← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 115

Sashe 93

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai ta fashe da kuka tace "wai ya kake son in yi ne? Me kake nema a gurina, na ɗora rai a kanka amma ka yaudareni, a haukana na sakankance zaka dawo ka Aureni, a lokacin da nake tsaka da neman ɗauki, soyayarka na barazana ga rayuwata, amma ka yanke alƙa dani ba tare da ka sanar dani dalili ba, haka na haƙura da son yiwa iyayena biyayya in auri wanda ba na so, soyayyarka ta hanani sukuni da nustuwa, na fara neman maganin da ze mantar da ni kai, wanda iyayena suka zaɓamin ya bi ya ɓatamin suna yana cewa ni mutuniyar banza ce, ko da yake hakane,. Lokacin soyayyarka ta rufemin ido, ina iya sakin jiki kai min koma menene saboda son da nake maka, aka zo aka fasa Aurena ranar ɗaurin Aure, ya cigaba da bina da sharri kala kala a gari.
Katsam na tsinci labarin kayi Aure Sadik, bayan duk alƙawarurrukan da kai min, kai Aure ka barni, ba amo ba labarinka, ta yaya ba zan shaye shaye ba, ka koyamin abubuwa masu wuyar mancewa da ƙuruciyata, ba abunda nake kewa, banda tausayawarka da daɗaɗan kalamanka na yaudara, na saba da kwanciya a jikinka, ƙamshinka da barkwancinka lokaci ɗaya ka yanke wannan alaƙa da ka gina, sannan duk a garin in samu mafita miyagun abokanka suka min fyade suka lalata min rayuwa ta.
Duk wanda ya zo neman Aurena, se Sunusi ya ɓata, Mubarak babba bayan cin zarafina ya kirani da ƙasƙantacciya mara amfani saboda bamu da kuɗi, shiyasa na yadda in nemi kuɗi in rama abunda yai min.
Sadik me yai saura da kake da shi wanda zaka gayamin menene?" Tai maganar cikin ƙaraji.

Lumshe ido yai, yana jin yadda magananunta suke tasiri a cikin zuciyar sa.

A hankali yace "ban san da wani suna ya dace in kira kaina ba, amma duk sunan da kika kirani, mayaudari maƙaryaci duk na cancanci hakan.
Farhan na so ki tun ban san menene son ba ma, kuma na shirya yadda zan rayu da ke, amma har kullum shi bawa ba shi yake da kansa ba, Allah ke tsara masa komai nasa.
Farhan kakanni na ne suka Auramin ƙanwata Nana a cewarsu zuwana ƙasar waje karatu nikaɗai hatsari ne, na sha gayawa iyayena ina son Aure, amma suka dinga dankwafeni, suna min kallon yaro, hakan ya bawa kakannina damar Auramin Nana, ba tare da sun tuntuɓi ko ina da wadda nake so ba.
Ban sani ba ko hakacewa nai Farhan, amma lokaci É—aya da ke, da makarantar mu, da abokaina Wallahi kamar an min formatting na manta komai, haryanzu na kasa gano dalilin yadda a kai haka ta faru da ni, na manta da komai a shekarun nan ko da wasa, ban iya tuna kowa da ya shafi makaranta da rayuwar da nai a cikin ta ba".

Ture shi tai tace "ai dole ka manta mana, tunda kai Aure, ka barni a wahala"
Matsawa ya sake yi daf da ita yace "idan ma hakane, mahimmancinki da soyayyar ki a gurina yasa na sake dawowa rayuwar ki a karo na biyu, in nemi afuwarki kuma in sake neman soyayarki, duk da nasan soyayyata haryanzu tana nan a tare da ke"

"Kar ka yaudari kan ka malam" tai maganar ranta a haÉ—e.

"Hmm, ba yaudarar kai bane ba Farhan, sannan zan nunawa Babba ke mace ce me tsabar daraja da kima, duk wanda suka ci zarafinki sena É—au mataki a kansa, kuma ni a haka nake sonki Farhan, zan Aureki ina sonki Wallahi"

"Se kuma kayi, dan an sa min ranar Aure, saura watanni uku, kuma ko ba'a sa ba ba zan Aureka ba".

Be damu ba yace "zan zo neman Aurenki, ba ki da mijin da ya wuce Sadik, ki rubuta ki ajiye wannan, and magana ta gaba, ba zaki min asara ba, shaye shaye yana kawo illa ga ƙwayoyin haihuwa, ban sani ba ko da yarana a cikin ki, dan haka na hana shan wani abu daga yanzu, dama saboda ni kike sha, to gani na dawo.
Na dena lallaɓa ki ko kina so, ko ba kya so zan Aureki Farhan dan tabbatar wa da Duniya soyayyar mu ba RUƊIN ƘURUCIYA bace, saboda so ba ruwansa da ƙuruciya".

Mamakin ƙarfin hali irin na Sadik take yi, harya juya ze fita ya dawo ya kalleta yace "kar kuma in sake ganinki tare da wannan farin mutumin, da koma waye suke zuwa gurinki, ki gaya musu ke matar Aure ce, matar Sadik ce idan suka cigaba da bibiyarki kuma, Wallahi se na yiwa mutum illa, kuma ki tattaro kayanki ki bar Hotel ɗin nan ba zan miki dole ki bar nan yanzu ba, amma Wallahi na kuma ganinki a hotel, kafin in gaya miki matakin da zan ɗauka bari in tuna baya, let's remember our first kiss". Kan tai Magana ya rungumota jikinsa, ya fara kissing ɗinta so deeply.

Lumshe ido tai, tabbas ta tuna first kiss ɗinsu, a gurin birthday ɗinta, she so much Miss him, ji take tamkar ta rungume shi, itama ta mayar masa, amma tuna yadda ya gujeta yai Aure har da ɗa, ya sa ta fara mutsu mutsu za ta ƙwace, ba ta tsinke da lamarin Sadik ba se da taji ya zuge rigarta, kokawa suka shiga yi, ta saka kuka tana girgiza masa kai tace "ba ka da hankali ne me kake yi haka?"

Ya cire rigar da ga ita se underwears, ta rurrufe jikinta, take hawaye ya wanke mata fuska, be damu da abunda yai ba, ya sa hannun sa ya fizge nata daga kare jikinta da tai Sannan ya kalleta yace "ko da tsiya, ko da tsiya tsiya in dai ina numfashi ke tawa ce, ba zan cigaba da lallaɓaki kina wahal da ruhi na da gangar jikina ba, ke har ma da matata da ɗana ba, ba jikinki nake so ba, zuciyar ki nake so, da jikinki nake so ba zan Aureki ba bayan wasu sun riga sun..... Se kuma ya datse zancen ya ɗora da
"Wallahi, Wallahi idan na kuma ganinki a hotel, i will sleep with you there, tunda abunda kike so kenan, ki ke zaman banza a hotel kina tara ƙarti"

Sosai Sadik ya bata tsoro, jikinta se rawa yake yi, a ranta tace 'wai ba jikina kake so ba, Sadik na sanka kamar yunwar cikina" amma a zahiri ko motsi ta kasa se hawaye.

Se kuma ya lumshe ido yace "kin ƙara girma da kyau sosai princess, am sorry na saki kuka, ban sanki da gardama ba, amma ƙwaya duk ta canza min ke, amma daga yau insha Allah se kin dena sha, tunda gani na dawo, sa rigarki muje ki ci Abinci in kai ki gida".

Ta ɓoye tsoronta ta dake tace "ka fita ka barmin ɗaki, kace ba jikina kake so ba amma kai min tsirara, ka fita ka bani guri"

Murmushi yai be kuma cewa komai ba ya fice.

Yau wani irin nishaɗi Sadik yake yi, sedai yana tunkarar gida gabansa ya shiga faɗuwa, saboda be san ta ina ze ɓullowa lamarin a gida ba.

Tunanin yadda Sadik ze sake tunkarar iyayensa da batun yana son sake ƙara Aure kuma ya baibaiye shi, dan ya san abune me wahalar gaske su amince, na farin ma da ya akayi balle ya sake zo musu da wannan sabuwar maganar.

Nan fa tunani ya sake komawa Sadik sabo.

Yau Abba ya zo hutun ƙarshen wata da yake zuwa, sedai shima ya lura da canjin yanayin Sadik, sedai be ɗau abun da mahimmanci ba, saboda yasan halin Sadik ɗin wasu lokutan ba gane kansa ake yi ba.

Sedai abun ya É—an dameshi, ganin ita kanta Nana duk tana cikin damuwa, wadda ita kanta ba ta san tana da damuwar ba.

Abba ne ya kalli Nana, da ke zaune a babban falo, gefenta Sahal yana bacci, ya zauna a É—aya daga kujerun falon ya kalleta yace "Nana, meke faruwa ne daga ke har Sadik gaba É—aya na kasa gane muku, duk kunyi wani iri ko akwai matsala ne?"

Nana ta girgiza kai tace "A'a"

Abba yace "A'a, kar ki ɓoyemin komai, baki san fuskar ki ta nuna bane?"

Kawai ta fashe da kuka, Abba ya barta tayi tayi, sannan yace "ina jinki"

Mother da tazo wucewa tace "lafiya take kuka?"

Abba yace "Abunda nake son ji kenan"

Nana ta share hawayen fuskarta tace "Abba, ni na kasa gane kansa gaba ɗaya, na tambaye shi idan wani laifin nayi masa yace A'a, gaba ɗaya ya dena kula da mu kamar da, har gara Sahal yana ɗaukar sa, amma ba ya wuni a gida, wataran se dare munyi bacci yake dawowa, na tambaye shi menene yaƙi gayamin, ko Abinci ba kullum yake ci ba"

Mother tace "Aikam nima nayi iya yina, akan ya gayamin meke damunsa amma fafur yace bakomai, ni kaina na lura da hakan a tare da shi, duk ya canza"

Abba yace "ki dena kuka, zan zauna da shi inji ta bakinsa, ki dena kuka kinji yarinyar kirki, dama haka auren yake ai"
Yaita rarrashinta yana kwantar mata da hankali.

Se da aka kwana biyu da maganar da su kai da Nana, Sadik yaje gaida Abba a sashinsa, Abba ya dinga jansa da hira, daga baya yace "kai ya akayi ne gaba É—aya ka canza fa, gayamin meke damunka ne?"

Sadik ya É—an sosa kai yace "bakomai Abba".

"A'a da komai mana, yanayinka ya nuna, don't forget that we are friends, so you can share your problems with me, to see if I can help"

Sadik ya É—anyi shiru yana nazari, tabbas wannan shine right time, da Yakamata yaiwa Abba Magana.

Ya kalli Abba sannan ya ɗan gyara zama yace "Abba, ina son in ƙara Aure ne!!!.
Littafin kuɗi ne, ku tuntuɓi wannan lambar dan samun naku akan kuɗi ₦300 kacal
07063065680

Abba ba tare da ya kalli Sadik ba yace "You must be crazy"

Sadik ya gyara zamansa yace "Abba am serious, wallahi da gaske nake dan Allah ka bani goyon baya, ina son ƙara Auren nan"

"Shut up!" Abba yai masa tsawa.

"Kwata kwata yaushe kai Auren, ko ka manta da ya kai Auren fari, kawai seka zo kace zaka ƙara Aure, saboda baka da hankali"

Sadik ya marairaice yace "dan Allah Abba ka fahimce ni"
Chapter 93 · 0% Book details