← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 115

Sashe 38

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gurguje taje ta karɓo saƙon nan, tana tafe tana haɗawa da Sauri, saboda ta koma dan hankalinta yaƙi kwanciya sam.

Sedai me tana shawowa kwanar gidan, ta tarar da cincirindon mutane a gurin, sunyi cirko cirko, duk da juma'a ce anyi sallar juma'a amma yanayin yadda taga mutanen hankalimta ya sake tashi.

Nan take gabanta yai mummunar faÉ—uwa, jikinta ya É—au rawa numfashinta ya shiga barazanar tsayawa.

Da gudu ta nufi gidan tana ture mutane, hawaye na bin fuskarta.

(RIP ALHAJI ALIYU MAMMAN RANO (HAKIMI)

Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.
Littafin nan ₦300 ne kacal.
0009450228
Aisha Adam
Jaiz Bank

07063065680

KO kuje manhajar AREWA BOOKS ku siya. domin kuwa ya fi sauƙi ta can.

Kutsawa kawai Nana take tana kuka, yayin da dandazon mutanen ke binta da kallo, kamar wadda ta zare.

Da gudu ta kutsa ta shiga, sedai tai turus saboda kasa banbance Alhini mutanen ke yi ko kuma farinciki.

Turakar Hakimi ta nufa, ta shiga da sauri.

Hango shi tai a zaune, ya sha fararen kaya da naÉ—i, sedai kana ganinsa ka san yana jin jiki ne.

Runhumeshi taje tayi tana kuka tana faɗin Alhamdilillah, Ka ji sauƙi? Ka warke?"

Yayi tari yace "Da sauƙi Alhamdilillah" ajiyar zuciya ta dinga saukewa, ta ɗaga kai ta kalli jama'ar da ke ɗakin.
Se a yanzu ta kula da Abba, da Faruk a zaune, gefe ga Inna se Sadik dake zaune, idonsa yai ja kamar garwashi.

Se da gabanta yai mummunar faÉ—uwa ganin idanun Sadik É—in, kamar ba idon bil adama ba.

Wani  irin matsiyacin kallo Sadik yaiwa Nana, wanda ya hadda sa mata ƙullewar ciki saboda razana.

Cikin ƙullewar kai Nana tace "Inna wai me ake a gidan nan?"

Inna tace "ba zaki gaida baban naki bane"

Jiki a sanyaye Nana ta kalli Abba tace "Ina kwana"

Jiki ba kuzari Abba yace "ina wuni dai ko"

Nana tace "eh ina wuni"

Yace "lafiya ƙalau Alhamdilillah"

Hakimi yai tari, sannan yai gyaran murya yace "Alhamdilillah ala kulli halin, dukkan godiya ta tabatta ga Allah, Abdullahi" ya kira sunan Abba.

"Na'am ranka ya daÉ—e" Abba ya amsa yana risinawa.

"Ka sani ban yanke wannan hukuncin ba, se da na nasan ina da ƙwararan dalilai na, kar ka kalli abunda nayi a  matsayin cin zarafi ko nuna maka baka isa da iyalinka ba, Komai nayi nayi shine da dalili, ko bayan raina ban yadda wani abu ya samu Auren nan ba, Nana amana ce itama 'yarka ce, kuma marainiyar Allah, dan Allah a kula da Amana, sannan ka jawa ɗanka kunne a kanta"

Ya kuma yin tari sannan ya kalli Sadik da ke ta ajiyar zuciya yace "Abubakar, na san na maka ba daidai ba, amma ka sani duk abunda babba ya hango ko yaro ya hau rimi ba ze hango ba, ban ɗau wannan hukuncin dan cuzgunawa rayuwarku ba, sedai ba zan zuba ido wani abu ya ratsa ta cikin iyalina mara daɗi ba, nasan ko bayan raina nan gaba zakayi Alfahari da hukuncin da na yanke, kaga kamar yadda kuke iƙrarin kun tsani juna, kaga se ku kashe kanku in kun ga dama, duk wanda ya ƙoƙarin raba abunda na ƙulla, ban yafe masa ba, Allah ya baka damar Auren mata huɗu, nan gaba in kana buƙata ka iya ƙarawa, amma ban yadda ka wulaƙanta 'yar uwakka ba"

Zare ido Nana tai ta miƙe daga jikin Hakimi tace "Wai Auren wa akayi? Wa kaiwa Auren?"

Inna ta daka mata tsawa tace "rufe mana baki ki, nemi guri ki zauna"

"Inna a ina zan zauna, wai meyafaru ne?"

Duk da jikin Hakimi ba ƙwari, haka ya janyo Nana ya zaunar da ita a kusa da shi, yace "kalli cikin idona"

Ba musu ta kalli idonsa, take taga yai mata wani irin kwarjini, jikinta ya hau tsuma, Hakimi yace "Zaki bi Abubakar turai karatu, kema a can zaki ƙarasa naki karatun"

Cikin rashin fahimta tace "Alhaji meyasa, ni fa bance maka zani ba"

"Saboda na yanke hukunci, na Aurar da ke ga Abubakar Abdullahi Rano, É—an uwanki"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un! Alhaji laifin me nai maka, meyasa zaka ce haka?, in bishi turai banda uwa banda uba se Allah se ku, idan ya cutar dani fa?"

"Baze cutar da ke ba, muma kuma ba zamuyi abunda ze cutar da ku ba"

Fizgewa tai daga jikin Hakimi jikinta na tsuma tai hanyar waje, Inna tace "ku riƙeta karta fita" ai kan ta gama Magana Nana ta kasa da gudu tai waje, Faruk yabi bayanta, tana zuwa babban soro ta faɗi ba tare da sanin in da kanta yake ba.

Tunda garin Allah ya waye, Farhan ke wani irin matsanancin faɗuwar gaba, har idan zuciyarta ta buga seta dafe ƙirjinta, ta koma fizgo numfashi da ƙyar.
A hankali take shirin Makaranta, tana yi tana jin wani irin tsoro da fargaba suna shigarta.
A makare ta isa makaranta, gaba É—aya har aka gama lesson ba ta fahimci komai ba.

Sannu a hankali take tafiya, tana tafiya tana jin Kamar numfashinta ze É—auke har ta isa gida, Umma sarai ta lura da yadda Farhan take komai sanyi sanyi, amma ba ta tambaye ta meya sameta ba.

Farhan Ta ɗauro Alwala, ta zo ta tada salla, ta kai raka'ar farko da kyar, ta miƙe zata kawo ta biyu ta faɗi a gurin.

Kasancewar duk ƙannenta sun tafi Islamiyya, Umma kuma tana cikin ɗakinta, dan haka babu wanda ya san meyafaru.

Ko motsi ba tayi balle numfashi, tana ƙasa kawai a kwance.

Su Amira ƙannenta suka dawo daga Masallaci, suka ci Abinci amma ba su ji motsin Farhan ba, kasancewar sun sa ba me son hayaniya ba ce, ga ta da son bacci dan hala suka ƙaddara bacci kawai take.

Wajen la'asar Huzaifa ya zo gidan, a tsakar gida ya tarar da Umma suka gaisa, yace "Umma Ina Yaya, ta zo taga sabuwar wayar da na siya, ta sa mun Albarka"

Umma tai murmushi tace "tana É—aki"

Hauzaifa ya shiga ƙwala mata kira yana "Waliyya zo kiga sabuwar wayata" amma yaji shiru.

Yai knocking ƙofar ɗakinta yace "in shigo?" Amma shiru.

Ya É—aga labulen É—akin, ya ganta a kwance akan sallaya kamar ba rai a jikinta.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Umman Farhan zo ki ga" yai maganar yana nufar in da Farhan ke kwance.

Da Sauri Umman ta tashi tana faÉ—in lafiya.

Tana zuwa ta tarar da Farhan a kwance, tazo ta taɓa ta taɓata amma babu alamar motsi a tare da ita.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Huzaifa kamar fa ta rasu ne"

"A'a Umma ba ta mutu ba, tana da rai"

Umma ta girgiza kai tace "kalli fa ba in da yake motsi a jikinta"

Huzaifa ya fita da gudu, ya É—ebo ruwa yazo ya shiga shafa mata a gishinta zuwa fuskar ta.

Tai yunƙuri Kamar za tai numfashi, amma ta kasa.

Yace "Umma kin gani, mu kaita Asibiti"

"Ni ina naga abun hawa, kawai ka kira baban ta a waya ka sanar masa"

"Umma idan akace se Abba ya dawo ai abun ze zama worst, bari in fita neman abun hawa, kiyi tai mata fifita.

Ƙannen Farhan suka kewaye ta suna kuka, Amira na mata fifita, Umar na karanta mata Alqur'ani.

Kai tsaye gidan Hajiyar nan Huzaifa ya nufa, saboda yana fita yaga mota a tsaye a ƙofar Gidan.

Sallama ya shiga kwaÉ—awa, ta amsa ta bashi iznin shiga.

Tana ganinsa ta gane shi, ya tarar da ita da babban É—anta, shine ya zo da mota Gidan.

Nan Huzaifa ya gayamata abunda ke faruwa, nan da nan hankalinta ya tashi, ta É—au hijjabi tabi Huzaifa.

Tana zuwa ta tarar da Farhan, a mawuyacin hali.

Hajiya ta hau faÉ—a tace "ni tun ba yau ba na fuskanci yarinyar nan ba ta da lafiya, tayi rama sosai ba ta da kuzari"
Ta kalli Amir tace "maza jeka gida ka kiramin Daddyn Arham kace nace ya taho da motarsa ƙofar Gidan nan.

Nan suka fara ƙoƙarin ɗaga Farhan, amma abu ya gagara saboda Farhan na da jiki, kuma gaba ɗaya jikin nata ya saki.

Hajiya da kanta ta leƙa, tacewa ɗanta ya zo ya temaka musu.

Yana zuwa ya É—aga Farhan, Kamar ya É—au karauni haka yai waje da Ita.

Hakan yai daidai da zuwan Sunusi, dan ganin meke faruwa yaga mutane a ƙofar Gidan su Farhan.

Yaga an fito da Farhan, hijjabin ta ya ɗage sam bata hayyacinta, amma babban abunda ya dame shi ba rashin lafiyar bane, illa ɗakkota da ya ga wani ƙato yayi.

Maimakon Umma tabi su Hajiya, tace ba zata bisu ba, ta bawa Huzaifa kuɗi tace ko za'a buƙaci wani abun, ga kuɗi nan kan babanta ya dawo.

Da sauri Sunusi ya ƙaraso, sedai kafin ya ƙaraso tuni sun ja motar sun tafi cikin hanzari.

Amir ya samu a tsaye yana kuka a ƙofar gida, ya kalleshi yace "Kai meya samu yayarka?"

Amir yace "ba ta da lafiya, suma tayi an tafi Kaita Asibiti"

"To waye wancan da ya É—akkota?"

Amir yace "nima ban sani ba" daga nan ya jiya ya shige cikin gida.

Sunusi yai shiru yace "ko dai shine Sadik ɗin?" Se kuma ya tuna Sadik be kai wannan jiki da tsayi ba, kuma a Muryar Sadik da ya ta ɓa ji, akwai yarinta a muryarsa, amma wannan babba ne sosai.

Umman Farhan kuwa tai zuguum a gida, tana tunanin meya samu Farhan haka.

Suna tafe a mota É—an Hajiya yace "Hajiya wai meya samu yarinyar haka?"

Hajiya tace "Nima ban sani ba wallahi"

Huzaifa yace "ni a iya sanina ban ga tana rashin lafiya ba"

Hajiya tace "Ai ba kusa ba nesa ga Allah, Allah ya bata lafiya"

Kasancewar É—an Hajiya wato Abbas likita ne, wani private Hospital ya kaita, Asibitin na abokin Aikinsa ne amma tare suke gudanar da Asibitin.

Suna zuwa aka bawa Farhan gado, aka fara bata taimakon gaggawa, da alluran da zasu taimaka mata.

Aka bar su Hajiya a reception, kusan mintuna Arba'in, sannan Abbas ya fito.

Hajiya tace "Abbas ya jikin nata?"

"Eh ta samu releif, mun É—ora ta akan drip, na rubuta teses an É—ebi jininta an kai lap, za'a duba".

"To Allah ya bata lafiya, meye bill É—in a biya?"
Chapter 38 · 0% Book details