Sashe 39
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbas yai murmushi yace "lallaima Hajiya, yanzu kawai seki biya"
Tace "eh mana"
Yace "to ni meye amfani na in har zaki biya? Wai ina mamanta ma, ina iyayenta naga wannan yaron ne kawai ya biyo mu, in sunzo se su biya kuÉ—in, an rage musu 30% saboda ke"
Huzaifa yace "ga kuÉ—i Umma ta bani, nawa za'a biya"
Hajiya tace "ƙyaleshi Huzaifa"
Ta kalli Abbas tace "Ina tausayin Yarinyar ne, ai ita ce nake cewa da zan maka mata ta biyu da ita, amma a kace an mata miji, ai 'ya ta ce"
Kawai Abbas ya hau dariya yace "wannan 'yar Yarinyar, da da wuri nai Aure ai na haife ta, wannan ai 'ya ta ce"
Hajiya tace "wallahi Yarinyar akwai nutsuwa, ga tarbiyya she's first child of her Fulani parent, so ba kulawa Sosai, yanzu haka in ka bibiya ta daÉ—e tana rashin lafiya basu sani ba, kuma maybe ba ta faÉ—a ba, tunda ba ta da magana"
Abbas yace "Allah sarki, Allah ya bata lafiya, tunda 'yar ki ce shikenan ba se kun biya ba"
Se Wajen magariba, se ga Abba hankali a tashe ya isa Asibitin, ya tarar da Hajiya a Asibitin.
Suka gaisa Sannan yace "Naji labarin karamcin da ki kai mana, ubangiji Allah ya saka da Alkhairi yasa ki É—auka a gidan Aljanna"
Hajiya tace "Ameen bakomai, ai yiwa kaine, bismillah muje ka ganta"
Suka nufi É—akin da Farhan take, tana kwance an sa mata Oxygen, hannunta É—auke da drip, harta faÉ—a Sosai fatar ta tayi wani iri alamar oxygen ba ta wadatar jikinta.
Ga SPO2 machine yana ta reading vitals É—in ta.
Ganin halin da Farhan ɗin ke ciki, seda Abbanta ya firgita sosai, ya ƙarasa gaban gadonta, ya shafi gashin kanta da yake a hargitse yace "Allah kai ka halicce ta ka ɗora mata, Ubangiji Allah ka tashi kafaɗunta in ciwon na tashi ne, in bana tashi bane Allah kasa ta tafi a sa'a" yai maganar ƙwalla na taruwa a idonsa.
Hajiya tace "ka kwantar da hankalinka, insha Allah zata samu sauƙi"
Abbas ya shigo da file É—in Farhan, suka gaisa da Abba, Hajiya tace "Abbas ga mahaifinta'
Abbas yace "Allah sarki, ai naga kama, Allah ya bata lafiya"
Abba yace "to nawa ne aka ce kuɗin Asibitin, in biya mu maida ita na gwamnati, naga wannan Asibitin na masu ƙarfi ne"
Hajiya tace "baka da damuwa da wannan, tayi sabon uba ai yace an mata kyauta" tai maganar tana nuna Abbas.
Hajiya tace "sedai batun wanda ze kwana da ita, naga ka taho kai kaÉ—ai ina Umman nata?"
Abba yace "Ai ba zata zo ba, kin san ita ce ta fari, ina ga ni zan kwana a gurinta, zuwa da safe ƙanwata za ta zo se ta cigaba da kula da ita"
Abbas ya jinjina kai yace "Baba ba kai ya dace ka kula da ita ba, a wannan halin da take ciki, tana buƙatar kulawar uwa ne"
Abba yace "Ai da yake ita ce ta fari, kuma dangin uwar ba a garin nan suke ba, da za a samu me kula da ita, amma bakomai zan kula da ita"
Abbas yace "No ba za ai haka ba, muna da Nurses, za suyi mata duk abunda ya dace, zamu kula da ita"
Abba yace"haba ai wahalar se tai yawa, ba a É—ora muku nauyi da yawa bax
Abbas yace "karka damu, aikinmu ne ai, ka bari zuwa an jima ka tafi kawai, zamu kula da ita, Hajiya tai min kyautar ta ai, 'ya tace nima zan kula da ita, muna da ma'aikata wanda aikinsu ne"
Abba yai ta godiya, har seda Abbas yaji godiyar tayi yawa, ko Lafiya suka bawa Farhan iya godiyar kenan.
Nana kuwa ana ta fama amma ta gagara farfaÉ—owa, se surutai kawai da take da fizge fizge, se da aka dangana da yi mata rubutu da Addu'oi sannan ta dawo hayyacinta, a hankali ta kalli Inna, ta rintse idonta tana faÉ—in Allah ya sa ba gaskiya bane.
Inna tace "Nana kina jina?" Ta jinjinawa Inna kai alamar eh.
Tace "to É—ago ki kalleni"
Ta É—aga kai ta kalli Inna, ta kalli É—akin still ga Hakimi, ga Abba da Faruk sedai ba Sadik.
Ta miƙe zaune ta kalli kayan jikinta, tun Uniform ɗinta ne da ta dawo da su, tai shiru dan tayi tunanin gaske ne ko mafarki tai, amma komai ya dinga dawo mata tiryan tiryan.
Fashewa tai da kuka a gigice tace "dan Allah Inna kice min ba gaske bane mafarki nake, wallahi ban isa Aure ba"
Inna tace "ki saurareni da kyau, kina jina, Kakanki ya riga ya yanke hukunci, An aurar da ke ga Sadik, yanzu Sadik shine mijinki, ina son ki karɓi ƙaddara a yadda ta zo miki, Allah ya riga ya ƙaddara haka zata faru, dan haka kiyi haƙuri ki karɓe shi a matsayin miji, gobe in Allah ya kaimu zaku tafi, wataƙila a satin nan ko na gaba zaku tafi can ƙasar"
Kawai Nana ta fashe da kuka, tana wani irin sheshsheƙa kamar zata shiɗe, amma ta kasa Magana, se wani irin zazzaɓi ma da ya rufeta.
Abunda ya faru shine, Ranar Juma'a Abba da Faruk suka ƙaraso, suka tarar Likita yana duba Hakimi, saboda jikinsa da ya tashi.
Allah yasa zuwa sha biyun rana, aka samu ya ɗan samu sauƙi, Sadik yana ta murna yasan in Allah ya yadda wannan karon ze tafi gida, aka kawo masa sababbun kaya farare, aka ce su zesa, da farko abun ya bashi mamaki se yai zaton dan yau za'a tafi da shi ne.
Bayan idar da sallar juma'a, akace za'ai É—aurin Aure a Masallacin, Sadik Alla Alla yake ayi a gama abunda za ai, su tafi.
Can aka fara É—aurin Aure, yaji an ambaci Nana Asma'u, da Abubakar Abdullahi Rano.
Da fari be san wa aka É—aurawa Auren ba, se daga baya ya fara tunanin wannan ai sunansa ne?.
Seda aka gama ɗaurin Aure, yaga Abba yana zufa, Faruk ya miƙo masa hannu yace ""burinka ya cika Auta, Allah ya Sanya Alkhairi ya baka wuyan ɗauka"
Zaro ido Sadik yai yace "wa aka É—aurawa Auren?"
"Kai da Nana mana" ya bashi amsa.
A gigice ya nufi in da Abba yake, yace "Abba da gaske ni aka É—aurawa Aure?"
Abba yace "Eh, kai aka É—aurawa Aure"
Gigicewa Sadik yai, ya fara zazzaro ido "Abba meyasa? Meyasa za'aimin jaka? Meyasa za'amin Aure ba tare da sanina na?" Ganin ze tada hayaniya yasa aka sa dogarai sukai cikin gida da shi.
Nan da nan aka fara bushe bushe, Hakimi ya miƙe ze tashi, amma ya yanke jiki ya faɗi.
Aka É—auke shi aka shiga da shi cikin gida, ana tunanin koma ya rasu ne, nan da nan aka dakatar da wannan busar da ake.
Se kuma daga baya cikin ikon Allah ya farka.
Gaba ɗaya Sadik ya fita hayyacinsa, yai kuka yai kuka har idonsa yai jawur, shi a lokacin nan da Hakimi ya mutu ma ba abunda ze ji, ya rasa laifin me yai musu suka tsane shi haka, ko Auren za'ai masa ai a bari ya zaɓi wadda yake so.
Magana ma ta gagari Sadik, se sheshsheƙa da ajiyar zuciya, wata muguwar tsanar Nana ta ƙara baibaye shi, ko ƙaunar jin an ambaci sunanta ba yayi.
Tun saura kwana biyu Abba su zo garin, Hakimi yace masa in ya tashi tahowa, ya taho da Sadakin É—ansa.
Abba sam ya zaci kawai barkwancin Hakimi ne, amma be taɓa zaton Hakimi zewa Sadik Aure da Nana ba.
Ba shi da ikon ja da maganar mahaifinsa, amma sam be ga tsari a wannan Auren ba tsakanin Nana da Sadik waze tsawatarwa wani? Banda shirme da Yarinta babu abunda za'a tsinana a wannan Auren. A haka ma kullum ba su da aiki se faÉ—a, ina ga zaman Aure?
Shikan sa Auren babu lallai sun san meye Auren balle suyi zaman Aure, ta guri ɗaya yaji sanyi a ransa, kasancewar Nana boarding aka samar mata, kafin dai ta gama Makaranta, su tare ƙil sunyi hankali.
Ga Hakimi yai jan kunne sosai akan Auren, dan yace be yafe ba idan aka sake wani abu ya samu wannan Aure.
Cikin dare kusan ƙarfe biyu da rabi na dare, Aka kaiwa Abbas sakamakon gwaje gwajen da a kaiwa Farhan.
Ya sa aka kawo masa magunguna, ya tafi da kansa yai mata serving medication.
Ulcer tai mata mummunan kamu, peptic Ulcer irin me riƙe numfashin nan, ga jininta yai ƙasa, ga kuma very high BP, nan ya shiga mamakin yadda a kai wannan 'yar ƙaramar Yarinyar ta samu wannan ciwuka haka.
Ba yadda za'ai ace lokaci ɗaya duka wannan ciwukan suka kamata, sannu a hankali suka kaita ƙasa haka.
Se da ya ja gajeren tsaki,da ya tuna yadda Hajiya ta bashi labarin yadda take zaune a gidan su.
A fili yace "Wannan ai shirme ne, Al'ada ai ba Addini bace"
Yai mata Allura ta cikin canula, yana yi yana monitoring vitals É—inta, duk da an samu improvement ba Kamar lokacin da aka kawota ba.
A hankali ya ga ta fara motsawa, dan haka ya tsaya ya zuba mata ido.
Ƙoƙarin ta da kabbarar salla take, a cikin yanayin da take, harta fara ƙoƙarin tashi zaune.
Abbas ya maida ita ya gyara mata kwanciya yace "Sannu"
A hankali ta fara buÉ—e idonta, dishi dishi take gani, ba ta gane a ina take, ta kalli Abbas amma taga fuskar Sadik.
A hankali ta kai hannu, ta riƙo hannunsa ta fara Magana "Sadik, Sadik dan Allah, dan Allah ka dena min haka, you are the only.. only...Sadik I need you....." Allurar da yai mata da ya shigo ce ta cigaba da ɗibarta, dan haka a cikin magagi take.
Abbas yai shiru yana Nazarin ta, da abunda take faÉ—a.
Ganin ta fara bacci, yasa ya fara ƙoƙarin zare hannunsa daga nata, amma ta riƙe gam tana tura baki.
"Kowane Sadik ɗin nan ya na da alaƙa da damuwarta, wanda ya kai ta ga wannan rashin lafiya"
Wata Nurse ce ta shigo za tai masa Magana, amma ya girgiza mata kai da alamar tai shiru, baya son mara lafiyarsa ta tashi.
A hankali ya zare hannunsa daga na Farhan, ya fice daga Office É—in.