← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 115

Sashe 114

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna cin abinci Nana na bata labarin zaman London da sukai, da irin wautar da ta dinga yi, musamman lokacin yace ta sha Nonon karya.

Sosai suke dariya, ta dinga bawa Farhan labarin yadda Inna take sata a gaba, akan kula da kanta da yanayin rayuwar da tai tare da kakanninta.

Se taga jikin Farhan yai sanyi, Nana tace "meyafaru, ko na faÉ—i abunda ba kiji daÉ—insa ba?"

Farhan tace "A'a, kawai dai kin tunan wani abu ne, ke gashi ba ki rayu da iyaye ba, amma kin samu kyakkyawar kulawa, Besty har ga Allah ni na ajiye batun wani kishi, ban ɗauke ki kishiya ba, se 'yar uwa shiyasa zan gaya miki wani abu da ya shafi rayuwata, kinga ni ga uwata ga ubana, amma mahaifiya ta sam bata damu dani ba, har gara ma yanzu akan da, kinga Inna itama ba fulatana ce, amma kimga halayarta ta sha bamban da ta Ummana, abubuwa da dama ban san su ba, har sonake in ga mutum da mamansa kamar ƙawaye, kinga Inna ta tsufa, Allah ya maye miki da Mother, rashin kulawar uwa ba daɗi" Nan ta ɗan ɓincinawa Nana wani abu na daga Rayuwar ta.
Nana arhar hawaye, kawai ta kama kuka, ita ma Farhan ba ta da zaɓin da ya wuce tai kukan, Sahal ya tsaya yana binsu da ido.

Sadik ne yai sallama ya dawo daga makaranta, amma ya tarar da su a zaune suna kuka, se yai turus, ya ƙaraso yana tambayar su ko Lafiya.

Nana tace "bakomai hira muke"

"To kuma hira se ku hau kuka, wace irin hira ce haka?"

Farhan tace "Sirrinmu ne ai, ba se kaji ba"

Sadik yace "iyeee, to Allah yasa ba laifi nai muku ba, kalli kun sa É—anku a tsakiya kuna kuka, wannan abun kunya da yawa yake. Yai maganar yana É—aukar Sahal da jin daÉ—in yadda ya gansu.

Babban abunda ya ƙara burgeshi shine yadda Nana ke kiran Farhan Princess ita kuma take kiranta Besty, hakan yai masa daɗi ƙwarai da gaske.

Lilly kuwa a ss2, tai graduating, Kamar yadda Mummynta ta bata shawara, haka ta amince dan ba ta son sake aikata abunda za tai dana sani kamar yadda take yi a yanzu, dan haka ta bi shawarar Mummynta don Auren wancan soja shine rufin Asirinta.
Gashi ya manyanta, amma sonta yake kamar ze haɗiyeta dan so da ƙauna, dan haka ta amince ya kawo kuɗi aka tsayar da Ranar Aurensu, yayin da Sir Nazir yake can gidan yari.

Khairat ma Faruk ya kai kuÉ—in Aure, an saka rana tana yin Candy za'ai biki, tare da walimar graduation É—in ta.
Ya haÉ—a lefensa na gani na faÉ—a, Sadik yace su shirya suje su gani.
Farhan se fartabar zuwa gidan su Sadik take, saboda Mother har kashedi tai mata, akan kar ta ƙara zuwar mata gida.

Se dai yau ma bata canza zani ba, dan tunda sukaje Mother tai mata wani irin mugun kallo, musamman da ta ga alamar ciki a jikin Farhan, ta dinga zazzaga mata masifa da baƙaƙen maganganu, Nana da Faruk na niyyar su dakatar da ita, amma suma ta ƙare musu, ba shiri Farhan ta miƙe ta nufi hanyar fita, Sahal ya bita yana kuka, ta sa hannu ta ɗauke shi tana share hawaye ta tafi.
Nana ma kuwa ta saka kuka, har da sheshsheƙa, Mother ta buɗe baki tana kallon ikon Allah, da mamakin sakarci irin na Nana.
Nana tace "dan Allah Mother ki dena zaginta, Wallahi tausayi take bani, bana jin daÉ—in hakan, tana da kirki sosai".
"Rufen baki, ko in zo in mangareki shashasha, wannan É—aukar É—an naki da take ne yasa kike wannan rawar kan"
Sadik da ke zaune Mother tai faÉ—anta ta gama, har Farhan ta tashi ta tafi bai motsa ba, shi kansa Faruk be ji daÉ—in abunda Mother tai.

"Kai kuma dama baka kake so, ga mata nan ka tara, yau Wannan da ciki gobe waccan da ciki shine babban burinka, kaje kai tayi".

Abba da ya shigo Yanzu ya shiga tambayar Lafiya kuwa, ya gansu jingum jingum ga Nana na ta uban kuka.

Sadik ya tafi gaban Mother ya durƙusa yace "Mother, idan rabuwata da Farhan, ze sa ki samu kwanciyar hankali, insha Allah daga nan idan na bar nan, zan sawwaƙe mata, dan ba ta cancanci a cigaba da maita haka ba saboda ni, amma kan nan bari in faɗa muku dalilin da ya sa na dage, na Auri Farhan duk da ba kwa so, ban sani ba ko zaku fahimce ni, Mother Farhan Yarinya ce ta gari me tarbiyya wadda kowa ze so haɗa zuriya da ita, sedai ni da tarbiyya tai min ƙaranci na kutsa rayuwarta, na liƙe mata se da ta fara sona, Mother zina ce kawai ban aikata a rayuwata ba, na tafka ta'asa iri iri......
Nan ya fayyace labarin soyayyar su da Farhan, ba ɓoye komai ba, har rayuwar da tai bayan rabuwarsu, zuwa Aurensu a yanzu, ya ɗora da cewa "a yanzu haka Mother na fara tara zuriya,kuma nasan duk abunda ana aikata akan ɗan wani se anwa nawa, na auri Farhan saboda ina sonta, kuma saboda ina fatan Aurenta ya zama silar Allah ya yafe min kuskuren da na tafka, idan baki ysdd6ba kuma ku tambayi Sabo direba ya san wasu abubuwan, amma tun da ba kya so, zan rabu da Farhan, in dai hakan ze zama masalaha" ya ƙarasa Maganar hawaye na zuba daga idonsa.
Gaba ɗaya ɗakin yai tsit, saboda abun ya bawa kowa mamaki da tausayi, asje Sadik ne ƙwallon se a hankali, shine silar komai.
Nana ta taso ita ma ta zo gaban Mother ta durƙusa tace "Mother na, ke uwace, kuma ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, be kamata mata 'yan uwanmu su dinga shiga matsala saboda mu ba, bayan muna iƙrarin ciwon 'ya mace na 'ya mace ne ba, dan Allah a karo na biyu, ina nemawa Abban Sahal alfarma, dan Allah kiyi 6ya rayu da Mummyn Sahal, tabbas gaskiyar ki me ɗa wawa, son da takewa ɗa na da kyawawan halayenta ya sa nake sonta nima.
A wannan gaɓar nice ƙaddararsu da na raba wannan Soyayya, dan haka be kamata kowa ya goyan baya ba, ina son Sadik, amma ina kwatanta kaina idan ni na tsinci kaina a matsayin da Farhan take, dan Allah Mother karki bari Auren nan ya mutu, dan girman Allah"
Kuka Nana take sosai tana riƙe ƙafar Mother.

Abba ya nisa yace "Allah sarki Nana, halinki irin na marigayi Hakimi, ya yadda ya rasa na sa farincikin saboda wani ya samu, shiyasa ya samu soyayyar mutane.
A karo na biyu kenan tana nema maka alfarma, lokacin da kake neman Auren nan, haka ta saka gwiwowinta a ƙasa akan mu bari kai Auren nan, a karo na biyu tana nema maka wata alfarmar, tabbas idan ka wulaƙanta Nana, kanka ka wulaƙanta.

Abba "ya za'ai in wulaƙanta ta, wallahi Abba ina son Nana, so na gaske"

Abba yace "kaje kar ka rabu da matarka, Allah ya kyauta ya tsare gaba, ya ƙara haɗa kanku"

Mother kiyi magana, Sadik yai maganar yana kallon Mother.

Mother tace "Ai kuma ba ni da ta cewa, ai ban san haka abubuwan suka gudana ba, Allah ya kyauta"

Abba yace "É—au matarka ku tafi gida"

Sadik ya sa Nana a gaba suka bar falon, suna tafe a mota, ya kasa magana, se riƙe hannunt da yai cikin nasa, yana jin wani irin sonta a ransa, ga wat kima da ta ƙara yi a idonsa.

Sukaje gida suka tarar Farhan, ta hsÉ—a Akwatinta, abun tausayi ta goya Sahal a bayanta, zata tafi.

Da sauri Nana ta karɓe Akwatin, Sadik yace "Ina zaki?"

Cikin kuka tace "gida zani, gara in haƙura da Auren tun da Mother ba ta so"

Nana tace "Haba Princess, in kika tafi bamu da Princess ɗin da zata maye mana gurbinki, dan Allah a madadin Mother ina baki haƙuri, dan Allah karki tafi, Farhan nice ƙaddarar da ta ratsa tsakanin soyayyarku, ban san haka abubuwan suke ba, dan Allah kiyi haƙuri ki zauna"
Rungume Nana Farhan tai tana kuka tace "Besty Mother ba ta sona"

"A'a tana sonki" Nana tai maganar cike da tausayin Farhan, tana ji a jikinta idan har ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, to be kamata ta ga Farhan na zub da hawaye ba, saboda ta sha wahala.

Sadik ya ƙaraso ya rungumesu gaba ɗaya, yana faɗin 'kukan ya isa haka, ke kuma da kika goya Sahal ina zaki da shi?"

Ta share hawaye tace "da shi zan tafi"

Sadik ji yai kamar yai dariya, saboda wauta da yarinta, za tai yaji amma za ta tafi da É—an da ba nata ba.
Yayin da yake sake mamakin Nana, saboda ita a rayuwarta ba ta son ta ga wani yana kuka, sosai kimarta ta ƙaru a idon Sadik.

Mother da kanta taje gidan Sadik, cike da borin kunya, ta nunawa Farhan komai ya wuce.

Sunusi kuwa ciwo yake tuburan, da fari abun kamar aljanu, daga baya kuma likitoci sukace ya samu brain tumor, ya dinga wani irin ciwon kai, da fizge fizge irin na mahakata, ana neman wasu uban miliyoyi ai masa aiki, wanda ba wanda yake da wannan uban kuÉ—i.

Wata irin kulawa Sadik yake bawa iyalan nasa, cikin taka tsantsan ba tare da ya shiga haƙƙin wani ba, da tsohon ciki Farhan ta gama sakandare, idan kai baƙo ne ka zo gidan ba zaka ce kishiyoyi bane, balle ka gane wacece ta haifi Sahal, dan tunda Nana ta yaye shi, Farhan ta karɓe shi.
Watan cikin Farhan tara, ta haifi sankaceciyar jaririya, ta haihu daf da bikin Faruk da Khairat, Nana ta dinga murna kamar ita ta haihu, dan ba ƙaramin son 'ya mace take ba.
S kace za'a haÉ—e bikin Khairat da sunan Farhan, idan Sahal ya ga Farhan ta rungume jaririya tana shayarwa, se yai ta tureta, wai dole se an saketa daga kan cinyarsa.

Nana tace "ban taɓa ganin garujen yaya ba, irin Sahal.
Chapter 114 · 0% Book details