Sashe 103
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kwanaki bakwai da rasuwar Hakimi, Abba yace za su tafi da Inna can Kano, su cigaba da zama amma Inna fafur tace a'a ita su barta a ɗakinta taiwa Hakimi takaba, ta duba a dangi ta samo wadda zasu dinga zama tare, amma ba zata bar gidanta ba, ba yadda Abba be da ita ba, amma taƙi yadda se haƙura yai ya ƙyaleta.
 Nana kam haka tai kwanakin nan sam ba walwala, abinci dama ba ciwuwa yake a gurinta ba, daga salla se kwanciya, duk ta rame.
Ranar kwana bakwan Abba yace tare da ita zasu koma gida, jikinta babu ƙwarin da za tai jayayya, dan haka ta bi su suka taho, tana ta kuka tana sake jin yadda mutuwar ke sake dukan ta kamar lokacin akayi ta.
Huzaifa ne zaune tare da Malam Zakari, wato mahaifinsa suna hira, Huzaifa yace "Baba ka san wani abu?"
Yace "A'a seka faÉ—a Huzaifa"
"Wannan yaron da Farhan take so fa ya dawo"
"Ya dawo ina?" Cewar malam Zakari.
"Ya dawo, yace aurenta zeyi yana sonta, amma Abba ya koreshi yace karya sake zuwa"
Malam Zakari yace "Subhanallaahi, garin yaya ai ni be gayamin ba, idan da yadda za'ai kawai gara a bashi kar wata matsalar ta kunno kai".
Huzaifa yace "Baba, ka manta da anzo an tambayi Aurenta za'a kawo kuÉ—i"
"To ai Huzaifa, komai masalaha ake dubawa, shi wannan tunda su kai magana, shiru ba su turo ba, zanje in samu baban naku, a wannan karon ba zan so a kuma ganganci da rayuwar yarinyar nan ba, hakan akai a wancan karon aka jefa rayuwarta cikin matsala".
"Husna, duk me rai mamaci ne, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki dena wannan kukan mu cigaba da yi masa Addu'a, Allah ya sa ya dace, ki É—au Abincinki kici kinji"
"Ka ƙyaleni, ni bana son komai bana jin daɗin komai, ka rabu da ni da wani Abinci"
"Dan Allah Nana, kici ko ba yawa Please"
"Ni ba zan ci ba, ka rabu da ni".
"Sadik, Sadik" ya jiyo muryar Abba yana kiransa a falo.
Cikin sauri Sadik ya tashi, ya fito yace "Abba gani".
Abba yace "Yawwa, ina son cika wasiyyar Hakimi da ya bari, ka gayawa iyayen yarinyar nan ranar Asabar in Allah ya kaimu, zamu kai maka kuÉ—in Aure, amma a cikin kuÉ—in ka za'a É—auka a kai"
Sadik yace "Abba, amma me ze hana a bar kai kuÉ—in Hakimi yai Arba'in, kuma ga Nana haryanzu tana cikin alhini"
Abba yace "kaga, bana son wani kame kame kaji ko? Ai ka san da haka kaje gurinsa ka dage akan se an nema maka aure, abunda yafi kyautuwa a cika masa wasiyyar sa, dan haka kaje ka sanar da su" Abba be saurari abunda Sadik zece ba yai waje.
Jiki a sanyaye Sadik ya koma in da ya bar Nana, yadda ta kalleshi ne kawai ya tabbatar masa taji duk yadda su kai da Abba, gaba ɗaya ya rasa murna ze ko takaici, yana matuƙar jin tausayin Nana, ba ta shirya jin komai daga Sadik ba, dan haka ta kwanta ta juya masa baya.
Mother ta cewa Sadik ya ƙyale Nana a nan ɓangaren cikin gida, saboda yanayin da take ciki.
kullum Sadik se ya zo gurin Nana, sedai haka nan take ba walwala, cin abincin ma ba yi take ba, ba dan Sadik ya tsaya ba, da Sahal se ya yaye kansa, saboda sam ba ta damuwa da shi balle ta shayar da shi, ga shi da kukan banza.
 Nana ta rasa meyakamata tayi, ga alhinin rashin Hakimi, ga kuma tsabar kishi da ke damunta, ta rasa in da zata saka kanta ta ji daɗi.
Yau a cikin tsananin sa'a, Sadik ya je gidansu Farhan dan yana zuwa ya tarar da Huzaifa na shirin shiga gidansu Farhan.
Huzaifa ya tsaya cikin sakin fuska suka gaisa da Sadik.
Huzaifa yace "Farhan É—in zan kira maka ne?"
Sadik yai murmushi yace "eh, Allah ya sa tana nan, dan naga gudu na take"
Huzaifa yace "ka barta kawai, ka san taji zafin abunda ya faru a tsakanin ku, haryanzu akwai wannan pain ɗin a tare da ita, gaskiya ta soka so na gaske, ta sha wahala ta azabtu a sanadin barinta da kai, ta afka mummunar hanyar shaye shaye, ga binta da sharri daban daban da wanda da za'a aura mata yai, duk wanda ya zo gurinta ko akai niyyar Aurenta, se ya bi ya hana, yaita ɓata a gurin mutane, haka ya sa ta shiga shaye shaye, da yawon kwana a hotel, ta dinga rashin lafiya ga gida babu daɗi, ta sha wahala dole ta gujeka ɗan uwa".
Sadik kamar ya fashe da kuka yace "Wallahi ba laifi na bane, Wallahi ka ji na rantse maka, yadda ka san anyi formatting memory na, haka na manta da komai, ba Farhan ba hatta makarantar da nai da abokaina da duk wata rayuwata makamanciyar wannan haka na manta da ita, ban yi dan in zalunci Farhan ba, Aure kuma da nai, na gaya mata kakana ne ya Auramin ita muka tafi karatu tare, ƙanwata ce, amma dan Allah ka tayani bata haƙuri Wallahi ina sonta da gaske, ni ba ruwana da wace rayuwa tayi, komenene nasan nine sila, amma dan Allah ta yafemin, ka ga ni yanzu haka, nai magana da babana, za'a zo tambayar min Aurenta, ina da halin da zan riƙesu gaba ɗaya".
Huzaifa ya É—anyi shiru sannan yace "to ai anyi Magana da wani, ze kawo nasa kuÉ—in"
Sadik yace "ina jin tsoron ta auri wanda ze wulaƙanta ta a gaba, saboda tambarin da taiwa kanta, ni ɗin dai tunda nine silar komai ban isa in mata gori ko wulaƙanci ba, saboda nine sila, yanzu idan ka ban Alqur'ani zan dafa in rantse maka Farhan duk yawon Hotel ɗin da take ba ta bin maza, saboda Soyayar kanta nine na koya mata, nasan halinta kamar yunwar cikina, shikuwa wancan ba si da wannan tabbacin, kai nifa ko mazan take bi, naji na gani ina so zan aureta in zauna da ita ina sonta, ita na fara so, dan Allah ka tayani rarrashinta, da kuma bawa Abba haƙuri akan ya amince dan Allah"
Gaba É—aya tausayin Sadik da na Farhan ya kama shi, yai ajiyar zuciya yace "bakomai, Allah ya wuce mana gaba, bari inje in mata magana"
Sadik yace "to shikenan nagode sosai"
Sadik be wani sa ran fitowar Farhan ba, kuma sam ba ya jin fargabar Abba ya sake ganinsa, ko da kuwa ze kuma yi masa faÉ—a idan ya ganshi.
Yana nan tsaye yana tunani, ya ɗaga kai ya hango Farhan, cikin dogon hijjabi, a hankali ta ƙaraso in da yake tsaye ta kalleshi, ya ƙara rama se tsawo, yana cikin farar jallabiya, sedai ya ƙara kwarjini sosai, a ɗan tsiwace tace "Sannu ko"
ÆŠan tsura mata ido yai sannan yace "Yawwa ya kike?"
"Lafiya ƙalau, ashe Allah yaiwa kakanku rasuwa"
Sadik yace "Wallahi kuwa, Hakimi sa'i yayi, ashe kin samu labari?"
Tace "eh na gani a social media, ina Addu'a Allah yai masa rahama, yasa aljanna ce makomarsa, ku kuma Allah ya baku haƙurin jure rashin sa"
Sadik yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nagode sosai da sosai Princess" juyawa tai za ta koma yace "A'a Farhan ya haka, ina zaki kuma?"
"Au har ka manta kashedin da Abba yai maka ne? In ka manta ni ba manta ba"
"Nasan da kashedin Abba, kuma ba dan in fatali da kashedin na sa na zo ba, Abba ne za su zo nema min Aurenki ranar Asabar insha Allah".
"Wai kai Sadik ba ka ganewa ne? Sau nawa zan gaya maka wani ya riga ka, Aure zanyi dan Allah ka ƙyalemin rayuwata ta huta"
"Ke zaki bada damar rayuwata da taki su huta"
"Aikuwa sedai kar su huta, dan ranar Asbar Abbas ze kawon kuÉ—in Aure, kuma sati biyu za'a saka"
"Hakan ba damuwa ta bace, kaina na sani" daga haka ya juya ya barta a tsaye tana jinjinawa ƙarfin halin Sadik.
Ganin damuwar ta Nana tayi yawa, ya sa Abba ya nema mata makaranta, a satin ya sa direba ya fara kaita, ya É—akkota Sahal kuma yana gida, sedai babu wanda za'a cewa Nana matar Aurece ya yadda.
Abba yai mata nasiha sosai akan ta saki ranta ta maida hankalinta tai karatu, sannan ta kula sosai tunda ta san cewar ita matar Aurece.
Nana ta koma ɓangaren su na BQ, sedai tsakaninta da Sadik sedai ido, gaba ɗaya ta dena walwala ta zama kamar wata me jinya, daga salla se kwanciya, se taji yunwa zata kassarata Sannan ta nemi Abinci ta ci.
Umman Farhan na ta murna Farhan ta dena yawo, gashi za'a kawo kuÉ—in Aurenta, se murna take yi, akan za ta samu ta aurar da ita, ta huta da wannan zullumi da tashin hankali, se Addu'a take Allah ya tabattar da lamarin nan.
Farhan kuwa na É—akinta, tana kwance tana karatun Alkur'ani a hankali, tana tunanin yadda ta bar makaranta ta ada karatunta na Addini, gaba É—aya taji wata Nadama na zuwar mata.
"Farhan! Farhan kina ina?" Ta jiyo muryar Abba a tsakar gida.
Da sauri ta tashi ta fita, tana tunanin kiran Me Abba yake mata haka?.