Sashe 37
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba da Faruk suka kama hanyar komawa gida.
Suna tafiya a hanya, Faruk ya lura da yadda Abba yai shiru kamar yana nazarin wani abu.
"Abba meke faruwa ne" Faruk yai maganar cikin ladabi.
Abba yace "Bari kawai Faruk, ban san me Hakimi yake shiryawa ba, yace se an nemawa Nana Makaranta a London, abun tambayar a nan a ina zata zauna? Waze kula da ita? Kaga Sadik yana hostel ni kuma ba zanso ta zauna a cikin turawa ba, saboda addinin ta da tarbiyyar ta, da se ince ko gidan Steve zata zauna, ban san yadda a kai Hakimi ya yanke wannan hukuncin ba, duk da tarin tsantsenin sa akan tarbiyya, abun mamaki naga ita kanta Inna ma ba ta san zacen ba"
Faruk yace "aikuwa duk wani hukunci da Hakimi ze É—auka, baze É—auka haka nan ba seda dalili"
"Hakane, na so sanin dalilin amma naga baya son in fiye tambayar dalilin, shiyasa ban tambaye shi ba"
"Amma Abba meyasa baka tambaye shi mu tafi da Sadik ba"
Abba yai murmushi yace "kana son in ja wa kaina ɓacin rai ne? Bari dai in yi abunda yace in gani, samun Admission ɗin nan kusa abune me wuya amma dole zan bincika"
Suka cigaba da tafiya kowa yana saƙe saƙe a zuciyar sa.
Sadik zaman dirshan yayi, zuciyarsa ta bushe gaba É—aya, ga kansa ya kulle ya rasa abunda yake masa daÉ—i gaba É—aya.
Farhan na tafe tana jefa ƙafa, kai kace bata da jini a jiki, tunani kawai take a ranta daban daban, haka kurum zuciyarta ke raya mata, anya Sadik ba Yasmeen ɗin ajinsu ya koma so ba, shiyasa yai watsi da ita ba, in ba haka ba meya kai Yaseen gidansu Sadik harta san yana ƙauye?.
Dummm zuciyarta tayi, taji jiri na nema ya kwasheta ta faɗi ƙasa, da Sauri ta kauda wannan tunanin daga ranta.
" 'yan Makarantar bokoko" da sauri ta waiga jin anyi magana a gefen ta.
Haladu ne, abokin Sunusi, ba ta kulashi ba ta cigaba da ƙoƙarin tafiya, yace mata "Ina wuni"
"Lafiya ƙalau"
"Amm Farhan" ta waigo ta kalleshi.
Ji yai kamar ya gayamata abunda Sunusi yake akanta, amma se ya kasa yaga be dace ya tona masa Asiri ba suna tare.
Dan haka yace "An kusa kawo kuÉ—i ko?"
Banza tai masa ta cigaba da tafiya, Haladu ya jinjina kai ya ƙara tabattar da Farhan ba ta ƙaunar Sunusi, dama ba su dace ba sam.
Lilly ce zaune a Office É—in Nazir, yana aiki suna hira ta zubo masa ido.
Yace "ya dai wannan kallon fa?"
"Yaushe zaka zo gidan mu?"
"Lilly haryanzu baki cemin komai game da batun za'a bani ke ko ba za'a ban ba, ya za ai na fara zuwa?"
"Maganar gaskiya nayi attempting faÉ—a a gida amma na kasa, yanzu shawara É—aya ce kawai ka fara zuwa gidanmu"
"Lilly se in zo gurinki ba iznin iyayenki?
"Nifa haÉ—uwar nan da muke a school am not comfortable kawai ka zo gidan"
"Amma idan aka ganni a gidanku hakan ba ze janyo mana matsala ba?"
"Ba wata matsala, ai ina ga next week in Allah Ya kaimu zasu Sakwatto, se kazo Please"
"Shikenan, Allah ya kaimu kin san bana son ɓacin ranki"
Murmushi tai masa ta miƙe ta bar Office ɗin.
Ko da Abba suka koma gida ya sha tuhuma a gurin Mother, dan yana shiga gidan ta miƙe tana faɗin "Ina Autan yake?"
Abba yace "kamar yaya?"
"Ba É—akko shi kaje yi ba?"
"Ni nace miki É—akko shi naje yi? Kiran Hakimi naje"
"Amma kasan a can zaka barshi, maimakon mu tafi tare in ganshi"
"Ban niyya ba" ya bata amsa ya wuce ya barta a gurin.
Mother ta fara ƙulewa matuƙar gaske, akan abunda ake mata akan Sadik.
Tunda yaga sunyi haka, be yi gangancin gaya mata batun Nana ba da ita ma Za'a nemawa Makaranta a London ba, ya ƙyaleta.
Cikin fargaba da É—ari É—ari Nazir ya shirya zuwa gidansu Lilly.
Tun bayan sallar azahar tai wanka ta shirya tana jiran zuwansa, tai kwalliya ta sa masu aiki sun shirya masa Abinci.
Daga nesa kaɗan da Gidan ya tsaya, ganin masu kaki a ƙofar Gidan.
Ya kirata a waya, ya gaya mata ya zo.
Mintuna kaÉ—an ta kuma kiransa a waya tace yaje Zasu buÉ—e masa ya shiga.
Yana karanta fatiha da salati haka ya ƙarasa gaban gate ɗin, ba su ce masa komai suka bashi hanya ya shiga.
Ƙarewa gidan kallo yake, gida kamar ba za a mutu ba, yanzu wannan gida dan dai rayuwar tsirarin mutane a ciki, da ana tuna mutuwa da ba a gina shi ba.
Wayarsa ce ta fara ringing ya É—aga Wayar.
Lilly tace "ka miƙo hanyar da take facing ɗinka zamu haɗu.
Haka ya bi hanyar yana rarraba ido.
"Oyoyo" ya jiyo Muryar ta, ta taho da gudu ta rungume shi.
Shima rungumeta yayi yace "Kinyi kyau sosai Baby"
"Dama dan kai nayi, tunda ka yaba masha Allah"
Yai murmushi tai masa jagora zuwa cikin wani haÉ—aÉ—É—en falo.
Ta gabatar masa da kayan ciye ciye, ta zauna a kusa da shi, Kamar zata shige jikinsa, ga wani irin fitinanne ƙamshi da dukkanin su suke yi.
"Baby a tsorace fa nake"
"Meye abun tsoro kuma? Ba kowa a gidan fa, daga mu se maids da guard É—in gidan nan"
Ta dinga jansa da hira, yana cin Abinci Kamar wasu miji da mata.
Sosai suke ƙoƙarin sake kauce hanya, da ƙyar Nazir ya aro jarumta ya ture Lilly, yana sauke numfashi.
Yayin da tai shiru tana kallonsa.
"Lilly alƙawari mu kai ba zamu sake ba, Aure zamuyi kar sheɗan yai tasiri akan mu, kuma kinga matsalar da aka samu wancan karon, bari in tafi"
Ba ta ce masa komai ba, yabi hanyar da ya shigo ya fice.
Nana ba ta san su Abba sunzo ba, kasancewar tana makaranta, sedai tunda ta dawo ba taga Sadik ba ko a tsakar gida.
Ta kalli Inna tace "wai Inna ina wannan suƙundumin?"
Inna tace "me kenan?"
Nana ta nuna mata ƙofar ɗakin Sadik.
Inna tace "wallahi idan ya fito ya dake ki, ki kaimin kuka sena ƙara miki" ba shiri ta tsuke bakinta.
Seda daddare Inna take gayamata su Faruk sunzo tana Makaranta, amma ba ta sanar mata da batun tafiyar ta ƙasar waje ba.
Tace "Amma Inna meyasa basu tafi da shi ba?"
"Nima ban sani ba seki tambayi kakanki"
"Ni duk da yana bani haushi, amma wataran tausayi yake bani wallahi, ya gaji da zaman nan, muma fa lokacin da muka zauna a gidansu gajiya nai da zama"
Banza Inna tai mata ta cigaba da sabgarta.
Nazir da ƙyar ya kai kansa gida, saboda halin da ya shiga, ita kanta Lillyn ta daɗe a gurin da ya barta a kwance, sannan ta tashi ta koma ɗakinta.
Babban abunda ya bata mamaki be wuce yadda su Daddy suka dawo a ranar da daddare, bayan sunce zasu kwana uku sannan su dawo.
Tai pretending kamar tayi bacci, taƙi fitowa, balle tai musu sannu da zuwa.
Ta rufe ƙofarta da key, ta shige cikin bargo tana waya da Nazir, tare da nuna masa yadda tai kewarsa ba tare da kunya ko jin nauyin komai ba, shima haka ya saki baki su kai ta waya.
Se Washegari da safe, sannan Lilly ta gaida su Daddy tare da mamakin dawowarsu a jiya, suna tsaka da karyawa Daddy yace "Lilly waye ya zo min gida jiya da bana nan?" Gabanta ya yanke ya faɗi, ta kalleshi tace "Ammm.."
"Kar ki min ƙarya, bayan tafiyar mu jiya wani yazo gidan nan, kuma ya shigo bisa umarnin ki, waye shi?"
"Amm...mmm....Dadd.....
"Karki kuskura ki min ƙarya! Ba a banza na saka masu tsaron gida na ba, uban waye ya shigomin gida jiya?!" Ya faɗa cikin kakkausar muryar sa.
"Daddy saurayina ne" ta faÉ—a kamar za tai fitsari.
"Whta! Saurayi Lilly?" Mummy ta faÉ—a tana kallonta.
"Au ke yanzu nan har kin san kiyi saurayi ki kawo min shi cikin gida na? Lilly are you out of your sense? You are only fifteen years har kin san ha'inci"
Lilly ta shiga girgiza kai tana rarraba ido, dan bata san hukuncin da ze É—auka a kanta ba.
"Waye shi kuma a ina yake!" Yai mata tambayar cikin tsawa.
"Daddy wani corper ne? Cewa yai yana sona ze Aureni"
Yace "good, kema kuma kina son sa?" Yai tambayar yana tsatsare ta da ido.
Tai saurin É—aga masa kai alamar eh.
"A ina yake?"
Tace "Nima ban san a in da yake ba kawai haÉ—uwa mu kai"
Mummy tace "ke Aure kike so kenan?"
Ba Kunya Lilly ta É—aga kai alamar eh.
Daddy yai murmushin takaici, ya kalli Lillyn da yake ganin ba ta fi ya kamata yai mata wanka ba, amma ita ke cewa wai Aure take so, me ta sani game da Auren da harya bata sha'awa take cewa za tayi.
Ya sassauta zuciyarsa yace "shikenan tunda haka kike so, in dai dagaske yakw, kice ina son ganinsa"
Wani irin farinciki ne ya ratsa Lilly ta gyaÉ—a kai.
Mummy za tai magana amma ya girgiza mata kai, ya kalli Lilly yace ta koma É—akinta.
Bayan ta tafi Mummy tace, "kana nufin aurar da Lilly zakayi?"
Yace "sekace bani da hankali, ai daga ji hure mata kunne yake, Allah ne kaÉ—ai yasan tun lokacin da suke tare, sonake yazo in ganshi, in wanda zan yiwa warning n Kawai shikenan, in ma casa shi Yakamata in sa ayi zanyi wanda ya dace".
Yau Friday, Nana na shirin tafiya Makaranta, Inna ta bata sallahun in an tashi daga Makaranta, taje ta karɓo mata saƙo a can wata unguwa, Nana ta amsa da to.
Dan da farko ko makarantar ba tai niyyar zuwa ba, saboda yau jikin Hakimi ya motsa, jininsa ya hau ga zazzaɓi da tari yana ta fama da shi. Dan seda aka kira likita ya duba shi, ana tunanin ko Asibiti za'a ka shi.
Amma inna tace Nana ba zata zauna ba ta tafi makaranta, dan in ta zauna koke koke za tai ta musu.
Har aka tashi daga Makaranta, jikin Nana a Sanyaye yake, ji take kamar kan ta koma gida Hakimi ze mutu.