← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 115

Sashe 88

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kayi haukane Amin? Ina tambayar ka kana nema ka raina min hankali?"

"Kai zan tambaya ko kayi hauka ne? Ni ka barwa ajiyarta ne? Ka tafi ka manta da batun Yarinyar mutane tsawon lokaci, kaje kai Aurenka kuma ka zo nan kana min hauka, kaje gidansu mana ka tambaya"

A fusace Sadik ya fizgo Amin, ya haɗa shi da jikin mota ya zuba masa ido jikinsa na rawa yace "Al'ameen kai na barwa Amanar Farhan kan in tafi, ko ka manta Sadik baya mantuwa? Amina meye haɗin Farhan da Mubarak, Ɗan Ala ya gayamin ranar ƙarshe da ta zo makaranta tare ya ganku kai da ita da shi"

Sadik ya haɗa hannayensa kamar me neman gafara 🙏 cikin rauni yace "Amin, kar ka gayamin kun ɓata min Farhan, ka buɗe baki kaimin bayani, ka tsaya kana kallona" ya ƙarasa maganar cikin tsawa idonsa yai wani irin ja.

Amin yace "Am sorry Sadik"

"Sorry for what? Kai min bayani"

"Sadik, ba laifina bane, nayi iya yina gurin bata kariya, but i fails you, I don't know how to explain amma koma mene da sa hannun Babba da Taslim da kuma Nas"

Sadik ya danƙi sumar kansa yana jin yadda kalaman Amin ke sukar zuciyarsa ɗaya bayan ɗaya.

"Just cut the story Amin, nagode Sosai da sosai, ka gayawa Mubarak Babba da Nas, idona idon É—aya daga cikin su sena kashesu, mussaman Mubarak"

Amin yace "Sadik kabi komai a hankali, kar kai kisan kai, kuma koma menene laifinka ne daka tsallake ka tafi ka barta kaje kai Auren ka, ka sa......

"Shut up kan in fara ta kanka" yai maganar yana shaƙe Amina. A guje megadin ya zo ya raba su yana mamakin meya haɗasu haka? Yasan abokaine sosai da sosai amma ya haka ta faru a tsakanin su bayan shafe dogon lokaci basu haɗu ba.

Sadik be jira komai ba ya hau mota, da fari farautar Mubarak ya so yayi, amma se yaga ɓata lokaci ne, sanin in da Farhan take shi yafi mahimmanci, dan haka ya nufi gida, jikinsa na wata irin tsuma kamar wanda ake bugawa gangi.

Yana zuwa gida beyi wata wata ba, ya É—au wayarsa ya kunna, ya saka lambar Farhan a ciki, ya shiga kiran layin.

Sedai ko da yaji wayar ta shiga, se ƙirjinsa ya tsananta bugawa, har ya fara jin Kamar zuciyarsa na barazanar tsaga ƙirjinsa, amma haka ya dake cike da ƙwarin gwiwa yana sauraron amon shigar wayar.

Farhan kuwa tana cikin maye, dan haka ko yatsanta kasa ɗagawa tayi, tana kwance tana jin wayar na ringing ta miƙa hannunta ta ɗau wayar abu ya gagara, idanunta suka cigaba da lumshewa ta cigaba da baccinta.

Sadik ya kirata ya kai sau talatin, amma ba wanda ta ɗaga, be san lokacin da zuciya ta ɗebe shi, yai jifa da wayar ba, Ta faɗi ta tarwatse a gurin, ya koma gefe yana huci, ya kai idonsa kan hoton Farhan a jikin laptop ɗin sa, yace "Why Princess, why don't you pick my calls? Kina son in mutu ne?" Ya ƙarasa maganar yana dafe goshinsa.

A ranar Sadik ya fita ya siyo wata wayar, Mother se masifa take akan ta gaji da wannan jigilar da yake, na tare da tasan in da yake zuwa ba, ai be kula Mother ba ya shige ɗakinsa ya rufe ƙofa.

Haka ya wanzu har cikin dare yana kiran layin Farhan, amma ba bu amsa.

Wata shawara ya yanke a ransa, kasamcewar ya san kan computer sosai da sosai, nan ya shiga ƙoƙarin bin diddigin layin Farhan, amma Network ya hanashi samun abinda yake so.

Yadda yaga rana haka yaga dare, ko kaÉ—an be rintsa ba, sam baya jin baccin ma.

Wayewar garin Allah, haka ya koma ka computer yana cigaba da ƙoƙarin locating in da Farhan take ta hanyar lambar wayarta.

Se yamma sannan Sadik ya iya gano in da Farhan take, Cikin azama ya kuma fafarar mota, ya bar gidan sannu a hankali ya shiga rukunin gidaje na Nassarawa GRA da ke garin Kano, yana yi yana duba wayarsa, a haka ya ƙaraso wani katafaren Hotel.

Saboda sauri a waje yai parking É—in motar, ya shiga cikin Hotel É—in, tuni zuciyar Sadik ta karaya ganin Farhan na cikin Hotel.

Sannu a hankali se gashi a ƙofar ɗaki me lamba ta goma sha ɗaya, wanda ya kasance VIP, hamshaƙan manyan mutane ne ke kama irin wannan ɗakin.

Sadik ya sa hannunsa a jikin handle ɗin ƙofar ɗakin, zuciyrsa na wani irin harbawa, cike da Zullumi da fargaba ya buɗe ƙofar yaji a buɗe take, ya shiga ɗakin, ba ya fargabar koma ba ɗakin ya shigo ba, babban burinsa kawai ya sa Farhan a idonsa.

Ɗakin ba kowa, ya ƙarewa ɗakin kallo, ya kuma kiran lambar Farhan, ai kuwa yaji ringing ɗin wayar a ɗakin, yana ɗaga kai ya kalli in da sautin ke tashi, idonsa ya sauka akan wayar da ke kan side bed, ga manyan kwalaben magani da wasu tablets a akai.

Jikinsa ya ɗau rawa ya ƙarasa gaban side bed ɗin, Sadik ya shiga jujjuya magunan zuciyarsa na wani irin zafi, irin ƙwayoyin da Mubarak ke ta'amalli da su ne, na saka maye.

Ƙofar banɗaki yaji an buɗe, ya ɗaga idonsa ya zubawa ƙofar.

Sanye take da wata matatsiyar riga doguwa iya gwiwar ta, sosai rigar ta fitar da shape É—in jikinta, kanta ba É—an kwali, tana É—an dafa kanta alamar ko yana mata ciwo, ko haryanzu tana maye.

Ƙamshin turaren da ya daki hancinta ne yasa kanta ya sara, ta san babu wanda take irin wannan ƙamshin se Sadik, tun da ya bar duniyarta ba ta sake jin sa ba, ta ɗago manya manyan idanunta da suka ɗan yi ja.

Wani irin ƙuuuu cikinta ya bayar, ta shiga ƙifta idanuwa, dan ta tabattar da ƙwayar da ta sha ta saketa, ko kuma gizo ne abunda take gani.

Sadik ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba yayi, ta tabbata Farhan ɗin sa ta sauka daga turbar da ya santa  a kai.

Jiki a sanyaye Ya fara tunkararata, wata irin ƙaunarta na fizagarsa.

"Stop their!" Ta daka masa tsawa.

Ƙoƙarin tunkararta yake amma ta kuma cewa "kar ka zo in da nake, i said you should Stop their".

"Farhan, nine fa Sadik É—inki ne"

"Shut up, bad lier ko suna in dai da kai ake ba na ƙaunar jinsa, azzalumi mayaudari leave my room now, get out from sight".

Kamar Sadik ze kuka yace "Farhan dan Allah ki saurareni"

"Wallahi ka zo in da nake se na caka maka abu, bana sonka bana son ganinka na tsaneka, na tsani me sonka ka fita ka bani guri" ta ƙarasa maganar kanta na juyawa, da son tabattar da mafarki take ba, dan yana yawan yi mata gizo a cikin mayenta.

Ya ƙaraso in da take, amma ta ja da baya ta ɗago fuskarta da tai jawur, kamar mayunwaciyar kura ta cigaba da Magana "nace maka ka fita ka barmin ɗaki na, nan gurin sana'ata ne, bana buƙatar mutum irinka a nan"

Sadik yace "Farhan ko sau É—aya ki saurareni"

"Ba zan taɓa saurarar ƙarya da yaudar ba, daga bakin maƙaryaci, kalli halin da nake ciki duk sanadiyyar ka, ka fita nace maka kan in maka illa da kwalba yanzun nan"

Daskarewa Sadik yai yana kallon Farhan É—in sa, me tsananin kunya da bin unarninsa yau ita ke masa tsawa haka.

Ai be Aune ba ta dinga hankaɗashi, gudun kar taiwa kanta illa yasa ya ƙyaleta ta hankaɗashi har waje, ta rufe ƙofarta ta zauna a bayan ƙofar tana rera kuka.
Sadik ya jingina da jikin ƙofar, yana sauraron sautin kukanta, dake ƙona zuciyar sa.

Wani baƙin ciki ne ya tasowa Farhan, jin yadda ƙasan zuciyarta ya ƙawata mata girma da kyan da Sadik ya ƙara yi, ta tabattar wa da kanta zahiri ne abunda ya faru ba Sharrin ƙwaya ba.

Sautin fasa kwalba Sadik yaji, daga nan yaji ta ƙwala ƙara, a gigice ya jinjina ƙofar amma yaji ta rufeta gam.
AYI HAƘURI A LALLAƁA BA EDITING, WAYAR TA SAMU MATSALA.

A gigice Sadik ya shiga jijjiga ƙofar yana kiran Sunan Farhan, Amma ta ƙi buɗe ƙofar, ya nufi reception cikin hanzari ya sanar musu da abunda ke faruwa, aka zo da spare key, aka buɗe ƙofar, tana zaune tana kuka, ta yanka hannunta yana ta zubar da jini.

Sadik ya shiga cikin ɗakin da Sauri ya tunkareta, amma ta miƙe ta ɗau sauran kwalbar, ta saita shi tace "wallahi ka zo in da nake se na caka maka ita"

So makaho ya cigab da nufarta, yana faÉ—in "ki tsaya Farhan, ba ki ga yadda hannunki ke zubda jini bane? Ki tsaya ki ji"

Ganin ba shi da niyyar dena kusanto in da take, ya sa ta saita cikin ta da tsinin kwalbar, tace "Wallahi ka zo in da nake se na sokawa kaina kowa ya huta".

Receptionist ɗin da suka zo tare da Sadik tace "kaga malam, dan Allah tunda kaine ba ta son gani ka ƙyaleta, kar ta kashe kanta ku janyo mana bala'i"

Jiki a sanyaye Sadik ya juyo ya baro É—akin, ya fito waje ya zauna, ya dafe kansa yana jin yadda kan ke sara masa, wai yau shi Farhan ke gudu haka, take jifa da miyagun maganganu.

Farhan ba ta damu da yadda jini ke zuba a hannunta ba, sedai yadda take jin haushin zuciyarta da ƙasan zuciyar ke ƙoƙarin shiga cikin farincikin ganin masoyinta.

Ta yanke shawarar barin Hotel É—in ta canza wani, dan idan ta koma gida ma ze iya binta can, dan haka ta zura doguwar rigar ta, ta zauna a gefen gado ta É—au wayarta missed calls rututu ta gani, abun ya bata mamaki wannan lambar waye haka?.

Sadik na nan zaune ya ga wani hamshaƙin mutum ya taho, tinkis tinkis ya nufi ƙofar ɗakin da Farhan take, ai a zuciye Sadik ya miƙe, ya rufa masa baya, cikin azama ya sha gabansa ya tare ƙofar ɗakin.

Mutumin ya kalli Sadik yace "kai Samari lafiya kuwa?"

Sadik yace "kai zan tambaya ko lafiya"

"A'a kaga matsa ka bani hanya"

"Wallahi in dai ina motsi a gurin nan ba ka isa ka shiga É—akin nan ba"

Mutumin yai saroro yana kallon Sadik yace "kai wai meye matsalar ka ne?"
Chapter 88 · 0% Book details