Sashe 48
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amin na shiga class É—in Nas ya fara murmushi yace "kai baba yane? Ko kai zaka maye gurbin Prince ne?"
Amin yace "kai bari Nas, Yarinyar nan tausayi take bani, ba ƙaramin so take wa Sadik ba, wai ashe more than a month, ba suyi ko waya ba shine ta zo tana leƙo ajin nan"
Nas yace "to shine me?, Dama wannan har wata Soyayya ce, ɓata lokaci ne kawai, soyayyar Makaranta ai shirme ce"
Amin yace "ba kowace Soyayya ce shirme ba, har kuka take wallahi, ta bani tausayi sosai"
"To kai meye naka a ciki, ya manta da ita, maybe yayi wata ne, mu da ya sanmu kafin ta, muma ai ba nemanmu yake ba, tun da mukaje gidan su akace baya nan"
"Ai ni ka san munyi waya, yace min yana ƙauye, gurin kakanninsa, amma insha Allah zanje gidansu in ji abunda ake ciki, ko dan Yarinyar nan"
Nas yace "ai se kayi"
Kamar an jefota haka Nazir ya ga Lilly a office É—in sa, yace "lafiya?"
"Dole ka tambaye ni lafiya mana, haba Nazir ya kake so in yi ne? Ka ƙi zuwa gurin mahaifina so kake yai fushi da ni ne?"
"Lilly ba haka bane, wallahi tsoro nake ji"
"Au tsoro kake ji ko?"
"Wallahi abunda ya hanani zuwa kenan, ban san ya ze krɓe ni ba"
"Nazir in kaga dama, yau da daddare kaje, dan na ce masa yau zaka zo, idan kuma ba haka ba shikenan shi ze zo ya sameka"
A gigice yace "ai ba za'ai haka ba ma, zan zo insha Allah yau É—in nan ba se gobe ba"
Tai ajiyar zuciya tace "da ka temaki kan ka" ta jiya ta fice.
Dafe kansa yai yace "wannan wane irin bala'i ne? Wace irin masifa na jefa kaina a ciki haka?"
Farhan har ba ta son a tashi daga Makaranta ta koma gida, saboda ba ta san abunda zata tarar a gidan ba, gaba É—aya ta kuma susucewa ta zama wata iri kamar mara jini a jika.
A daren Nazir ya shirya ya tafi gidansu Lilly, cike da Zullumi da tsoron abunda ze tarar, dan tun a gate aka tare shi, aka kira baban Lilly, yace a kai masa shi guest room É—in sa.
Yana nan a zaune yana tsuma, yana rarraba ido, Daddyn Farhan ya shigo ɗakin, seda kayan cikin sir Nazir suka juya.
Ganin baban Farhan, babban mutum me cike da siffar ƙarfi da kwarjini, dan da hannu ɗaya ze iya sama da sir Nazir.
Ya nemi guri ya zauna ya kalli Nazir, sir Nazir cikin rawar jiki yace "barka da yamma ranka ya daÉ—e"
"Kai ne corper É—in da kake son Lilly?"
"Eh nine"
"Meye sana'arka, sannan kuma É—an waye kai?"
"Sunana Nazir, ni É—an Jigawa ne, na kammala degree na ne nai service a Kano, yanzu ina aiki da wata private school ne, kafiiin samu aiki"
"Kaine kake hure mata kunne kenan, kar tai karatu tace aure take so ko?"
"A'a ranka y...
"Shut up! Ƙarya tani za kai kenan? Kana hure mata kunne, yarinyar guda nawa take, me ta sani a Auren da zata ce ba ta son karatu se Aure? Ba dan na ganka a kamile da siffar mutunci ba, da sena sojoji sun ragaragaza min kai, an casa min kai aje a watsar da banza, kai kalli rigar jikinka ma kawai, har kana da ƙwarin gwiwar da zaka tunkari 'ya ta kace ka na so? Ba ma wannan ba da ma ta kai munzalin auren ne, na nema maka abunyi in aura maka ita, amma 'yar mitsitsiyar yarinya kamar wannan har ta samu ƙwarin gwiwar cewa Aure take so, ai daga jin wannan batu ka san zigata ake"
Ya kalli wani Soja yace "kiramin Lillyn dan ubanta"
Cikin ƙanƙanin lokaci, se ga Lilly, dan ba ta ma son Nazir ɗin ya zo ba.
"Daddy gani"
"Ke yanzu dama wannan ne ke hure miki kunne, kike cewa ba zaki karatu ba aure kike so? To ki buÉ—e kunnenki da kyau ki saurareni, ba ke ba wannan mutumin, ke da Aure sekin kammala degree, dama na kirashi ne dan in ga ko mutumin banza ne, in sa a koya masa hankali, amma se na ganshi a kamile dan haka bake ba shi kaima ba kai ba 'ya ta, idan ba haka ba i will show you what am capable of doing, tashi ka ban guri mutumin banza kawai"
Jiki a sanyaye sir Nazir ya miƙe ya nufi hanyar fita, yaji zafin abunda baban Lillyn yai masa, kuma se yaji ba daɗi hana shi Lillyn da babanta yayi.
"Ke kuma wuce ki koma ciki, sakarya kin bi ƙyal ƙyal banza kin bi kyau, kalli sosasshen yadin jikinsa, har kina gayamin Aure kike so, get inside before I slap you, hopeless kid"
Da gudu Lilly ta shige tana kuka, bata taɓa zaton Daddyn ta ze disappointing ɗinta ba, ta ɗauka dagaske ze mata Aure kamar yadda ta buƙata, amma yaci zarafin Nazir haka.
Nana kam ta kasa dena kuka, har a kai lesson ɗin ranar ba ta fahimci komai ba, ɗakin da aka kaita ita da wata yarinya ne, su biyu ne a ɗakin, komai akwai a cikin ɗakin nan na buƙata, Nana ba ta komai se dai tai wanka tai salla, idan tana salla se Yarinyar tai ta kallonta.
Idan yarinyar taiwa Nana Magana, sedai tabi Yarinyar da ido, dan ba ta fahimtar abunda Yarinyar ke cewa, gashi tana son tayiwa Nanan Magana, amma Nana ba ta kulata, wani abun tana jin abunda yarinyar ke faɗa kaɗan kaɗan amma ba zata iya mayarwa ba, se in ta gaji ta ƙarewa Yarinyar zagi da hausa 😂.
Washegari Abba ya koma Nigeria, Sadik ma ya tafi tasa makarantar, sedai a hostel yake shi, Sadik be sha wata wahala ba, dan ya saba zuwa ƙasashen waje, kuma ya iya turanci sosai, nan da nan ya fara mantawa da halin damuwa da yake ciki da haushin Auren da a kai masa, sedai in sunyi waya da Mother ne yake tuna yana da Aure, dan kullum sun kai waya cikin kashedi take masa akan Nana.
Farhan taji sauƙi, sedai jiki kam babu ƙwari, se idanuwa a cikin fuskarta, duk tayi fayau, saboda kuka da damuwa, bacci dama sedai in ɓarawo ya ɗauketa, Amma kullum cikin tunani take.
Farhan na kwance a ɗaki, tana matsar ƙwalla, tana tunanin anya zancen Abbas ba gaskiya bane da yace ta manta da Sadik ba, ya barta.
Abba ta jiyo a tsakar gida yana gayawa Umma, wai sun haɗu a gidan su Huzaifa an karɓi kuɗin Aurenta daga gurin iyayen Sunusi Naira dubu Ashirin da biyar, sunce sun saka watanni biyar!
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank
07063065680
KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Wani makirin kallo Sunusi ya bi Farhan da shi, amma tai kamar ba ta ganshi ba, ta miƙe ta fara tafiyarta.
"Ke, saboda tsabar baki da mutunci, ba ki da ta ido wato har yanzu baki fasa bin maza a mota ba ko? Kuma dan wulaƙanci in ganki amma ki nuna ko a jikinki, kamar baki ganni ba?"
"Idan har zan bi maza ban ji kunyar Ubangiji ba, kai waye da dan na ganka zanji tsoro? So kai in zura da gudu ko kuma in yi yaya?"
A fusace Sunusi yace "wallahi tirr da halinki, kuma sena gayawa mahaifinki yawon fasiƙanci kike, ko da yake na sha gaya masa amma banga wani mataki da yake ɗauka akan ki ba, idan tsoron ki suke ji ba zasu iya tsawatar miki ba, ni dai dai nake da ke, kwaɗayayyiya kawai"
Kalmar fasiƙa da ya gaya mata ta doki ranta fiye da kima, take taji jikinta har wani rawa yake ta kalli Sunusi tace "Allah ya karɓa min hakkina na sharri da kai min" nan da nan se hawaye.
Abbas ya fito daga mota, ya nufo in da suke da sauri yana faÉ—in "lafiya kuwa, meke faruwa ne?"
Sunusi na ganinsa ya gane shi yce "to munafukin Allah, dama ba tun yau naga alamun watsewa ku ke ba, shine da iskanci ka É—akko ta a mota, tana matsayin matar Aure"
Se yanzu Abbas ya gane shi, ya kalli in da Farhan ke tsaye tana kuka yace "Farhan waye kuma wannan?"
"Shine zaɓin iyayena, wai shi suke da burin su aura min, yana nuna musu shi na Allah ne amma kullum yana jifana da miyagun furuci, na barka da Allah"
Ta juya da sauri ta nufi ta nufi hanyar gidansu.
Ƙarewa Sunusi kallo Abbas yayi, tun da ga sama har zuwa ƙasa, ya kalli kayan jikin Sunusi kamar ɗan gudun hijira, be ga in da Sunusi ya dace da Farhan ba.
Sunusi yace "ƙaremin kallo da kyau, nine zan Aureta mata ta ce"
Baƙin ciki ya hana Abbas magana, se shiga cikin gidan Hajiya da yai a fusace.
Hajiya tana zaune tana kallon Sunna TV, taga Abbas ya faÉ—o ba ko sallama.
"Kai ya haka kai da wa kake wannan hucin?"
Be iya magana ba se cigaba da gwagwagwama numfashi da yake, se da ya sakko dan kan sa sannan yace "wai dama dagaske kike Aure za'aiwa Farhan?"
"Dan ƙaniyarka na saba yi maka ƙarya ne? Meyafaru to?"
"Na zaci wani mutumin kirki za a aura, ashe wani sakaran yaro ne da nake gani a layin nan, kwanaki yaje Asibiti duba ta, yau a wajen makarantar su na ganota, muka taho tare Shine ya tare ta yana mata masifa"
Hajiya ta zare glashin fuskarta tace "Ya salam, gaskiya nima nayi mitar haɗa Aurenta da wannan yaron, Yarinyar ba ajinsa bace sam, duk da shi mutum ba abun ƙyama bane, kuma arziki na Allah ne, amma kyakykyawar yarinya me nutsuwa kamarta, wallahi da gidan hutu ta dace"
Tsaki Abbas yai yace "Ni wallahi ji nake kamar in kai iyayenta ƙara human rights"
Buɗe baki Hajiya tai tace "kai ka kiyayeni, akan me zaka kai su ƙara su da 'yar su, su suka san me suka gani suke yanke mata wannan hukuncin"