Sashe 27
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka kuwa akayi, koda aka kawo wayar Lilly ta duba, kusan missed calls goma sha na Sir Nazir. Tsaki tai ta ajiye wayar tana ƙunƙuni.
"Dan Allah ni dai in ba zaka iya zuwa ba, ka barni inje da kaina in É—akko Sadik"
"Saboda kece sarauniyar 'ya'ya ko? Saboda rashin ta ido seki je ki cewa sirikan ki su baki É—anki ko, to bari kiji in gayamiki wallahi Kika je garin nan da sunan É—akko Sadik, ko kika ke ba tare da izina na ba wallahi a bakin Airenki!"
Ras! Gaban Mother ya faɗi, dan Abba be taɓa makamancin wannan furicin ba, duk laifin da za tai masa, lallai wannan karon he is very serious on what he is saying.
Kuma da ya gama maganar yai tafiyarsa ya barta a gurin, aikuwa ta zauna sosai tana kuka.
Faruk ne ya shigo falon, ya tarar da ita zaune ta ma faman hawaye.
Yasan tatsuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi, ya taka a hankali yaje kusa da ita ya zauna, ya fara share mata hawaye yace "haba Mother, dan Allah kiyi haƙuri da batun Sadik, ki kwantar da hankalinki ki dena wannan kukan, baze maganin komai ba"
"Haba Faruk, dole in kuka Sadik yarone ƙarami, be taɓa nesa dani na kwanaki masu yawa ba, amma an baro shi a ƙauya, in da be taɓa zuwa ya zauna ba, kuma an hanani magana"
"Hakane ba a kyauta miki ba, amma dan Allah kiyi haƙuri Mother, duk fa kukan nam da kike be canza Komai ba, kiyi haƙuri kukan ba shine magani ba, insha Allah in dai Sadik ne zasu dawo miki da abun ki"
Haka yaita rarrashin Mother, yana cikin rarrashin nata sega Khairat ta zo Gidan, dan ta cigaba da taya Mother zama, dan ta É—ebe mata kewa.
Da daddare bayan magariba tuni 'yan dubiya sun fara zuwa duba Lilly, ta samu Mummy ta tafi rakiya ta É—aga wayarta ta kira Haseena a wayar mamansu.
Maman Haseena na ganin Lilly ce ta bata wayar.
"Hamshaƙiya, ina kika shiga ne yau kika ƙi zuwa school bayan kin san exams ake?"
"Bani da lafiya ne" Lilly ta bata amsa.
"Subhanallah, meya sameki ko Asmar ce ta ta shi?"
"A'a zazzaɓi ne ina Asibiti anyi admitting ɗina, dan Allah ku sanar a school, duk da ma dai Mummy zata turo uncle ya sanar"
"Eyya Allah ya baki lafiya, se munzo dubiya habibin naki kuma ya sani?"
'ke dalla ƙyaleni da wannan mutumin se anjima" Lilly ta katse wayar.
Gaba ɗaya Sadik ya koma salihin ƙarfi da yaji, ba sawa ba fitarwa daga masallaci se ɗaki se zaman fada.
Nana kam tausayi yake bata yanzu sosai da sosai, duk ranar da ta tabattar za a girka abunda ba ze iya ci ba, se ta nemo wani abun da zata bashi a ɓoye yaci, ze karɓa ya cinye amma baze iya godiya ba.
Nana na cikin turakar Hakimi tana masa surutu, yace "je ki kiramin wancan Yayan naki"
Nana ta miƙe tana faɗin "ni ba Yayana bane" tai waje zuwa ɗakin Sadik.
Yana zaune yayi shiru yana zancen zuci Nana tace "kai ka zo ana kiranka"
Ya É—ago ya kalleta ya maida kansa ya sunkuyar.
"Da kai fa nake"
"Ki ka kuma cemin kai sena ɓarar da ke a gurin nan"
"An faɗa, kai kai kai ƙaton kai"
Sadik ya tsani tsiwa, shiyasa Farhan ke burgeshi akwai girmama mutum ba wannan tsigaggaiyar ba.
Yasan yanzu in beje kiran ba se ya janyowa kansa wata damuwar, haka ya miƙe ya biyo bayan Nana.
A tsakar gida ya tarar da Nana, ta kamo kunnen wannan muzurun da take cewa Autan Mother.
Ta riƙe kunnensa tana cewa "kai dai jarabarka tayi yawa, ga masifa ga ba'a maka gwaninta sena cillar da kai a waje, ɗan bantan uban me dogon kunne"
Sarai Sadik ya san da shi take, Sedai ganin ba kowa a tsakar gidan, yasa ya ƙarasa in da take ya danƙota ya miƙar da ita tsaye.
"Wayyo Allah na Inna!" Ta faÉ—a tana rarraba ido
Sadik ya tsare gida sosai, ya ƙare mata kallo yace "Ni sa'anki ne? Ko na miki kama da abokin wasanki?"
"Dallacan ni ka cikani, meye haka Inna wallahi ya taɓa ni"
"Uban me zan taɓa a jikin naki? Shashasha ƙwailar banza da ta wofi, mara Kunya wallahi kika kuma cemin kai, ko na taho kika ɗau wannan magen kina zagi sena miki rashin mutunci sena kikkifa miki mari"
Inna Kuwa a tare suka fito da Hakimi suna kallon ikon Allah, Sadik ya riƙe hannayen Nana, shi kam ko a jikinsa ya cigaba da yiwa Nanan warning.
"To ni ka sakarmin hannu, ni ba 'yar Iska bace da zaka riƙen hannu"
"To waye ɗan iskan? Wallahi idan ba ki kiyaye ni ba sena zubar miki da haƙora, stupid girl"
"Wallahi ni ba stupid bace" bakin Nana yaƙi mutuwa, se zubo masa rashin kunya kawai take.
Hakimi ya sake jinjin tsantsar fitsara irin ta Sadik, ganin idonsu ko a jikinsa balle ya cika Nana ko ya dena zaginta.
Inna kam riƙe haɓa tai tana ganin ikon rabbi.
Sannu a hankali Hakimi ya tako zuwa in da suke tsaye, ya cire hannun Sadik a na Nana.
"Kai yanzu ka rasa da wa za kai faɗa se ƙanwarka? Kai ba abun kunya bane a gurinka?"
"Allah ya rufan Asiri wannan ta zama ƙanwata, ni ba ƙanwata bace"
"To mecece ita a gurin ka?"
Hakimi yai maganar yana kallon ƙwayar idon Sadik.
Sadik ya sunkuyar da kai, saboda tsananin kwarjini da dattijon yai masa.
"Ni dai a ja mata kunne ta dena shiga sabgata, in ba haka ba sena ji mata ciwo"
"Ahh kasheni za kai, ji min ciwo ai ba kai da yawa ba"
Inna tace "dan ubanki ki biye masa yai miki illa, uwar marasa kunya"
Nana ta tura baki tace "dama ai yace ya tsaneni, seya kashe ni ya huta kawai"
"Eh na tsane ki" ya maimaita jijiyoyin kansa suna miƙewa, alamar ya zuciya ƙwarai.
Hakimi ya kama hannun Sadik suka fita waje daga gidan.
Suna fita Inna ta dirarwa Nana da faɗa "ki cigaba da masa rashin kunya, idan yai miki illa ke kila jiyo, kuma wallahi kika kuma bari ya taɓa jikinki sena miki dukan tsiya, 'yar banza shashasha"
"Inna fa shine kawai ya riƙen....."
"Zakimin shiru ko sena zo na tura kanki a cikin murhun nan" Nana tai shiru tana zumɓura baki.
Wani ɗaki Hakimi ya kai Sadik, ya sa Sadik ɗin ya zauna yana ta huci, ya kalli Sadik yace "meyasa ba ka da ta ido ne? Kasa ƙanwarka ta raina ka, kuma a Gabanmu babu ko ta ido, su baka san mata haƙuri ake da su ba?"
Hakimi yai maganar yana monitoring moves É—in Sadik.
Sadik yaƙi magana ya sunkuyar da kai yana huci.
Yace "shikenan, ka zauna a nan ka baro musu cikin gidan, ka dena ganinta kana jin haushinta, idan ka huce zaɓi ya rage naka, ko ka zauna a nan ko kuma ka koma ciki.
Amma kai baka san a cikin horon da nai niyyar yi maka, wani ƙasurgumin ƙauye na so kai ajiyarka ba, amma ta dage ta dinga bani haƙuri? Ita rayuwa ka kiyayi furta ka tsani mutum, mussaman a gaban makusantan sa in ba haka ba wataran za kai nadama"
Sadik be ko gezau ba, har Hakimi ya gama nasihar sa ya baro shi a É—akin.
Baban Lilly da sassafe ya dira, dan an sanar masa Lillyn ba lafiya harda ƙarin jini.
Dogo ne sosai, giant baƙi ne ga idanunsa jawur kamar gauta, alamun girma sun bayyana a tare da shi, dan lokacin retire ɗin sa ya kusa, kallo ɗaya za kai masa ka ga tsagwaron kwarjini a tare da shi.
Yana zaune a bakin gadon Lilly, ya riƙe ɗan ƙaramin hannunta a nasa, hannu ɗaya yana shafa kanta yace "Sannu Mamana, ya kike jin jikin naki?"
Cikin shagwaɓa tace "Daddy na warke ai, ni sonake a sallame ni mu koma gida, am tired na gajinda zaman Asibitin nan"
"Ohhh sorry, amma idan ya kamata a sallame ki za'a sallameki ai, haryanzu jikinki ba ƙwari"
Lilly tace "Daddy na gaji ne"
Uace "ok shikenan, bari likitan ya shigo in masa magana"
Ana haka se ga likitan ya shigo hannunsa É—auke da file É—inta yana dubawa.
Baban Lilly yace "yawwa Doctor dama nemanka nake"
Doctor yai murmushi yace "Ai gani nazo"
"Doctor jaririyata fa ta gaji da zaman nan, ai discharging É—in ta Please"
Doctor yai murmushi yace "wannan ƙatuwar budurwar ce jaririya?"
"Jaririya ce mana, aka ban zani ai goya abata zanyi, fifteen to sixteen years ai jaririya ce haryanzu"
Doctor yai murmushi yace "in ba zaka damu ba yallaɓai ina son ganinka a office ɗina"
Baban Lilly yace "ba damuwa muje"
Gaban Lilly yai mummunar faÉ—uwa, saboda fargabar kar likita ya gano abunda ya sameta ya gayawa Babanta, ai take wasu irin hawayen tsoro suka fara zubo mata.
Wayar ta ce ta hau ruri ta duba taga Nazir ne, a fusace ta É—aga wayar tace "wai meye ne?"
"Ban gane meye ba? Ina ta kiranki ba kya ɗagawa, ashe kina Asibiti harda ƙarin jini!"
"Tabbas ina Asibiti harda ƙarin jini, babana ya dawo likita ya gayyace shi Office ɗin sa, dan haka ka shirya komai ze iya faruwa!!!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Jikin sir Nazir ne ya É—au rawa jin abunda Lilly ta faÉ—a.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Lilly yanzun meye abun yi?"
"Nima ban sani ba, sedai kawai muyi ta Addu'a, ni kaina a tashin hankali nake wallahi".
Doctor kuwa suna zuwa Office ɗinsa, Daddyn Lilly ya nemi guri ya zauna, ya kalli baban Lilly yace "yallaɓai, ba yau na fara duba iyalinka ba, mun daɗe tare muna wannan al'ammura na kula da rashin lafiyar iyalinka"
Daddy yace "hakane, ina jinka"