lafiya kuwa?" Mother tai maganar tana ƙarasowa cikin falon.

Nana ta miƙe zaune a hankali tace "bakomai"

"To me kike a zaune a falo haka?"

"Na kasa bacci ne"

"Ko kina jin wani ciwo ne?"

Nana ta girgiza kai alamar a'a.

"Ina Sadik É—in?"

"Yayi bacci"

Mother ta wuce É—akin na su, ta tarar da Sadik ya baje yana ta bacci.

Ɗala masa duka tai ya tashi a gigice yana mutsutsuke ido tace "ka bar 'yar mutane na fama, kai kana nan kana bacci, se ka tashi kaje kaji me take buƙata"
Sadik yai miƙa ya sakko daga kan gadon, ya fito falo, ya tarar da Nana a zaune akan kujera, Kamar za tai kuka.

"Friend lafiya kike kuwa?"

"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa.
Mother kuwa wucewa tai part É—inta ta barsu.

Sadik yace "ko Asibiti zamu tafi?" Tace "A'a"

"To menene?" Ya faÉ—a cikin kulawa.

"Na kasa bacci, duk na gaji, ko ina na jikina ciwo yake cikin nan ya min nauyi, na rasa ta yadda zan kwanta inji daɗi, gashi abincin da na ci ya tsaya a ƙirjina yaƙi wucewa kuma na kasa amayar da shi" tai maganar hawaye na zubo mata.

Sadik yace "shikenan na gane, zo muje É—aki nai miki tausa ko zaki iya baccin"

Tai saurin girgiza kai tace 'kaje ka kwanta ka barni a nan"

"A'a ba za'ai haka ba" ya zauna yana mammatsa mata ƙafafunta, se hamma yake yi kamar ze ci babu.

Nana tace "zo ka kwanta, naga kana jin bacci" ba musu yai kwanciyarsa a kan cinyarta yana baccin sa.

Ita kuwa Nana, naƙuda ta fara ba ta sani ba, dan a hankali yake tsira mata, se taji mararta ta ɗaure amma ta daure.

Se gefin Asuba ciwon ya lafa mata, bacci ya kwashe ta, Abba ya ci karo da su Nana a falo, Sadik ya kwanta a cinyar ta yana baccinsa, ita kuma ta jingina da kujera tana baccinta.

Abba ya koma ya kira Mother, yace "kizo ki tashi É—anki"

Mother da ta fito ta gansu tace "yanzu da haka za'a raini ɗan idan an haife shi, kai Sadik, Sadik" a firgice suka farka gaba ɗaya, Kunya ta lulluɓe Nana, Abba ya fice kamar be ga Komai ba.

Gaba ɗaya wunin ranar Nana haka tayi shi babu daɗi sam, daurewa kawai take, amma tana jin ciwo kaɗan kaɗan, Mother kuwa ita yanzu Nana ce take bata tausayi, saboda abunda take tunkara, wato naƙuda ga nauyin ciki duk se haƙuri.

Seda Nana ta jera kwana tana ciwo a tsaye, Mother tace Nana ta koma ɓangarenta ta dinga kwana, Nana tai matuƙar mamaki dan rabonta da shiga sashin Mother, tun bikin dr. Da ta shiga aka korota.

Tace su kwana tare da Khairat a ɗakinta da ke cikin sashen Mother, Nana tace ita a ƙasa zata kwanta ba ta jin daɗin kwanciyar Kan gado.

Khairat ko kallon kirki ba taiwa Nana ba, dan haushin Nanan take ji.

Cikin dare Khairat ta dinga jin nishi, ta farka ta kunna wayarta, taga Nana ta haÉ—a gumi se salati take tana kiran sunan Inna.

Da sauri Khairat ta kira Mother, ta sanar mata da halin da Nana ke ciki, aikuwa Mother ta taso cikin magagin bacci.

A daren suka sa Nana a mota zuwa Asibiti, sedai aka duba akace haihuwa ce Amma da saura.

Sadik yana can yana bacci be san budurin da ake ba, se da Safe ya samu labari, ya shirya ya tafi Asibitin.

Sadik duk a zatonsa haihuwar ba wahala, yaje ya tarar da Nana a zaune, fuskarta duk tai wani iri, gumi kawai take.

Yace "wai haryanzu baki haihun ba?" Ji tai kamar ta kife Sadik da mari, dan a yanzu hausinsa take ji, dan duk shi ya sata a wannan bala'in.

Yace bari yaje gida ya ɗakko ruwan tofin da suka zo da shi daga ƙauye.

Harya koma gida ya dawo Nana na cikin jazabar labor, kuma ance haihuwa da saura, Mother ce a gurinta se sannu take mata.

Ko da Sadik ya kawo tofin nan Nana ta sha, tamkar an tunkuÉ—o ciwon, ta gigice gaba É—aya, aka shiga da ita labor room, Sadik ya zata ana shiga da ita za'ace ta haihu, amma abu shiru.

Abba ma da kansa ya zo Asibitin, amma Nana babu labari, nan Sadik jikinsa ya fara sanyi, dan be zaci abun ya ka haka ba.

Gashi an hana kowa shiga gurin Nana, suna nan tsaye Nurses suka kira likitar da take duta akan tazo ta duba Nana, dan sun kasa gane kan labor É—in na ta, kamar ba ya progressing, Sadik ya faki idon Mother ya shige ciki shima.

Yaje ya tarar da Nana ta fita hayyacinta, ga fanka amma kamar an jiƙata da ruwa, ga wata a gefe tana danna cikin Nana, wata na ƙoƙarin yadda za'ai kan ɗan ya fito, ga Nurse ɗin riƙe da forcep zata bata tear.

Ai gigice ya ƙarasa ya ture Nurse ɗin, idanunsa su kai ja yace "wace irin mara imani ce ke? Ya zaki sa mata wannan ƙarafan a jiki" ya ɗago Nana da zuwa yanzu ta fara galabaita, idanunta sunyi ƙanana saboda Azabar ciwo.

"Nana, buÉ—e idonki kina ganina?" Yai maganar yana girgiza ta.

"Sadik mutuwa zanyi, ba zan iya haihuwa ba, na gaji ba zan iya ba, ka yafemin"

"No, ba zaki mutu ba Nana, zaki haihu lafiya Insha Allah"

Likitar ta fita tana faɗa akan dan me Sadik ze shiga ɗakin haihuwa ze han su aikinsu, shi kuwa ya rirriƙeta se hawaye, saboda ya tausaya mata, be taɓa tunanin Azabar labor ta kai haka ba.

Usman ne yace "Doctor dan Allah kiyi haƙuri, mijinta ne bakiga duk yara ne ba, ba hankali kiyi haƙuri"

Ta zaro ido tace "mijinta? Amma gashi na ganku manyan mutane wayayyu, akaiwa yara Auren wuri haka mussaman ita"

Mother tace "doctor, yanzu ba lokaci ne na tattauna wannan magana ba, ya ake ciki?"

"Eh to, ta samu prolonged labor, aiki za'ayi a cire babyn, kuje a biya kuɗin nan da ƙarfe goma insha Allah surgical team ɗin za su iso, ayi mata aiki"

Da ƙyar aka ɓanɓaro Sadik aka fito da shi daga ɗakin, sedai yana fitowa yaji ance aiki za'ai ya kuma gigicewa, ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro.

Usman yace "wai kai wannan wane irin shirme kake, kai da zaka bata ƙwarin gwiwa"

Abba yace "de na yi masa faɗa, ka kwantar da hankalinka auta na, insha Allah Lafiya ƙalau za'ai mata aikin a fito da ita"

Se da Sadik ya bawa Mother haushi, yadda yake kuka Kamar wani yaro, rabon da ta ga yai kuka har ta manta, amma shine yake kuka haka, Hakan ya tabattar mata da cewa yana son Nana kenan.

Jidda kanta da ba ita ke naƙudar ba, ta shiga tashin hankali nesa ba kusa ba.

Ana ta shirin shigar da Nana tiyata, tana ta ambaton Allah, dan sam ta dena jin nishin ma gaba ɗaya, ƙarfinta ya gama ƙarewa, cikin ikon Allah tai wani yunƙuri sega sankacecen jariri ƙato ya fito gaba ɗaya tare da mabiyiya.

Nurse É—in tace "Alhamdilillah ala kulli halin, sannu kinji"

Nana ta lumshe ido kawai, saboda wani sanyi da ya dinga ratsata, ta ƙudurce a ranta ita da haihuwa har abada, Auren ma ta haƙura dan wannan Azabar da ta sha yau, ba ta san ya zata kamanta ta ba, tun da ta ɗau cikin nan take wahala har zuwa haihuwa, Nurse ɗin ta yanke cibiya, ta ɗagowa Nana jaririn tace "kalli me kika haifa?"

Nana tace "ke dan Allah ƙyaleni, haba wannan wahala haka, Allah ka jiƙan Mamana, Allah duk wata uwa ka sata a Aljanna, wanda ba su haifa ba Allah ka basu, ka shirya al'ummar Musulmi"
Ta ƙarasa Addu'ar tana hawayen wahala.

Sosai ta bawa Nurse É—in dariya, aka gama gyara jaririn aka zo É—inki, Nana tace Allah kar ta baza'a kuma gana mata wata Azabar ba.

Sadik kuwa tuni aka sanar musu ta haihu, Sadik ya dinga murna, dan dama Addu'a yake tayi kar ai mata aikin, ba ya son a yanka mata jiki.

Nurse É—in ta kalli Nana tace "kinga in baki tsaya anyi ba, nan gaba da kansa ze sako ki gaba ya zo a É—in ke ki, ki nutsu ayi"

Nana tace "taɓ waya gaya miki zan koma, ai bani ba Aure na gama dama ban isa Auren ba"

Tai dariya tace "Yarinya man kaza, ƙil nan da wata taran zaki dawo mana haihuwa ta biyu"

"Wallahi Allah ya kiyaye, ba dai ni ba"

Da ƙyar ta tsaya akai ɗinkin, ta gyara jikinta, akace ta bawa yaron Nono ama tace me za ta bashi, ba su kai girman yadda ake shayarwa ba, sedai in magani za'a bata su ƙara girma" haka Nana tai ta shirme suna mata dariya.

Kan ace su shigo tuni Oga Sadik ya zura kai ɗakin, ya ƙarasa gaban gadonta da Sauri ya rungumota yana "Sannu Besty na, sannu My Asma"

Tura baki tai taƙi kallonsa, "Sannu kin sha wahala na tausaya miki Sosai"

Tace "Ashe dai ba ka son in mutu, harda kuka" tai maganar tana masa dariya.

Yace "Kuka nake karki mutu, alhalin ki na wa miji rashin Kunya, wallahi ban san haka haihuwa take ba Nana"
Chapter 82 · 0% Book details