← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 115

Sashe 35

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na sani Autana, amma dan Allah kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, kar kaje kayi wani abun da zasu hanaka tafiya, Abbanka yana nan yana nema maka admission a London, insha Allah da ya samu zaka tafi, naji ance an saki Waec ma, amma ban tabattar ba"

"Amma ai Swiden Abba yace min ze kaini"

"Ai Sweden ɗin ne, su se nan da kusan wata huɗu za su fara bada admission, su kuwa nan very soon, abunda ya sa nafi bada ƙarfin ka tafi London ɗin dan kayi ka baro ƙauyen nan"

Sadik yace "shieknan, ina bro ko nemana ba ya yi, tunda suka tafi suka barni a nan, dama dr. Wannan da ina nan da ba na nan duk É—aya a gurinsa"

Mother tace "Wallahi Faruk yana Maganar ka, da zuwa ya so yi ma, amma yana tsoron abunda mahaifinku ze ce dan kwanan duk ya canza kamar ba shi ba"

"Shikenan Mother"

Jiki a sanyaye Mother tace "kayi haƙuri kaji Autana, ka kusa baro garin nan Insha Allah, Abban ma a satin nan ze dawo insha Allah"

"To Mother Allah ya sa"

"Ameen ya Allah"

Su kai sallama.

Messages sun kai goma a wayar, amma ya kasa buÉ—e ko É—aya, ya Ajiye wayar ya murgina ya juya, ya lumshe idonsa.

Yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani irin bugu da sauri da sauri, ya rasa dalilin jin fargabar nan da yake yi.

Da sauri Kamar an mintsine shi, ya tashi zaune, ya kuma É—akko wayarsa ya shiga dubawa.

Messages É—in Farhan ne a wayarsa , se yanzu ya tuna da Farhan, a gigice ya shiga duba messages É—in.

"Am missing You so much, please ina kana lafiya ko message kai min"

"Akwai matsala Please pick my call, or check my messages"

Wayar Farhan ya shiga kira, amma a kashe, take wani irin gumi ya ding tsatsafowa a goshinsa, yayi mamakin yadda ya kwashi tsawon lokaci ba tare da ƙoƙarin sanin halin da Farhan ke ciki ba.

Take Ya shiga tunanin meke damunsa haka? Har yake ƙoƙarin mantawa da abunda ruhinsa ke bege ba dare ba rana.

Ya kira wayarta, ya kira ya kira amma ba ta shiga sam.

Gaba ɗaya hankalinsa ya ƙi kwanciya, har kusan kwana biyu yana faman neman layinta amma ya ƙi shiga.

Hankalin Sadik fa yaƙi kwanciya, kasancewar rashin samun Farhan a waya, abun duniya ya dame shi, ya cigaba da mamakin yadda a kai, tsawon lokacin nan be damu da sanin halin da take ciki ba.

A rana ta uku ne, yaji wayar ta shiga, sedai taƙi ɗagawa sam.

Sadik ya kirata ya kai sau ashirin, Sannan ta É—aga sedai tana É—agawa kukanta ya fara ji.

"Farhan" ya kira sunanta a hankali.

Bata amsa ba ta cigaba da kuka.

"Ban san da wace kalmar zan fara miki Magana ba, Farhan ban san meya sameni ba"

"Sadik har ka manta dani ko, Sadik kuÉ—in Aurena za'a kawo next month, Ina cikin matsala"

"What the fucking shit are you talking about, ban gane kuÉ—in Aure ba"

"Zan maka ƙarya ne? Wallahi Abba ze karɓi kuɗin Aurena, Sadik na shiga uku zuciyata kamar ta tsaga ƙirjina ta fito, wallahi bana son shi kai nake so"

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Sadik ya sauke, yace "ba wanda ze aurar da ke ga wani, ke tawa ce, wallahi ko an Aura miki wani, sena biki har Gidan na ɗauke ki, kuma wallahi duk wanda yai gangancin Aurenki sena illata shi, sena masa tabo me muni, koma in sa a ɓatarmin da shi, ke tawa ce Farhan" ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji.

Kasa cewa komai Farhan tai se sheshsheƙar kuka da take, a hankali ta furta "Ina sonka Sadik, dan Allah kar barni, kar ka juyamin baya, ka riƙe alƙawari dan Allah, ina sonka sosai Sadik".

Duk wuya duk rintsi Farhan, ke tawace kuma Wallahi duk wanda yai gangancin taɓa abunda yake nawa se na masa illa, ko waye shi.

Yana cikin maganar be sake sanin in da kansa yake ba, seda Asuba tayi, ya buÉ—e ido cikin hanzari.

Sedai yai yai ya tuna abunda ya faru, amma abu ya gagara, tabbas yasan bacci ko makamancin haka ya É—auke shi, yana tsaka da wani abu me mahimmanci, Amma ya kasa tuna ko menene, ga abun yana ji a ramsa amma ya kasa tuna komai!

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Ɓangaren Farhan suna tsaka da waya, tana masa magana, kawai taji yayi shiru, ta kira sunansa amma taji kamar ya amsa cikin magagin bacci, zuwa can taji yayi shiru.

Abun ya bata mamaki ba ta taɓa sanin Sadik da magagin bacci ba, ko ƙarfe nawa za su kai na dare suna waya ba ya jin Komai, wataran ita ce me cewa ma ita bacci take ji.

Take taji jikinta yai sanyi ƙalau, ba ta da wani kuzari, se yanzu ta samu damar yin hawaye, amma da zuciyarta ta bushe.

"Ohh Allah meke shirin faruwa ne haka?" Tai maganar tana sheshsheƙar kuka.

Bacci kuwa dama wannan gagararta yai, ta kasa shi gaba ɗaya, se tarin saƙe saƙe da tunani.

Da garin Allah ya waye, gaba É—aya Sadik ya manta sunyi wata waya da Farhan, dan shi ya manta da ita ma gaba É—aya.

Ƙarfe kusan goma na safiya, ya fito daga ɗakin sa, a gefen ɗakin Inna ya hangi Nana tana watsawa tattabaru Gero, tana sanye cikin hijjabi, tunda ya zo Gidan nan, kullum cikin hijjabi yake ganinta, se Ranar da ya mareta ya ganta da ɗaurin ƙirji, amma duk zafin duniya Nana tana sanye da Hijjabi, ba ta taɓa rabuwa da shi, abun har mamaki yake ba shi.

A hankali ya furta "Stupid girl" dan in za'a lissafo abunda ya tsana, to da Nana a ciki, duk da tarin Alkhairan da tai masa a zamansa a gidan, amma ba ya duba wannan se tsagwaron rashin mutuncinta da tsiwa da yake gani.

Zancen zucin da yake ne, ya sa ƙureta da ido, ba tare da yasan yayi hakan ba, seda yaji saukar ruwa a fuskarsa sannan ya farga ya kalli Inda Inna take shirin yin alwalar sallar walha, ita ta watso masa ruwan.

A hankali ya janye idanunsa daga kan Nanan, tare da goge ruwan da Innan ta watsa masa.

A ransa yace 'yanzu fa wannan tsohuwar se ta zata wata tsiyar nake kallo a jikin wannan komaÉ—aÉ—É—iyar yarinyar, aba kamar taliya, dan ita ba wahala ta yiwa abu fassara, ko abunda kake nufi kenan ko ba shi kake nufi ba"

Wayarsa dake cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya zura hannu ya É—akko wayar, tare da nufar soro dan amsa Wayar.

Muryar Amin yaji yace "Mazaaa, Allah ya temaki yarima namu"

Murmushi Sadik yai yace "gayu dama kuna nan? Ba waya ba saƙo?"

"Kai zamu tambaya ai, you just disappeared, mun zaci karatun ka tafi, har gidanku muka je amma akace baka nan wai kayi tafiya, ko a waya ba a samunka gaba É—aya ko ta social media ba a ganinka"

Sadik yace "ya ma za'ayi in tafi karatu baku sani ba, kuma ma ai Jarrabawar ta mu ba ta fito ba"

"Ahh ta fito almost two weeks ago fa"

"Haba dai, bani da labari ne sam, ya school É—in?"

"School Lafiya ƙalau, wai dan Allah ina ka tafi ne haka?"

"Wallahi ina wani useless village ne"

"Village as how? Babban yaro me kake a ƙauye kuma for whole this long?"

"Kai bari kawai, daga zuwa garin nan dubiya Granny ya hanani tafiya, gaba É—aya a takure nake, na rasa abunda yake min daÉ—i, sam bana jin daÉ—in garin nan, ji nake kamar ma bani da lafiya, kamar me jinya haka nake jina"

"Amma kai kana me ka bari aka barka a ƙauye kamar ba Prince ba, sekace wani ɗan yaye kaine ma ka yadda"

"Haba Amin, ka san da hankalina ba zan bari in zaunaa ƙauye ba, anfi ƙarfina ne kawai ba yadda zanyi, amma very soon insha Allah zan dawo, na kusa tafiya karatu"

"Wow, ai gara ka dawo É—in, haba a É—anyi chilling before you leave the country, kai kaga wasu zafafan babies da aka kawo makarantar nan, kai Makaranta fa ana ta yi ba kai"

Sadik yace "ai koma ina nan bani ɗin za'ai, tunda barin ƙasar zanyi"

"Duk da haka school É—in babu daÉ—i ba ka nan wallahi"

"Please my regards to all, insha Allah kan in tafi zan shigo school É—in"

"To shikenan, ba ka tambayi ya beb É—in ta ka ba?"

Sadik be tsaya sauraron me Amin É—in ke faÉ—a ba, ya katse kiran wayar. Tare da sakin ajiyar zuciya a jejjere.

Farhan dai gaba É—aya ta rasa nustuwar ta, a makaranta ma kiran Sadik ta dinga yi a waya, amma idan ya duba se ya manta lambar waye, kawai se yai ignoring É—in kiran, ya cigaba da sabgogin gabansa.

A gida Sadik ya saba masu aiki ne ke gyara musu É—aki, wasu lokutan dan sangarta ko Abinci suka ci a gurin suke barin kwano, sedai a zo a kwashe, a gyara gurin amma yanzu shi yake fitar da kwanon da yaci Abinci da gyaran É—aki.

Gashi wataran yana tsaka da hutawa, za'a taso shi a haÉ—ashi da dogarai suyi sharar burgarr dawaki, tun yana toshe hanci kamar ze amai saboda warin kashin dawaki har ya saba.

Yanzu ma Har ya koma ɗakin da yake, ya kalli ɗakin kusan kwana uku be share ɗakin ba, duk da ɗakin ba wani datti yai ba amma se yaji duk ƙyamar ɗakin yake.

Ya É—akko kwanukan da yaci tun Abincin safe, da na rana ya fito da su, Nana na zaune tana wanke Wanke, yazo ya zube mata, dan kusan ta ma gama wanke wanken sannan ya kawo.

Sheƙeƙe ta kalleshi tace "wannan wane irin wulaƙanci ne haka? Dan me ba zaka fito da kwanukan tun da Girma da Arziki ba, se sun gama bushewa, kuma kana kallon na gama Wanke wanken sannan zaka kawo min"

Maimakon ya bata amsa yace "in kin gama, ki sharen É—akina"
Chapter 35 · 0% Book details