Sashe 79
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shhhhhh, ki dena wannan maganar dan Allah, keep it aside, ina sonki Farhan dan Allah ki bani dama na Aureki"
Noƙe kafaɗa tai irin na yara tana sake tura bakinta gaba.
"Ikon Allah, is all this for me? Ni in ki na hakan nan burgeni kike"
Take jikinta yai sanyi, haka Sadik ma yake mata, yai ta cewa tana shagwaɓa, wadda ba ta san ta na yi ba.
"To munafukin Allah ta'ala, ka zo duhu zaka cigaba da lalube min mata, wanda kai a baya be isheka ba, to wallahi babu me mallakarta tunda ban mallaketa ba" Sunusi ne tsaye akan su Farhan yana Wannan banbamin.
Wani irin ɓacin rai ne ya baibaye Farhan, ta rasa yadda za tai tai maganin wannan katsalan dan da yake mata a cikin rayuwarta, ya hanata sakat duk wani motsinta akan idonsa, kuma se ya san yadda yai ya ci mutuncin ta.
Abbas yace "dan Allah, kai kuwa me mu kai maka haka? Allah be yi ka Aureta ba, kuma seka dinga masifa wani baze Aureta ba?"
Sunusi yace "ai wallahi yadda ban Aureta ba babu me Aurenta, in kaga wani ya Aureta se dai in bana raye, sedai ta ƙare rayuwarta a karuwanci amma ba dai tai Aure ba"
"To Sunusi dan ban Aure ba se me, da dai in Auri sakarai irinka gara ban Auren ba, ka cigaba da min shishshsigi a cikin lamurana, zan sa ai min maganinka banza kawai"
Sunusi ya gama banbamin masifarsa yai gaba.
Abbas ya girgiza kai yace "dan Allah Farhan, duk sanda ya zo yana wannan abun ki dena kula shi, kuma kiyi ta addu'a, kar bakin nan da yake miki tai taisiri a kanki"
Cikin rawar murya Farhan tace "tasiri kuma na nawa? Bayan yadda ya dinga aibata ni da bakinsa tun a baya yana ɓatamin suna, na bar shi da Allah kawai, ka gaida gida se da safe" daga haka ta juya gida tana zubar da hawaye.
Ba zato ba tsammani taji Umma ta shigo É—akinta, ta zauna a gefen katifar Farhan tace "har ya tafi ne?"
Idon Farhan duka hawaye ta kalli Farhan tace "lafiya kuwa?"
Farhan tace "lafiya ƙalau"
"Amma kike kuka?" "Umma bakomai fa"
"Shikenan, nace to ya batun Abbas É—in, shi kina son nasa?"
"Umma nifa ba zan yi Aure ba"
"Saboda me?"
"Na ɗau darasi a Soyayyar RUƊIN ƘURUCIYA, sannan ga abunda ya faru da rayuwata Yanzu, gara in rayuwata kawai nika ɗai"
"Yanzu kin zaɓi ki cigaba da yawo, Shekarunki ba sj kai sun kawo ba, amma kalli yadda kika maida kanki, Auren shine rufin Asirinki ai"
Tsurawa Umma ido Farhan tai, a hankali ta matsa kusa da Umma, ta kwanta a jikin Umman, ta maƙalƙaleta kamar wani ze ƙwaceta sanann cikin hawaye tace "wannan nake buƙata Umma, idan da wannan ba na buƙatar wani namiji ya kuma shigowa rayuwata, kulawarki da addu'arki, dan Allah Umma ki dinga sona kamar yadda ake son kowane ɗa, ki dena tsanata dan Allah ina sonki sosai Ummana amma kin ƙi bani damar more Soyayyar uwata" tausayin Farhan ya mamaye zuciyar Umman, a hankali ta rungume Farhan ɗin, tai shiru tana jin yadda Farhan ɗin ke kuka cike da ajiyar zuciya.
Ya zubawa Nana ido da cikinta da ya fito sosai, ta ƙara ƙiba ga wani shape da tai, wani ɗan gajeren wando ne a jikinta da half vest, hakan ya sake bawa cikin nata damar fitowa ras.
Se shirya musu kaya take a cikin akwati, cike da farinciki, se ta É—ago riga tace "Friend kalli, ni ina ga base mun tafi da wannan ba, ta dena shiga ta, kalli wannan wandon ma, duk son da nake masa, amma sedai kawai in ajiye ba ze shigeni ba"
Ta kalli Sadik taga yadda yai zuruuu da ido yana kallonta.
"Tunanin me kake ne?"
"Mhmm, bakomai naga bakinki yaƙi rufuwa ne"
Nana ta ɗan yi fari da ido tace "ta yaya bakina ma ze rufu, zan koma in ga Innata da Hakimina tsoho me ran ƙarfe, idan muka koma Nigeria ni da ƙasar nan se da ziyara"
Ya kalleta yace "saboda me?"
Ta É—an yatsuna fuska tace "to idan na haihu da É—an zan taho?"
"Eh, da shi zamu taho"
"Kuma se in dinga zuwa da shi Makaranta? Gaskiya ni ba zan dawo ba"
Yace "ashe kuwa zaki zauna, ba tare da kin koma gida ba" É—an haÉ—e rai tai ba tare da ta kuma cewa komai ba.
Murna a gurin Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna da farinciki, yau ita ce za ta koma gida Nigeria, bayan shafe shekara guda da watanni ba tare da taje ƙasar tata ta haihuwa ba, seda sukaje gidan Steve su kai masa sallama, shine ya kaisu har airport, suka hau jirgi.
Nana kam murna take tana lissafa kala kalar Abincin da za ta ci wanda tai missing, Sadik jinta kawai yake, amma tunanin artabun da za suyi da Mother kawai yake.
Gefe guda kuma yana jin, wannan abun da yake damun zuciyarsa, wanda ya rasa ko menene, se Alla Alla yake su sauka ko Allah ze temake shi ya tuna wannan abu da yake damun zuciyarsa.
Abba da Dr. Tuni suna airport, suna jiran saukar su Sadik, tun daga nesa Sadik ya taka da gudu yaje ya runume Abba yana Abbana i miss You.
"I miss You too my lovely Auta"
Usman yace "ji sha sha sha, se kuma ka bar mata dakon Akwatunan"
Nana ta ƙaraso tace "gaskiya Akwatunan nan sun min nauyi, da wanne zan ji"
Ta kalli Abba ta durƙusa har ƙasa tana gaishe shi.
'Abba yace Masha Allah, Mamana kinga yadda kika koma kuwa, Alhamdilillah ya karatu?"
"Lafy ƙalau Abba, Uncle Usman ina wuni"
"Lafy ƙalau ya school"
Tace "School Alhamdilillah"
Sadik yace "Abba ina Mother?"
Abba yace "tana can tana ta shirin tarbar ku" haka suka rankaya zuwa gida baki É—aya.
Mother na jin ƙarar mota ta fito harabar gidan cikin hanzari, Khairat ta biyo bayanta tare da Jidda matar dr.
Sadik da Mother suka rungume juna, cike kewar juna tana cewa "I miss You Autana"
Nana kuwa se bin su take da kallo gwanin sha'awa tana murmushi.
Cikin rawar jiki Nana take gaida Mother, amma Mother ta amsa a wulaƙance, Sadik ne kawa ya lura da abunda Mother yai, ya basar bece komai ba.
Jidda ta rungume Nana tana faɗin "Masha Allah, Nana kinga yadda kika ƙara girma kuwa, lallai Sadik ya iya kiwo"
Nana ba abunda take se yaƙe, dan ta san ba zasu samu jituwa da Mother ba, ta dinga fatan Allah ya sa a yau ba se gobe ba a maida ita ƙauye gurin Inna.
Ma'aikatan gidan kansu se barka da dawowa sukewa Sadik.
Suka rankaya zuwa cikin gida gaba É—aya, Mother kamar ta maida Sadik cikinta saboda murna, Khairat ma se wani shishshsigi ta kewa Sadik, sedai ta lura Sadik É—in yanzu ba irin na da bane, se wani basarwa yake yana kamewa.
Suka gabatar da sallar la'asar, jikin Nana duk yai mata tsami, gashi ta kasa sakewa, ƙafafunta duk sun kukkumbura se sake duƙunƙunewa take ciki doguwar rigarta me haɗe da hijjabi, saboda kar a ga cikin nan.
Aka baje kayan Abinci, fried rice ya sha kayan lambu se ƙamshi take, ga nama nan ya sha kayan ƙamshi da lemuka, duk saboda Dawowar Sadik, sedai fuskar Nana kawai Sadik ya kalla ya san ba tai na'am da wannan Abincin ba ba lallai ta ci.
Ta dinga zuba zoɓo tana sha, amma ta ƙi cin Abinci.
Sadik se kallonta yake gashi ba ya son yai wani abu da ze sa Mother, ta fuskanci wani abu a tsakanin su.
Jidda tace 'Nana ki ci Abincin mana, naga se juya spoon kike"
Sadik ya wani maze, Nana tace "ina ci fa Anty Jidda"
Jidda tace "kunya dai kike ji, ko a kai miki É—aki ki ci?"
Abba yace "waye baƙonta a nan dan ƙaniyarta, ki zage ki ci Abinci Mamana"
Nana kawai tai murmushi tana sunkuyar da kai.
Yayin da Mother se wurga mata uwar harara, Sadik ya faki idon Mother yaiwa Nana alamar ta ci Abincin.
Amma ta tura baki tana yatsuna fuska.
Ta É—au spoon É—in ta fara cin abincin, se dai sam ba ta ji dadin Abincin ba, ji tai ma yana taso mata.
Nana ta miƙe tace "bari inje ɗaki"
Duk da rashin magana na Usman amma seds ya magantu yace "kamar a takure take ne, anya Sadik ba wani abun kake mata a can ba naga kamar duk a takure take"
Sadik ya ɗan ɗage kafaɗa cike da basarwa, ya cigaba da cin Abincin sa ƙasan zuciyarsa kuwa so yake ya bita, yasan tana jin yunwa Sosai, kuma tunda ta ƙi cin Abincin be mata ba, da suna can ma haka take yi, in Abinci be mata ba ba zata ci ba.
Nana kuwa se da ta amayar da Abincin da ta taci tas, sannan ta samu katifa tai kwanciyarta.
Aka gama cin Abinci aka zauna hira, Mother tana gayawa Sadik yadda tai missing É—in sa, har kusan sallar magariba ana zaune ana hira, yayin da hankalinsa yana kan Nana.
Se da aka tashi, za'ai salla sannan Abba yace "wai ina uwata ne?"
Jidda tace "tun ɗazu ta tafi ɗaki, wataƙila gajiya ce tai mata yawa"
Sadik se wani basarwa yake irin be damu ba É—in nan, amma a ransa kamar yai layar zana ya tafi gurin matarsa.
Bayan sallar magariba, Jidda da mijinta suka shirya tafiya gida, Jidda ta leƙa ɗakin da Nana take, ta hango ta sanye da Hijjabi, alamar Salla ta idar.
Tace "Amarya, mu mun tafi Allah huta gajiya"
Nana tace "Anty Jidda tun Yanzu zaku tafi?"
"Eh mana, naga kin zo kin ƙule a ɗaki ke kaɗai"
Nana ta ɗan ɓata fuska tace "wallahi duk na gaji ne Anty Jidda"
"Eyya sannu, gara da kika huta ai, seda safe"
Nana tace "to Allah ya tashe mu lafy, ku gaida gida"
Sadik ya faki idon Mother ta shiga sashin Abba, ya nufi É—akin da Nana suka saba zama, in sun zo gidan.
Ya tarar da ita kwance akan sallaya, ya ƙarasa ds sauri yace "lafiyar ki kuwa?"
Ta kwaɓe fuska tace "yunwa nake ji, kuma wallahi se juyawa cikin yake ya hanani sakat"