← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 115

Sashe 44

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hmm, ai ni nama rasa ta in da zan fara maka bayani, baƙin ciki ya hanani in kiraka in sanar da kai"

Dr. Yai murmushi yace "that's good"

"Kamar ya that's good?"

"Ahh abunda yake so ne ai ya samu?"

"Kai Maganar Sadik wata maganar kirki ce? Me Sadik ya sani banda salon lalata shi da za'ai masa wani Aure? Me Sadik ya sani guda nawa yake? Ko degree be haɗa ba yaron da Just recently ya kammala secondary, shima dan an masa jumping, wai shi a kaiwa Aure, kuma a rasa wadda za'a aura masa se wannan 'yar ƙauyen jikar ta su"

Usman yai murmushi yace "Children of now adays are beyond your expectations, karki zafafa ki zo ya baki Kunya"

"Ai bazan É—au wannan abun da a kaimin ba, dole in kashe Auren nan"

Usman a ransa Yace 'haifar Sadik ki kai, amma baki san waye ba, baze iya haƙurin da nai ba, ya fito gatse gatse ya gayamiki Aure yake so, amma kina cewa be san komai ba, be san komai ba ya akai yasan yana son Aure?"

Wani murmushi ya sake yi a fili yace "bari inje mu gaisa da Abban"

Mother ta ɗan taɓe baki tace "seka dawo"

Ya miƙe ya bar part ɗin Mother, yana mamakin yadda ta rintse idonta taƙi kallon gaskiya.

A falon sashin Abba ya tarar da shi yana kallon CNN.

Dr. Yace "barka da hutawa Abba, ai ban san ka dawo ba"

Abba yace "na shigo tun É—azu ai, naga motarka na san kana gurin mahaifiyarka, kaima tana maka famfo akan yadda zaku haÉ—u ku juyan baya ko?"

"Haba dai Abba wane ni? Ba haka bane ba"

"Amma dai ta gaya maka abunda ke faruwa, ina ga tun a shakranjiya ta kiraka ta sanar da kai abun da ya faru?"

Usman ya gyara zama yace "No, ban san meke faruwa ba gaskiya se yanzu da na zo take gaya min"

Abba ya numfasa yace "Usman, ni kaina banji daɗin matakin da Hakimi ya ɗauka akan Sadik ba, Sadik yayi ƙanƙanta da Riƙe Aure baze iya ba, amma ba zan iya bijirewa umarnin mahaifina ba, saboda dani da ku duk mallakinsa ne, amma abun mamaki se ga mahaifiyarku tana nema ta ɗagan hankali ta sa in bijirewa umarnin su dan in faranta mata".

"A'a ba haka bane Abba, ka san tana kallon Sadik É—in ne yaro har yanzu, kuma ya nuna mata baya son Auren, kasan yadda take son sa"

Yace "duk da haka dr. Ba yau mahaifiyarku ta fara nuna min iyakata ba akan dangina na ƙauye, tana nuna min abubuwa da dama amma ina kawar mata da kai ta kasa ganewa, yanzu kalli yarinyar nan matar Sadik ɗin, tare muka zo gidan nan da ita, tare zasu tafi London, amma Yarinyar nan ta wuni ta wayi gari ba a bata Abinci ba, ta kwana da zazzaɓi ba wanda yabi ta kanta seni, ai yau ku 'yar tsintuwa na kawo nace Hauwa ta riƙe min,be kamata tai min haka ba"

"Hakane Abba, amma kayi haƙuri dan Allah"

"Haƙuri ai sedai in ɗora akan na baya, sedai zan nuna mata ku da ita a ƙarƙashin ikona kuke, idan ita ban isa da ita ba, ku na isa da ku ai, dama dalilin da ya sa na kiraka shine, in ban takura maka ba, sonake ka tafi da Nana gidanka, zuwa lokacin da zasu tafi, dan tata visa haryanzu bata fito ba, amma in kana ganin ba matsala ban takura muku ba"

"Haba Abba, babu wata matsala ko takura, zan tafi da ita Insha Allah, ko cewa kai in riƙeta a gidana zan riƙe ta"

Abba yai murmushi yace "Allah sarki, haihuwa me rana, nasan da kai akaiwa Auren nan ko Faruk ba wanda ze ɗagan hankali, ta ɓangaren ka ba zan gane kai murna ko akasin haka ba, Faruku kuwa baze taɓa nunamin ɓacin ransa ba, se Sadik amma shima zanyi maganinsa, zuwa da safe in Allah ya kaimu se kazo ka ɗauketa koma in kawo ta da kaina"

"A'a Abba, a taso ta mu tafi yanzu kawai"

"Kana ganin ba matsala?"

"Abba babu wata matsala sam"

Abba yace "to shikenan, Allah yayi albarka ya a baka masu jin ƙan ka" ya amsa da Ameen Abba.

Abba da kansa yaje ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da Nana take, ta taso ta buɗe yace "maza ɗakko akwatinki"

Seda ta É—an tsure, dan ba ta san dalilin hakan ba.

Ta É—akko Akwatin ta, ta fito falo karon farko tun randa suka zo bata fito ba.

A falo taga Usman, ta gaishe shi ya amsa tare da cigaba da abunda yake.

Jin hayaniya a falo yasa Mother ta fito, ta tarar da Nana da Akwatinta, ga Dr.

Yace "Mother seda safe, dare ya fara yu"

Mother za tai magana amma Abba na tsaye a gun, ya kasa ya tsare ya raka su har bakin mota, se da suka tafi sannan ya dawo, da ya dawo É—in ma be kula Mother ba, ya wuce sashinsa.

Nan Mother ta tsaya tana tunani, meyasa Dr. Ya tafi da Yarinyar nan.

Ɗakin Sadik ta nufa amma taga ya kashe fitila, dan haka tai tunanin ko bacci yake, Sadik kuwa idonsa biyu kallo yake a system ɗin sa, wanda ya haddasa masa damuwa, ya dafe kansa yana ƙoƙarin yin tunanin wani abu me mahimmanci a tare da shi amma ya kasa, gefe guda kuma ga wata irin fitina da take damunsa, a hankali ya fesar da iskar bakinsa ya kashingiɗa ya lumshe idonsa.

Tunda suka fara tafiya da Nana, ba wanda ya cewa wani komai daga dr. Har Nana, dama dr. Ba me magana bane dama Faruk ne.

Suna tafiya Mother ta kira dr. A waya, ba tunanin komai ya É—aga ya sata a hansfree.

"Dan ubanka me kuke shiryawa kai da ubanka, ina zaka kai Yarinyar nan?"

"Gidana zata koma" ya bata amsa kai tsaye.

"Akan wani dalilin? Meyasa zata koma gidan naka?"

"Eh Abba ne yace ta koma can, shiyasa na zo na tafi da ita"

"Amma kuma shine baka gayamin ba? Za kai gaban kanka"

Usman yace "to Mother ai banga wani abu a ciki ba"

"Ai baka da hankali dama, kai da Faruk wasu lokutan baku san abunda yakamata ba dama, ka kyauta"

Usman kawai ya Ajiye wayar tare da girgiza kai.

Suka ƙarasa gidan dr., Ya buɗe bayan motar ya ɗakko Akwatin Nana yai cikin gida, ba ta da zaɓin da ya wuce tabi bayansa.

Cikin sauri tabi bayan nasa, sedai da yake cikin sauri yake tafiyar ya rigata shiga falon.

Tana zuwa ta tarar da shi a tsugune a gaban 3seater, Jidda na kwance da wasu irin fitinannun sleeping wears, yana magana ƙasa ƙasa "ko dai zamu tafi Asibiti, har yanzu jikin ki da zafi fa"

"A'a Baby na sha magani fa"

Kallo ɗaya Nana taiwa Jidda taji wata kunya ta kamata, yadda take zaune ƙanin tsirara ga dr. Yana kallonta (lolz🤭😂)

Yace "Munyi baƙuwa fa"

"Baƙuwa kuma?" Tai maganar tana ƙoƙarin tashi zaune, idonta ta sauke akan Nana, take Jidda tai murmushi tace "Ƙawata, yaushe suka zo?"

"Eh tun shekaranjiya tana gida, yau Abba yace inje in É—akko ta"

"Kai amma naji daÉ—i, Nana ya kike ya Inna?"

Nana tace "lafiya ƙalau, tana sunkuyar da kai"

Usman yace "ga É—akin dake kallon dining nan, ki shiga ki ajiye Akwatin naki, kije Kitchen ki É—ebi Abinci ki ci"

Nana ba tace komai ba ta ja Akwatinta, ta shiga É—akin da akai mata umarni, tana jinjina fitsara irin ta Jidda.

Usman ya maida kallonsa kan Jidda yace "muje daga ciki, ki wanka da ruwan É—umi seki kwanta zaki ji daÉ—in jikinki"

Ta kwanta a jikin dr. Tace "Nikam naji daɗin zuwan Nana, amma naji kunya baka taɓa kaini naje na gaida Inna ba, ga Hakimi yai rashin lafiya shima banje ba, gobe in Allah ya kaimu ka kaini gida mu gaisa da Innan"

"Ke in da ita aka zo zata bari a É—akkota a taho da ita nan ne? Matar Sadik ce fa" yai maganar yana wata shu'umar dariya.

Jidda tace "kace 'yar gida za'ai idan ya kammala Makaranta, to Allah ya nuna mana kuma sunyi matching Sosai"

"Ai an riga anyi ma"

"Akayi me?" Tai tambayar cikin mamaki.

"Akai Auren, jiya ma Abba yai walima da abokansa"

"Dan Allah Baby be serious, wane irin Aure kuma ana zaune ƙalau"

Usman yace "na saba yi miki ƙarya ne? Am serious Hakimi ya masa Aure, tare ma zasu tafi London, maganinsa kenan dama ba shi mara kunya ba, a gaban uban kowa ma faɗa yake Aure yake so, yanzu kuma an masa wai baya so"

Kawai Jidda ta kwashe da dariya, Usman ma ya tayata.

Nana fitowa tai dan ta nemi ruwan da zata sha, dan tana jin ƙishirwa.

Ta tarar da su a manne da juna suna dariya, Nana a ranta tace "Wannan wace irin watsewa ce?"

Tace "zan sha ruwa"

Dr. Ne ya É—ago ya kalleta yace ta shiga Kitchen ta duba fridge.

Jidda kuwa na kallon Nana se dariya ta kuma kamata, tace "but seriously dr., She's still young an katse mata hanzari, bana tunanin zata iya ɗaukar ɗawainiyar Aure, yarinya ce Sosai daga ita har Sadik ɗin sunyi ƙanƙanta sosai"

"Su sukace miki sunyi ƙanƙanta?"

Jidda ta toshe baki tana cigaba da dariya, Usman ya miƙe ya ɗagata suka nufi ɗaki suna cigaba da dariya.

Nana kam daskarewa tai a gurin, wannan wace irin taɓara ce da watsewa haka? Kamar ba Musulmai ba.

Dama haka Usman É—in nan yake tana kallonsa wani shiru shiru da shi, wannan ai ba yi bane.

Jiki a sanyaye cike da kunya, Nana ta koma in da aka bata ta zauna, tana mamakin abunda su Jidda su kai.

Kwana biyu 'yan ajinsu Farhan ba sa ganinta, Lilly ce kawai ta damu da tambayar wai Ina Farhan ta shiga kwana biyu ba ta zuwa.

Rashin samun amsar ta ne yasa ta tafi Ofishin Sir Nazir, cike da É—okin sanar da shi mahaifinta ya amince ya fito.

Ta tarar da shi da su Taslim a Office ɗin nasa yana koya musu karatu, kasancewar yanzu sune zasui jarrabawar ƙarshe.
Chapter 44 · 0% Book details