← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 115

Sashe 85

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe Abbas yaje har gida yai sallama da Abba, suka gaisa yai masa bayanin mai da Farhan Makaranta da yayi, Abba ya nuna farincikinsa amma yace "ka dena zura jiki gurin ɗawainiya da Yarinyar nan, kasan haryanzu tana ƙasa tana dabo ne, ba ta amsa cewar za ta Aureka ba, kuma kaga haryanzu ba ta dena yawace yawacen da take ba, ka dena ɓarmar kuɗinka akanta"

Abbas yace "bakomai Abba, ko ban Auri Farhan ba, idan Allah yasa ta dena shaye shaye, ta cigaba da karatunta, anci riba sosai, a cigaba da yi mata Addu'a , Allah ya sa ta tsaya tai karatun"

Abba yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, Allah yai maka albarka"

Abba yana shiga gida ya tarar Farhan, ta shirya cikin dogon hijjabi, yai mata nasiha da Addu'oi Sannan ta fita.

Har makarantar Abbas ya kaita, ya danƙata a hannun shugabar makarantar, wadda kusan 'yar uwace gareshi, dan haka tun kan ya kai Farhan yai mata bayanin Komai.

Ta karɓi Farhan hannu bibbiyu, a kai mata interview ta jinjina kaifin ƙwaƙwalwa irin na Farhan tace za ta kaita ss2 kawai.

Abbas ya ja mata kunne akan in an tashi ta jira ze zo ya É—auketa ta amsa masa da to, sedai tun bayan kaita aji an mata jumping É—in Class É—aya, ta tuna romon bakan da Sadik ya dinga yi mata, yai jumping É—in Class É—aya shima, saboda ya gama Makaranta ya Aureta, aikuwa maimakon ta maida hankali akan karatu, se kuka haka taita kuka har aka tashi.

Sadik yaji daɗi da ya zamana Nana ba zata tafi ƙauye tai Arba'in ba, ko ba komai jaririnsa ba ze yi nisa da shi ba, dan da sedai ya bisu ayi Arba'in ɗin tare da shi, ko Mother ba ya yiwa kara akan Sahal, wanda yake kira da Junior papa, ko yace masa J papa, kowa so yake ya ɗauke shi, tun yana koke koke har ya saba da jagwalgwalon hannun mutane.

Sadik suka haÉ—u da Abba a masallaci gurin sallar isha'i, akan hanyar su ta dawowa Abba yake cewa Sadik "yaushe zaka koma Makaranta ne? Na san kun kusa cigaba da lectures"

Sadik yace "Abba ni dai a nemo min transfer, in cigaba da karatuna a Nigeria"

"Saboda me?"

Sadik yace "Abba ka ga baze yuwu in tafi da su Nana ba, a ina zamu dinga barin Sahal in zamu tafi school? Kuma ba na son ya tashi a tsakanin masu raino ne"

Abba yace "hakane, shikenan zan duba in ga me yakamata ayi, amma dai gara ka koma É—in" haka suka cigaba da hira har zuwa gida.

Suka haÉ—u da Faruk, Faruk ya dinga yiwa Sadik mitar yayi É—a ya dena kwanan quarters wai shi me mata, Sadik yai ta murmushi yace "yes call me abu Sahal, wo ni Daddy da ya fara magana zaka ji yana cewa Daddy ina yes my boy"

Faruk yace "eh kuma kai ma a gabansa za'a dinga kiranka boy ba, ana ce mak Autax

Sadik yace "naji bakomai" haka suka cigaba da zolayar juna.

Sadik ya wuce É—akinsa, yai wanka ya canza kaya, yana son ya fita ya ci Abinci ya je ya ga Nana, ya janyo wata drower, se ga System É—in sa da yake amfani da ita a Nijeriya, dama be tafi da ita ba a nan ya barta.

Ya sa hannu ya ɗakkota, sedai yana ɗakkota kansa ya sara, gabansa ya faɗi take bugun zuciyarsa ya ƙaru.
Maida system É—in yai ya ajiye, ya tashi yana layi, ya nufi sashin da Nana take, yai sa'a ba kowa tana zaune tan kallo a É—akinta.

Zuwa yai ya zube akan cinyarta yana kokawa da numfashi.

A rikice tace "Subhanallah besty menene?"

Ya kamo hannunta ya ɗora akan ƙirjinsa saitin zuciyarsa.

Tai ajiyar zuciya tace "Anya kuwa kana Azkar, bana saka a gaba muyi tare ka dena ko?"

Shiru yai bece komai ba, a hankali ta fara karanto masa duk Addu'ar da ta zo bakinta, sun kai mintun ashirin a haka, ta tsinkaye shi yana ajiyar zuciya alamar yayi bacci.

Inna ce ta shigo ta samesu, Inna tace "Au har ya fara lallaɓowa yana zagayowa, har kin mata wahalar naƙudar kenan, kin shirya yin wata?"

Nana tai mata alamar tai shiru bacci yake, nan ta kwashe komai ta gayawa Inna, yadda yake shiga wannan yanayin tun suna London.

Inna tace "iyayensa ne 'yan boko, yanzu da kace wani abu se su ce su ba haka ba, ba se a zuba musu ido ba"

Nana ta marairaice tace "Inna, kar abi ta tasu, dan Allah ai waya ƙauye, ko in kin koma a dinga yi masa saukar Alqur'ani, da ya fara idan nai masa Addu'a se yai bacci"

Inna tace "to Allah ya kyauta, ba shi kaÉ—ai ba ma, dukkanin ku yakamata ai muku dan neman tsari da kariya daga miyagu, kana da ido bana ganin gari ba".

Kwanci tashi asarar rai, Nana ta kwan Arba'in cif da haihuwa, Sadik kam kwana Arba'in É—in nan kuwa a takure yayi ta, dan Inna ta kasa ta tsare, ko É—an shishshsigi ta ga yana yiwa Nana, se ta fara yi masa kwakwazo a cikin mutane, ta kunyata shi.

Anyi shirin tafiyar su Nana ƙauye, se murna take zata yawon Arba'in, dan a ƙalla za tai sati biyu a ƙauye ta ɗan sake ta huta sosai.

Sega Mother da yin rakiya har bakin mota, kamar tace su tafi su a bar mata Sahal, Inna kallon Mother kawai take tana girgiza kai, hadda Sadik za'aje kai su Nana ƙauye, ji yake kamar yace a bar masa ɗan sa a gida.

Se da su ka kai su Nana har can, Hakimi kamar ya maida Sahal cikinsa dan murna, yai ta masa Addu'a da shi da iyayensa. Hakimiya kalli Abba yace "yanzu ka gane dalilin da yasa mu kaiwa ɗanka Aure? Ba muyi dan muna ƙin sa ba, amma ka sani da ba'ai masa Airen nan ba idan lokacin zuwan ɗan nan duniya yai, ko kuna so ko ba kwa so ta halak ko ta haram, se ya zo duniya, zaman Sadik a gidan kawai na ga abubuwa da dama da ku da kuka daɗe da shi ba ku lura ba, ina fatan Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarsu baki ɗaya" Abba ya amsa da Ameen.

Sadik kuwa yana can yana sallama da Nana yana mita "ina Alla Alla ki Arba'in É—in nan, mu koma ruwa, kuma kinyi Arba'in an wani ce se kin zo nan kin yi sati biyu haka akeyi?"

Nana tace "kai da wa zaku koma ruwan? Ai ni kuwa da É—in hakan naji yaseen"

Harararta yai yace "zaki bayani idan nace a nan zan zauna, Allah sarki J papa na ze missing É—ina na san"

Nan tace "To ka tafi da shi mana na huta nima"

"Dan dai babu abun ba shi ne, da da shi zan tafi, ko ki tara masa bokiti bokiti in yai kuka a dinga ba shi"

Nana tace "eh tun da ga Nonon saniya ko?"

Dariya ya dinga yi yace "ba ruwana bani na faÉ—a ba, ke kika faÉ—a da bakinki"

Tace "Ali shike nan, dan Allah ka kular min da kanka kaji Besty, ka dinga Azkar yadda yakamata, Tun kan mu taho Inna ta sa ana mana saukar Alqur'ani, Allah ya ye maka damuwar ka, kuma ina ta maka Addu'a"

Yai murmushi yace "Allah yai miki Albarka, insha Allah zan kula Sosai, let me kiss you am missing you"

Murmushi Nana tai, jin takun Inna da maganarta ne ya sa shi cika Nana, ya fita daga É—akin da sauri, yana jin yadda yake kewar ta Sosai.

Su kai musu sallama suka juya, wanda ba su samu damar zuwa can yi musu barka ba, suka dinga zuwa suna ganin Jaririn Nana, fari sol da shi gashi da cikar suma gwanin sha'awa.

Kwanan su Nana uku da tafiya, Ama Sadik ji yake kamar sun shekara, duk yai kewarsu mussaman É—an jaririnsa, Mother kanta kullum se tai zancen Sahal.
Faruk ma tuni yai shirinsa ya koma in da yake karatu.

Sadik na kwance akan gadonsa, yana kallon musabaƙar Alqur'ani, shi duk irin wannan ba su dame shi ba, a dalilin Nana yake jin wani wa'azi da sauran su.

Ɗauke wuta a kai, Solar ta kama ya miƙa hannu ya kashe socket ɗin TV, ji yai kamar an yaye masa wani bargo daga kansa.

Kamar an tsikare shi, ya miƙe ya kuma zuwa gaban drower nan, ya ɗakko system ɗin nan ya goge ta, ya jona ta a caji, yana son ya gwada ya ga ko haryanzu tana yi, ya tashi dan ya ɗakko memoryn hotunan sunan Sahal, dan tunda a kai masa copying ɗin sa a jikin memoryn be dub ba, yana cikin dubawa se ga sim cards ɗin sa nan da ya ɗakko a ƙauye.

Ji yai kansa yana sarawa, cikin hanzari ya buÉ—e wayarsa ya zare layukan cikin wayar, ya saka wannan layukan, ya buÉ—e system É—in ya kunnata, kamar me jiran wani abu ya faru haka zuciyarsa tai ta azalzalarsa.

Hoton Farhan ne ya Bayyana a jikin screen ɗin wayar, wanda tun Asali dama hotonta ne a jiki, turus yai yana bin hoton da kallo, wayarsa kuwa wani irin vibrating ta dinga yi, tamkar zatai tsalle sama, saboda Azabar saƙonni da suke shigowa.

Jikinsa ne ya ɗau rawa, ya zubawa screen ɗin ido yana kokawa da zuciyarsa zuwa ƙwaƙwalwarsa akan ya tuna sunanta.

A hankali ya janyo wayarsa dake ta vibrating, ya shiga duba tulin saƙonnin da ke ciki.

"Dan Allah Sadik kai responding in kaga message É—ina, zuciyata tana kewarka, za'a Auramin Sunusi idan ba ka dawo rayuwata ba"

Wani irin jifa yai da wayar, ya ambaci "Farhaaaaaaaaaannn!" Ji yai kamar ya farka daga wani irin nannauyan bacci da ya jima yana yi.

Tashi yai a zabure jikinsa na wata irin tsuma, yai waje ba tare da yasan ina za shi ba!
Kamar wanda ya ga wani abun tsoro, haka Sadik ya fito falo ya nufi hanyar fita, be san ma ina Yakamata yaje ba, kawai tafiya yake, hakan yai daidai da shigowar Usman, ya tunkari Sadik yan faÉ—in "kai lafiya kake kuwa? Meye haka kake yi ne?"
Chapter 85 · 0% Book details