← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 115

Sashe 106

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Unguwar su Farhan ta ɗauka, an kai mata kuɗin Aure, dubu ɗari amma an rasa waye mijin, an bi diddigi an tarar ba Abbas bane, lallai tayi goshi saɓanin lokacin da Sunusi ya kai mata dubu Ashirin da biyar, sam Abbas ya ɗauke ƙafarsa, dan baya son ya cigaba da zuwa, su samu Matsala da Sadik, dan haka daga gefe ya cigaba da yi mata fatan alkhairi, tare da rarrashinta ta waya, wanda shima daurewa kawai yake yi, amma har ga Allah yana ƙaunar Farhan dagaske ba wasa ba.
Sadik kuwa in dai yazo wataran taƙi fitowa, ko ta fito suyi faɗa ya tafi, wanda hakan shima ya sa ya dena zuwa, hakan yasa 'yan unguwar ba su san waye ya kaiwa Farhan kuɗin ba, dan an dena ganin kowa yana zuwa in da take.
Da Sunusi ya samu labari kuwa ji yake kamar yai hauka, dan be taɓa tunanin wani ze fito haka ya iya yunƙurin Auren Farhan ba, yai iya yinsa amma be gano waye ba, dan sam be kawo Sadik ba, saboda a ganinsa yarone waze bashi Auren 'ya?.

Sosai aka gyara gidan da Sadik ze zauna, wanda ba shi da wani nisa sosai daga gidan su Sadik, gidan yayi kyau sosai da sosai, Sadik shikaÉ—ai yake fafutukar shirin Aurensa, se Anty Jidda da ya kan tambaya wasu abubuwan se É—an uwa Faruk, duk da har ga Allah daga Faruk har Anty Jidda Nana suke yi suma, amma Sadik abun a tausaya masa ne shima.

A gidan dr. Ya haɗa lefensa cif, Abba yai Maganar ze saiwa Nana furnitures, Sadik yace Abba ya bari shi ya sai mata, tunda kayan lefenta suna nan ba abunda ta taɓa, base yai mata kayan faɗar kishiya ba se yai mata furnitures, amma Abba yace basa buƙatar kayansa.

Abubuwa har mamaki suke bawa Nana yadda Mother ta sauya, dan ita ta sai mata komai na kayan kitchen, duk abunda uwa za taiwa 'ya, Mother ta saiwa Nana shi, dan dama bata da 'ya mace, bata taɓa Auren 'ya ba, dan haka ta kashewa Nana kuɗi sosai, aka zuba a sashin Nana da ke sabon gidan da zasu zauna.

Gashi musamman Mother ta biya kuɗi aka ɗakko me gyaran jiki, take gyara Nana, wanda ko da aurenta ba wanda yai mata wannan haka nan zallarta aka bawa Sadik (lolz🤣).

Gidansu Farhan na ta shiri, ita kuwa sam ta rasa farinciki take ji ko haushin wannan Auren take, dan sam ba ta farinciki ji take tayi butulci na gaske na ƙin Auren Abbas, musamman idan ta tuna irin ɗawainiyar da shi da mahaifiyarsa suka dinga yi da ita.

"Amm dama nace, dan Allah ina son zuwa ƙauye, ko sati ɗaya muyi".

"Se yanzu da buƙatar kanki ta taso kika tuna dani Husna?" Banza Nana tai masa tana tura baki.

"Gaba É—aya kin mai da ni hoto ba ruwanki dani, anya rayuwa za ta tafi a haka? Dan kawai nace zan aure shikenan kika watsar da ni"

"Dan Allah ni a bar wannan zancen, bana so"

Sadik yace "wane zancen?"

"Zancen Aurenka ni bana so".

"To na dena" ya bata amsa.

"To ka barni?" Tai maganar idonta fal hawaye.

Wata irin kewarta ce ke fuzgarshi, shi kansa ya san yayi dauriya, dan rabonsa da ita har ya manta.

"Uhmm kayi magana mana" tai maganar a shagwaɓe.

Rungumota yai cikin bazata yana kissing É—in ta.

"Wayyo Allah na, Mother" da sauri Sadik ya cikata yace "Besty meye haka kamar wata ƙaramar yarinya?"
Yadda take tura baki tana hararsa ne, ya ga ta koma yarinyarta sosai, ya É—an lumshe idonsa yace "kinyi kyau sosai, nai missing É—inki zo kiji"

Noƙe kafaɗa tai tana share hawaye, yace "Shikenan, dan Allah goge hawayen, idan Mutan gidan nan sukaga kina hawaye se su rufeni da duka yadda suke jin haushin nan nawa, jeki Allah ya kaiku lafiya".

A ciki ta amsa Ameen ɗin, tai waje ita kanta tai missing ɗin Sadik, amma tsabar yarinta, taurin rai da baƙin kishi yasa Nana ba ta jin hakan da take a matsayin wani laifi.

Tun da Hakimi ya rasu Nana ba ta sake zuwa ƙauye ba yau, tai murna sosai da ganin Inna, amma tana kallon turakar Hakimi se kuka, Inna tai ta mata nasiha akan ta de na yi masa kuka Addu'a za tai masa.

A yanayin bugun cikin Nana da Inna tai, ta fuskanci sam Nana bata shiga shirgin Sadik, haryanzu Nana tana fama da tarin ƙuruciya da wauta.

Inna ta zauna ta dinga yi mata nasiha da hatsarin de na shiga sabgar Sadik da tai har take bata misali da "da uwar mijinki ai bata ƙaunarki, amma sannu a hankali da ki kai haƙuri ba gashi komai ya wuce ba, har siyayya tai miki kamar 'ya da uwa ba? To komai na rayuwa haƙuri ake me wucewa ne. Kuma tun da sabon Aure yai zakiga abunda ba kya so, amma ni daure ki ɗauke kai ki kwantar da hankalinki, komai ze wuce bance ki saki jiki a wulaƙanta ki ba, ki kama mutuncinki amma karki wulaƙanta mijinki, yana ƙaunarki sosai".
Nana dai tai shiru tana sauraren Inna, amma tana jinjina lamarin dan babu sauƙi sam.

Yau da Sadik yaje gidansu Farhan, Abba na nan dan haka dolenta ta fito, suna tsaye yana ta Magana tai banza da shi, sega wata danƙareriyar mota, Wannan mutumin da suka taɓa Faɗa da Sadik akan Farhan ne ya fito, a fusace ya tunkaro su yana zuwa ya kalli Farhan yace "mayaudariya munafuka, nai nai ki Aureni kika ƙi, amma naji labarin wai zaki Aure, bayan kin gama sawa na kashe miki kuɗi, to ki tattaro duk abunda kika san na baki, na kashe miki ki dawon da abina".

Sadik yai caraf yace "An cinye ƙarfi ya ƙwata, kaje ka kai duk in da zaka kai, lokacin da kake bata kunyi a rubuce cewar zata Aureka dan haka zaka kashe mata kuɗi? Ko kuma ita ta roƙe ka? Dan haka ka saurara, kaje ka kai in da kaga za'a ƙwatar maka"

A fusace yace "kai ka kiyayeni,kar ka min rashin kunya"

"Anyi maka rashin Kunyar, kaje ka kai in da duk zaka kai"
Haka Mutumin nan ya ƙaraci borin kunyarsa ya tafi, Sadik ya sanarwa da Farhan cewar saura kwana uku su kawo lefe.

Ko da aka kai kayan lefen nan duk da gidansu Huzaifa aka kai kayan, unguwar su Farhan ta É—auka, aka dinga zuwa kallo, Akwatuna Bakwai ne na gaske masu kyan gaske, kayanta 'yan cif se tsada, har da gwal biyu a ciki, kayanta manyan kaya sosai da sosai, da babban buhun shinkafa.

Akace se yanzu a kaiwa Farhan lefe, ba kayan Sunusi ba Akwati biyu har da hodar nan irinsu Aisha tsamiya a ciki.

Nana bata dawo ba se satin biki, shima Mother ce tai waya tace Lallai ta dawo.

Mutane nata surutun Faruk ko Auren fari be ba, amma an bar Sadik se Aure aure yake.

Nana kawai yaƙe take, amma ƙasan zuciyarta daurewa kawai take, ana gobe za'a fara biki Sadik ya tarar da Nana a ɗakin Mother, fatar jikinta har wani sheƙi take, gashin kanta an gyara shi an masa ƙananan kitso, ta sha lalle ja da baƙi, tai shar Kamar ba ita ba se ƙamshi take.

"Madam ina Mother?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace "tana gurin Abba"

"Sahal fa?"

"Yana gurin babansa"

Sadik yace "wane baban nasa?"

"To shi da yake da iyaye da yawa, yana gurin Uncle Faruk"

Sadik ya ƙara so kusa da ita ya zauna yace "You look young and beautiful, kamar in sace ki in gudu, dan Allah Nana ki dawo part ɗinmu mu kwana tare"

"Kana ganin gidan cike da mutane, Mother faÉ—a za tai min"

"Allah ba abunda za tace miki, Please Besty"

Kasa jurewa tai ta fara kuka, kuka sosai da hawaye saboda abun ya motsa.

"Besty kuka kuma? Na miki laifi amma kamar yadda na gaya miki Ina sonki Husna, ba zan taɓa wulaƙanta ki dan na Auri Farhan ba, dan Allah ki dena kukan nan se in zaci wani abun daban" ya rungumeta yana share mata hawaye tare da kwantar mata da hankali.

"Kina buƙatar wani abu ne?"
Nana ta girgiza masa kai.

"Dan Allah ki min alfarma ki dena wannan kukan"

"In ban kukan ba wani abu ne yake tsayamin a wuyana yaƙi tafiya"

Sadik yace "Yasalam, na san ba daÉ—i amma ki dena dan Allah".

"To zan dena insha Allah"

Ya ɗanyi ƙasa da murya yace "to yaya, zaki rakani BQ ɗin?"

"Mother za tai min faÉ—a Wallahi"

"To shikenan, kayan da Abba ya sai miki sunyi kyau sosai, bari in nuna miki"

"A'a ka bari in muka tare na gani"

"To shikenan, dan Allah Besty ki tayani basu haƙuri nasan suna fushi da ni, naga yanzu kece 'yar gaban goshi"

Nana tace "to ai Inna tace ze wuce, na gayamata ta yiwa Abba Magana ma"

"Akan suna fushi da ni ko?"

Ta jinjina masa kai.

Yace "Allah Sarki Besty na, You will remain my Besty forever inshallah, i will not fail you" yai maganar yana shafa hannunta.

Maganar Mother ya jiyo, hakan yasa Sadik cikin azama ya tashi, Mother ta shigo tana masa kallon tuhuma.

"Dan ubanka me kai mata?"

Sadik yace "Wallahi Mother ban mata komai ba".

"Ƙarya kake yi, me yai miki?"

Nana tace "bakomai"

"To fita ka bar min É—aki"
Bayan fitar Sadik Mother tace "idan kika kuskura kika yadda da shi, kan ku tare a gidanku ni da kene, ba ya zo yana kashe miki murya ba"

Nana tai shiru cike da jin nauyin Mother.
  Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680

Farhan jin abubuwan take tamkar a mafarki, wai ita ke shirin Auren Sadik abun Kamar almara.

Dangin Babar Umma se cewa suke Allah ya musanya mata me arziki, akan kayan tsiyar da Sunusi ya kawo mata.

A wannan karon Umma anyi abun arziki, dan cikin tsananin kunya, ta sa aka samo mata wata da take gyarawa Farhan jiki, a wannan karon ma É—aya gyaran Hajiya ce ta É—auki ragamar gyara Farhan É—in, tai shar da ita kamar ba ita ba.
Chapter 106 · 0% Book details