← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 115

Sashe 34

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan noƙe kafaɗa tayi, alamar ba zata tafi ba.

Yace "ai shikenan seki ta zama"

Ya maida idonsa ga tv, yana cigaba da shan juice É—in.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya É—auka tare da yin sallama.

"Wa'alaikum salam Malam Faruku"

Cikin sauri Faruk ya gyara zama yace "ranka ya daÉ—e barka da warhaka"

"Yawwa barka, kuna lafiya?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah"

"Ka manta da mu, tunda kuka tafi ba ka sake zuwa ba"

"Ranka ya daÉ—e ai kai kace karmu sake zuwa, kuma wayarku ba ta shiga, saboda ba network"

"Ƙwarai kuwa anyi haka"

Faruk yace "Ya Sadik É—in yake?"

Hakimi yai murmushi yace "yana lafiya ƙalau, muma sa'a akai wayar ta shiga, tun jiya ake neman layin mahaifinka yaƙi, kaima da kyar naka yayi, amma duk matsalar network ɗin nan ne, muna muna ƙoƙarin ganin yadda za'a shawo kan matsalar"

Faruk yace "Allah sarki, Allah ya temaka ranka ya daÉ—e"

"Ameen ya Allah, nace baban naka yana gari ne?"

"A'a ranka ya daɗe, kwanansa biyar da tafiya kuma ina ga se ƙarshen watan nan ze dawo"

"To shikenan, idan kunyi waya ka gaya masa, lallai lallai idan ya shigo gari ya zo ya sameni a nan"

"Insha Allah zan gaya masa ranka ya daɗe"  Faruk ya so tambayar Hakimi a bashi Sadik su gaisa, amma se yaji nauyin hakan, tunda shi Hakimin be bashi ba, kawai ya ƙyale sukai sallama, ya bawa Hakimi saƙon gaisuwa ga Nana da su Inna.

Harya gama wayar Khairat kallonsa take.

Faruk kam haka nan ya tsargu da kallon da take masa yace "can You excuse me please?"

Seda ta É—an tura baki sannan ta tashi, ta koma cikin gidan, a falo ta samu Mother tana Shan kankana, Mother ta dubeta tace "ya na ganki kina tafiya a hankali menene?"

"Bakomai Mother, yanzu Faruk su kai waya da kakansu"

Da sauri Mother ta ajiye kankanra da ta É—auka take shirin kaiwa bakinta tace "meya ce masa?"

"Na dai ji yace wai yana neman Abba ne, idan Abba ya zo ace yana nemansa"

"Ko dai wani abun ne ya samu Sadik É—in?"

Khairat tace "Anya kuwa? Ni dai banji yace wani abu ya sameshi ba, dan da wani abun ya sameshi baze ce se lokacin da Abba ya dawo Sannan zeje ba"

Mother ta girgiza kai tace "Allah sarki yarona"

"To Mother tunda Abban baya gari, ki shirya mana kije garin da kanki, ki É—akko shi"

Mother ta girgiza kai tace "da ze yuwu ai da tuni nayi, zan fuskanci fishi da tashin hankali a gurin babansa idan naje, amma zan zuba musu ido in ga iya gudun ruwansu, fiye da watanni biyu an riƙemin ɗa an hanani ganinsa"

Ta ƙarasa maganar tana jin ƙwallar baƙin ciki.

Abban Farhan yana shirin fita aka shigo a kai sallama da shi, yace yana zuwa.

Yana fita yaga malamin su Sunusi ne, ya tsaya suka gaisa Sannan malamin Yace "to kamar yadda mukai magana da kai, naje garinsu Sunusi na samu mahaifinsa nai masa Magana, yayi murna ƙwarai yayi farinciki da jin hakan, yace a basu lamuni nan da wata guda zasu kawo kuɗin Auren"

Abba yace "Ahha Masha Allah, naji daɗi ƙwarai da gaske, nayi farinciki, ai nan da wata ɗayan kamar yaune a gurin Allah, Allah ya nuna mana ya sa zamu gani"

Ya amsa da "Ameen"

Abba ya nisa yace "Amma ina son idan anyi Auren nan, Farhan ta cigaba da karatun ta, saboda shine babban burinta a rayuwa, duk da shima Sunusin zan masa maganar"

"Eh ai karatu abune ne mahimmanci, mussaman tunda da abunta aka ganta, wannan ma abune me kyau, zan yiwa Sunusin Magana Insha Allah, fatanmu Allah ya tabbatar mana da Alkhairi".

Abba ya amsa da Ameen.

Kusan sati biyu, Sadik be sake shiga harkar Nana ba, duk yadda take takalarsa wasu lokutan ko in da take baya kallo, ga wayoyinsa da ya bata ta kai masa caji, ko sau É—aya be yi mata maganar wayoyin ba, shi mantawa ma yake da waya, kawai dai gashi nan yana rayuwa, se ya dinga jin kansa kamar ba shi ba.

Farhan Kuwa sun koma zangon karatu na biyu, sedai jin makarantar take tamkar maƙabarta, gaba ɗaya ba ta da kuzari, ba abokin hira dama ita ba ƙawaye ne da ita ba, gashi ko a waya ta kasa samun Sadik fiye da wata guda, ga matsaloli sun taru sun mata yawa, hakan harya fara shafar karatunta, ya zamana ko excusing ɗin kanta tayi ta tafi Library karatu, ba ta iyawa, se tai ta kallon gurbin da Sadik yake zama yana tayata karatu.

Tana matuƙar kewarsa, se taji gaba ɗaya ta dena gane karatun, bata iya maida hankali yanzu sam.

Ga 'yan ajinsu lalacewa taci uban ta da, yanzu bayan karance karancen litattafan da suke, har memory suke bayarwa a turo musu abunda be dace ba, banda masu shaye shaye da sauran lalacewa, makarantar se ƙara lalacewa take.
Dama Sir Nazir ne me tsawatarwar, shima kuma Yanzu ya faɗa tarkon RUƊIN ƘURUCIYA, dan haka kowa yake cin karensa babu babbaka.

Bayan ta koma gida, ko Abinci ta kasa ci, duk ta rame tayi wani iri, tana kwance a ɗakin ta da Yamma, Taji Abba yana ƙwala mata kira.

Cikin hanzari ta fito tsakar gidan, ta durƙusa a gabansa.

"Yawwa, É—azu malamin su Sunusi ya zo munyi Magana da shi, yace min in Allah ya yadda watan gobe za su kawo kuÉ—in Aure, dan tun kwanaki mu kai Magana zasu kawo kuÉ—in, amma yau ya tabattar min da watan gobe zasu kawo"

Gaban Farhan ya yanke ya faÉ—i, taji ta dena ganewa na wasu lokuta, ko motsi ta kasa yi a gurin.

Abba yace "ya naga duk kin canza, ko ba kya son Auren ne?"

Za tayi magana ta É—ago ta kalli Abba, se taga yai mata kwarjinin da ba zata iya buÉ—e baki tace masa ai ba ta son Sunusi ba.

Sedai cikin rauni da sanyin halinta tace "Abba karatuna fa?"

Abba yace "karki damu da wannan Farhan, nayi magana da malamin su akan ze barki ki cigaba da karatunki, nayi niyyar Aurar da ke ne saboda wani dalili, amma zaki cigaba da karatun ki insha Allah, tashi kije yadda kike mana biyayya Allah ya baki 'ya'ya masu biyayya kema, Allah ya albarkaci rayuwar ki ya tsare ki daga sharrin lalacewar ƙarshen zamani, Allah yai miki Albarka"

Farhan ta kasa amsawa, sedai ta miƙe akan ƙafafuwanta da take ji kamar an ɗaura musu duwatsu, ta koma ɗakinta.

Zuciyarta ta dinga zafi, hawayen ta suka ƙafe ta kasa kukan se ajiyar zuciya da take tayi.

"Sadik dan Allah ka dawo kar amin Auren nan, na kasa gayawa Abba bana son Auren, Kai nake so Sadik, duk wanda na Aura ba zan iya dena sonka ba"
Tai maganar tana jin yadda zuciyar ta ke ƙuna, ga kuka ya gagareta.

Wunin ranar Farhan ba tayi shi cikin kwanciyar hankali ba, haka da dare yayi shima bacci ya gagareta, dama kwana biyun nan dama baccin ma ba samuwa yake ta daÉ—in rai ba, balle ga wannan batun mafi dunguzuma mata zuciya, ko kusa ba ta ga yadda za ta iya zaman Aure da Sunusi ba, dan zuciyarta na tare da Sadik.

Washegari da safe haka taje makaranta, babu kuzari sam a jikinta, dan har a kai lesson aka gama ba ta fuskanci komai ba, sedai lokaci lokaci ta kanji hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idanunta, amma se ta neme su ta rasa sedai zuciyarta ta cigaba da zafi.

Sam hankalin Farhan ba ya jikinta se da ta jiyo Muryar Yasmeen ta ambaci sunan Prince.

Take hankalin Farhan ya dawo jikinta, ta tattara hankalinta akan Su Yasmin dan jin me zasu ce akan masoyin nata.

Yasmeen tace "Ashe su Prince ana ƙauye, ni Wallahi ban taɓa tunanin gayen nan ze zauna a ƙauye ba"

Mamakine ya kama Farhan, ya a kai Yasmeen ta san Sadik yana ƙauye? Amma ba abun mamaki bani, wataƙila a bakin abokan Sadik na ajinsu taji" wata zuciyar ta bata amsa.

Yasmeen ta cigaba da cewa "gaskiya gidan su Sadik akwai zafafa Allah yai musu kyau masha Allah, kunga wani yayansa me kyau"

Lilly tace "wai ke me ya kaiki gidansu ne?"

Yasmeen tace "ina ruwanki da abunda ya kaini, ni da gidan sirikai na"

Se da Farhan ta É—ago ta kalli in da Yasmeen take, aikuwa Yasmeen ta galla mata harara.

Lilly tace "ba uwar da ta haÉ—aki da su Sadik wai gidan sirikanki"

"Ahaaf kika sani" Yasmeen ta faÉ—a tana murmushi.

Farahan taji jikinta har wani rawa yake, tana Addu'ar Allah yasa ba wani abun ne ya haÉ—a Yasmeen da Sadik ba.

Seda wayar Sadik tai sati uku ba ta tare da shi, gaba É—aya ya rasa meke damunsa, ya rasa tunanin ma meya kamata ya yi.
Gaba É—aya kamar deprssion ke nama ya kama shi.
Ji yai an ajiye masa abu a jikinsa, ya É—aga kai ya kalli Nana, ba ta ce masa komai ba tai waje.

Ya É—aga ya duba me ta ajiye masa, yaga wayoyinsa ne.

Kawai ya bi wayoyin nasa da ido, gaba É—aya wayoyin ma sun fita daga kansa.

Ture wayoyin yai ya kwanta, yana ta ƙoƙarin yai tunani amma ya kasa.

Kusan kwanaki uku da kawo masa wayoyin, sannan ya kunna ƙaramar wayarsa.

Lambar Mother ya shiga dubawa, ya kira yaji ko wayar zata shiga, by luck yaji ta fara ringing, da Sauri ya tashi zaune yana gyara zama.

"Hello Autana"

Ajiyar zuciya yai Sannan yace "Mother kin manta da ni ko?"

"Haba Sadik kai kana tunanin akwai lokacin da ze zo in manta da kai? Kullum kana raina, wayarka ba t shiga nayi kuka harna gaji, babanku ya hanani ko zuwa in ganka ba yadda na iya"

"Shikenan Mother a nan zan cigaba da zama kenan?"

"A'a ya ma za'a ce a nan zaka cigaba da zama, ai anyi wa Faruk waya ance ana neman babanku a nan gidan"

Sadik ya ɗan taɓe baki yace "ni ban ma sani ba, Allah yasa idan ya zo ya tafi dani, Mother na gaji am tired wallahi"
Chapter 34 · 0% Book details